Author : AYSHA ALKALI Category : Taskar Novels
taja towel dinta dake
kugun'shi nan take towel ya fado kasa waro idanu oga yayi yana kallonta.
"To mey take nufi dani ne ni ta hanani ganinta ita gata sarkin wayo ta budeni "
Ya Ida maganar yana kokarin daukar towel din da sauri Faheema ta janye wannan towel din,
allah ya sani a mugun tsorace take da Faheem amma tanaso su shirya dole tayi haka.
Ganin iya shege Faheema ke son yi masa kuma gashi ta kasa komai yasa ya matso kusa da ita
aiko sai aikin matsawa baya take a haka har suka kai karshen dakin don daga nan sai bango.
"Dole saikinsa na miki abinda bansoba koh"? ya fada yana hura mata iskar bakinshi a wuyanta,
saurin girgiza masa kai tayi tace "Dan allah kayi hakuri" "Hakurin mey kike bani na kunce min
towel ko na hanani halal dina da kikayi wane daga ciki"?
"Uhmm Uhm Uhm dama dama" haka ta kama magana rabi da rabi "Uhm mey menene abinda
kikeso ne zan maki bake kika kunce da Kanki ba shine nake tunanin ko haqqin ki kikeso na
baki"
Cikin aro jarumta Faheema ta bude idanunta aiko sai cikin nasa haka suka fara Kallon juna har
na wani lokachin Faheema ceh ta hura masa iska a fuskarshi "To menene dan mace ta tambayi
mijinta haqqinta ko haramun neh"?.
Faheem ne sake da baki yana Kallon wai Faheemar sace ke wannan maganar yaji dadi sosai
amma bai nuna mataba don so yake saita gane kuskurenta," Tau naji jeki shirya Kizo na baki
haqqin'ki".
Saida gabanta ya fadi dan tasan halin Faheem allah ne kadai yau zai kwaceta a hannunshi,
Haka ta maze bata nuna masa tsoro ba, juyawa tayi ta wuce toilet kai tsaye, Faheem kuwa
murna fall cikin shi.
Mai ya shafa ya dauko kayan baccin shi ya saka yana zaune ta fito jin shuru bata karasoba
yasa ya daga kansa ya kalli inda yake tunanin take.
Mamaki ne ya cikashi ganin Faheema da towel kuma duk ta tankwaheshi ya dage sama sosai
dan da kadan ya rufe mata bayanta.
*Wannan kenan saiku biyomu a next page comments and share*
* ____________YARINYAR RUWA
________✍️___________________________________________ water
girl________________❤️_________________________ *
Daga alkalamin
AYSHA ALKALI
# YARINYAR RUWA
*WATER GIRL*
*AISHAALKALI*
*PAGE 61&2*
paging karshe
Ido kawai Faheem ya zuba yana kallon ikon allah, karasowa tayi tana mashi Kallon yane
shidai Faheem mutuwar tsaye yayi ga baki bairufuwa haka yake mata Kallon kurillah, Faheema
ansamu abinda akeso sai wani iyayi ake Ana karairaya.
Tsaye Ogan nata ya mike ya mika mata hannu alamun tazo gareshi, "baby bari na shirya" ta
fada tana wucewa gurin mirror ta zauna, ai Ogan naku kasa hakura yayi saida ya cimmata,
daga ta yayi gaban mirror ya maidata bakin bed ya zaunar da ita, ita Kam mey zatayi banda
Kallonshi tana mai kara godema Allah daya bata Faheem a matsayin abokin rayuwarta.
Daga zaunen da suke Ogan nata ya cigaba da sarrafa abarsa ganin haka yasa na tattara kayan
rubutuna nayo gaba
Bangaren su Abaya
Sosai Khalil yake kula da Abaya yana nuna mata soyayya Sosai saidai mutuniyar taku haka
take kamar inji sbd bata taba gajiya da Khalil komai jarabarsa saida yaga tashi karama ceh
amma Abaya najin jiki sosai a hannunshi hakan baisa ta taba ce mishi Aa.
Sarauniya Fauna ceh tsaye gaban Papa tana huci tana kari "Ni zaka mamaya ka Jaye dana
daga gareni karabani da Komai Wlh bazai taba yuyuwa'ba" ta karasa tana buga kasa" nayi
maka alkawarin tarwatsa iyalanka baki daya har Khalil bazan taba ragama tunda har yaci
amana'ta ".
Sarki ne wato Papa yayi gyaran murya sbd mutanen fadar da Jama'r gari kowa ya hallara a
gurin, ji kake guri yayi tsit kamar anyi ruwa an dauke, wazirin'shi shi ne ya fara jawabi kamar
haka " Assalamu Alaikum "suka amsa ji kake guri ya kirmitse gurin amsa sallamar sbd kowa so
yake yasamu wannan Rahama.
" Kamar yadda kuka Sani a wannan masarautar Bayan gane addinin gaskiya munbar amfani da
wasu tsafuka da da can muka dogara dasu, to a wannan taron bana kowa bane saina
Sarauniya Fauza" ya karasa zancen yana nuna ta inda take daure ga wata gina, "wannan
baiwar Allah ta cutar da Sarki sosai tayi kisa kuma hukuncin kashe rai shima a kasheshi, itace
ta kashe tsohon mijinta wato mahaifi fa Khalil bata tsayanan ba saida taga bayan Sarauniyar
mu wacce kowa yasan ta dason yin adalci a cikin al'ummarta, Wannan Dalilin ne yasa zamu
ratayeta taje can ta hadu da ubangijin ta.
Khalil ba kadan zuciyar shi ta karye koba komai uwa uwace amma baiyi dacan uwaba, Abaya
ce ke rarrashinshi dan bazai iya kallon Ana rataye mahaifiya Shiba, barin gurin sukayi gaba
daya, shidai Sarki har aka gama shirye shiryen rataye Fauza baice Komai ba.
Da akazo ratayeta ba yanda ba'ayi da ita kan ta karbi kalmar shahada amma fafur takiya, Haka
aka ratayeta tana kahira.
Sosai Abaya ke rarrashinshi sarki ne ya aika ake masa Khalil jiki ba kwari yaje gurin Sarki nan
dai shima yayi ta aikin rarrashinshi shi abin ma saida ya tashi bashi dariya, cikin haka Khalil ya
hakura ya cigaba da yimata addu'a , Koda ya koma ya isko Abaya ta fito daga ita sai towel a
kugu, karasowa ya rungumeta ta baya nan salon soyayyar ya sauya nima na fito na basu guri
sbd su sake.
Awannan daren su Faheem ba karamar soyayya suka kwasaba, Haka rayuwa take tafiya cikin
farin ciki da kaunar junansu Ana haka Faheema ta fara rashin lpy alamar ciki duk ta bayyana
agurinta hakan yasa yake shirin komawarsu masarauta sbd lokachin yayi.
Faheema na kwance Dan ynx batada aiki sai kwanciya "wai baby shirin mey kake haka"
"Wani gurin zamuje Karki damu yi kwanciyarki " ita Kam meye nata a ciki aiko nan da nan bacci
yayi awon gaba da ita bata samu ta farkaba, yana gama hada kayan su jirgin su na isowa duk
wasu abubuwan amfani saida ya tabbata ya kashesu sannan ya dau Faheema kamar karamar
Yarinya Har zuwa cikin jirgin Bama tasan anayi ba, average yayi sannan ya Koma ya Ida kwaso
sauran kayan ya dawo cikin jirgin.
Surutu ne ya farkar da ita Koda ta bude idonta da mahaifiyar Faheem ta fara cin karo sai Abaya
rufe idanun tayi Dan tunanin mafarki take to in ma mafarki nake mey ya kawo Ummie Innalillahi
haka take ta maimaitawa.
Faheem ne ya taba mata fuska ta bude idanunta "ki tashi zaune" aiko tana tashi nan ta fara
kallon su daya Bayan daya "wai da gaske" ta fada a fili Papa ne ya matso ya na kallon yar tashi
cikin so da kauna.
Abaya da khalil ne suka matso kowansu da abinda yake gaya mata dan Faheem ya mata
bayanin Komai a Haka dai Wannan Family ke ta farin ciki mahaifin Faheem mahaifiyarshi da
kuma kaninshi Fahad sai murna suke.
Tammat bi hamdullah
Kuskuren dake ciki allah ya yafemin Amin nan na kawo karshen YARINYAR RUWA
ALHAMDULILAH ✍️✍️✍️
INA MASOYANA INA MAI FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA SABON LITTAFINA YANA NAN
ZUWA MUKU BADA DADEWA KUDAI KU KASANCE DANI AYSHA ALKALI NA MARABA DA
MASOYANTA NAGODE