Chapter 4 Reading Zuciar Mutum Book 1 Complete Hausa Novels By Takori .txt Arewa Novels

Zuciar Mutum Book 1 Complete Hausa Novels By Takori .txt

Author :  Sumayya Abdulkadir (Takori Kabara) Category :  Love Story

Chapter   4 / 7

9K to 12K   out of 19K words

da ya san mallakinshi ne daga dakinsu da Abdallah yana sanyawa a katuwar jaka, ya kammala ya kira Sadi mai wankin Hajiya ya soma diba yana kaiwa gidanshi. Bayan ya ba shi mukullin dakin da zai sanya su.
Ladiyo tana dakin da ya zama nata tana barci, ni kadai ce a falo kishingide a three seater, cikin doguwar riga kirar Bahrain baqa wuluk. Da ‘remote’ a hannuna ina kallon yadda sojojin Amurka ke ragargaza ‘yan’uwa musulmin Palastine da tankokin yaki. Hawaye shabe-shabe a idanuna don tausayi.


Wata sassanyar murya mara amo, wadda ke dauke da rashin kuzari ta yi sallama a falon, mamallakin gidan ya bayyana zahiri yau a gabana.
Ba sai an gaya min ba, kallo daya na yi mishi na gane shi ne dan Alkali Khalil Ribadu, kuma mijina, saboda tsabar kamannin su.


Abdulhakim ya dade a tsaye hannunshi zube cikin aljihun sassalkar farar shaddar ‘getzner’da yake sanye da ita dinkin Mohammed, yana nazarin yarinyar da aka kira, SAKINAH, kuma MATARSHI. Kallo na rahama da salama, wanda bai san yaushe kwayar idanunshi ta rikide ta ke yi ba. A zahiri kuka take, tana kallon talabijin, amma bai taba ganin wadda hawaye ya yiwa kyau irin wannan yarinya ba.


Duk wani kulli, fushi, bacin rai da ke cikin zuciyarshi sai ya ji yana bacewa. Ya ci gaba da kallon ta, kallon rahama, cikin dakikan da basu gaza biyar ba. Kafin ya yiwa kanshi mazauni a daya daga cikin kujerun da suka yiwa kayataccen falon qawanya.
Da bayan hannu nake share hawayen kamin in sauko da gwiwoyina kasa ina gaishe shi, alama ya yi min da in koma in zana bisa kujera. Allah mai juya al’amura, a take Abdulhakim ya ji nan duniya ba abin da yake so irin Sakinah.
“Ke kadai ce a gidan?”
Ya tambaya cikin kallo na. Girgiza mishi kai na yi alamar “A’a, ba ni kadai ba ce”.
“Kukan me kike yi?” Ya sake tambaya.
Da dan yatsana na nuna mishi talabijin,
“Suna ta harbin musulmi ne”.
Ya kai ganin shi ga tashar CNN ya yi murmushi, “Ni a ganina addu’a ya kamata ki tayasu ba kuka ba”.
Na sake share hawayen ba tare da na yi magana ba.
“Kin sanni?”
Ya tambayeni yana nuna kanshi da dan alinshi.
Gyada mishi kai na yi alamar, “Eh, na sanshi”.
Ya yi murmushi ya ce,
“Kin sanni ke nan Sakinah?”
Na ce, “Eh”.
“Ya ya sunana?”
Wannan karon girgiza kai na yi, wato ban sani ba.
“Ashe mace tana manta sunan mijinta?”
Ya tambaya with a low tune.
“Ba mantawa na yi ba, ban sani bane”.
Ya yi murmushi, “To daga yau in kin ganni na zo gidanki, sunana MIJIN SAKINAH”.
Da sauri na dago na dube shi, “Mijin Sakinah?” Na tambaye shi cikin sigar tambaya.
“Eh, mijin Sakinah”. Ya maimaita cikin tabbatarwa, dauke da siririn murmushi bisa siraran lebbansa.
Nima sai na yi murmushi na ce, “Wannan ba suna bane”.
“In ba suna bane mene ne?”
“Inkiya ce”.
“Ashe kina da wayo? Su Hajiya suke cewa Sakinah yarinya ce?’
Murmushi na yi, “Ni ba yarinya ba ce, ina da kannena ma Nadiya, Ilyas, Nazir da Abba, duk na girme su”.
Ya yi dariya wadda ta fiddo wasu fararen jerarrun hakora kamar kankara, ya ce, “Ina ma nine ke Sakinah, ni bani da kanne”.
Na ce, “Kai kadai ne a gidanku?”
“Ni kadai ne Sakinah”.
Na ce, “To ba gani ba an kawoni gidanku sai in zame maka kanwa”.
Ya dara sosai, kafin ya ce, “I like you girl…., zo mu kulla abota”.


Na rufe fuskata da tafukana ganin ya miko min hannunshi. Wanda ke daure da wani irin sassalqan agogo samfurin ‘swatch-blustery’. Ganin na rufe ido naki mika mishi hannun. Sai ya taso ya iso har gabana, ya kai hannunshi ya bude tafukan da na rufe fuska dasu. Na kuwa kyalkyale da dariya.
“Kin ce fa ni Yayanki ne don me za ki ji kunyata?”
Dariya ta kamani, na cigaba da kyalkyalawa sosai, bai katseni ba sai da na gama. Yana murmushi ya ce,
“Wani ya taba gaya miki kina da kyau Sakinah?’
Kamin ince komi ya miko min dan yatsanshi na mika nawa, muka sarqe su, ya ce, “Friends…?” Na gyada kai cikin murmushi.
Daidai lokacin da Inna Ladiyo ta fito daga daki ta ga mutum durqushe gaban Sakinarta ya kama hannuwanta ya cukuikuiye, ta saki salati mai razanarwa ta ce,
“Wane ne kai?”
Mikewa ya yi yana dariya ya russuna yana gaishe ta, amma ba ta amsa ba tambayar shi ta sake yi,
“Wane ne na ce?” Ya sunkuyar da kai kafin a hankali ya ce,
“Abdulhakim”.
Ta ce, “Ba sunanka na tambaya ba, cewa na yi wane ne kai? Ko kuma don kana Abdulhakim sai ka shigo gidan matar aure ka cacumi hannayenta?”
Dariya ya sake yi sosai kafin ya yi magana nayi hanzarin cewa.
“Inna shi ne MIJIN-SAKINAH”.
Ya kama baki yana mamaki, ya ce da Inna,
“To kin ji Sakinah ta hutassheni”.


Kunya ta kama Inna ta juya tana cewa, “Au maigidan ne? Ai ni fushi nake da kai tunda na zo gidan nan yau sati hudu baka kawo min kudin cefane ba”.
Ya ce, “Ki yi min uzuri Inna, bana nan ne ina wajen aiki, amma tunda gani na dawo cefane sai kin ce ya ishe ki”.
Ta koma daki ba ta kara magana ba. Aka danna kararrawa, ya isa ga kofar ya bude. Hajiya Laila da Abdallah suka bayyana a falon.
Ta kalli kowannenmu, sannan ta yi murmushi cikin jin dadin ganin fuskar Abdulhakim da walwala. Ta ce,
“Sakinah yau ga maigida ya zo, babu sauran damuwa ko?”
Na yi murmushi ban yi magana ba. Shi kuma Abdallah sai ya tintsire da dariya ganin ‘yar kwailar matar Abdulhakim.
Don haka Hajiya tana ba da baya Abdulhakim ya harare shi, “Uban me kake yiwa dariya?”
Bai ba shi amsa ba ya ce,
“Sakinah baki sanni ba ko?”
Na yi murmushi. Ya ce, “Laifin angon ki ne da bai yi introducing dina (gabatar dani) ba. I’m Abdallah Ribadu”.
Na ce, “Sannu da zuwa Abdallah”. Ya ce, “Kema sannunki da zuwa cikin family dinmu. Ga nan Abdulhakim shi ne angonki, yana ba da hakurin rashin ganinshi tun lokacin da aka kawo ki, wannan ya faru ne a dalilin ayyuka da suka sha gabansa.
Abdulhakim mai kirki ne Sakinah, ki saki jikinki cikin gidan auren ki kike. Ai kina son shi ko?” Ya fadi cikin daga gira.
Na rufe fuska da hular da ke jikin rigata, kafin in falfala da gudu in yi daki. Ina jiyo dariyar su da hirarrakin su, har aka yi kiran sallar magariba suka fita.
Karfe tara na dare na fito falo saboda in ci gaba da kallon yakin Larabawa da nake son gani. Mijin-Sakinah ne a kan dining yana cin abinci.
Ya ce, “Kawo min ruwa Sakinah”. Na nufi kicin inda firij yake, Uche (kukun gidan) ne yake wanke kwanukan da ya yi amfani dasu a sink, ya russuna yana gaisheni kamar kullum muka hadu a kicin din.
Na dauko robar ruwan FARO da lemun Squashda kofi na dora a karamin faranti, na kawowa Mijin-Sakinah.
Murmushi ya yi ya nuna min kujerar kusa da shi ya ce in zauna. Na zauna ina cewa, “Ina Abdallah?” Ya yi murmushi ya ce,
“Shi gwauro ne, yana can dakin gwauraye yana cin nasa abincin”
[9/14, 9:59 PM] Asmau: Abin ya baiwa Kawu Tasi’u dariya, har sai da ya murmusa a mamakance da abin da M.T ya yi mata a yau, ta figi waya ta yi kiran aminiyarta Hajiya Laila.


A tare dukkansu suka hada baki suka ce,
“Kin ji abin da M.T ya yi min ko?” Amma ita Lailar cewa ta yi,
“Kin ji abin da Ribadu ya yi min ko?”
Mami ta ce,
“Wai ya aurar da Sakinah”.
Hajiya Laila ta ce,
“To ai nima haka yake gaya min yanzu, wai ya karbawa Abdulhakim aure, yaron da ke cikin halin jinyar zuciyarshi a kan rasa yarinyar da yake so?”
Mami cikin tangardar harshe da matsanancin faduwar gaba ta ce,
“To ko dai Sakinah ce ya aura mishi?”
Hajiya Laila ta yi wata sassanyar ajiyar zuciya a ranta ta ce,
“Allah ya sa!”.


Amma a fili sai ta ce,
“To wa ya sani ne? Ni aikin Na-dutse ban ga yana ci kamar na dan Ikko ba. Kwata-kwata na kasa gane kan Ribadu a kwanakinnan. Idan ya yi kamar ya zo hannu sai kuma ya baude ya dinga yi min abubuwa na gadara.
Yanzu saboda Allah ya dace ya yiwa dana aure ba tare da sanina da yardata ba? Idan ke bake kika haifi Sakinah ba ai Abdul ni na haife shi”.
Mami ta ce,
“Na shiga uku ni Lami! Idan Abdulhakim ne mijin Sakinah na fadi ba nauyi, na tabbata daga Safinah har Nadiya babu wadda za ta yi sa’ar da ta yi.
Wato Sai da ya daddage ya zabo miji na nunawa sa’a, ya tsallake ‘ya’yana ya ba ta.....”. Ta rushe da kuka.


Hajiya Laila wadda ke ta hamdala a zuciyarta ta ce,
“A’a, Lami kar ki kuka, babu abin kuka a nan”.
“Ya ya ba zan yi kuka ba? Abdulhakim mijin Sakina........duk mugun burin da naci a kan yarinyar nan ya ruguza min shi, ya shammaceni, ya yi min bazata.
Ni ina tutiyar na mallake shi, ashe har yanzu gangar jikinsa na mallaka zuciyarsa na kan Sakieenah da ‘yarta. Ki taimake ni Hajiya Laila kada ki bari auren nan ya je ko ina”.
Hajiya Laila ta ce a ranta, me zai kaini yin surukuta da ke Da na ya zama M.T Liman? A fili kuma tace.
“A wane dalili? Kina tunanin idan na raba auren zai yiwu ya auri Safinah ne?”
Ta ce, “Na san ba zai yiwu ba, amma akalla duk sun rasa”.


Hajiya Laila ta yi murmushi ta ce, “In gaya miki gaskiya? Irin auren da nake so Abdulhakim ya yi ke nan, ba wannan auren da ya je nema aka hana shi ba.
Bana son Abdul da auren macen da yake so, don ni hoto zan zama, in zama kura da shan bugu gardi da amshe kudi.
Don haka na karbi Sakinah a surukata, ba ya sonta kuma ita ma ba ta san komi ba, sai abinda muka koyar da ita, don haka ki sanya ranki a inuwa.
Idan har Sakina ce surukata na karbe ta da hannu bibbiyu, ga kyau ga kyan hali.
Ga shi ta fito tsatson mutumin kwarai irin M.T Liman. Ni kuwa Laila me zan nema a suruka tagari banda wannan?”
Mami ta saki kunnuwa tana sauraron aminiyarta cike da mamaki, ta ce,
“Haka za ki min Hajiya Lailah?”


Ta ce,
“To ya kike so ayi? Don Sakinah tana ‘yar kishiyarki cewa nake ita ma ‘yar M.T Liman ce?”
Mami ta kara rikicewa da mamakin Hajiya Laila, ta kashe wayarta tana jujjuyata cike da zargin ko karya ta gaya mata? Ko kuwa mafarki take? Laila ta fi kowa sanin yadda ba ta kaunar Sakinah, amma yau ta zabi su bata a kan Sakinah.


Karfe biyar na yamma Kubra, Dije da Zainaba kannen Abba da Suwaiba ‘yar Baffa Sule, da Innarta Ladiyo suka iso Abuja a 506 din Abba da ya tura a debosu daga ‘Yan Leman. Abba ya ce ba ya son wani bidi’a, su gyara ni washegari su rakani dakin aurena, kada su damu da Mami da duk abin da zatayi bata da cikakken hankali.


Ban san abin da ke faruwa ba, ina bayan gida ina wankin kayan Mami. Nadiya ta lallabo ta rufe min idanu da hannunta ta baya, na soma kici-kicin ture hannunta ta rankwafa dai-dai kunnena ta rada min;


“Albishirinki, wai Abba ya yi miki aure, wai yau za a kai ki gidanki, ga ‘yan ‘Yan Leman can ma sun zo tafiya dake”.


Na dube ta galala! Ban damu da abin da ta ce ba na ci gaba da wankina. Ta ce, “Wallahi Sakinah da gaske nake, har goro da alawa mun ci”.


Ta waiwaya ta tabbatar ba mai kallonmu, ta kara kaskantar da murya ta ce, “Har da kudin sadakin mun gani, Mami ta watsar dasu a falo”.
Ba ta rufe baki ba Ladiyo da Zainaba suka shigo daga kofar cikin gida, ta kwasa da gudu ta yi ciki. Na cika da mamakin ganin ‘yan ‘Yan Leman yau a gidanmu, kada dai zancen Nadiya gaskiya ne???
Ba su ce min komi ba, Ladiyo ta kama jikakken hannuna suka nufi sashen baki dani, ta hada ruwan dumi cikin kwami ta yi min wanka irin wanda ba a taba yi min ba.
Ta tsefe birkitaccen kitson da ke kaina ta wanke min da ruwan kumfar wanke gashi na (Fa). Ladiyo na cewa,


“Mu a wurin mu ai har haihuwa Sakinah za ta iya yi tunda mai manyan barage ce, a haka wani sai ya ce ta yi shekaru sha biyar”.
Zainaba ta ce,
“Ni ba ina kamarta aka yi min auren ba? Me ya cini? In banda zamani da bature da ya lalata duniya ai haka ya kamata al’ummar musulmi su dinga yi don koyi da Manzo (S.A.W); $$# da zinace-zinace sun ragu, alfasha ta ragu, Allah ya yiwa Yaya Muntari arzikin duniya da lahira, ya dubi niyyarshi ta alheri ya shirya mishi zuri’arsa ya zaunar da Sakinah a dakin mijinta har abadan-abadan”.
Sai na fashe da kuka da dai na tabbatar zancen Nadiya ya tabbata gaskiya. Gidanmu za a bari dani a kaini wani gida da ban sani ba.


Duk da izayar da Mami take min daidai da rana daya ban taba tunanin in bar gidanmu ba, wai saboda wahala. Ni ina son ‘yan’uwana kamar yadda suke sona, bana fatan abin da zai rabamu.
Ladiyo ta ce, “Daina Kuka Sakinah, aure dole ne a kan duk wata diya mace. Sai in lokacin bai zo ba, idan ya zo kamar habo yake, dole sai ya zubo, wato dole sai anyi ana so ko ba’a so.
Don haka ki daina kuka, ki yi addu’ar Allah ya baki aljannar da ake samu a dalilin aure”.
Kubra na tsane min dimbin gashin kaina da tawul ta ce,
“Wannan ango ya more, gashi kamar a India, kyau kamar a birnin Omani. Allah ya sa ki yi hali irin na mahaifiyarki ba halin marikiyarki ba”.
Suka sanyani a tsakiya, Yaya Dije ta sa kakkaifar kibiya tana yarfa min kananan kitso suna ta yi min fada, duk a kan zaman aure, wanda ban taba ji ba, ban taba kawowa wai nan kusa za a yi min ba. Kallon komai da jin komai nake kamar almara.
Karfe shida daidai motocin daukar amarya suka iso. Wata daga cikin kawayen mahaifiyar ango ta kawo wasu kaya cikin (kit), ta ce su za a sanyawa amarya, lefe sai daga baya don ba lokaci basu kintsa da wuri ba”.
Zainaba ta ce, “Babu komai”. Ta karba ta bude, wani lallausar farin cotton lace ne da yarfin ruwan kasar furanni da kananan (stones), a qalla kudin shi ya kai naira dubu saba’in, a dinke, dinki na alfarma da haiba.
Sai wata laffaya ita ma ruwan kasa mai laushi da mannewa a fatar jiki. Yaya Zainaba ta sanya min da saitin Dubai da warawarai masu nauyi mahadin set din guda hudu a hannuna na dama.


Tuni na fito a Sakinah ta, na yi kyan da ban taba yi ba. Ni kaina ban san ina da kyau ba sai yau. Duk abin nan da ake Mami ba ta fito ba tana daki tana fama da kuncin rai, ta nunawa duniya adawarta dani da bakin cikinta a fili, sannan ga bakin cikin ‘yan uwan Abba sun zo sun cika mata gida.


Safinah ko ta yi nan ta yi can tana kara kawo kayan da za a yi min kwalliya. Bayan an gama shirya ni an fesheni da turaren (Avon) aka kaini falon Abbana, ya ce da su Zainaba su jira a waje yana son yin magana dani ni kadai.
Abba ya dube ni ina ta kuka cikin yadin laffaya, kuka nake haikan kamar raina zai fita. Abba bai yi magana ba har sai da shesshekar kukan ta tsaya mini na yi shiru. Ya sauko daga kujerar shi ya dawo gabana ya zauna a kan gwiwoyinsa ya ce.
“…..Sakinah ‘yar Sakina-ta, jikar Liman Tukur!”


Na yi saurin dagowa na dubi Abba domin ji na yi yana magana da wata murya mai wani irin amo tamkar ba tashi ba. Sai na ga hawaye suna gudu a kundukukin shi, yana kuma murmushi duka a lokaci daya.
Ya ce, “Yau ce rana ta biyu da zan kara dandanar wani bakin ciki da farin ciki duka a lokaci daya. Bakin cikina shi ne, zan rabu da Sakinah…. mai tuna min da Sakinah ta. A kan dole ba don na so ba, ba don ta kai munzali ba sai don hankalina da nata ya kwanta.


Farin cikina shi ne, ban kai Sakinah mugun hannu ba ko hannun da za ta tozarta ba, na kaita hannun da nake da yakinin cewa da nawa da shi duk daya ne. Ko bayan rai na.
Sakinah ki yi hakuri na yi gaggawar yi miki aure a lokacin da baki isa ba. Ban yi hakan don cutar dake ba, sai don hankalina da naki ya kwanta. Don kullum zan fita daga gidan nan cikin fargabar halin da kike ciki nake, wanda har hakan ya shafi lafiyata.
Sakina na yi duk iya kokarin da zan iya in mai da ke ga Mamanki in ba ta amanarki, amma hakan ya ci tura, don haka ne a karshe likitana ya bani shawarar in yi miki aure don hankalina ya kwanta naki ya kwanta, wanda nake fatan ni da ke mu ci ribarsa a duniya da lahira.


Na aurar da ke ga dan aminina Alkali Khaleel Ribadu. Ga nan sadakin ki”.
Ya debo kudin da Tasi’u ya tattaro a falon Mami ya danqa min cikin hannuna, ya kara da cewa.
“Ki yi abin da kike so dasu don hakkinki ne, ki zamo mace ta gari kamar mahaifiyarki Sakina. Halayenki na kwarai da na sanki dasu su zamo jagoranki a gidan aure.
Allah ya yi miki albarka Sakinah, Sakinah Allah ya yi miki albarka. Na yafe miki duniya da lahira, nima ki yafe mini rayuwar kuncin da kika rayu cikinta a gidana na kasa daukar wani mataki a kai.
Allah kadai ya san cikin halin da nake rayuwa, ina neman waraka daga gareshi, ki dinga sanya ni cikin addu’arki a duk lokacin da kika yi sallah, kin ji Sakinah?”
Na gyada kai, na fyace majina da gefen laffayar. Ya ce,
“To tashi ku je, ina kara cewa ALLAH YA YI MIKI ALBARKA!”


Yasa murya ya ce, “Zainaba!” Ta shigo da sauri. Ya ce, “To ku je sai kun dawo. A bar Inna Ladiyo ta yi sati tare da ita don ta saba ni da kaina zan

4 / 7