Chapter 3 Reading Zuciar Mutum Book 1 Complete Hausa Novels By Takori .txt Arewa Novels

Zuciar Mutum Book 1 Complete Hausa Novels By Takori .txt

Author :  Sumayya Abdulkadir (Takori Kabara) Category :  Love Story

Chapter   3 / 7

6K to 9K   out of 19K words

kai alamu ne na sun yi saranda sun yi amanna. Basu da ta cewa. Justice Ribadu ya nemi alfarmar su bar wannan magana a tsakaninsu, bai yarda mata su ji ba, suka bar asabar mai zuwa matsayin ranar daurin aure.


****






MUHARRAM/HIJRIYYA


Mutane goma da ke cikin babban falon M.T Liman, ciki har da Baffanshi Malam Sule, dan’uwanshi Tasi’u da likitanshi Dr. Saddiq. A bangaren Justice Ribadu akwai manyan alkalai ‘yan’uwansu guda uku, sai yayyensa maza biyu, suka gabatar da sadaki naira dubu goma kacal da huhunan goro ga Baffa Sule, aka gudanar da daurin auren Abdulhakim Khalil Ribadu da Sakeeinah M.T Liman kamar yadda shari’ah ta tanada.


Shaidu sun shaida, iyaye sun karba. Saura da me? Abba ya shigo yana gyaran murya yana cewa,
“Ina Lami ne? Ko ba ta gidan ne?”


Ina duke a jikin famfo ina wanke kayan fitsarin Nazir na dago na dube shi. Ya bini da wani irin lallausan murmushin kauna, ban yi nawa ba wajen mayar masa da wanda ya fishi.
A ransa ya ce,


“Wahalarki ta kare Sakinah!”.


Tasi’u ya biyo bayanshi rikle da huhun goro. Ta fito daga (store) tana gyara daurin kallabinta, ta fara da yankawa Kawu Tasi’u harara.
Ya yi murmushi ya dauke kai kamar bai gani ba. Ta ce,
“Lafiya ake yanka min kira kamar ana bina bashi?”
Ya sa kai cikin falonta. Tasi’u ya bi bayanshi ba tare da ya ba ta amsa ba.
Jikinta ya yi sanyi da ganin goro da alawa, Abba ya karkace ya zaro kudi daga aljihunshi ya mika mata ta ki karba. Ta ce,
“Na mene ne?”
“To ki karba tukunna sai in miki bayani”.
A sanyaye ta karba tana jujjuya su. Ya ce (ba tare da wata fargaba ba) “Sadakin Sakinah ne, na aurar da ita. Gwaggonninta na nan zuwa su sadata da dakin mijinta”.


Ta yi watsi da kudin suka tarwatse a tsakiyar dakin, ta mike tsaye tace,
“Zancen banza, na ga mai fitar da Sakinah daga gidan nan, ban yarda ba ban amince ba, tunda ba a yi shawara dani ba”.
Abba ya rausayar da kai ya mike, Tasi’u ma ya mike ya tura mata huhun goro don ya kara kular da ita, ta kuwa dauka ta watso su waje gabadaya.
Abba ya ce, “Ni dai babu ruwana tunda na fita hakkinki na sanar dake. Don haka Sakinah ta fita daga ikonmu ta koma ikon mijinta. Kuma ubansa Alkali ne idan ya maka ki a kotu babu ruwana”.
[9/14, 9:59 PM] Asmau: Na sanya kafa zan shiga motar kamar an ce dani daga kanki, na hango Abbanmu a bakin tagar falonshi yana kallona. Hawaye fal idanunsa. Na daga hannu na yi mishi bye-bye shi ma ya yi mini.
Wasu hawaye suka shimfido a kundukukina, hakika ina son Abbana son da bana yiwa kowa a duniya!!!


****












Kugin karshe da motar ta yi a harabar gidan Justice Khalil Ribadu ne a unguwar Maitama, Hajiya Laila da kanta ta fito ta kamani zuwa cikin gidan a hamshakin falonta.
Bayan an gaggaisa anyi abin nan da ake kira amana, sannan suka tafi suka barni tare da Inna Ladiyo. Hajiya Laila da kanta ta rakamu gidan da zamu zauna wanda ke opposite din su.


Har bakin gadona ta zaunar dani, sannan ta budewa Inna Ladiyo wani daki da ke can gefe ta ce ta zauna a can.
Ta duba ko ina ko da abin da yake bukatar gyara ta ga babu, don haka ta yi mana sallama ta koma nata gidan. Sannan ta turo mai aikinta da abinci kala-kala na alfarma ta kawo mana.
Inna Ladiyo na zaune a gefena ta soma bubbude kulolin abincin tana diba a faranti tana cewa,


“Gara ma ki bar kukan nan, tunda ba kabari aka kawoki ba dakin aure ne, dakin kowacce mace”.


Ta tura min farantin gabana,
“Ajiye mayafin nan maza-maza ki cinye ki bani farantin”. Ganin ba alamun wasa a tare da ita na karbi farantin na soma ci, amma hawayena basu bar ambaliya ba.
Ita ma ta zuba nata tana ci tana cewa,
“Haba! Yarinya sai kukan tsiya, maimakon ki yi murna ki gode Allah, dubi irin dukiyar da ubanki ya shirya miki a gida. Ga surukar kirki Allah ya baki, in ba ki yi dariya ba to ba za ki yi kuka ba, kika kara yi min kukan nan bige miki baki zan yi, shashasha kawai”.
Ta gama cin abincinta ta goge baki, ta kwashe kayan ta yi kicin dasu. Ta dawo ta dau filo ta jefa a kasa ta yi kwanciyarta, ba ta dade ba ta soma jan minshari.


Na yi zaune a gefen gado, tunanin duniya ya ishe ni, duk da nake yarinya karama ban taba jin wani aure irin nawa ba. Ban san angon ba, shi ma bai sanni ba. Bai san za’ayi ba nima ban san za’ayi ba sai a labari.


Har dare ya mika na kasa barci, ga minsharin Inna Ladiyo dake bani tsoro. Babu motsin wani mahaluki cikin gidan, sai haushin karnuka a makota. Na kankame jikina wuri daya na ci gaba da kuka a hankali ina roka wa kaina afuwa cikin ita wannan sabuwar rayuwar.


****


Dogo ne baki, amma bakinsa mai kyau ne, saboda baki ne da ya hadu ya cakude da gogayya cikin zuzzurfan ilimin boko. Ma’abocin fadin kirji da alamun karfi ta ko’ina. Kyakkyawa matuka, abin alfaharin kowacce mace, har maza ‘yan’uwansa ba za su bar dakacen ina ma a ce su ne shi ba.
A kan ce wai duk mutum tara yake bai cika goma ba, to amma ABDUL-HAKIM KHALIL RIBADU, ya kai 95% ma, a dabi’a, sura da halayya. Tunda iyakar kushen mai kushe, da iyakacin kwakkwafin mai kurullah, ba zai ce ga ta inda Allah ya rage shi ba.


Duk wani dake tare da shi ya yi shaida a kan kyawawan halayensa na hakuri, rikon addini, juriya da kaifin kwakwalwa. Wata irin kwakwalwa kamar computer, wadda in ta zana maka gida, makaranta, titi, asibiti ko ma’aikata za ka yi tsammanin baturen Ingila ne ya zana su.
Da daya kwal! Kuma jallin jal ga Alkali Khalil Ribadu da Hajiya Laila. Bayan shi kuma ba a haifi wani ko wata ba har inda yau ke motsi. Don haka shi din dan gata ne na karshe.

Bayan karatu mai suna karatu a kan Quantity Survey daga jami’ar Ahmadu Bello. A halin yanzu ma’aikaci ne na ‘Julius Berger’ reshen jihar Lagos. Dan kimanin shekaru talatin da biyu.
Abdulhakim ya tashi tare da Abdallah, dan Yayan mahaifin shi, duk wata dabdalar kuruciya tare suka yi ta, a cikin gida daya daki daya, ta yadda in baka san tarihin gidansu ba da wuya ka san cewa Abdallah ba Yayan shi bane na ciki daya ba. Domin kamar su daya, saidai hali kowa nashi daban.
Abdallah mai harka ne sosai da faram faram da jama’a (jovial), ga son mata da son raha, inda suka sha bambam da Abdulhakim kenan
Abdallah zai bai wa Abdulhakim shekaru biyu, shi kuma ma’aikacin DSTV ne a Kaduna, don haka duk karshen sati suna tare a gida Abuja, sai yammacin lahadi suke komawa garuruwansu.


Saukar Abdulhakim ke nan daga jirgi, ya hada layi ya kira Abdallah ya sanar da shi isowar shi ya zo ya dauke shi.
Cikin abin da bai haura mintuna sittiin ba, Abdallah ya iso airport din Abuja, suka hade a reception ya karbi jakar hannunshi bayan sun yiwa juna murmushi, suka doshi inda Abdallah ya yi parking.
Sai dai cikin ransa yana matukar tausayawa dan’uwanshi halin da ya samu kanshi ciki, gaba daya ya rame ya rasa kuzari kamar ba Abdulhakim ma’abocin haba-haba da jama’a ba, fara’a da sanyin zuciya.
Ya tabbata abin da Daddy ya yi bai kyauta mishi ba, don shi din shaida ne a kan son da yake yiwa Farida. Yiwa Abdulhakim AUREN HUCE HAUSHI ba dabara ba ce so-karbau (inji malaman Hausa) da za ta gusar mishi da azabar zuciya da soyayyar da yake ciki.


Suna tafe babu mai cewa uffan, don Abdallah ya kame bakinsa, bai gaya mishi auren da Daddy yai mishi ba da sanin shi ba. Shi kuma dama ya dade da zama silent tun daga lokacin da ya rasa abin da yake so a rayuwarshi.


Suna isowa gida Daddy ma na sanyo hancin motarshi cikin gate din gidan, don haka duk suka dakata har ya karaso. Abdallah ya bude mishi owner side tare da karbar brief case din shi, ya dafa kanshi ya ce,
“Har kun iso?”
Abdallah ya ce, “Shi ne dai sai yanzu ya iso, amma ni tun goma na safe ina cikin Abuja”.
Abdulhakim ya karaso shi ma yana kwasar gaisuwa, suka rankaya falonshi dukkanninsu.
Hajiya Laila ta shigo ta sha kwalliya cikin shadda da zinare, sai walwali take. Kallo daya za ka yi mata ka fahimci tsantsar farin cikin da take ciki. Kafin dan lokaci ta cika dining da abinci, har da ita aka hau tebir.
Tana kallon Abdulhakim wanda ke ta zuba ruwa a kofi yana daddaka, amma ko loma daya bai yi ba.
Ta cika filet da abinci ta tura mishi,
“Cinye maza ka bani kwanon”. Ya girgiza kai,
“I’m o.k Hajiyata, ban jima da cin abinci cikin jirgi ba”.
Ba ta ja da nisa ba sai ta kyale shi, amma kallo daya za ka yi mata ka tabbatar ta damu da yanayin da yaron ke ciki.
Sai da suka kammala Daddy ya dube shi da murmushi ya ce, “Sai kuka ji kirana babu zaton ku ko?”
Abdallah ya ce,
“Ko baka yi kira ba Daddy dama zamu zo ne”.
Ya ce, “In ce ko ka yi mishi bayanin abin ALHERIN da na yi mishi?” Abdallah ya girgiza kai,
“A’a, ai nima zuwana ke nan Hajiya take gaya mini”.
Ya daga fararen idanunshi yana kallon su da alamar tambaya a kan kyakkyawar fuskarsa, Abdallah ya juyar da kai, don haka ya mai da kallon shi ga Daddy.
Daddyn ya yi murmushi ya ce,
“Abdulhakim!”
Ya amsa “Na’am”. Ya sake cewa, “Abdulhakim!!”
Shi ma ya amsa.
Ya ce, “Ka bani hankalinka magana ce zamu yi ba ta wasa ba”. Ya ce,
“Ina jinka Daddy”. Ya ce,
“Yauwa.
Na tura a nema maka aure kamar yadda kake so, ka kuma neme ni da in yi, iyayen yarinya sun wulaqanta Baffana da ‘yan’uwana, sun yanka mana sadaki na rashin hankali da rashin neman albarka, tare da wasu manyan bidi’o’i na neman magana da son kure mutum, wanda ba sai an fito fili an nuna min cewa raina ni aka yi ba, da na ce a rage ya yi yawa aka maido min da kayana duka.
Don haka na karba maka aure na mutunci, diyar aminina M.T Liman wanda ba sai na tsaya ina yi maka bayaninsa da matsayinsa wajena ba. Sai dai Sakinah yarinya ce karama da nake fatan ka yi mata riko na kanwarka kuma matarka.
Na san na isa da kai, shi yasa na yi hakan ba tare da shawara da kai ba. Na san har kullum kai mai biyayya ne a kan umarnina. Na san ba za ka watsa min kasa a ido ba, ba za ka ki rike diyar M.T Liman da mutunci ba ko da ace bana raye”.


Wata irin zufa ce ta ketowa Abdulhakim daga goshi har zuwa yatsun kafa. Ya dago a firgice ya dubi mahaifinsa, hankalinsa a kwance yake maganarsa, idanunsa suka kankance cikin tashin hankali.
Cikin firgici da sarqewar murya ya ce,
“Amma.......amma Daddy.....ai...”.
Ya kasa karasawa don harshensa ya kasa daidaituwa.
Ya ce, “Ai me? Fadi ra’ayinka na baka dama”. Ya ce,
“..Ai an daina irin wannan auren yanzu, Daddy ban santa ba, ita ma ba ta sanni ba. Baka sani ba ko da wanda take so, nima da wadda nake so. Duk da cewa na hakura da Farida amma Daddy i’m sorry ban san ya zan yi da wannan auren da ka karba mini ba”.
Daddy da Hajiya suka yi murmushi, Hajiya ta ce, “Ka kwantar da hankalinka Abdulhakim, Sakinah yarinya ce karama, ba ta san komai ba sai abin da ka sanar da ita. Ka zauna lafiya da matarka, yarinya ce sai girman kashi da manyan barage.
Abin da nake so ka yadda da shi shine, Daddynka ba zai dauko maka mummunan abu ko abin da ya san ba zai amfane ka ba”.
Sai juya kai ya yi kamar ya yi ihu, amma babu dama, ga yadda ya gama fahimta Daddy bazai taba sauraron uzurinsa ba, ko wace ce wannan yarinya ta ruguza mishi tsarin rayuwar da ya riga ya tsara ma kanshi.
Ga shi suna ta ambaton wai yarinya ce, to yarinya kamar ya ya? Amsar da bai samu ba ke nan har suka fito daga falon Daddyn shi da Abdallah. Daddy da Hajiya na ta sanya masu albarka.


Abdallah sarkin zolaya suna shiga daki ya juyo ya kama hannunshi ya ce, “Oya ango! Muje na rakaka dakin amarya”.
Wata muguwar harara ya zabga mishi, ya ja bakinsa ya bame da makulli yana dariya kasa-kasa. Ya zauna gefen gadonshi ya kama kai, ya dafe da dukkan hannuwanshi. Idanunshi sun kada sun yi jawur, jijiyon kanshi duk sun fito rada-rada.
Wannan shi ne alamun bacin ran Abdulhakim, amma ba kuka ba. Cikin ranshi yana cewa, “Gidan da na kwashe shekaru uku ina zanensa, na kwashe shekaru uku ina gininshi, shi aka sa matar da ban ce ina so ba! Ban san kalarta ba! Ban taba ganin ta ba!.


Har zuwa wayewar gari barci bai ga idon Abdulhakim ba, tun Abdallah yana rarrashi, yana magiya a kan suje ya raka shi wajen amaryarshi, har ya koma ya mishi barazanar to zai gayawa Daddy.


Ya nuna mishi hanya ya ce, “Have your way out.......Allah ya baka nasara”.
Abdallah Ya ce, “To me kake nufi? Ka bar ‘yar mutane ta kwana ita kadai? Wallahi ka ji tsoron Allah”.
Ya ce, “Ko me ya same ta ita ta jiyo, tunda ta ce ta ji ta gani, auren mijin da ba ta san ko waye ba?”


Washegari ya tattara ya koma bakin aikinsa, ko Daddyn bai sani ba. Sai sallahu ya bar mishi a rubuce cewa ya koma Lagos ana kiransa a office da gaggawa.
Daddyn bai kawo komi a ranshi ba, don a zatonshi Abdulhakim ya hakura ya karbi auren da ya yi mishi da hannu bibbiyu.
***


Tashinmu ke nan da safe bayan komawa barcin asubahi, aka danna kararrawa misalin karfe takwas na safe. Inna Ladiyo na ta barci, don haka na nufi kofar na bude.
Na zo na tsugunna har kasa ina gaishe su. Hajiya da Daddy ne da kansu, ta dora hannunta a kaina ta ce,
“Kin kwana lafiya Sakinah? Yaya bakunta? Ina Innar?”
Ladiyo ta fito tana cewa, “Gani nan barci ne ya sace ni daga lazumi”. Suka gaisa sosai, Daddy ya tambayeni ko inada matsala nace babu sannan suka tafi, mai aikin Hajiya ta kawo mana karin kumallo.


Haka muka yi zamanmu lafiya ni da Inna Ladiyo, mu ci mai kyau mu sha mai kyau, mu zauna a mai kyau, mu daura mai kyau, ba abin da ya dame mu.Har satin da Abba ya debar ma Inna Ladiyo ya wuce.
Hajiya Laila da kanta ta roki Abbana da ya kyale Inna Ladiyo mu zauna tare in har ba wani uzuri ne a kanta ba. Tunda Abdulhakim ba mazauni bane, sai karshen sati yake zuwa gida.
Karshen wannan satin ko garin bai zo ba, ya sanar da Daddy ba zai samu damar zuwa wannan satin ba saboda an tura shi (surveying) ginin wani titi da suke yi a Akwa-Ibom. Alhalin a zahiri ba gaskiya bane, kawai yana gujewa Sakinar da har yau bai san wace ce ba, ba kuma ya bukatar ya sani.


Nutsuwar zuciya da sauyin muhalli dana samu ya haifar min da murmurewa cikin ‘yan kwanaki qalilan. Babu aikin Mami na sassafe, babu fargabar jibgarta da rankwashinta.
Ban damu ba wai don har yau ban ga angon ba, ni a wajena ma gara hakan. Sai dai makaranta da bana zuwa shi ne abin da ke damuna.
Zuwa lokacin na saba da Daddy saboda yadda yake jana a jiki, tare da nuna kulawarsa gareni. Duk bayan kwana biyu ko uku yana shigowa ya ga lafiyata mu gaisa.


Don haka yau litinin da ya shigo cikin shirin ofis da hularshi ta Alkalai a kansa, bayan mun gaisa sai na ja bakina na yi shiru.
Ya ce, “Ya ya dai Sakinah? Na ga bakin yana ta motsi”. Na sunkuyar da kai na ce,
“Daddy ina so in koma makaranta”.


Ya ce, “Wacce kike zuwa?” Na ce, “Al-Amin International”. Ya ce, “Bari zan yi waya da Abdulhakim in ba zai samu zuwa ba wannan satin sai Abdallah ya mai da ke”. Na ce, “Daddy na gode”.
Ya yi murmushi,
“Babu godiya tsakaninmu Sakina, ni Babanki ne kin ji?” Na gyada kai.
Daddy yana isa ofis ya kira Abdulhakim a waya, ya yi qasa da murya yana gayar da Daddyn. Ya amsa, ya ce,
“Ya ya Abdulhakim za ka samu zuwa gida this week?”
Don kada Daddyn ya dago shi a kan kin zuwa gida da yake yi ya ce,
“Zan zo insha Allahu”.
Ya ce, “To shi ke nan Allah ya yi maka albarka”.
Karshen satin ya tattaro ya nufo gida Abuja. Wannan satin ya riga Abdallah sauka, wanda bai iso ba sai yamma lis. Tunda ya zo yana tare da Hajiya suna zancen tsarin filinta da za a soma gini, ta bar zancen gini ta dube shi sosai ta ce.
“Abdulhakim”.
Ya dago ido ya dube ta ba tare da ya amsa ba. Ta ce, “Fisabilillahi me kake nufi da auren ka? Ina lura da kai har yau baka je inda matarka take ba. Ba fa kare aka ajiye maka ba dan mutum ne mai kima da daraja. Idan har kana so mu shirya, to a yau nake so ka tattara komi naka ka koma gidanka, kada ka bari Daddy ya san halin da kake ciki ranshi ba zai yi dadi ba”.
Haka ya taso ya fito duk jikinshi babu kwari. Ba ranshi ne ya baci ba, yarinyar ce kawai ba ya so. A ganinsa he is old enough da ya yi ma kanshi zabin abokiyar rayuwa tunda Daddy bai fi shi idon ganin mata ba. Ba kowacce mace ce ke da abubuwan da yake so a diya mace ba sai FARIDA.
Ya soma tattare duk wani abu

3 / 7