Author : Sumayya Abdulkadir (Takori Kabara) Category : Love Story
maidota ‘Yan Leman insha Allahu”.
Cike da mamaki suka ce, “To”. Suka amince lallai ba abin da ya fi karfin addu’a. Addu’ar da suke kwana da yini yi a kan dan’uwansu, yau Allah ya karba ya fara juyo musu da hankalin dan’uwansu.
Zainaba ta yi mishi murmushi, shi ma ya yi mata. Sai ta ji hawaye sun ciko idanunta. Don haka ta yi saurin kama hannuna muka fita inda motocin daukar amarya suke jira a harabar gidanmu.
[9/14, 9:59 PM] Asmau: Na ce, “Shi ba a yi masa aure ba?” Ya yi dariya, ga dukkan alamu Abdulhakim gwanin dariya ne, abin dariya bai da wuya a wajensa, ko kuma yarintar amaryar tashi ce ke ba shi dariya da sanya shi nishadi?Allah A’alam.
A yadda ya fahimta ba ta san mene ne mijin ba, baya ga abokin hira, kuma yana jin dadin hakan. Gaskiyar Hajiyarshi ne Sakinah yarinya ce danya sharaf, ba ta san komi ba sai abin da zai koyar da ita.
Ya ce, “Shi ba a yi mishi aure ba Sakinah, saboda yarinyar da yake so ya aura ba ta son shi”. Na ce,
“Ba sai ya rabu da ita ya nemo wata ba?”
Ya murmusa ya ce, “Gane min hanya dai matas, nima akwai wata wadda nake so mai kyau sunanta Farida, amma iyayenta basa sona saboda ni ba millonnaire bane. Da na hakura ba gashi Allah ya bani Sakinah ba? Wadda ta fi Farida kyau da komai?”
Na dube shi sosai na ce, “Ba wanda ya taba gaya mini haka cewa ina da kyau, sai na dauka ni bani da kyau irin na Safina”.
Ya yi murmushi ya ce, “Wace ce Safinah?’
“Safinah Yayata ce”.
Ya ce, “Kin fi Safina kyau Sakinah, duk da ban ganta ba, don dai ita babba ce, ta san yadda zata gyara kyanta, kema in kika girma za ki kara kyau fiye da wannan da kike da shi”.
Ya debo fried-rice a cokali ya ce, “Bude bakin matar Abdulhakim”. Na bude cikin murmushi ya saka min na tauna, ya lumshe ido yana kallon taunar matar shi very gently. Yana kallon wadannan kissable lips da ‘beauty point’ din da ke lotsawa ciki sosai ayayin taunarta. Ga uban gashi cunkus dunkule cikin tafkeken ribbon na larabawan usli. Wani al’amari ya soma zarya cikin wasu sassa na jikinsa da bai taba ji a rayuwarshi ba.
To amma ya yi alqawarin rainon Sakinah ne, har sai ta zama mutum kamin ya mai da ita cikakkiyar matar aure.
Ya ce, “Kin iya girki Sakinah?” Na daga kai, “Amma Mami ta ce jagwalgwalo nake yi”.
“Ke kika yi wannan girkin?”
“A’a, bani ba ce wancan kabilan da Hajiya ta kawo ne”.
Ya ce, “To daga yau in zan zo zan yi miki waya in gaya miki ki yi min duk irin jagwalgwalon da kika iya shi nake so. Bana son na Uche, kina jina?’
Na daga kai.
“Kin ga da kamin ki zo Hajiya ce take yi min da kanta, sai dai ki dinga yi a hankali kada ki kone. Ki daina kallon fadan Larabawa tunda kuke suke sa ki”.
Na girgiza kai, “Ai Abba ya gaya min Mamana tana can, shi yasa nake son su”. Ya dube ni sosai ya ce, “Wace kasa ya ce miki?”
Na ce, “A Libya”. Ya ce, “Na yi ta tunani tun dazu kan jinsin da matar Abdulhakim ta fito, ashe Sakina-ta babban tsatso ne. Na kara GIRMAMAKI, na kuma kara GIRMAMA zaben Babana. Haka na kara son sa, sannan na yi nadamar wautar da na so na yi a baya, na kuma yi alqawari Sakinah watarana zan kai ki Libya idan mun samu adires a wurin Abba......
Manzon Allah (S.A.W) yace “ku so larabawa sabida abu uku; na daya ni balarabe ne, na biyu Alqur’ani balarabe ne, na ukku harshen ‘yan Aljannah shine larabci”.
Ban san sanda na kamo hannunshi ba ina murmushi, kamin hawaye su ballo su mirgino. Ba wanda ya taba gayamin kalaman da suka farantamin a duniya irin wadannan bayan Abbana, ya kai hannu yana share min ya ce,
“Kada ki yi kuka, bana son hawayenki, tukuicin da nake so ki yi min idan na kaiki Libya shine, ki tsaya ki yi karatu, ki bani sakamakon da zan yi alfahari da ke.
Dazu Daddy ya yi min zancen makarantarki, don haka zan kai Monday don in kai ki. Sai dai ina so ki kula da kanki Sakinah, ki sani da da yanzu ba daya bane, yanzu ke babba ce tunda kina da aure.
Ba ruwanki da kawaye barkatai, ki mai da hankali kawai kan abin da ya kai ki, ki kawo min kyakkyawan sakamakon da zan ji dadi. Kina jina matar Abdul?”
Na ce, “Ina ji Mijin-Sakinah, kuma na yi alqawarin zan yi abin da ka ce”. Ya shafa gashin kaina ya ce,
“Na gode”.
Har dakina ya rakani, Ladiyo tuni ta yi barci a dakinta. Sai da ya ga kwanciyata ya ja lallausan bargo ya rufe ni, ya kashe lantarki ya bar min na gefen gado mai raunin haske.
Ya yi kamar zai sumbaci goshina, ko me ya tuna? Kuma ya fasa. Ya yi min murmushi ya ce, “Good night”. Nima murmushin na mayar masa, mai nuna jin dadi da kulawar shi.
Da baya da baya ya fita daga dakin, ya maido kofar ya rufe. Na lumshe ido barci mai dadi ya fizge ni, cike da mafarkai masu dadi, duk rabi a kan Abdulhakim din da ya kirayi kanshi da mijin Sakinah.
****
Agogon alarm da na saita shi ya tashe ni, na gabatar da sallar asubahi. Ina lazimi bisa darduma barci na dibana kadan-kadan, na ji an murda kofar an shigo.
Mijin Sakinah ya bayyana a dakin cikin farar jallabiya da carbi a hannunsa. Wani lallausan qamshi ya bakunci hancina.
Ya zo ya tsugunna a gabana, tuni barcin ya wartsake, na yi murmushi na ce, “barka da asubah an tashi lafiya?” Ya ce, “Ai ni ban yi barci ba matas sai tunaninki”.
Na rufe fuska da hijabina, ya rike gefen hijabin ya ce, “Na roke ki, ki daina yi min wannan rufe fuskar, kinga ni da ke yanzu we are one. Tashi muje kicin mu yi abin karyawa kafin Baba Ladiyo ta tashi”.
Na ce, “To, jeka waje in cire rigar baccin”. Ya ce, “To, na yi waje”. Ya fita.
Na mike na canza rigar barci na da pakistan ruwan madara, na je toilet dina da ke manne a dakin na yi brush yadda na saba na kuskure bakina da ‘listerine’, sannan na cimmashi a kicin har ya soma firar dankali.
Na ce, “Ai akwai na’urar fere dankali”. Ya ce, “To kawo”. Nan da nan ya kammala na zuba mai a ‘fryer’ na kunna. Nan da nan muka gama sassauqan karin kumallo.
Soyayyen Dankali ne chips da plantain, sai soyayyen kwai da ruwan lipton, na kwaso na kai dining yana biye dani da flask din ruwan zafi. Daga nan muka yi daki kowanne ya nufi toilet dinsa don ya yi wanka.
Cikin kayan da Hajiya ta bani matsayin lefe na zaro wata lallausar super ruwan kwaiduwar kwai da ratsin blue, na fesa turare ‘Azzaro Visit’, na taje sumata na hadeta waje daya a tsakiyar kaina. Sai ban daura dankwalin ba na kawo dan karamin gyale na nade kaina na matse da fil.
Na fito dining na zauna ke nan sai ga Mijin-Sakinah ya fito, wannan karon cikin kananan kaya, bakin wandon jeans da shirt din Armani, sai qamshi yake.
Ban taba jin wanda ke qamshin Abdulhakim ba, turarenshi na daban ne, haka komi nashi is special kamar yadda shi din ma yake na daban, da sauran al’umma dana saba gani.
Ya ja kujera kusa dani ya zauna, kafadunmu na gugar na juna. Har yanzu ban daina kallon shi ba. Ya murmusa ya ce,
“Wannan kallo haka matas?’
Na yi murmushi tareda saurin dauke ido a kanshi na ce, “Ka yi kyau ne”. Ya ce, “Allah ko matas?’ Na ce, “Allah da gaske”. Ya ce, “To ai ban kai ki ba”. Na ce, “Allah ka fini”. Ya ce, “A’a, ban da washi Sakina-ta”.
Aka danna kararrawa ya je ya bude, suka shigo tare da Abdallah. Ya ce, “Wane irin sammako ne haka Abdallah?” Ya ce, “Don ka samu abokiyar hira ni sai ka manta dani bayan ka san ni bani da kowa”.
Ya yi murmushi ya ce, “To ka yi zuciya mana? Kai ma ka samu mai tayaka hirar”. Bai ba shi amsa ba ya ce, “Amaryarmu wane delicious aka shirya mana?” Ya fadi yana bude filet din.
Mijin Sakinah ya ce, “Ci ne fa da shi uwa rumbu, yanzu in kika yi wasa sai ya tashi da dukkan abincin nan”.
Na yi murmushi na ce, “Ba zai iya cinyewa ba”. Ya ce, “To sa ido ki yi kallo”. Abdallah ya ce, “Ki dinga yin girki dani Sakinah in ina nan, gwauro sai da taimako. Don Hajiya ta hanani ta ce nima in yi zuciya in yi aure”.
Na ce, “Ai gaskiya ta fada, in wadda kake son ba ta sonka, ni ina da kanwa mai kyau zan baka”. Ya hangame baki yana mamakin inda naji wannan zancen ya dubi Abdulhakim yana girgiza kai ya ce, “A’a, Sakina bana son ‘yar kwaila, ke kanki nawa kike balle kanwarki?
Barni da Safiyyata in nan ina lallaba ta a hankali za ta so ni”. Na ce, “To Allah ya sa”. Mijin Sakina dai cin abincinshi yake bai sa mana baki ba.
Uche ya zo ya kwashe kayan ya yi kicin dasu. Inna ta fito suka gaisa suka fita tare da Abdallah. Na kaiwa Inna abincinta har dakinta na zauna muna hira.
Ta ce, “Tunda maigidan ya dawo ni ya kamata in koma ‘Yan Leman gobe insha Allahu”. Nasa mata kuka na ce, “Nima wallahi ba zan zauna ba sai dai mu tafi tare”.
Kuka nake kashirban. Ta ce, “An taba haka Sakinah? Nima nawa tsohon angon jirana yake yi, muje mu lallaba tsufanmu. Ga mijinki yaron kirki mai son mutane da girmama su, auren ke nan Sakinah, kowacce mace haka ta gada”.
Na sake tsananta kukana, “Ai ba zama zai yi ba, ya ce ran Monday in ya kaini makaranta zai koma”.
Ta ce, “To bari ya dawo sai mu yi maganar ko wata ce ba sai a samo miki ba, amma ni zamana har yaushe?”
Suna tafe cikin motar Abdulhakim, sanyin raba na ratsa su. Wani nishadi ne na musamman tattare da Abdulhakim Khalil Ribadu. Wanda dan uwansa Abdallah bai taba ganin sa cikin kwatankwacinsa ba. Abdallah ya dube shi yana murmushi ya ce,
“Yar yarinya ta ci gari ga dukkan alamu”.
Shima ya yi murmushin ya ce, “Kasar ta ci gaba daya ba garin ba. Abdallah, sai yanzu na gane son da nake yiwa Farida ba natural bane, burgewa ce da sha’awa. Ga son da nake ji har cikin kashi da bargo ba kuma don wani dalili ba, sai Allah da ya sanya mini.
Abdallah na kamu da love at first sight na yarinyar da ba ta gama sanin kanta ba balle ta san ina yi”.
Abdallah ya ce, “Nima na lura da hakan, shi yasa ake so mu zamanto masu biyayya ga iyayenmu, don ba za su taba yi mana abin da ba alheri bane a garemu. Na gode Allah da ya ganar da kai da wuri da ka zo kana dana sani wadda ba ta da amfani”.
Daidai sanda suka iso ofishin Daddy cikin federal high court, kan wasu takardu da ya ce ya debo masa don ranar ta kasance lahadi babu aiki.
Ya yi parking a inda aka tanada don adana motoci, shi kadai ya shiga ya dakko ya fito suka juya. Ya tsaya a wani kasaitaccen shago cikin wata Plaza suka shiga tare.
Sayi banza sayi wofi duk bai san dalilinsu ba, duk saboda Matar Abdulhakim. Ya yi mata shopping mai yawa da tsada, sannan suka juyo gida.
Ya tarar da ni na ci kuka na qoshi duk a kan sai Inna ta zauna da mu. Ya zauna dab da ni ya kama hannuna ya ce, “Ni ba kya son zama dani Sakinah?”
Na yi shiru ina share ido. Ya ce,
“Ki bi Inna tunda ni ba kya so na”. Ya fadi cikin alamun hushi, don lallashin karamin yaro.
Inna ta ce, “Rabu da rigimar Sakinah, tafiya ba makawa gobe zan yi ta”. Ya ce, “A samo wata su zauna tare mana”. Inna ta ce, “Sai dai uwarta Suwaiba, tunda ita maigidanta ya rasu, idan na tafi gobe ita za ta zo jibi”.
Abbana da kanshi ya zo daukar Inna, murna a wajena kamar-kamar me. Na kama shi na rungume abin da ban taba yi ba a rayuwata, saboda ban isa ba, ban kai wannan matsayin ba.
Sai yau da ya zo da kafafunshi gidan aurena, inda nake da ‘yanci. Mijin Sakinah ya cika da mamakin ganin kukan da nake saboda ganin Abbana, maimakon in yi farin ciki. Abba Ya kawo kudi masu yawa ya bani, ya kuma godewa Abdulhakim makaranta da zai mai dani.
Ya ce, “Suwaibar ma ba za ta zo ba rana ita yau daurin auren shi da ita, amma za a samo min mai aiki a can ‘Yan Leman su taho tare”. Da wannan suka lallaba ni suka tafi.
Shi ma Abdulhakim fita ya yi tare da su. Bai shigo gidan ba sai karfe tara na dare. Ina falo ina sana’ar tawa (kallon Larabawa). Ya sa ‘remote’ ya kashe, na daga ido a hankali ina kallon shi.
Ya karaso ya zauna gefena bayan ya ajiye ledojin da ke hannun shi. Ya juya min baya ya ce, “Fushi nake dake Sakinah”.
Na ce, “Ai ina son Inna ne”. Ya ce, “Ni ba kya sona?’ Na girgiza kai, “A’a, ina sonka”. Dariya ta kama shi amma ya gintse, saboda yadda na fadi, “Ina sonka”, din kadai zaka karanta tsabar kuruciyata karara. Sannan ban san wane irin so ma yake nufi ba.
Ya janyo ledodin dake gefe ya bude ya soma zaro tsala-tsalan kayan dake ciki riga da wando, siket da riga, dogayen riguna da abaya kala-kala.
Ya ce, “Duba ki gani za su yi miki daidai?” Cikin murna nake karasu a jikina ina cewa, “Sosai ma kuwa, na wane ne?”
“Na Sakinah ne, mijinta yana so ta dinga sanyasu a gida tana yi mishi kwalliya”.
Na kyalkyale da dariya na ce, “Na gode, Allah ya kara budi”.
Ya ji dadin addu’ar da na yi mishi. Ya kama tafukana ya rike cikin nasa ya ce,
“Gobe zan koma Sakinah, I will miss you so much…., ko za ki bini?’
Na ce, “Makaranta fa?’
Ya ce, “Hup! Na manta ne, in ina tare dake sai in manta komai”.
“Za ka dawo wani satin?’
Ya ce, “A’a, sai sati na sama saboda zan je Ibadan kan Shimfida wani titin jirgin kasa da zamu yi”.
Na ce, “Titi kake ginawa?”
Ya yi murmushi ya ce, “Ni magini ne Sakinah, ba abin da bana ginawa. Tun daga makarantu, jami’o’i, gidaje, ma’aikatoci da asibitoci kin gane?”
Na daga kai. Ya ce, “Nima in tambaye ki, me yasa dazu da kika ga Abba kike kuka?”
Na ce, “Saboda ban taba rungume shi bane a rayuwata sai yau”.
Ya kwanta sosai cikin kilishi ya ce, “Bani labarinki Sakinah, kin ce Mamanki tana Libya, ga Abbanki kuma a nan, basa tare ne?”
Na ce, “Basa tare, nima ban santa ba, Abba ya ce tun sanda ta yayeni ta tafi”.
Ya ce, “To wace ce ta rike ki?”
Na ce, “Mami matarsa”.
Ya ce, “Hajiya Lami ke nan qawar Hajiyata?”
Na ce, “Eh”.
Ya ce, “Bana son matar nan ban san me ya sa ba. Bana son tarayyarta da Hajiyata, tun daga lokacin da Hajiya ta sani na kaisu wani qungurmin jeji tare a Bidda”.
Na yi shiru ban ce komi ba, don ba zan iya zagin Mami a idon kowa ba. Na riga na yafewa Mami duk abin da ta yi mini, tunda dai ta rike ni da dadi ba dadi har na kawo munzalin da nake a halin yanzu.
Na soma hamma, yana magana bana jin shi sosai saboda barci da ya ci karfina. Ya mike ya miko min hannunshi na kama, har dakin barcina.
Na kwanta a gado, ya ja bargo mai laushi da taushi ya rufe ni, sannan ya dauki ‘remote’ ya rage karfin A.C
“Sleep well matar Abdulhakim……!”. Na ji shi yana fadi sama-sama. Sabida tuni barci ya ci karfina. Ya fita ya ja min kofar.
***
Washegari ma tare muka hada kalaci, sannan na shirya cikin ‘uniform’ dina. Na juya na dubi kaina a mudubi. Ni kaina na firgita da irin kyawun da na ga na yi cikin dan lokaci qalilan.
Ya fito shi ma cikin shiri na dakakkiyar baqar shadda galila, sai maiqo take. Na ce, “Mijin Sakinah ka yi kyau”.
Ya ce, “Allah Sakinah? Don baki ga naki kyan cikin uniform din nan bane”.
“Ina uniform ya ga kyau Mijin-Sakinah?”
“Yana yin kyau a jikin special people (mutane na musamman) irin Sakinah Abdulhakim”.
“A’a, Sakinah M.T Liman nake, kowa haka yake kirana a makaranta”.
Yace “tuni kika tashi daga Sakinah M.T Liman, kin dawo Sakinah Abdulhakim Khalil Ribadu”.
Sai na yi murmushi ban ce komi ba.
Muna tafe a hanya kira’ar Abdurrahman Sudais na tashi cikin (Suratul A’araf), har muka iso makarantarmu. Ya yi parking a inda aka tanada don adana motoci muka karasa ofishin principal, ya yi ta bata hakuri kan rashin zuwana makaranta na lokaci mai tsawo bana jin dadi ne, da kyar ta hakura.Ya ce dani, Daddy zai zo da kanshi ya daukeni in an tashi, daga gobe kuma akwai direba John da zai dinga kawoni yana dauko ni kullum”.
Ya kara jaddada min in kama kaina ba ruwana da kawaye, kuma kada in dinga fada musu an yi min aure, kowa ya ce me ya sa bana zuwa in ce bana jin dadi ne. Shi zai wuce Lagos sai ya dawo.
Ina yi mishi bye-bye har ya qule na daina ganin shi bai daina daga min hannu ba.
Da aka fito break muka hadu da Nadiya muka yi ta tsalle muna labarin bayan rabo. Daga bayanmu Safinah ta daka mana tsawa.Ta ce,
“Ke Sakinah yanzu fa ba daya kike da Nadiya ba da za ki biye mata kuna tsalle-tsalle. Girma ya hau ki, kada in kara ganinki kina wannan tsallen”.
Karfe biyu Daddy da kanshi ya zo ya dauke ni. Na tarar da Sabuwa mai aikin da Abba ya dauko min daga ‘Yan Leman har ta rigani isowa, muka gaisa na wuce daki don in cire kayan makaranta.
Zaman mu ni da Sabuwa gwanin sha’awa, Sabuwa mace ce mai tsafta da zafin nama, kafin in tashi barci ta rigani ta tsaftace gidan, kafin