Abu-turaab Book 1 Complete Hausa Novel By Asmau B Aliyu.txt

Author :  Asmau B Aliyu Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   2 / 9

3K to 6K   out of 25.7K words

da nake ganin girmanta da na ajey wannan aikin."dan baayi maccen da zata zauna tana wulakantani ba.
Arziki haukane!"ya qarasa maganar a tsawace,
da yasa nainah ta tsorata haka ta tsura masa ido.
Zaki iya daina ka'llona dan ni ba Tv.bane ,sosae nainah taji kunya amma da yake kafiya gareta nan take ta sha to'ka wai kai waye boss tsakanin ni dakai?"haan? Kanme zaka tsaya akaina kana yimin fada tamkar wani ubana!"have your way out?"
Ta fada masa cikin daka tsawa tana nuna masa qo'fa ranta abace ,
Ko a kwalan rigan Abutturab ya nufi ko'fa farin cikinsa day'a ya bata mata rai hakan dama yakeso.
Zubewa tayi akan soofa tana maida numfashi fuskarsa take qa'llo yana mata tsawa da matsifa ,mai makon taji haushinsa bataji hakan ba .Amma ranta a bace yake wani gefen kuma batason Abutturab ya daina aiki akarkashinta,
Tafiso ya cigaba da zama akarkashinta yarda zata samu damar wulakanta shi.
*
Washe gari.karfe takwas nainah tayi shirin zuwa office sauri takeyi suna da meeting ,
Tana cikin shigar traditional kaya atamfar super sharaton che ajikinta dinki Riga da skirt Wanda yakamata sosae ya Riga yagama bayyana siffar Jikinta ,sae dan qaramin veil kalar dark blue ,
Da ta aza akan kafarta .
Sae talkamin qafarta shima blue amma hill ne,
Fuskarta tasha make up har tagaji sai zuba qamshi takeyi tayi kyau na fitar hnkali ,dan irinsu nainah baka yimasu kallo day'a ka dauke kai.
A babban falo suka hadu da nana.
Tana ka'llon agogon hnnunta take tambayr Nana Mami fa?"tana barci bata tashiba.
daukomin lunch box dina zuwa mota achan zanyi break fast."
Abutturab na awaje yana Jiranki yazo baki tashi ba!"Shaye da to'ka nainah ke fa'din karfe nawa yazo?"
7:00@m.
da haka ta fice daga falon,,
A harabar gidan ta hango Abutturab yana hira da Isah mai baiwa Flowers Ruwa.
Yana ganinta ya taho da sauri ,yamika mata car key na Benz dinta da ya wanke.
Ka baiwa wanchan yazo mutafi.
Ta fada cikin basa umurmi,
Shigar English wear's ne Ajikin Abutturab farar shirt.da bakin wando na Jean's,
Sumar kansa ta kwanta luf tamkar ta larabawa.
Ba karamin kyau yyi ba.
Kafin ta nufi motar Abutturab ya rigata ,gaisheta yyi fuska a ha'de ta Amsa batareda ta kallesa ba.
Back side ya bu'demata ta zauna ,
Ya amshi lunch box a hnnun nana ya saka agaban motar.
A mota zaman shuru suka zauna,
da Isar su .suna gama parking ,
Aka fara gaisheda nainah cike da isa take da'ga hnnu wasu ma a haife sun haifeta Ran Abutturab ya qara baci.
daukar lunch box yyi yabita dashi a katafaren office nata.
Office ne mai girman gaske ,mai ha'de da master bedroom.fridge California bed ,TV.soofas bbu abunda bbu aciki.
Zama tayi akan soofa ,
Yyinda shi kuma Abutturab yyi tsaye tamkar gunki."
Leg's dinta ta nuna masa,
Ciremin shoe's din kafana ,
Ta fada tana basa umurni,
Bbu musu ya durkusa agabanta ya shiga cire talkamin kafarta,
Ajey su yyi agefe sai yaga ta Ciro tissue tana goge dai dai wurin da ya taba akafanta,
dauke Kansa yyi ransa na tafasa.
Ha'damin tea ka zuba min chip's akae ,
Ta fada bata kallesa ba tana danna wya .
Hada mata yyi yaja dan qaramin center table dake tsakiyyar office din ya tura agabanta,
Yana tsaye ta fara break fast bata ko kalli inda yakeba,
Still tana danna wayarta,
"Shaye da to'ka ta dago fuskanta tana kallonsa ,I will appreciate it in xaka daina qa'llona hakan kanemi wuri ka zauna.
Ta fada ta maida hnkalinta kan wyarta..........
💝ABUTTURAB💝
~Written by Asmy b Aliyu~
Haske Writer's Association.

6..

ciro wayarsa yyi techno W4 shima ya shiga dannawa cikin qwarewa ta wutsinyar ido nainah ke qallonsa komae nasa so gentle and classy.
Jin yyi ajikinsa tamkar ana qa'llonsa sauri dago kansa yyi suka hada ido ware ido tayi tana ka'llon blue eye's dinsa.
dafe kirji tayi tana qaranto duk addu'ar da tazo mata haka kirjinta na wata irin dokawa.
da yaga ka'llon yyi yawa ,
Ya da'ga mata hnnu ,da husky voice dinsa yake fa'din."hello !
Are yhu OK?"
A kunyache tayi nodding kai tareda dauke kanta.
30minute latter tabashi wasu file's tache ya duba mata.
But sai da tafara tambayarsa yyi karatu ?"
Kai tsaye yabata amsa da Ehhh."
Meye matakin karatunsa?
digree! "
Zata tambayesa course dinda ya karanta sai taga Rashin dachewar hakan,
Haka taga ya hade rai haka yasa tasha Jinin jikinta.
Ta nuna masa yana cikawa ,
Sun kusan Awa biyu suna famar cika files tana taimaka masa.
4:00pm.na yamma lokacin tashi office yyi nan P.A ta ya shigo mai suna fawaz cikin girmama yake hada stuff's din office din.
hand bag nata ta dauka ta nufi hnyar fita ,
Abutturab yabi bayanta.
A hnakali take tafia Dan har ya rigata kai mota .
Hangosa tayi yana cilla car key yana cafkewa cike da Sha'awa wasu ma aikatan wurin mata suna tsaye agefe suna kallonsa cike da burgewa haka kurum nainah taji duk bbu ddi ,
Suna ganin nainah ta tunkaro wurin rai a hade kowache tasha Jinin jikinta tare da dauke kanta dan da alamr ,
Boy friend din tane acewarsu ganin yarda ya ha'du.
bude mata back side yyi ta shige ba tareda tayi mgana ba.
Ya Rufe ya shige driver side yyiwa motar key gamida barin wurin .
Har sun dau hnyar da kyar ta iya fa'din ka kaini wani eatery mai tsada achan zanyi lunch,
Ta fada sounding so command!"
Wani hadadden restaurant ya nufa daita Wanda sai wane da wane ke zuwansa.
Tana fitowa ta manna bakin glashin frada a idonta,
dan akwae yaya'n manyya a wurin sai binta sukeyi da qa'llo Wanda itakuma nainah ta raina Ajinsu,
Wuri na mussaman ta nufa ta zauna ,
daya daga cikin waiter's din dake aiki awurin namiji ya nufo wurin da take da sauri ta kalli Abutturab,
Banason Waiter namiji nafison macce ta fada shaye da toka ,
Haka yasa Abutturab yyi saurin dakatar dashi yache ya turo macce cikin minti biyu sai ga wata inyamura wacce bazata wuche shekaru goma sha biyar ba.ganin Abutturab yasa ta ware idanunta tana qa'llonsa ,
Cikin harshen Turanci take gaishesa .shima murmushi yyi mata yana tambayarta dama anan take aiki ?"tabasa amsa da ehh."haka tana tambayarsa nooriyya fah?"
"Tana gida yabata amsa fuska a sake ,cikin buga mata tsawa nainah ke fa'din zaki fara aikin ki ko se kin gama surutun naki na banza.
" Am sorry maah."
"Esther tayi mganar cikin muryar tausayi ,
Irritating look nainah tayi mata ,cikin daka mata tsawa take fa'din barnan !" Ta fada tana nuna mata hnyar da tafito Jiki na Rawa Tabar wurin Ran abutturab ya baci,
Suna hada ido ta gallara masa harara Afusace ta nufi hnyar barin Eatery din.
"Ya kamata ki daina wulakanta dan Adam bbu kyau hakan,haka bakisan kalar mijin da zaki aura ba.
" Abutturab ya qarasa maganar cikin taushin murya shi wanene da zai Riqa saka mata ido akan komae tayi ba dai-dai bane.?"
" I don't have faith in love to talk more in marriage,I wish to finish my life in single basai nayi aure ba .karma namijin da yaga damata ya takani yarda yakeso,dama ana Aurene dan a hada family to ni inada family na I have my daddy with Mami su kadai sun isheni Rayuwa.
Kwabe baki turab yyi batareda yyi mgana ba ,
Yamaida kansa kan tuki a haka suka isa gida bbu mai magana yana gama parking ya miqo mata key ,Amsa tayi batareda ta kallesa ba ta nufi hnyar Reception din gidan su.
Masu aiki sai sannu da dawowa suke zubamata amma ko takansu bata bi ba.
*
Abutturab bamalli place..."Aunty kinsan Noor da kafiya batason Allura bansan ya zaayi da Rigimarta ba?"
Aliyu yyi maganar sounding so sad.
Yana fusakantar wata kyakkayar macce mai kama da Abutturab sak !"
Wanda sai dai ta gwada masa shekaru amma kamarsu daya ,
Mai kimanin shekara 32 a dunia,
Hankali Hajia Asma'u na kan laptop take fadin ae sai kuyi kuma ,
dakai har ita taurin Kaine gareku me doctor Hafiz ya fada maku a kwanakkin baya.?"
Shaye da toka turab ke fa'din pls Aunty ki daina wannan mganar dr.dinan bayada hankali kwata 2 shekarun Noor nawa?"she Just a 14 year's ,
Kinsan bata isa daukar hidimata ba?"
Aliyu tashi ka fice min A daki plss.......Aunty Asma'u ta qarasa mganar cike da bacin rai bbu shiri ,Abutturab ya miqe ya fice Ransa a bace ,
dakin Noor ya nufa tsakiyyar gado ya sameta a zaune ta hade kai da gwiwa da Alamar kuka takeyi.
"Murya a sarqe yake fa'din my chaculaty !"
Jin muryarsa da sauri ta dago idonta da sukayi tsabar Ja sabida kuka."
"Yaya na!"...........ta fada tana fashewa da kuka bbu shiri ya tunkarota fadawa tayi Jikinsa ta fashe da kuka lokaci daya haka tana cusa fuskarta cikin qirjinsa,
hnkali Abutturab duk yabi ya tashi murya a sarqe yake fa'din ciwon maran ne?" Nodding kai kurum ta iyayi ,
Kin ci Abinci ?"dakyar tabasa amsa da tasha tea.
"When?
da safe ,Oya tashi kici Abinci sai muje clinic kuka ta fashe dashi banason clinic ni bana son Allura !" Ta fada tana qara volume kukanta ,OK naji bazaayi maki Allura ba mgani kurum zamu amso.
Shuru tayi batareda ta qara mgana ba.
Kusan 8:30pm.na dare yana kwance a Falon sa Noor na kan Jikinsa tana barci ,Yaji wyarsa ta fara Ring kamar ya share dan yaga bakuwar lamba .sai kuma ya daga batareda yyi mgana ba,
Sanyayyar muryarta ta daki dodon kunnensa."
"Pls wake mgana?" Dan harga Allah bai gane mai magana ba.
"Nainah........!"
Jin yyi lokaci daya zuciyarsa na dokawa ,kada suturunsa ya tada Noor yyi saurin katse wyar ,
A hnakali ya daga noor chak!"
Tamkar wata baby dool ya nufi bedroom dinsa daita.
Kwantar daita yyi gamida Jamata duvet.
Komawa yyi A falon ya dauki wyar ya kara kiranta sai dai har ta katse baa dagaba.
Har zai Ajey wyar sai gashi ta qara kira ,kana ina?"ta tambayesa cike daisa."baki iya sallama bane?"bata amsa saba taci gaba da magana ina son kazo yanzu zan fita club!"
Yanayin muryarta yaji kamar ranta abace yake ,
Tabe baki yyi gamida fa'din ."bana da lokacin yanzu gaskiyya kinsan ina da iyali matata che bbu lfy!"
"dif!"
Yaji an kashe wyar bin wyar yyi da kallo lokaci daya cike da mamaki."
*
"Nainah !"....
Batasan meyasa taji xafin kalaman sa akan yana da mata ba?"
dolema ne tasha 2bottle na syrup haka tana sha'awar shan giya a yau ta kwana biyu bata sha ba, canja kayan Jikinta tayi zuwa wata farar Rigar body hook ta Rooba Wanda ta tsiya iya gwiwarta .sai black veil da tayi rolling kanta dashi black cover shoe's ta tasaka ,
Ta dauki car key ta nufi motar ta........
💝ABUTTURAB💝
~Writeen by Asmy b Aliyu~
Haske Writer's Association.

7..

kusan karfe goma da Rabi na dare yana baiwa Noor tea Sai shagawaba take zuba masa shikuma Sai tarairayarta yakeyi wayarsa dake Ajey agefe tafara Ring.nainah!"................lokaci daya Noor ta kurawa screen din wyar ido nan take kuma ta hade Rai ,
Tayi saurin dakatar da Abutturab dake kokarin kai spoon abakinta .shima hade rai yyi yana kallonta ,meya faru kuma?"
Nainah!"
Ta basa Amsa simple in short! "Sae akayi yaya ?" Turo baki tayi gatanan tana kiran ka awaya ni gaskiyya ka cire lambarta a wyarka ,
Ta karasa mganar cike da yarinta gamida turo baki.
Har lokacin kuma baa daina nacin kiran ba,Afusace ya da'ga wayar maimakon yaji muryarta tamkar yarda ya zata, sae yaji sabanin haka.
"Wat !".... Ya fada da qarfi yana miqewa tsaye okey okey!ganinan zuwa ,
Kallon noor yyi gaba daya baya cikin natsuwarsa.
" my chaculaty!"
Harde hannayenta tayi akan kirjinta haka tasha toka sosae batareda ta Amsa ba,
Bbu shiri Abutturab ya russuna agabanta gamida kamo hannayenta,
Ni nake maki mgana kike shareni ko?"haka aka koya maki a islamiyyar Ku?hawaye yaga sun fara Rolling akan fuskarta ,
Kuka kuma?"mezakaje kayi a wurinta?"ta fada cikin kuka "bana son katafi wurinta I don't like her!"
I so much hate her!"
Sakin baki hambal yyi yana kallonta lokaci daya ya hade rai ,waye ya fada maki wurinta zani?"
Mum dinsu mamdud che bbu lfy shine xamu kaita hospital, yana maganar zuciyarsa na dokawa.
Qaro na farko da yafara yimata karya.
Oya share hawayen idanunki ,mutafi na rakaki wurin Aunty kafin na dawo.
"Zan bika!".....
Hade rai yyi tareda fa'din." Dare yyi haka kurum kitafi maza na kallonki keda bakida lfy!"
Kara fashewa tayi da kuka !
Nidai ban yarda ba!"Noor ni abokin wasan kine ?"zaki tsaya musu dani?yyi mganar cikin tsawa."da alamr ransa ya fara baci.
bata kulasa ba tafita dakin da gudu tsoki yaja ,ya cire jallabiyar jikinsa ya saka kananan kaya.
Part din Aunty ya nufa knocking yyi ,aka basa izinin shigowa.
"Kallonsa kurum Aunty keyi ,
Tana shan daman man fura acikin wani dan qaramin bowl .
Sai ina ?" Ina kuma Noor?"Aunty tajefo masa tambayar lokaci daya,
daurewa yyi yace tana daki tasamu barci fita zanyi .
Aunty bata kara mgana ba tamasa Allah ya kiyaye da haka ya Juya yyi ficewarsa ko dakin Noor bai kallaba ,da alamr ta bata masa rai.
*
Nainah!..."
Zaune take kan motar ta kwalbar beer CE a hannunta, yyin da driven ta ke dan nesa daita yana kallonta hango Abutturab da yyi yasa yaji hnkalinsa ya kwanta,
Kafin ya karaso ya qarasa garesa kallo daya zakayiwa madu driver kasan a tsorace yake ,
Yallabai !"dama da.....kasa karasawa yyi da hannu ya shiga nuna masa nainah ,Karasawa yyi gaf daita gabansa yaji ya fadi lokaci daya dama wannan yarinyar yar shaye -shaye CE?"
Bin wurin ya shigayi da kallo tabbas nan gidan giya ne!"Afusace ya Juya kan madu yana binsa da wani matsiyacin kallo ,meyasa ka kawota a irin wannan wurin?"
Wlhi idan ban kawota ba zata iya korata ,tsoki Abutturab ya buga afausace yashiga fa'din ."ko kasan duk zunubin da ta aikata Dana ka kamisho aciki?"ya zanyi yallabai ,Aunty nainah batada mutunci."Abutturab bai kara sauraren driver ba ya nufeta Afusace ,ya fisge kwalbar veer din ya watseta a kasa.
Lokaci daya ta ka'llesa tana langabar da kanta Sai kawai ta fashe da kuka cike da shagwaba take fa'din meyasa ka fasamin?"kallonta kurum yakeyi Sai yaga ta qara kyau!"
Ki rufemin baki!"
Yyi mganar cikin daka mata tsawa!"
Hannunta duka biyu tasa ta toshe kunnuwanta ,
A hnkali ta sauko daga kan motar .
Baya tayi zata fadi yyi saurin tarota ajikinsa ,umurni yyiwa madu driver akan ya bude masa back side ,cikin bin umurni ya bude masa .ya sakata ya shige front side madu driver yaja motar sukabar wurin .ga mamakin Abutturab Sai yaga yabi titin maska Road !"ina zaka kaimu ?"ae yallabai idan Hajia tana cikin wannan yanayin agidanta take kwana dake maska Road!"shuru Abutturab yyi bai kara cewa komae ba amma kallo daya xakayi masa kasan Ransa abace yake......
💝ABUTTURAB💝
~writeen by Asmy b Aliyu~
Haske Writer's Association.

8..

kallon fuskarta kurum yakeyi ga macce har macce but sai kyawon Dan maciji .
"I hate you so much Mrs.nainah canJi from d bottom of my heart!" Abutturab ya qarasa maganar afusace gamida tura center table din dake tsakiyar falon.
Afusace ya Juya yabar falon ,nainah duk da bata cikin hayacinta tana ganin fitarsa .
qoqarin miqewa zaune takeyi ta kasa dafe kanta tayi da duka hannayenta biyu ,Ahnkali ta shiga lumshe idonta .cikin mintunan da basuyi biyar ba tasamu barci.
Dakyar ya samu Abun hawan da zai maidasa gida ,
dare ya farayi sosae shabiyu saura minti goma.
Koda ya koma gida basu da nepa, har ya nufi dakinsa sai kuma ya tsaya chak!
Sae lokacin ya tuno da halin da yabar Noor aciki,
Hnyar dakinta ya nufa da sauri fitilar wyarsa yyi amfani daita yana haske dakin ,
Hangota yyi kwance akan bed ta dunkule kanta wuri daya.
Haka yana jin kukan sauro a dakin tunda batashiga net ba dole sauro ya dameta ,A hnkali ya dagata atsorace ta bude ido tana shirin saka masa ihu yyi saurin rufe bakinta .
Cikin muryar Rada yake fadin nine fa!"
Jin muryarsa yasa tayi lamo Ajikinsa,
Tana sauqe ajiyar zuciya.
da haka ya nufi dakinsa daita.
adaren bai samu wani barci ba ,sae tunanin hali irin na nainah yake.
Wai tasamu gata bazaayi mata fada akan Abunda takeyi ba,gudun kar a bata Ranta.
*
Kusan qarfe goma sha daya na safe tashigo falon nasu.mamin dinta che hakimce acikin custions din dake zagaye da falon.Nana CE agefenta tana hada mata tea.
qallo Hajia zulfa tabita dashi lokaci daya kuma taji gabanta ya fadi !"badai nainah ta sake dawo ma shaye -shaye ba?"
Zama nainah tayi gefen mahaifiyar ta ,murmushi dauke afuskarta take fadin."good morning Mami!"Hajia zulfa ta hade rai lokaci daya batareda ta amsa ta ba take fadin!"badai kin dawoma halinki na shaye-shaye ba nainah?"
Kin manta irin bakar wahalar da kika sha a baya?"har sai da akayi maki dashin Hanji!"Hajia zulfa ta qarasa mganar cikin daga murya da zafin Rai!"
."Mami plss!
"Nainah." ta fada cikin qunar Rai,
Ki daina daga min murya Dan Allah!
Ae Kadan nasha Raina ne naji ya baci shiyasa kawae nasha."sai kace wadda tayi mummunan Abu zaki riqa daga min murya agaban Ya'r aiki!"this is d last tym da zakiyi min Haka mami ,Iam not taking it any more...........this is my life am not your!"Afusace nainah tabar wurin da gudu ta haye up stair's da ido Hajia zulfa tabita tana goge kwallar dake son zubo mata.
Ba laifinki bane nainah laifin duka yana ga Alhaji!"
*
Alh.Ibrahim chanji shine asalin sunan mahaifin nainah Dan Asalin Jihar danbatta ne karamar hukumar Kano.
Su ukku kacal mahaifinsu ya Haifa .yana da shekara goma sha takwas mahaifinsa ya Rasu sakamakon hadarin mota.
Mahaifinsa cikakken Dan kasuwane,
Wanda yake da babban shago acikin kasuwar Kano,mahaifinsa Attajirin gaske ne ,kannensa biyu duka mata Hafiza da saratu .hafiza a Kaduna take aure yyinda saratu ke Aure acikin garin danbatta.
Ibrahim Awaje yyi karatunsa ,
kasancewar mahaifinsa yabar masu dukia mai yawa.
Yana kammala degree dinsa a fannin Economic computer nan mahaifiyarsa tayi masa sha'awar yar uwarsa Rabi'a .akan ya aureta
Anan yabuga hnnu ga kasa yache baisan zancen ba ,shi bayasonta.
Hnkalin mahaifiyarsa ya tashi sosae Dan lokacin Ibrahim yana da shekara 34 adunia.
Anan kannensa mata suqa riqa tausarsa.nan yache zai samo wata amma bayason Rabi.
Wata daya da mganar ya Auri Zulfa'u wadda asalinta shuwa Arab ne kasuwanci ya kawo Baban ta kano ,
Biki akayi nagani na fada acikin kawayen danbatta .
Haka Ibrahim ya Gina gida acikin garin Kano ,
Haka yyiwa mahaifiyarsa part nata katon gaske gidane na gani na fada haka na zamani.
Anan mahaifiyarsa tabuga kai ga kasa tache ita Sam bazata koma tabar dangintaba.
Bbu lallashin da Ibrahim baiyi mataba amma taki .
Haka yan uwansa suka basa hkuri ,haka ya hkura yatare da amaryarsa macce mai kirki da Alkunya asalinsu shuwa Arab ne.
Wata biyu da Aurensu mahaifiyarsa ta kwanta jinya satinta biyu Allah ya Amshi Ranta,
Mutuwar ta ta girgizasu bakadan ba.har akayi kwana arbain Ibrahim baidawo cikin natsuwarsa ba.sai da taimakon matarsa zulfa ya fara walwalah.
Bayan wasu shekaru ,zulfa ta haiho ya'rta kyakkyawa sak

2 / 9