Author : AYSHA ALKALI Category : Taskar Novels
godiya kowane hali kika tsinci kankin.*
*"INA SONKA ZAUJI" takara rungeme kayan ta kamar za'a kwace mata shi. *
*"Wayyo Ummi zata karya maki yaro batare da kinga jikokin kiba" dukan kirjinshi take cikin
Shagwaba "Nika daina ba yanzu zan haihu ba haka kawaii nayi ciki ni wlh kunya nakeji. mey
zan gayama abaya gaskiya ni za'ayi abin kunya dani ba".*
*Takare maganar tana masa dukan wasa cikin Shagwabar da tazama mata jiki dan ynx har
tasaba da rigimar mijin nata. *
*Da sauri yadago kanshi ya kalleta* *"Waike mey kike nufi? *
*Bazaki haihu dani ba?"*
*Cikin sauri ta rufe masa baki da hannunta "Karka yimin haka kadaina bari wannan tunanin na
tasiri a zuciyarka kadaina wannan tunanin dan Allah "*
*Ta maganar ta kamar zatayi kuka," In ba haka ba mey kike nufi bayan bakya bari nayi" yafada
kamar maraya, Nifa karka sauyamin magana tafada tana juyadda kanta gefe dan wani lokachin
'Faheem' na bata kunya, "ke wai duk wannan kunyar ta mecece wane dare ne jemage bai gani
ba eyeee?" *
* Ita dai komai bata ce dashi ba, kara matsawa yayi jikinta "in har da gaske kike yau inaso
ki tabbatar min da soyayyar ki agareni. *
*kishayar dani har saina daina numfashi kema ki rama abinda nayi miki kinga anyi 1-1"
yakarasa maganar yana kallon fuskarta yaji mey zatace. *
* budan bakin ta tace "ni dama ban rike ka arainaba tun ranan na yafe maka sbd babu
komai, wlh na yafe maka mijina" tafada sbd tasamu ta waske dan har ynx tsoron shi takeji*
*Dariyar da Faheem keson dannewa ne ta kucce masa ai ko dariya kawaii yake mata, ita dai
Kala batace dashi ba saida ya gama dariyar sa sannan yace *
* "kekam bansan wace iri ceh ba ke inkowa yanason ya faranta ma mijinshi ke banda ke,
sai iyayi ga tsiwa da bakin surutu amma sai shegen tsoro kamar farar kura. *
*Ita dai Faheema bata ce mishi Komai ba sbd taga so yake ya kadata itako bata shirya ba
gaskiya *
https://chat.whatsapp.com/DPpBhXyzIVKLbDQwVsQJXzhttps://chat.whatsapp.com/DPpBhXyzI
VKLbDQwVsQJXz
♥︎☆*YARINYAR RUWA*☆♥︎
✦ *Water girl*✦
*✦~N̶A̶
AYSHA ALKALI
page 53&54
__________Faheem haka yagama shirmen shi yadda Faheema ta fada. dan nidai ba ruwana
bana shiga tsakanin ma'aurata
Haka suka cigaba da rayuwar'su gwanin burgewa Faheema na biye mashi susha
soyayyar'su ko kadan Fahema bata taba kaurace masa a bed ba koda kuwa sunyi fada neh
hasalima koda sunyi fada dare nayi zasu shirya sbd sun saba ma kansu da kwanciya tare da
junan su.
*Bangaren Abaya da Khalil*
Haka ta hakura ta dau maganar papa wanda yake matsayin mahaifi agurinta.
Kwana biyu Khalil yafara rage shirmen da yake sukan zauna da Abaya suyi fira amma bai
taba kokarin kusantar'taba , ita kam wannan ba karamin dadi yake mata ba ,koba komai zata
huta .
Faheema na bukatar sanin halin da Papa da Abaya suke ciki saidai Faheem bazai
bartaba sbd haramun ne a addini duba ko tsafi ,haka ta fawwalawa allah komai tana addu'a
allah yasa Abaya da Khalil su sasanta koba komai zatayi farin ciki .
Faheem ne ya dawo agajiye leda ceh hannun'shi jifah da ita kawai yayi da ita shi kuma
ya fada kan kujera ya kwanta, Faheema da ke toilet bata san da dawowar'shi ba ,tun yana saka
ran zata fito har ya tashi ya wuce bedroom din kai tsaye, koda ya shiga tana ciki bata fito ba
dama Faheema gwanar zama toilet ce shi kanshi yana mamakin wannan zaman toilet din ko
gajiya batayi mutum yayi ta jiran'ta .
Wanke kanta tayi tayi wanka ta dauro alwala, fitowa tayi da towel a kirji dan bazata iya
maida kayan da ta cire ba () kasancewar tasan ba kowa a gidan kuma tasan lokacin
dawowar'su baiyiba , tana kawowa tsakiyar dakin ta kunce towel din tana sharce gashin kanta .
Ido ya waro sbd tunda sukayi aure bata taba bari ya ganta ba kayaba ko wanka suka shiga
saita shige mashi jiki amma sai gashi yau ya gani a bazata .
Cigaba tayi da harkar gaban'ta dan batasan sa wani Faheem ba , takawa tayi zuwa gaban
mirror ta shafa mai , koda ta karasa bata tsaya kallon mirror ba man'ta kawai take shafawa cikin
nishadi dan ba wani abu dayake damunta ba .
Iya kunnuwa oga Faheem ya kunnu amma ko `kwakkwaran motsi bazai iyaba sbd ji yaje kamar
shocking ne aka jorna masa jikin shi gaba daya ya daina aiki idon shi kawai ke aikin kallon
wannan baiwar allah .
Saida ta gama shafe-shafen'ta sannan ta juyo da niyar daukar towel din'ta .
*Ihuuu* !
Tayi wanda sanadin wannan ihun ne yasa hankalin Faheem dawowa jikin'shi ,kamar mara
gaskiya haka ya kama jujjuya idanu dan wlh baisan mey zaiyi a halin ynx ba .
Da sauri Faheema taja towel dinta ta daura duk da ko bayan'ta bai rufe ba .
*"Wai yaushe ka dawo*
*Meyasa baka gayamin ba*
*Kuma bakayi sallamaba"*
Kallon'ta Faheem yayi sai yanzu ya dawo dai-dai sannan yasamu damar yimata magana.
*"Iyee tambaya'ta ma kike nida gidana kuma da matata har kike tambaya'ta"*
*"Amma ai kasan ba kyau ganin mutum ba kaya"*
Matsowa yayi kusa da ita hannu yasa kan towel din, saurin rike hannun nashi tayi *"uhm uhm
uhm nidai dan allah ka daina banaso"* tafada kamar zatayi masa kuka, *"tau shikenan"*ya fada
ranshi a mugun bace ya sake mata towel din ya juya ya fice dakin duk da wannan wutar
sha'awar dake ruruwa a idanun'shi .
Tsaye tayi tana tunani "wai yana nufin fushi yayi na shiga uku" ta fada cikin tashi hankali, sauri
take ta karasa shirin'ta a gaggauce ta ida saka doguwar rigar ta bedroom sliipers dinta tasaka
ta fice zuwa parlor ,koda ta karasa bata ganshiba zama tayi tana tunanin mey yasa Faheem
fushi da ita har haka , ina ma zaije yanzun'nan,tambayar da.take ma kanta kenan .
Yana fita daga gidan bakin ruwa yaje ya zauna shidai ya nason mace wacce komai yace ya
naso ya gani ajikinta zata bari sbd halal disshi ce kuma in bai ganta yaji dadi ba wazaije ya gani
amma Faheema abinta yayi yawa tunda sukayi aure taki sakewa dashi yadda ya kamata baisan
dalili ba allah yasan shidai ya nason macen'da tasan sirrin kula da miji duk da ba laifi ko ita
tana bashi hadin kai amma wani lokacin kamar raping din'ta yayi, kwata-kwata Faheema
batada juriya kuma batada wayo.
Magana yake shi kadai kamar wani *MAJANUNI na binta umar * my favorite book allah ya kara
basira kawata
*Hmmm fans shin kunkaranci yar wanke wanke na oum sultan*
*Shin kin karanci kanwar maza na ayushercool*
*Shin kin karanci sarauniyar kyau na the nanarh kd*
*Nace shin kin karanci sawun giwa na Realesha*
*Ga wani Rainon sojah na aunty ayshat (maman teddy)*
*Ga wani kayataccen littafi wato *
*Maza biyu na slimzy*
*Nida ruhiey na Oum afreen*
maza ku karzaya domin samun wadannan littafan, nasan zasuyi daidai da ra'ayinku .
Kadan daga cikin daddadan littafanmmu
*Comment and share pls*♥︎☆YARINYAR RUWA☆♥︎
✦~Water girl ~✦
Page 55&56
A haka Faheem ya karasa yinin shi a bakin ruwa, Faheema taci kukanta ta koshi tana zaune
tana tunani a ranta "gaskiya ban kyauta ba amma ya zanyi ina jin kunyar'sa sosai har yanzu"
*wata zuciya take cemata ai gwara kiji kunyar'sa kar yace bakida kunya*
Ita kuma dayar cewa take *Menene najin kunya bayan da aurenku mijin'kine shidin
halalinki ne kema halal ceh a gurinsa to mey naji kunya, infa baki saki jikin'ki ga mijin'ki ba zaije
ne yana kallon matan waje bari ganin yana sonki indai bakya mashi abinda ya keso
hankalin'shi da zuciyar'shi zasu karka'ta izuwa ga wata macen gara ki zage dantse ki faranta
masa nidai shawara kenan.*
Tunani sosai Faheema keyi sbd bai taba Fushi da ita har haka ba gaskiya da sake.
Haka ta cigaba da sakawa da kuncewa, ahaka har bacci barawo ya fara sace ta gashi tanajin
yunwa kuma tasan yanzu duk inda Faheem yake ya najin yunwa sosai sbd baya dadewa bai
ciba sam Faheem baya wasa da cikin'sa sai gashi yau a sanadin Faheema ya kasa cin komai
sai faman tunani.
Saida ya gama zantukanshi na banza sannan ya dawo gida koda ya shiga parlon ya ganta
zaune ta aza kanta kan 3siter ta aza kanta jikinta na kasa da gani kasan kwanciyar bata mata
dadi ba ga wannan dan karamin bakin nata ta turo gaba daga gani saida ta gama mita sannan
ta kwanta daga gani ta sha kuka sbd fuskar'ta duk ta kunbura tayi ja abu ga fararen mata
Karasawa yayi ya dagata ya azata akan kujerar ya je bedroom ya dauko bedsheet ya lullube
mata jikin'ta, so yake yaje yayi wanka yayi sallah dan yasan itama bataci komai ba.
Haka akayi Faheem yaje yayi alwala yayi sallah sannan ya dawo parlon ,kitchen ya dafa musu
indomie da kwai ya juye a plate yasa spoon biyu ya dauko musu ruwa ya kashe komai sannan
ya rufe kicthen din ya fito .
Koda ya dawo har ta farka kuma taga alamar ya dawo jin motsin tahowar'shi yasa ta kara
tabbatar da shine , shiru tayi tana kallon kasa tana wasa da yan yatsun hannun'ta.
Komi baice mata ba ya aje plate din shima ya zauna hannun rigar'shi ya hau gyarawa batare
da yace mata komai ba , Faheema ganin baice tazo suci ba yasa tayi zuciya ta...........
Wannan page din bashida yawa sbd yakusa karewa
*Hmmm ina fan's din Faheema ku canka mey zatayi anan zata zauna ne ko tafiyar'ta zatayi
inajiran comment dinku*
*Ina masoyana masoyan yarinyar ruwa ku marmatso domin gab nake da yanke muku jin
dadin'ku*
*wayyo allah yarinyar ruwa yana gab da karewa Duk wacce take bukatar document dinshi
tamun magana sbd 1&2 neh*
*Comment and share*
*YARINYAR RUWA*
*Water girl*
*Na Aishaalkali*
*Page 57&58*
______zuciya Faheema tayi ta ta so zuwa kusa dashi ta zauna tana kallon fuskar'shi , turo
masa baki tayi tace "nima fah yunwa nakeji" ta fada sbd kawai ya tanka mata amma yayi mata
shuru, haushi ne yakama Faheema kamar ta tashi ta bashi wuri amma bataso su kwana suna
fada da juna duk ma yadda zatayi sai tayi sbd su shirya.
Spoon dinda yake hannun'shi ta kwace da sauri ya dago kanshi ya kalleta amma kala baice
mataba, har taji dadi zai kulata kuma sai taga ya girgiza kanshi yaci gaba da cin abincin shi da
hannun'shi.
*BANGAREN ABAYA DA KHALIL*
Tana samun kulawa sosai a gurin Khalil sbd ynx har wasa suke tsakanin su yana shiga
sashin'ta suyi fira yayi ficewarsa duk wannan abun dake faruwa fauza batada masaniya,
sarauniya tana nan kan kokarin ta na samun wannan ikon so take ta mulki wannan masarautar
koda bala'i ne.
Khalil ne zaune kan bed dinshi yana tunani shi kadai "waini yanzu zanyi wata biyar carrr batare
da mace akusa dani ba to kodai banida lpy" haka ya keta tunani shi kadai amma taya zan gane
wata zuciyar ce tace masa ba kanada mata ba ka gwada je mata ka gani, daga karshe dai
malam Khalil ya yadda da shawar wannan zuciyar tashi.
Kai tsaye part din Abaya, yaje koda ya isa yaci sa'a ba kowa haka ya karasa ciki bayan ya shiga
ya samu kanshi da rufe kofar parlon, koda ya karasa uwar dakar baiganta ciki ba "Ina taje neh"
yake tambayar kanshi, karar ruwan'da yaji ne yabashi tabbacin tana wanka ne, yana nan zaune
har ta fito.
Bata kula dashiba ji kawai tayi anyi hugging dinta ta baya tasan ynx duk duniya daga ita sai
Khalil ke shigowa wannan gurin shiyasa bata wani damuba "Kamar akwai wani abu mey yake
faruwa" ta fada tanaso ta juyo amma yaki bata wannan damar, cikin rauni dan shi a tunanin shi
bashida lpy ne, Abaya banida lafiya ya fada kamar zaiyi kuka.
Mamaki ne ya kusa kashe Abaya cikin dimaucewa da sarkakakiyar murya take fadin? Ya akayi
kasani, waya gayamaka niba Faheema bace? Ajiyar zuciya yayi yace "Papa ne ya gayamin
komai tun kafin ya gayamiki ya gayamin ke ba Faheema bace" "amma kasani ka zauna dani a
matsayin Faheema"? dariya Khalil yayi yasa hannun'shi ya rufe mata baki "Abaya dama ke
allah ya kaddari matata ceh bantaba son Faheema ba, Dama can Koda nake ikirarin Inason
Faheema Wlh bana cikin hayyacina, Abaya nasan komai gameda abubuwan da ke faruwa
sannan inaso na miki albishir da kaso 96% acikin wannan masarautar sun musulunta ciki kuwa
har dani" Abaya bata san sadda ta fadi kasa ba sujjadar shukur tayima ubangiji mai jin kukan
bawa sbd sai ynx ta gane hikimar da ke tattare da sadaukarwa da kuma fawwalama allah
subhanahu wata'ala lamarinka lalle wannan ya nuna mata cewa a rayuwa ka kasance mai
shuka alkhairi koda kuwa anzaluncekane.
Kuka take sosai tana godewa Allah, Khalil ne ya matso kusa da ita ya dagota yana sakar mata
da murmushin'shi mai sanya zuciya sanyi.
Jikin'shi ta shige tana sunsunar jikin'shi, dariya ce ta kucce masa "wai wannan kishin baiyi
yawaba na lura duk Sanda muka hadu saikin yi wannan" ya karasa yana murmushi sbd Abaya
na burgeshi ko Don wannan kishi nata salon na daban neh.
Salon soyayyar ne ya sauya dan oga Khalil ya wuce sanina da Haka na rufe masu kofa Bayan
na fito sbd koroni sukayi wai kar in tona musu asiri a gurinku readers sai hakuri fah
Haka Abaya da Khalil suke rayuwar su cikin jin dadi basuda wata matsala dan Khalil na ankare
da tukun shi gurin magaifiyar'shi Papa ma yana saka ido Sosai kuma ya dage gurin ganin ya
canjama sauran al'ummarsa ra'ayi sbd su shiga addinin musulunci kuma ba laifi Ana dacewa
kunsan sai wanda Allah ya nufi ya nada rabon shiryuwa wannan kenan daga BANGAREN
Khalil da Abaya .
*Mu hadu a next page muji ya wannan fadan na tsakanin Faheem da Faheema zai kasance
Shin zasu shirya ko kuwa*
TAKU HAR KULLUM @aysha Alkali ✍️
*YARINYAR RUWA*
*WATER GIRL*
*NA AISHAALKALI*
*PAGE 59&60*
____________Haka su Faheema suka cigaba da zaman kurame, Faheema ce ke tura masa
baki a tunanin ta baya kallonta batasan idon shi na kanta Tun dazu.
Hannun'sa da yasa yana cin abincin sbd Faheema ta karbe spoon din, yana saka
hannun'sa yaji saukar spoon akai, da ganga ta soka masa shi, dago da idanunshi yayi ya kalleta
tana jiran jin mey zai cemata amma shuru sai ma kara gyara zaman sa, bawai baiji ciwo ba da
sani ya kyaleta dan yasan sbd yayi magana shine ta mishi wannan aika-aikar.
Tana tsaka da tunani batasan lokachin da ya tashi ya shige ciki ba, yana tashi kai
tsaye bedroom dinsu ya wuce, toilet ya wuce yayi wankan shi.
koda Faheema ta dawo daga duniyar tunanin da ta lula ba Faheem ba alamar'sa "wai
ynx sai ya tafi ya barni" ta fada tare da mikewa tayi hanya dakin dan tasan bazai wuce can ba.
Koda ta shiga ya fito hannun'sa rike da towel dinsa ya daura towel dinta a kugun'shi, Kallon
sama da kasa ta masa "Lalle na tabbata wannan mutumin yama raina min da wayo yana ikirarin
yana fushi dani kuma ya daukar mun da towel hadda daurawa" ita kadai ke wannan surutun
dan yama wuce gurin mirror batare da tasani ba.
Aiko tana dawowa duniyar tunani naga ta sake wani lallausan murmushi bansan mey Faheema
ke shiryawa ba naga ta nufi Faheem dake kallonta ta cikin mirror "To wai wannan mey take
shirin yi neh" ya tambayi kansa kafin ya samu amsa yaji Faheema