Author : Asmau B Aliyu Category : Romantic Hausa Novels
Raunin murya take fadin."Wannan ba Abutturab dina bane Aliyu na ba zai Yi Abu batareda na sani ba?"meyasa kayi haka Aliyu?"idon sa rau rau yyi yazo ya Dora kansa akan cinyar Auntynsa ya dunkule wuri daya tamkar karamin yaro yake fa'din."kiyafemin Aunty bada niyyyar Auren nooriyya naje gun sarki ba............!"nan ya zayyane mata abun da yafaru ,Asma'u ta girgiza haka ta tausayawa Rayuwar Noor ,
Shafa lallausar suman kansa ta shigayi mai zubin Fulanin asali take fadin."Anya yarona Abutturab ya isa aure a irin wannan yananyin?"dago kansa yyi yana kallonta murmushi dauke afuskarsa ya miqe zaune yana fuskantarta,
Ya daqune fuska yana qallonta gamida langabar da kansa ,nima ban sani ba Aunty!"Amma ni Auren Noor bai dagamin hnkali !sabida turab yanason Noor tun ashekarun baya Aliyu yake cikin tsananin soyayyar kanwarsa nooriyya!"Asma'u zatayi mgana sukaji an turo kofar da karfi !"baffansu ne ya shigo a wulakanche yake kallonsu kafin ya maida hnkalinsa kan Aliyu"cikin kunfar baki yake fadin wato kai ka Girma?"har kai zaa daurawa aure agarin nan batareda sani naba?"yyi kyau ba laifinka bane!"amma daga yau din nan haka daga yanzun nan zaka kwashe komae naka kabarmin gidana!"ke kuma!"ya fada yana nuna Asma'u wadda ta zuba masa ido nabaki nan da sati 1 dal !"kifitar da miji kiyi aure idan bahaaka ba kema zakibi sahunsa!"Afusace yajuya yabar dakin yana banbamin fada Ran Abutturab idan yyi dubu to yabaci ganin yarda Auntynsa ke zubar da hawaye.cikin bacin rai yabar dakin ,
Cikin sati daya ya saida duka kaddarorinsu,
Batareda sanin Auntynsa.
Ranar Assabar da karfe shidda ya nufi gidan sarki akayi masa iso a turakarsa ,
Bayan sun gaisa yake fadin zasubar garin giwa.
"Shida Auntynsa a Kano zasu koma achan ya samu aiki awani company!" Yyiwa sarki karya!nan sarki yamasa murna ,gamida samashi Albarka anan ya aika akan Noor ta shirya mijinta zai tafita daita.
Murna awurin Noor tamkar meye?"kusan kwana biyar bata ga yayanta ba ,gashi mama ladi nabata kulawa uwargidar sarki!
Tana kula daita har wani fresh tayi.
Karfe bakwae Abutturab sukabar fadar sarki sukayi masa sallama Wanda sarki yabaiwa Abutturab sadakin Noor dakuma kyautar dubu goma.godia sosae hambal yyi masa,hannunsa cikin na Noor suka nufi gidan baffan sa."A hnya Noor sai surutu take zuba masa duk inda suka wuche sai an kallesu ana nunasu !"
cikin daka mata tsawa yake fadin kiyi shuru haka Noor!"...Idonta yyi rau rau kamar zatayi kuka bbu abunda Noor tafi tsana irin ayimata tsawa!"amma yau yayan ta datake so shiyake yimata tsawa kamar yarda iya Jummai keyi mata.har suka kawo gidan baffa bata qara magana ba,tana dai ganin Aunty ta saki hannun Abutturab ta Ruga da gudu ta shige Jikinta.wannan shine dalilin dawowarsu hambal acikin birnin Kano da zama ,cikin Rufin Asiri Asma'u ta hada diploma dinta haka qaramin gida ne sukaya siya acikin unguwar Jan bolo.da Rufin Asirin ne suka saka Noor a makarantar secondary wato government girl's day.har kuma lokacin Asma'u bata qarayin aure ba,
Haka Alh.sule Wanda a unguwarsu yake matansa ukku yana balain son Asma'u amma fir taki haka shiya Samar mata aikin karantar wa a wata private skull Wanda duk karshen wata Albashinta dubu talatin ne!"Asma'u tana girmama Alh.sule amma tana hango gobarar dake ci acikin gidansa.
Kawar Noor dayache Wanda a unguwarsu take duka sa'anin junane haka uwayenta masu kudine sosae!"duk da hambal baya barin Noor na fita ko makwafta haka bai hana kullum bikra zuwa gidansu Noor.
2days latter!
"Abutturab na zaune agida yadaina zuwa aiki ,da Auntynsa tafita tareda Noor zuwa skull shikenan da yake yanzu a skull dinda Asma'u ke koyarwa achan Noor take Wanda duk bayan wata ukku dubu biyar ake biya.
Kwance yake afalo ,Yana game da wayrsa kiran nainah ya shigo a wayarsa.
Agogo ya kalla kusan karfe sha daya na safe.
Sai gafda zata tsinke ya daga ,
Sallama yyi baa amsa ba!
" cikin cool voice nata take fadin ."kasameni office da kwalin karatunka ."tana maganar sounding so very command! "Zaiyi magana ta katsesa da cool voice nata take fadin." Aliyu pls!"da sauri ya cire wayar daga kunnensa ,yana son yakara tabbarwa kansa shin da nainah chanji yake magana?"Ashe tasan sunan?"Ashe zata iyayiwa mutum mgana cikin sanyi murya haka?"mezatayi da kwalin karatunsa?tambayoyin da Aliyu bamalli ya shiga jerawa kansa kenan!."
💝ABUTTURAB💝
~Written By Asmy b Aliyu~
Haske Writer's Association.
12..
Kai da kawo ta shigayi cikin qata faren office nata .gaba daya ta kasa sukuni da zama burinta tasaka turab a idonta!"batasan meke damunta ba ,kwana biyu duk tabi ta damu kanta da Rashin ganinsa.
Haka idan ta tuno Abutturab yaronta ne da matsayinsa agareta sai ta ha'de rai.yanzu ma hakan ta faru Dan tsiririn tsoki ta buga gamida Dan beating head nata tayi gamida fadin ."Be a good gal nainah chanji!"tayi mganar sounding so cwt tamkar wata qaramar yarinyar ,murmushi dauke a fuskarta!"shigar English wear's ne ajikinta as usual.long skirt ne Red ,sai bakar T.shirt ajikinta mai dogon hannu .sai Dan qaramin veil da tayi Rolling kanta dashi Red ,
Fuskarta tasha make up da Jan janbaki tayi kyau.
Window's din cikin office din nata ta bu'de tareda yaye labulen window din hannu ta harde akan kirjinta tana qa'llon masu shiga da fita acikin company din.
Kamar anche ta da'ga idonta ,ta hango Abuttyrab na tahowa sanye yake cikin polo shirt white mai guntun hannu haka ta kamasa sosae ,
Sai blue Jena's ajikinsa .
Haka yyi style din suma kansa kamar kullum!"
Yyi kyau sosae!batasan lokacin da tafara doka murmushi ba!"
Taku yakeyi megastically cike da kaisaita .
Koina ya wuche sai kallonsa akeyi.
Ta private elevator ya nufa Wanda yasan nanne wurin binsa shida nainah!"
Jin yyi anche excuse me sir!
Jin muryar wata yarinya abayansa yyi saurin Juyowa budurwar che wadda bazata wuce shekara Ashirin da biyu ba a dunia.
Tana da kyawunta dai-dai gwargwado.
Ina zaka ne?
"Office din nainah chanji!" Yyi mganar sounding so very serious! "
Dan murmushi tayi gamida harde hannunta akan kirjinta ,
Ina daya daga cikin receptionist din wannan company .
"Your name pls...........?"
"Aliyu Yusuf bamalli!
Ya fada mata " sounding so boring ,
Kana da appointment daita ne?"
Tasan da zuwanka ne?"is she expected you?"
Turab zaiyi magana Sukaji muryar fawaz akansa,
Wanda ke sanye cikin bakaken suit .
Hannu yabaiwa Abutturab suka gaisa ,wata hanya suka bi da mamaki Hambal ke fadin ,office din nainah zanje fah?"
Murmushi Fawaz yyi gamida dafa shoulder din Abutturab ,
Yeaah wancan da kasaba bi kai daita private elevator's dinta ne wannan kuma shine public kowa da kowa.you are so Lucky ka samu ka shiga wancan da alamr nainah naji dakai.kayi sa'a bata sakarwa kowa fuska amma yau abun mamki yau koda ta shigo office fuskarta look so bright.da haka suka karasa office dinta ,saida sukayi knocking aka basu izinin shigowa.
Zaune take kan kujerar offishin nata tana Juyawa daita ,
"Kallon Fawaz tayi tana fadin ." you can go fawaz!"tayi maganar sounding so cool!
Juyawa yyi yabar office din ,
Kallon fuskarta kurum Aliyu yakeyi lokaci daya tabi kuma ta hade rai yana mamakin ,wannan sudden change nata tabe baki yyi.
dan kallonsa tayi murmushi ta masa gamida daga masa hannu tana fadin ."Hi!
"You can sit Mr.Turab bamalli zama yyi yana fuskantar ta tasa hannu ta karbi jakar wannunsa Wanda tasan takardunsa ne aciki." Fiddosu tayi tana dubasu daya bayan daya.
Shuru yyi yana kallonta ,
"Meyasa kwana biyu baka zuwa aiki?" Ta fada batareda ta kallesa ba,still tana duba takardun hannunsa."haka kawae yabata amsa sounding so free."wannan qaron da sauri ta dago ta kallesa ,
Dan murmushi tayi gamida dauke kanta ."idan na dauke ka a company nan zaka yarda?"kana da Results mekyau!
"Why not.?" Ya fada yana kallonta da mamaki afuskarsa Dan murmushi tayi ,zaka iya zama manager awannan company din ?"he can't still believe akan abunda nainah chanji ta fada masa yanzu!"yarda yyi magana sai yabata daria ,
In a funny way.take fadin relax Mr.Turab bamalli !"da gaske fa nakeyi ,
"Ta fada sounding so cwt murmushi dauke a fuskarta haka ta tallabe fuskarta tana qa'llonsa,
Tana jin farin ciki aranta!" Wanda ta nemi dalilin hakan ta Rasa,
Ta langabar dakai tana qallonsa cikin sanyi murya take fadin ,so you accept my offer?karka damu ka fadi ko nawa kakeso na riqa baka a salary dinka I can pay you ,ko nawa kakeso."yarda kk biyan ma'aikatanki haka nakeso,
Dan murmushi tayi gamida miqewa kan kujerar da take cikin takunta na kasaita ta iso gabansa Dan russunawa tayi ta dafa kafadarsa ,
Cikin kunnensa take Masa Rada!"
Idan nace zan riqa baka 200 hundred thousands aduk karshen wata zaka yarda?"idan kuma bazasu isheka ba zan maka qari.
Cikin ido da ido yake kallonta kafin ya Jaye hannunta akan kafadarsa,
Idan dai zan riqa cin hallat dina na amince!"
gud boy!"ta fada tana shafa sumar kansa ,
Komawa tayi ta zauna .ta kallesa tana fadin bara na sa a hada meeting din gaggawa ,nayi introducing dinka a wurin sauran ma'aikata sa'annan na nuna maka office dinka,
Kansa ya shafa murmushi dauke a fuskarsa yake fa'din." thank yhu madam for everything !"wani irin farin ciki yakeji ya matsu ya koma gida yyiwa Auntynsa albishir dakuma love wify dinsa ,
bata taba ganin fara'arsa ba irin yau."
💝ABUTTURAB💝
~Writeen by Asmy b Aliyu~
Haske writer's Association.
13
After like 30 minute haka aka shirya meeting din gaggawa cikin wani hadadden building mai hade da wani qaton hall acikinsa ,cautions ne acikinsa na Alfarma Wanda hall din yaji kayan alatu ,
Ko ina standing ac.ne manne a wurin sai sanyayyar qamshi ke tashi.
Cikin minti qalilan turab da nainah suka iso wurin ma'aikatan wurin har sun gama hallarta ,kowa zuciyarsa badai dai take ba ana Jiran aji wani rashin mutunci nainah tazo dashi ,Uncle dinta wato saleem kallo daya yyi masu ya dauke kansa.
Ganin ta yasa kowa ya miqe tsaye cike da girmamawa."
Zama tayi gamida daga masu hannu ,nuni tayiwa Aliyul akan ya zauna kusada Kujerar da take .
Kowa baki bude ya saki yana kallonta cikin bin umurninta turab ya zauna.
Kusan sakon talatin da zaman ta wurin bakajin komae sai qarar Ac.dakuma ma'aikatan wurin masu gulma na ku's -ku's.
"Gyaran murya tayi kowa yyi tsit akaro na biyu kafin ta fara bayani haka ta gabatar da Abutturab amatsayin sabon ma'aikaci kuma sabon manager .
Kowa qallonta yakeyi da mamaki wuri ya fara har gitsewa da surutu masu bakin ciki sunayi masu hassada sunayi cikin daka masu tsawa take fadin." Ya isheku!kun cikamin kunne da surutu!
Ta fada tana toshe kunnuwanta ,haka tana Runtse idanunta da sauri numfashinta ke fita tamkar wacce tayi gudu.
"Tsit kowa yyi ba shawara nake nema kubani ba akan yarda zanyi da company na!" Right?" !Ra'ayina ne nayi Wanda bbu Wanda ya isa ya canja minshi koyache meyasa nayi haka Right?"agaban nainah chanji kuke ,Ku dakata na Dan wani lokaci hayaniyarku tayi min yawa.
sakin baki da ido Abutturab yyi yana qallonta ,Wanda ita batama kula da hakan ba ta cigaba da magana .
Sai da tagama magana sa'annan tache idan ."Akwae mai magana zai iya yi?"shuru kowa yyi ,cikin hali ko in kula saleem ya miqe ya nufi hnyar fita.
Kowa kallonsa yakeyi da mmki ,
"Uncle saleem!" Takira sa da cool voice nata.
"Karo na farko A Rayuwarsa da Yaji nainah chanji " ta kirasa cikin taushin murya.
Bai Juyowa ba amma sai dai ya tsaya cak!"Rada Abutturab yyi mata a kunne ,
Plss kije ki samesa a uncle dinki ne fah.dago kai tayi tana qallon Turab dage mata gira daya yyi sai tasamu kanta da yin murmushi."
Haka kawae ta tsinci kanta cikin bin umurnin Aliyu bamalli."
qaro na farko a Rayuwarta ,da tataba bin Umurnin wani Dan Adam.!"ko iyayen da suka kawota dunia bata bin umurnin su saidai su subi nata ,cikin takunta na kasaita ta qarasa gaban saleem .
Cikin kasa-kasa da murya take fadin "uncle ka taimakeni plsss!"
Hade rai yyi yana qallonta kafin ya tabe baki."cikin hali ko in kula yake fa'din. "Taimakon me?"
"Mota nakeso a baiwa Abutturab!"
Kaje dashi acikin building din da suke ya zabi duk kalar da yakeso nasan nanne fannin ka ,nabaka wuqa da nama kaima zaka iya daukar kalar motar da kakeso!"kwana biyu ban fitar da zakkah ba!"shiyasa nakeso nayi!"
Ta qarasa maganar tana kashewa uncle din nata ido daya."Tantiriya!"saleem yyi maganar aransa ,
Haka yana tunanin turab bamalli shi zay canja masu nainah!"wani murmushin mugunta saleem yyi ,
Gamida fadin lallai wannan Yaron yanada farar ka'fa .
Yasamu shiga agun nainah chanji!"Hade rai nainah tayi lokaci daya ,
Gamida fadin karka dauka wani abu ne a tsakanin mu nayi Ra'ayin taimakonsa!"har yau ba a haifi mijin da nainah chanji !"zataso ba!"cikin dariar saleem ke fa'din oh really?"to gamu gani ae da haka Ya juya ya nufi Abutturab magana sukayi sai suka fita atare,
Anan kowa ya koma bakin aikinsa ,Yana fadin Albarkacin bakinsa.
Kwance tayi akan soofa din dake cikin office dinta tana Juya maganar uncle dinta aranta ,
Tsoki ta buga akaro na farko tana fadin."idan mutum yyi niyar taimako sai a daukeshi da wata manufa!"kusan awa daya tana kwance akayi knocking kamar tashare sai kuma tache yes come in............."batareda ta qalli kofa ba,
"Bangane ba !" wannan wane irin aiki ne Mrs.nainah chanji!" Taji sanyayyr muryarsa na mata amo acikin kunne ,miqewa tayi zaune tana qa'llonsa da shanyayyun idanunta.
Wanda Abutturab ke hango wani Abu mai rikitar wa acikin su ,
"Zauna muyi magana!" Ta fada masa sounding so cwt "haka ta nuna masa gefenta bai zauna ba ya koma dayar kujerar ya zauna.
Murmushi tayi ta langabar da kai tana kallon innocent face dinsa,
Tun kafin akai koina har qa fara korafi Mr.turab bamalli!" Nan bada Jimawa ba ,kyautar gida zan maka!"idan naga kana tafiar da aikinka yarda yadache!"Amma nai........!saurin katsesa tayi gamida fadin nainah chanji bata kyauta amayar mata ,
Dan Allah murufe wannan babin ,kayi hkuri gobe zaayi settling motarka da komae da komae.
Tashi mutafi yunwa nakeji ,
Kamar ta Rufemasa baki haka ta tattara kayanta ta Rufo office dinta tareda taimakon turab!"
Suna tafia take tamabayrsa office din da aka kaisa yyi masa?"motar ma tayi masa ko achanja ,murmushi kurum yyi yana fadin duka sunyi Na........."shitttt ta fada gamida Dora yatsanta akan Dan karamin cut Lip's dinta.
Haka suka Jera har gaban ma'adana motoci.
Bude masa front side tayi ,zaiyi magana ta dakune fuska tana qallonsa bbu musu ya shiga ta maida kofar ta Rufe ta zagaya mazaunin driver.motar tayiwa key suka dauki hnyar zuwa wani hadadden Eatery!............
💝ABUTTURAB💝
~Written By Asmy b Aliyu~
Haske Writer's Association.
14
Tare sukayi lunch a wani hadadden Restaurant. Kowane motsi da Abutturab zaiyi idon nainah akansa,kusan qarfe Biyar da Rabi suka bar wurin.har sun dau hanya take fadin."awane unguwa kake."zan Ajey ka sa'annan na wuche gida" tana maganar ne ,sounding so cool.
Girgiza kai Abutturab ya shigayi gamida fadin."bazaa ayi haka ba ki ajey ni kan hnya mai Babur zai qarasa dani.
"ba girman ka bane hawan bbur Dan Allah ka daina danganta kanka da hawa Babur,wannan qaron cikin daga murya take magana "tabe baki yyi kafin yabata amsa da fadin." Unguwar Jan bolo.
Tafiar minti sha biyar sukayi cikin su bbu mai magana,
Haka ya riqa nuna mata hnya.
Har zuwa qofar gidan su ,
Ta qaramin mirror ya hango Noor na tahowa itada bikraa uniform din islamiyya ne ajikinsu.da alamar daga makarantar suka fito ,
Fitowa yyi daga motar itama nainah ta fito .Noor ganin yayanta da wata ta hade rai lokaci daya ,bikrah da batasan meke faruwa ba batama lura da Abutturab ba.
Sun kawo gaf dasu bikrah ta Dan bude ido cikin sanyin murya take fadin."sannu da zuwa yaya!"anan kuma ta gaisheda nainah"ta amsa da kina lfy ya'mmata?"
Murmushi dauke afuskarsa yake fadin "yawwa sannu bikrah an taso daga makarantar?amsa tabasa da " Ehh da haka tayi sallama da Noor tanufi hnyar gidan su.
Idonsa nakanta yyinda idonta ke kan nainah ,har Abada bazata mance fuskar wannan matar ba da tamarar mata yayanta?"batace komae ba tayi hnyar shiga cikin gida.turab Jikinsa yyi sanyi, kallon nainah yyi Sai yaga tayi murmushi."kanwarka che wannan?"tayi mganar tana qallonsa"amsa yabata da Ehh."tana da kyau...........".nainah ta fada ,
Agaisheda Aunty!
Zanxo mugaisa watarana!
da haka ta shige motar Tamata key tabar wurin ,
Sai da motar ta tabace sa'anan ya nufi cikin gida.
Kai tsaye dakinsa ya shige ,Sai da yyi wanka sa'anan ya fito cikin Riga da wando na shan iska.
tree quarter black ne da purple din T.shirt mai guntun hnnu,dakin Auntynsa ya nufa yasameta zaune akan lallausar Rug din dake malale atsakiyar falon ,
Tana duba book's din yan makaranta .gefe daya Noor che zaune cikin Riga da wando na Pakistan ,
Dan qaramin plate ne agabanta .
da alamr yanzu take cin Abinci "aunty kawae ta amsa sallamar sa idonsa na kan Noor." Aunty ke fadin ya aiki?Alhmdullh !yabata amsa."ina yini ya tsinkayi muryar noor tana gaishesa ,harara ya shiga aikamata rau rau tayi da ido tana qa'llonsa,
"Noor tashi ki zubowa yayanki Abinci." Aunty ta fada batareda ta qalli Noor ba"na koshi aunty,
"Turab ya fada yana shafa cikinsa."ita wannan itada waye kuma?"Aunty ta tabe baki .tana fadin ohon mata tunda ta dawo islamiyya a haka ta shigo,
Shuru noor tayi kanta akasa .turab ya cigaba da fadin "aunty na samu aiki fa" da sauri Aunty ta dago farin ciki dauke a fuskarta take fadin"Alhmdullh !a ina?"
A company nainah chanji".
"Noor jin sunan tayi tamkar dirar mashi acikin kwanyar kanta ,surar plate din abincinta tayi ta nufi hnyar kitchen da gudu. Tana isa tayi Jifa da plate din sauran abincin ya zube akan marble's din dake malale a kitchen din." A hnkali ta sulale kasa ta fashe da kuka.
da ido dukansu suka bita haka Suna Juyo shesshekar kukanta a hnkali.cikin raunin murya "Aliyu ke fadin bansan ya zanyi da yarinyar nan ba Aunty!yyi maganar cikin muryar damuwa." A hnkali Aunty ta ajey pen din hnnunta ,haka ta tsurawa turab ido na Dan wani lokaci."Ajiyar zuciya aunty ta sauke"Allah yyi Jagora acikin wannan aikin da kasamu ,nidai fatana akoina kake Aliyu karka manta da matsayin mu."muba kowan kowa bane ,a hkan kuma muke manejin Rayuwarmu ,aikin nan da kasamu karya chanja maka halayyarka da duniarka ,kada cudanyya da ya'ya masu hannu da shuni ya Rudeka ya canja maka duniarka.
"Kada kudin da zaka samu ya rudeka ka fara kula matan banza." Sai yanzu nake qa'ra Jin ddi idan na tuno Aliyu na yana da mata ,
Wanda matan banza na waje bazasu Rudesa ba.
"Kada ka kara ba kowace macce damar shiga Rayuwarka Dan Allah ka riqe alkawari kada kabari na kamaka da laifin da dukan mu bazamu Ji ddi ba,
Nooriyya ta isheka Rayuwa!" Anan ta qara yimasa nasiha ,duk da hankalinsa nakan noor .ta qare da fadin Jeka lallashi noor bansan meya hadaku ba?"amma nasan bakada gaskiyya Aliyu"Dan