Author : Sumayya Abdulkadir (Takori Kabara) Category : Love Story
ga shi ban kawo komi ba sai in amshe naki?”
Na ce, “Na neman albarka ne Mami”.
Ta ce, “To, Allah ya yi miki albarka”.
Bayan fitar Mami da Hajiya na cire uniform na yi wanka na zuba riga da siket cikin kayan Mijin-Sakinah, na kunnawa gidan burner da turaren touch me. Na tadda Sabuwa a kicin tana kwashe abinci.
Na ce, “Sannu da aiki”. Ita ma ta yi murmushi ta ce, “Sannu da dawowa”.
“Yau kin yi lattin gama abincin”.
Ta ce, “Gas ne ya kare, amma akwai electric da shi na yi, kin san kuma ba shi da sauri”.
Muna haka Sadi ya soma shigo da jakunkuna manya-manya. Fitowar nan da zan yi na yi ido hudu da Abdulhakim a falon yana zaune yana amsa waya, ya mike dogayen kafafunshi sumul-sumul dasu a kan kilishi ya jingina da throw pillow.
Fitowata ina murmushi bai sa shi ya daina wayar da yake yi ba. Na muttsike idona na tabbatar shi ne ba gizo idanuwana ke min ba.
Ya kara wani irin kyau mai sanyin gani a ido, fatar jikinshi da sajenshi sunyi sumul sun kwanta sunyi lumm sai sheki suke, wani lallausar qamshi na tashi a falon wanda ban taba jin qamshi mai dadinsa ba.
Da gudu na karasa gabanshi na zube daidai kafafunshi ina dariya. Ni kaina na rasa dalilin da yasa yau ban fada jikin shi ba kamar yadda na saba. Ya rufe wayar ya cillata kan kujera yana murmushi, “….This is not the kind of welcome I like....”
Ya bude min dukkan hannuwanshi, na fada ciki a hankali, ya rungume ni yana rada min cikin kunnuwana cewa, “….Sakinah na yi kewarki!”
Yinin ranar zungur, Abdulhakim ko masallaci bai je ba, duk inda ya yi ina naniqe da shi don tsoron, kada ya sake gudu ya barni.
Yana tambaya ta abubuwan da suka faru a bayanshi. Ya ce in dauko result ya gani. Jiki babu kwari na dauko na kawo mishi.
Ya karba ya duba, ya qura min ido cike da fushi ya ce,
“Alqawarin mu dake ke nan Sakinah?”
Na girgiza kai na sunkuyar da kaina. Ya ce, “Tunda haka ne tsarabar da na kawo miki na fasa baki su Nadiya zan aikawa, sannan kawo hannun ki maza mu kwance abotar tamu, daga yau bana yi da ke”.
Na soma sharar hawaye ina cewa, “Ka yi hakuri ABDULHAKIM ba zan kuma ba”.
Ya yi mamakin kiran sunanshi da na yi a yau, don ban taba yi ba. Ya ce, “To gaya min dalilin da ya sa ba kya mai da hankali a karatu”.
Na sunkuyar da kaina naki amsawa, ya cigaba da nacin tambaya da kyar na iya na ce,
“Tunaninka nake yi”.
Ba karamin mamaki ya yi ba. Ya ce, “Kuma don kina tunanin mijinki sai ki ki yin karatu? Ba kya tunanin nima karatun nake yi? Nima ai ina tunaninki, amma bana bari ya hanani ci gaba, ya hana min yin karatun da zai amfane ni.
Wannan shi ne kashedi na karshe, idan kika kara dauko sama da goma idan na tafi ba zan sake zuwa ganinki ba sai na gama duka. Ki yi ta tunanin nawa in kinga tunanin shi ya fi dacewa dake”.
Ya cillar da report din ya mike ya nufi shower.
Ganin yau Mijin-Sakinah ya yi fushi dani, duk sai na ji babu dadi, hankalina ya tashi. Yana fitowa na kama kafafunshi hawayena na diga akan tafukansa, na ce,
“Don Allah ka yi hakuri bazan sake ba”.
Muryarshi tayi sanyi. Ya ce, “Ni kam me kika yi min da za ki bani hakuri? Iyakaci in kin ki yin karatu in auro mai karatu wadda za ta koyar da ‘ya’yana karatu, ba wadda za ta koya musu tunanin miji ba.....”
Na kara tsananta kukana na ce, “Don Allah kada ka auro kowa wallahi ba zan sake ba”.
Ya juya baya yana dariya amma ya gintse, “Saboda me ba kya son a auro wata? Bayan hudu Allah ya ce in yi?”
Na ce, “Ni dai bana so, don Allah ka bari”.
Ya ce, “Ai ba zan bari ba, idan ba za ki yi karatu ba ni kuma ba zan fasa aure ba”.
Don haka wannan zangon bayan komawar Abdulhakim na nade hannun riga da kafar wando na durfafi karatu ba ji ba gani, na bokon ne ko na Islamiyyar.
Kuma kwalliya ta biya kudin sabulu na dauko na bakwai a ajinmu. Da Abdulhakim ya zo goyona ne kawai bai yi ba, don ya nuna min farin cikinshi.Har Daddy ma ya yi murna ya kuma sa min albarka.
***
Shekara kwana ga mai yawan rai, a yau muka samu hutu wanda daga shi in mun dawo zamu shiga aji daya na babbar sakandire.
Abdulhakim ya gama course din shi a Beirut ya kuma samu qarin girma a ‘Julius Berger’. Yana daga cikin ma’aikatansu da suke ji dasu saboda fasahar da Allah ya ba shi.
Idan ya tsara gini, ko bature albarka. Sai dai kokarin da yake na samun ‘transfer’ zuwa nan Abuja har yanzu bai samu ba.
Shekaru biyu ke nan da aurenmu, wadanda suka yi daidai da cikata shekaru goma sha hudu a duniya. Zuwa lokacin na fara sanin kaina, na kuma fara sanin wane ne mijina Abdulhakim Khalil Ribadu?
Dogo ne, ba shi da kauri sosai, kuma ba ya da rama. Wankan tarwada mai mikaqqen hanci, mai yawan sumar kai, ma’abocin yalwar fararen idanu masu sheki (oily eyes).
Duk inda ake neman mutum ma’abocin kwarjini da kamala za a sanya Mijin-Sakinah a ciki. Babban abin da ke burge mutane dashi shi ne halayensa masu nagarta.
Mijin-Sakina yana da saukin kai, sannan abin hannunshi bai rufe mai ido ba, kullum bayarwa yake, kuma kullum kara samu yake.Kin san dai ma’aikatan ‘Julius Berger’. Cikin shekaru biyu kacal da aurenmu Abdulhakim ya ce ya ga alhairori da budi kala-kala wanda yake da tabbacin falalar biyayya ga iyaye ne.
Don haka yake kara rike ni Sakinah da amana da soyayya ta gaskiya, wadda bai taba tunanin zai yiwa wata diya mace ba.
Har kuma inda yau ke motsi, bai taba daura min lalurar aure ba. Duk da hakuri yake yi, yana kuma tunanin Sakinah is too young....... har gobe ya dora mata bukatar auratayya.
Rainona kawai yake tare da koya min soyayyarsa, don haka yake yawan yin azumin tadauwa’i, wanda ni ban san dalilinsa ba. Illa duk ranar da ya ce yana azumi, in ce azumin me kake? Ya ce na neman lada man Sakinah!”.
Zan numfasa, muje ga littafi na 2, wanda tare yake da dan uwansa, maman Safah da Marwah ce……