Chapter 6 Reading Zuciar Mutum Book 1 Complete Hausa Novels By Takori .txt Arewa Novels

Zuciar Mutum Book 1 Complete Hausa Novels By Takori .txt

Author :  Sumayya Abdulkadir (Takori Kabara) Category :  Love Story

Chapter   6 / 7

15K to 18K   out of 19K words

in gama wanka in yi shirin makaranta ta kammala kalaci ta zuba min wanda zan tafi da shi cikin flask, sai in ci in fito in tadda John mu wuce makaranta.
Yau da aka fito break muka hadu ni da Nadiya muka nufi gindin bishiyar goba muna cin abinci, na Nadiya muke fara ci sannan mu ci nawa.
Muna ci ta ce, “Sakinah ya ya sunan mijinki?’ Na ce, “Sunan shi Mijin-Sakinah”. Ta ce, “Mijin-Sakinah?’ Na ce, “Eh, shi ya ce min sunanshi haka”.
Ta jinjina kai ta ce, “Uhm! Ban taba jin wannan sunan ba”. Na ce, “To haka ya ce sunansa”. Ta ce, “Kin san kuwa Abba ya auro Yaya Suwaiba ta ‘Yan Leman?”
Cikin mamaki na ce, “Yaushe?”
“Yau satinta daya, kuma Mami da Adama sun yi fada ta kore ta, don ta gane cutarta take, in ta aike ta wajen malamansu ba ta zuwa sai ta zuba kudin a aljihunta ta kawo mata magungunan karya.
Yanzu gaba daya Abba ya watsar da Mami sai Yaya Suwaiba, kuma ya hanata zuwa ko ina. Mami har tausayi take bani”.
Na ce, “Allah sarki Mami, gara ta rabu da Adama, don ba mutuniyar kirki ba ce, amma inda za ta gane ta zauna lafiya da Yaya Suwaiba don tana da kirki sosai”.
Ta ce, “Abin da Yaya Safinah ta gaya mata ke nan”.
Aka kada kararrawa muka koma aji. Har aka tashi yau ina tunanin hirar da mu kai da Nadiya. Gaskiya ne addu’a ba ta faduwa kasa banza, addu’ar da nake kwana da wuni ina yiwa Abbana a kan Mami, ba ta fadi a banza ba. Tunda gashi alqadarinta ya soma karyewa, Abba ya fara zama namijin duniya.


Tunda Mijin-Sakinah ya tafi, bamu gaisa ba, don bani da waya. Ga shi ya ce in zai dawo zai sanar dani in yi mishi girki.
Don haka na bi na damu, don ban san ranar da zai dawo ba. Sai na kintata tunda ya ce wannan satin ba zai zo ba sai sati na sama, don haka ranar juma’a ta sama na shiga kicin don ganin abin da ya dace in girka masa.
Sakwara na fi kwarewa da yi, saboda yadda Mami ke son ta, take kuma yawan samu mu yi ni da Adama. Don haka da kaina na kirba doyar a turmi.
Sabuwa na yankan alayyahun miya muna hira, sannan na fiddo kayan ciki a firji na wanke na dora sanwar farfesu. Ina gamawa na yi wanka na sanya daya daga cikin riga da siket da Mijin-Sakinah ya sayo min na fesa turare na dawo falo na zauna kallon mutanen nawa (larabawa) a tauraron dan adam.
Shiru-shiru tun ina duban kofa har na soma mikewa ina leka waje, babu Mijin-Sakinah babu alamun shi. Har magariba babu shi babu Abdallah.
Na dawo cikin kujera na yi zugum dani, damuwa karara ta bayyana a fuskata. Kamin ka ce meye wannan? Sai hawaye, wasu na korar wasu.


Aka murda kofar falon a hankali aka shigo, na daga kaina a hankali don ganin mai shigowa. MIJIN-SAKINAH ne, rataye da falmaran din baqaqen ‘Italian Suit’ da yake sanye dasu.
Ya yi tsaye a kofar yana kallona yana murmushi, hannayenshi duka biyu zube cikin aljihu, kafin ya bude min dukkan hannuwanshi da nufin in zo gare shi, na maida hannuwa na baya na sarqesu ina murmushin da ni kaina bansan irinshi ba.
Murmushin farin-ciki indeed! Amma hawayen basu bar ambaliya ba.
Da sassarfa ya karaso gareni, ya rage tsaho ya rankwafa ya kamani ya rungume, muka saki ajiyar zuciya mai nauyi a tare. Ya dago fuskata da hannun daman shi ya soma share min hawayen.
Ya ce, “is O.K matas, na yi laifi da na dade ban iso ba, ba zan kuma ba, ban taso da wuri bane sakamakon dimbin ayyuka da suka tare ni. Ki yafe ni........ I’m terribly sorry….!”.
Ya kai gwiwoyinshi kasa ya kama fatar kunnenshi, ya sake cewa, “I’m-sorry!”
Na tuntsire da dariya duk da maqalallun hawayen da ke idona.


Ya mike yana cewa, ‘Lemme take a shower, I’ll be back to you soon.... (bari inyi wanka ina zuwa gareki yanzu)”
Ya wuce dakinshi yana cewa, “Biyoni da brief case din nan”.
Na dauka na bishi a baya.


Ban taba shigowa dakin Abdulhakim ba sai yau, makeken family bed ne dan kasar Italy, sai wardrove ta jikin bango, sittirun shi ne a jere reras saqale jikin ‘hanger’ wanda duk rabi suit ne kala-kala, baqaqe da rowan toka samfurin Tommy Hilfiger, Armani, Louis Vuitton, Dolce and Gabbana, Versace, DKNY gasunan dai barkatai wanda kallonsu kadai ya isheka kimanta tsadarsu, sun kuma isa su nuna maka cewa mamallakinsu dan gaye ne na karshe.
Dakin shimfide yake da marbles farare sol har a jikin bango. Sai split mai kwararar da ni’imtaccen sanyi wanda ya gauraye da qamshin room-freshna respberry ya ba da wani nau’in sanyi da sassanyan qamshi mai ratsa zuciya.
Sai dai dakin a hargitse yake ko ina takardu da taswirar zane-zane. Don haka yana shiga shower na soma kintsa dakin.
Na hada takardun wuri daya na adana komai a muhallinsa, na sa mopper ina goge marbles, nan da nan dakin ya hau sheki.
Ya fito daure da tawul ya tsaya yana mamaki. Na dago ido na kalle shi na yi saurin dauke ido a kanshi, don ban taba ganin babba babu riga ba.
Ya yi murmushi ya ce, “Haka kike da aiki Sakinah?” Ban amsa mishi ba, na soma kokarin fita ya riko hannuna na kuwa tamke idona tam!
Ya langabar da kai abin tausayi ya ce, “Ni mijinki ne Sakinah, ki rage jin kunyata”. Na ce, “Ai fita zan yi kasa riga”. Ya ce, “To ai ni wai da tausa nake so ki yi min”. Na zaro ido. Babu bata lokaci na ce, “Ban iya ba”. Ya ce, “To zo in koya miki”. Ai kuwa na ce kafa……. me na ci ban baki ba…..na falfala da gudu na koma kichin. Ban kara dawowa ba.
Ina jera abinci a dining ya fito cikin caftan na wata jiqaqkiyar wagambari deep green, sai sheki take saboda maiqo.
Ya tsaya jikin tebir din yana kallona, na dukufa wajen shirya table, ya ce, “Dama kin daina wahalar da kanki, wajen budurwata dana gaya miki labarinta zan je in ci, kuma ta yi min tausa”.
Da sauri na dago na dube shi, na kuma yi saurin sunkuyarwa don fuskarshi babu alamun wasa. Na ji wani haushi ya zo ya tokare ni a zuciya.
Zai wuce na yi saurin shan gabansa, idanuna rau-rau suna niyyar zub da hawaye, “Don Allah kar ka je”.
Ya dube ni sosai kamar yayi dariya amma ya dake, ya ce, “In ban je ba za ki yi min ne?” Da sauri na daga kai. “To amma kar ka cire riga”.
Ya murmusa ya ce, “Ba zan cire ba, amma mu fara cin abincin”.
[9/14, 9:59 PM] Asmau: Na ji dadi, na dau filet na soma zuba mishi. Ya soma ci ya ce, “Amma dai da inji kika daka sakwarar nan”.
“A’a, da hannu ne, me ka gani?”
“Ta yi kyau ne sosai, ga dadin taunawa, you are a good cook, na gode Sakina”.


A kwana biyun da Abdulhakim ya yi wannan satin, na qware da yi mishi tausa, mun kara shaquwa, kauna ta musamman ta kara habaka a tsakaninmu. Har tsoro nake lahadi ta zo ta rabani da mijin Sakinah (kamar yadda ya kirayi kanshi) ya kuma ce min da hakan yake so in dinga kiran shi don yana jin dadi a ce shine mijin Sakinah.
Ya koma ranar lahadi nima na koma makaranta ranar litinin. Jarabawar karshen zango na uku ta matso, wadda daga ita zan shiga aji uku na karamar sakandire.
Mun samu hutu bayan kammala jarrabawa, Abdulhakim yana Lagos, sai karshen satin nan muke sanya ranshi.
Na duba kicin na tarar duk naman da ke cikin freezer ya kare. Na kira Sabuwa na ba ta kudin cefane har da naman.
Bayan ta kawo muna killace kowanne a inda ya dace, kararrawar kofar shigowa ta yi kara. Sabuwa ce ta je ta bude, sannan ta gaya min cewa ina da baki.
Na wanke hannuna da sabulu cikin sink na fito, nan na yi arba da Abbana, Safinah da Nadiya da autanmu Nazir.
Na yi tsalle na rungume su daya bayan daya, na rasa inda zan sa kaina don murna. Nan muka shiga hidimarsu ni da Sabuwa.
Safinah da Nadiya suka ce, “Mami na gaishe ki”. Na yi murmushi na ce, “Ni kuwa?” Abba ya ce, “Mamin ku na gaishe ki da gaske, da tare ma zamu zo to sai ta yi baki”.
Nadiya ta ce, “Baki san Mami bane ta sauya yanzu. Yaya Suwaiba ma tana gaishe ki, za su zo tare da Mami”.
Na ce, “Duk ina amsawa Allah ya kawo su”.
Mun kebe ni da Abba a karamin falon Abdulhakim, mun baro su Safinah suna ta ciye-ciye. Abba ya ce, “Babu matsala dai ko Sakinah?’
Ina murmushi na ce, “Babu Abba”. Ya gaya min cewa ya je Libya yana kara bincike har ya samu mutumin da ya gaya mishi sunan garin da su mahaifiyata suka koma a Egypt wato Qatar, yana nan yana fafutukar neman adireshin, da ya samu zamu je insha Allah.
Da wannan daddadan labari suka tafi suka barni. Ko da Abdulhakim ya zo a wannan satin da labarin da na tare shi da shi ke nan, shi ma ya tayani murna.
Ya sunkuce ni muka yi dakinsa yana cewa, “Ki yi min tausa..... I missed your tausa Sakinah….!”.
Sai da nayi mishi tausar ya tausu, ya kama hannuwana ya rike cikin nasa, ya soma murza ‘yan yatsuna a hankali yanayinshi yana sauyawa a yau. Yana kallona da wani irin murmushi mai sanyi da sanyaya zuciya.
Na kwace hannuna na ce, “Barci kake ji ne Mijin-Sakinah?”
Daga can karkashin maqoshinsa ya ce, “Uh!”
Na ce, “To bari in tafi ka kwanta”.
Ya girgiza kai ya kara damke hannuna, damka sosai kamar zai ballani, nayi ‘yar kara nace “zaka karya ni” yace “bazan karyaki ba, amma Sakinah Mata da mijinta basa raba makwanci Sakinah, yau dai daya da zan yi miki sallama, ki tayani kwana!”.
Cikin firgici na ce,
“Ina za ka je?”
Ya yi matashi da kafafuna yana ja min yatsu a hankali ya ce,
“Wajen aikinmu sun zabe ni zan tafi wani course a Beirut (Lebanon) tsayin shekaru biyu...... ba don makarantarki ba da tare zamu tafi, amma zan ke zuwa akai-akai ina ganin ki...”.
Kuka nasa sosai, “Ni ba zan zauna ba, wallahi sai dai mu tafi tare ko ka mai dani gidan Abbana”.
Ya ce, “Gidan Abba kuma? Kina so Mami ta ci gaba da lakadarki ko?”
Na ce, “To zan bika”.
Ya ce, “Makarantar fa? Na gaya miki zan dinga zuwa ba zan yi watanni uku ban zo ba”.
“To ka mai dani gidanku wajen Hajiya”.
Ya ce, “A gidanki za ki zauna, ita ma Hajiyar a gidan mijinta take”.
Na ci gaba da sharar hawaye yana lallashina.


Washegari tunda muka yi sallar asubahi bamu koma barci ba. Nasihohi yake yi min a kan in kula da kaina, in kula da amanar aurenshi, in mai da hankali a kan karatu.
Ya ce yana so kafin ya zo in dauko 1st position zai yi min babbar kyauta. Ya fada toilet ya yi wanka ya shirya cikin riga da wandon versace, yana kumbing kanshi, ya juyo ya dube ni na yi tagumi a gefen gadon shi, idona cike taf da kwallah.
Ya aje matajin ya karaso ya tsuguna a gabana, ya kama hannuwana sannan a nutse ya ja ni cikin jikinshi, ya soma kissing bakina zuwa dogon wuyana bayan ya rike tufkar gashina da hannun hagunshi, cikin wani irin ‘passionate kissing’ mai tsirgawa har cikin kwakwalwa…..
Da karfi na yi baya, na ce, “Wannan ai iskanci ne Mijin-Sakinah, meye haka? Sai kace wasu tantabaru?……”.
Ya rufe baki yana dariya ya gyada kai ya danne dariyar ya ce,
“To na daina iskanci, sallama ce nake miki matar Abdulhakim irin ta turawa, ko ba kya gani suna yi a talabijin”.
Na ce, “Ina gani, amma kai ai ba bature bane, don me za ka kwaikwaye su bayan su ‘yan iska ne daman?”
Ya kama baki ya girgiza kai yana so ya kara yin dariya amma ya dake, ya kama hannuna muka zauna a gefen gado. Ya jawo loka ya debo kudi masu kauri ya zube min a cinya.
Ya ce, “Ku dinga yin cefane kafin in zo”.
Sannan ya miko min kwalin waya yana nuna min yadda zan ke amfani da ita, na rike wayar nan ina murna. Ya kama hannuna ya lumshe ido ya ce,
“Sakinah me za ki bani? Wanda zan ke tunawa da ke kullum?’
Na ce, “Me kake so in baka?” Ya rufe ido ya nuna min kuncinsa na dama, “Kiss me here........” Na zaro ido na ce, “Allah ba zan iya ba”.
Sai ya kamoni ya rungume a kirjinsa yana saukar da numfashi da sauri da sauri. Ya ce, “I will miss you so much...... plz Sakinah kiss me....”
Jin roqon ya yi yawa, ga shi yana ta bata lokaci, sai na runtse ido na yi yadda yake so. Nayi mishi sumba, mai tsayi, da zurfi. Ya kara kankame ni qam-qam tamkar ya tsaga kirjinsa ya sanya ni.
Al’amarin ya soma kokarin sauya alkibla daga Abdulhakim a yau, gabadaya ya rikice mani, da wasu sabbin al’amura da ban sani ba, ban kuma taba tsintar kaina a ciki ba,ban sansu ba, cikin kananan shekaru na, wanda hakan ya haifar da matsanancin tsoro a gare ni.
Sallamar Abdallah a falo ita ta katse duk wani hanzarinsa, ta qwaceni daga hannun mijin Sakina, wanda nake tunanin babballani yake so ya yi, na rufe ido saboda kunya, duk ya cukuikuiye min shaddata da ta sha guga.
Ya ja babbar jakar na ja karamar muka fito falo. Abdallah ya ce, “Kana duba agogo kuwa? Ka san nisan airport din nan amma ka yi zamanka. Sakinah dauko mayafinki mu tafi su Daddy suna mota suna jira”.
Ya ce, “Ba za ta je ba, don kuka za ta yi”. Yasa murya yai kiran Sabuwa, ta fito suka gaisa. Ya ce, “Ni zan tafi, don Allah ki kula da gida da Sakinah”. Ta ce, “Insha Allah Alhaji”. Ya fita yana waiwaye na ni kuma ina sharar hawaye.


Tun tafiyar Mijin-Sakinah sai na zama wata irin sukuku ba kuzari, na saba da Mijin-Sakinah, matukar sabo kuwa. Ya shiga raina fiye da tunani, yau kwana bakwai da tafiyarsa amma har yau kewarshi ba ta sake ni ba, walwalata ta ragu, farin cikina ya taqaita.
A makaranta ba na tsinana komai, sai tunanin Mijin-Sakinah da al’amuranshi, tareda tuna abubuwanda suke gudana a tsakanin mu, masu kara min kaunarsa.
Mutum ne mai kyakkyawar zuciya, da kirki na gasken-gaske, tareda biyewa kuruciyata, da karbar rayuwa a duk yadda ta zo masa. Na samu kaina cikin wani sabon al’amari akan Abdulhakim. Na soma tambayar kaina shin me ke damuna ne? Ni ‘yar gidan Limamai?


‘Note’ ya taru ban yi ba, sai Nadiya nake kaiwa ajinsu idan ‘yan ajinmu sunyi ta yi min. Don haka da aka zo jarabawa na kwaso na talatin.
Yau da dare Daddy ya shigo, bayan mun gaisa na nufi kicin na kawo mishi ruwa da lemu, na zuba mishi a tambulan ya sha.
Ya dube ni sosai ya ce, “Wannan ramar ta mece ce Sakinah?”
Na sunkuyar da kaina ina murmushi, na ce, “Mun yi jarabawa ne Daddy”. Ya ce, “Ina sakamakon?”
Cike da tsoro na ce, “Yana daki”. Ya ce, “To kawon in gani”.
Jiki babu kwari na shiga daki na fiddo mishi result din.
Ya duba ya dago da sauri ya kalleni, “Na talatin Sakinah?” Na sunkuyar da kai cikin rashin jin dadi. Kamar ince da kasar ta tsage in shige sabida kunya.
“Sanda kina gida na nawa kike dauka?”
Muryata na rawa na ce, “Na goma ko takwas ko bakwai”.
Ya ce, “Hakan na nufin kina da damuwa a yanzu, wadda ban sani ba? Fada min ko ta mece ce.....”
Na ce, “Wallahi Daddy babu”. Ya ce, “To me yasa sakamakon ki bai yi kyau ba? Idan Abdulhakim ya ga wannan zai ji dadi ne?” Na girgiza kai ban yi magana ba.
Ya ce, “To ki dage next term kada inga sakamako irin wannan”. Na ce, “Insha Allahu zan dage”.
“Abdulhakim ya ce in tambaye ki, mene ne amfanin wayar da ya baki don ku dinga gaisawa kika rufe ba kya budewa?”
Na ce, “Na manta da ita ne Daddy saboda exam, amma yanzu zan bude”.
Ya ce, “Ki bude ki sata a caji, kada ki kara rufewa sai in za ki kwanta barci. Duk wata damuwarki ki sanar dani kin ji ‘yata Sakinah? Ki dauka ni da M.T duk daya ne, babu banbanci.
Na samu malamin Islamiyya wanda zai dinga zuwa har gida asabar da lahadi ya dinga koyar dake karatun Alkur’ani da sauran litattafan addini, kina so?”
“Ina so Daddy, na gode sosai”.
“To Allah ya yi muku albarkar biyayyar da kuka yi mana, kuma ya baku masu yi muku kwatankwacinta, ko fiye da ita. Ni zan wuce, ba kya son komai?”
Na ce, “Akwai komai, kuma akwai kudi, sai dai John ne ya ce yana tunin albashinsa”. Ya ce, “Babu damuwa, zan ganshi”.
“A gai da Hajiya”.
Ya ce, “Za ta ji”.
Yana fita na yi daki na soma laluben lokas inda na san na ajiye wayata, na fiddota na hada na jona caji. Kafin a jima ta cika.
Tun ina tunanin Mijin-Sakinah zai kira yau, gobe ko jibi har na hakura, na ci gaba da mai da hankali a kan karatuna na Islamiyya da boko.


Watanni biyar ke nan da tafiyar Mijin-Sakinah, na dawo daga makaranta ko uniform ban cire ba, na shiga gidan Hajiyar Abdulhakim don na gaishe ta, kasancewar na kwana biyu ban shiga.
Tun daga bakin kofar shiga falon Hajiya na soma jiyo muryar Mami, gabana ya fadi na juya zan koma sai gasu sun fito ita da Hajiya, ga dukkan alamu tafiya za ta yi.
Daidai sanda na juya zan tafi Mami ta ce,
“Sakinah, saboda na zo wajenki za ki juya?”
Na juyo na tsuguna a kasa ina gaishe ta. Ta kama hannuna ta dago ni ta ce, “Ki yafeni Sakinah, kan duk abin da ya faru a baya. Na zo ne in ga dakinki, in kuma baki hakuri”.
Na ce, “Ni baki yi min komai ba Mami”.
Ta ce, “A’a, na yi miki, sai dai ki ce kin yafe ni”.
Na ce, “To na yafe ki, muje kiga dakin nawa”.
Har Hajiya muka je, Mami ta shiga ko’ina ta yaba, dakin Abdulhakim ne kadai a kulle. Na debo kayan shafa na (Neutrogena) cikin leda na ba ta.
Da kyar ta karba, ta ce, “Ni ya kamata in kawo miki,

6 / 7