Chapter 10 Reading YAR IYA (Mai Hannun barna) BOOK 1 BY DIAMOND LADY.pdf Arewa Novels

YAR IYA (Mai Hannun barna) BOOK 1 BY DIAMOND LADY.pdf

Author :  DIAMOND LADY Category :  Taskar Novels

Chapter   10 / 16

27K to 30K   out of 46.7K words

faɗa maka yanzu polisawa takwas ne a karye, shida ƙafafuwan su biyu kuma
hannu da ƙafa” ya faɗa cike da ƙosawa da jin zancen.

Principal da yabi ya ɗimauce, rasa abun faɗa yayi sai kawai yayi shiru.
“Ohk ba zaka ce komai ba Misbahu, lemme hang off the call” ya faɗa cikin hasala.
“Aaah ehma sir mamaki kawai nake yi wallahi, how can that small creature defeat nearly 8police
officers?, Da farko ina tunanin dabara ce da ita ammah yanzu na gano tabbas ba mutum ɗin
bace.”

Nan Principal ya bawa DPO dabarin Ƴar Iya Tun ranar zuwan ta zuwa wannan lokaci. Cike da
fargaban abun da zai ƙara faruwa DPO ya bawa Principal shawara kan ya mayar da ita gida
lallai-lallai in ba haka ba duk matsalar da ya shiga shi ya jawo ma kan shi.

Yana katse ƙiran ya ƙira Baffi kan cewa ana neman shi da gaggawa. Duk da cewa yammaci ne
hakan bai hana shi amsawa da Toh ba. Nan da nan ya ƙira Shayibu don ya kai shi makarantar.

★★★★★★★★★

*ƳAR IYA POV*

Tun kafin motar ta gama daidaita tsayuwa Ƴar Iya dire tana wani muzurai.
Da gudu ta arta sai hostel ɗin su, tana shiga ta faɗa kan Aunty Ajiram dake zaune alamun
karatu ta gama.
Kukan da take yi kuwa har abun tausayi nan fa kowa ya zubowa Angel Ido ganin. Yadda take
kuka bilhaƙƙi, wasu na tunanin taci wahala ne wurin polisawa wasu kuma suna tunanin ta cutar
da polisawan. Kowa dai jira yake yaji me ya faru haka.

“Aishatu?” Aunty Ajiram ta ƙira ta cikin sanyin murya. Kukan da take yi ta ɗan tsagaita tana
sauƙe ajiyar zuciya.
“Aishatu me ya same ki kike kuka haka?”
Shiru tayi in banda ajihae zuciya babu abinda take sauƙewa. Sai da ta koma dai-dai ta fara
ƙoƙarin cire rigar ta babu ko ɓata lokaci, tana cirewa zanen dorinar da ta sha wurin polisawa ya
bayyana.

Ƙwalalo idanuwan su mutanen da ke room ɗin suka yi. Aunty Ajiram da ta rikice ganin irin shafin
bulalar yasa hawaye fara zubo mata. Cikin raunatacciyar murya tace
“Aishatu dukan ki suka yi?”
Sai a lokacin Ƴar Iya ta samu bakin magana.
“Ni wurin Iya na zan koma Aradu, duk Ƴan birni mugaye ne saboda haka na haƙura yanzu da
ABCD ɗin in na ƙara girma a can ƙauyen mu sai na dawo.”

“Yi haƙuri A'ishah kiyi zamanki, babu wanda ya isa ya ƙara taɓa ki har ji gama. In Kika koma
wurin Iya yi ba zaki zama Ƴar Gayu ba”

“Ni na fasa zama Aradu, in kuwa. Ba'a kai Ni wurin Iya ta ba Aradu kashe mutane zan far...”
Rufe mata baki Aunty Ajiram tayi saying
“Is ok za'a kai ki wurin Iya tunda baki son zama kusa da Aunty Ajiram” ta ƙarasa tana juya mata
baya.
“Halan kin ci wani abun a can koh?”
Sai a lokacin cikin ta ya fara ƙugin yunwa, tuni ta jawo Bagco nata ta ciro wani ƙunshin
ƙanzo,bata tsaya jiƙa shi ba kuwa ta cinye shi tas.
Tana gama ci kuma ta tayar da rigima ita fa yanzu zata tafi, da ƙyar Aunty Ajiram ta lallaɓa ta ta
Zauna kafin Baffi yazo su tafi.


, ★★★★★★★

*ALEE POV*

Tunda ya dawo ya zama busy, gaba ɗaya ayyukan da yake son kammalawa sun yi mishi yawa.
Batun wani attack da aka bar case ɗin a hannun shi yasa ya zama kamar mahaukaci sai dai ba
zaka taɓa fahimtar wani aiki yayi mishi yawa saboda irin yadda koyaushe fuskar shi take a

kame.

Motar shi ce ta danno hanci zuwa mansion nasu. Ko jiran Joseph bai yi ba ya fice abun shi. A
parlour ya tarar da Sarah taci ado, ba laifi Sarah kyakkyawa ce kamar Mommyn ta. Sanye take
cikin traditional kayan su na blue sari, hannun ta fari tas sai jan lallen da ya ƙara haska su.

Kallo ɗaya yayi mata ya kau da kan shi tare da wucewa bedroom ɗin Mom. Ganin tana toilet
yasa ya fito ya wuce bedroom ɗin shi. Wanka yayi ya sanya light kaya tare da fesa turare. Ya zo
zai fito har ya murɗa handle na ƙofar wayar shi tayi ringing.

Ganin number Major Kabir Joda yasa yayi picking da sauri.
“Hello, Is Captain Alee on the line”
“Yes sir, anything wrong?”
Cikin muryar tashin hankali yace
“Waɗannan mutanen sun ƙara attacking ƙauyen nan yanzu nayi recieving call daga sojojin da
muka tura, sun ce abun babu kyau”
“On my way, yanzu zamu shirya tafiya mu far musu”
Daga haka yayi hanging call ɗin. Komawa bedroom ɗin shi yayi ya sauya dressing nashi zuwa
uniform ɗin su na sojoji. Bai wani ɓata lokaci ba ya rataya bindigar sa ya fice.

Mom da ta bi ta damu tun ɗazu take zaman jiran dawowar shi ammah shiru yasa ta fito. A
parlour ta tarar da Sarah zaune kan sofa.

Murmushi Mom tayi mata, cikin harshen Hindu tace,
“Sarah, brothern ki bai shigo bane”
“Ya shigo har bedroom naki sai ya fito ya wuce sama. Bai ma daɗe ba ya fito inaga wanka yayi
sai kuma ya sanya uniform ya fita cikin tashin hankali”

Hankalin Mom in yayi dubu to ya tashi, fara jera mishi calls tayi ammah baya picking daga
ƙarahe ma wayar ta daina shiga. Tuni zancen ya bazu.

Duk irin tashin hankalin da suke ciki haka granny ta sanya su gaba tana kuka duk ta ƙara ɗaga
musu hankali.

“Hande enbone, Ni Shatu yau shikenan ɗan jikan nawa aka rasa, wayyo ni ƴar nan, wallahi
Muhammadu, Suraja har da kai Bello ku nemo min jika. In ba haka ba wallahi kar ku dawo min
gida”
Haka tayi ta surutai tana ƙara ɗaga musu hankali.

Lokaci ɗaya gidan ya koma tamkar maƙabarta, Yaya Saleem ma a ranar ya diro hankali tashe.

Har dare shiru number Hamma Zaki baya tafiya, su Fauzah da ƙyar aka lallashe su suka yi shiru
coz duk irin yadda yake haɗe musu da tsare musu suna matuƙar ji da su saboda yadda yake

hidimta musu.

Ɓangaren Hamma Zaki yana zuwa can Barrack a nan ya haɗa tawagar sojoji sannan ya haɗa
musu kayan aiki. Kai tsaye wucewa suka yi zuwa ƙauyen da tun kafin su shiga suke jin ihun
yara ga kuma ƙarar bindigu dake tashi.

Suna cikin tafiya basu kai ga ƙarasawa ƙauyen ba suka ji tsit kamar ba daga nan hayaniya da
ƙarar ke tashi ba ɗazu.

Hamma Zaki da shine commander a wannan gwagwarmaya, tsayar da shigar su ƙauyen yayi,
wasu har suna a shiga ya dakatar da su saying
“Suna da matuƙar wayo Ƴan ta'addan nan saboda haka ba zamu shiga yanzu ba, idan muka
shiga yanzu ba ma samun su zamu yi ba saboda sun gama na yau. So we'll stay here kamar
bamu zo ba, hakan zai sa su ƙara samun kwanciyar hankali gobe ma su kai hari, ammah
yanzu...” ya faɗa pointing to motar farko da a ciki akwai likitici sannan yaci gaba “Ku zaku shiga ku fara treating waɗanda suka raunata, mu zamu jira a nan. And kuyi taka
tsan-tsan kada su fahimci mun zo da ku”

Basu yi musu ba suka shiga suka fara treating waɗanda suka raunata. A nan suka tabbatar da
cewa waɗannan ƴan ta'adda ba ƙananan mugaye bane, sun kashe mutane da yawa wanda
yawancin su maza ne sai kuma waɗanda aka raunata suma kuma da yawa.

Gaskiyar Hamma Zaki ƴan ta'addar na da basira don kuwa babu wanda ya ƙara taɓa kowa cikin
ƙauyen sai ma samun maɓoya da suka yi.

Dr. Faruq yana ta saka musu ido ba tare da sun sani ba bare su fahimta coz yana shiga ya cire
labcoat da wndon shi ya sanya riga ƴar shara da wando da ya ara a wani gida bayan sanar da
su shi ɗin likitane.

Haka ya yawata cikin ƙauyen yana ganin maɓoyar ƴan ta'addar ba tare da sun gane ba. Sai
yamma ya dawo zuwa gidan da aka basu don kula da majinyatan.

Da yamma su Hamma Zaki ma suka samu shigowa ƙauyen su ma ammah basu shigo da mtar
su ba sai bindigun su da suka shigo da su. Wani ɗan gidan kara suka samu suka maƙale a ciki
har lokacin sallar maghrib, a nan kuwa suka yi sallah sannan suka yada zango.

Su kan su jama'ar ƙauyen basu san da shigowar su ba bare kuma ƴan ta'addar su fahimta.

Irin daidai lokacin da suka tada tsiyar au jiya irin shi suka fara yau. Sun fara sake bindigu suna
kashe mazajen ƙauyen ai kuwa sojojin nan suma suka afka musu.

Nan da nan fili ya kacame, waɗannan na kaiwa wannan farmaki har dai suka daina farmakar
ƴan ƙauyen. An shafe fiye da Hour uku ana wannan faɗa yayin da Hamma Zaki ya nuna ainihin

jarumtar sa, yadda yake harbi a dabarance kaɗai zai sa ka fahimci shi ɗin ƙwararre ne ga kuma
yadda yake sa ƙarfin shi wani lokacin.

Duk irin raunin da ya samu bai sa ya sare ba sai ma ƙara ƙaimi da yayi, tuni suka ƙarar da ƴan
ta'addan tass. Sai a lokacin suka lura da Commander nasu, nan aka fara treating raunukan shi
daga nan suka kwashi hanya har inda motocin su suke ba tare da an rasa rayuwar soja ko ɗaya
ba.
(Ya ubangiji ka ƙarawa sojojin mu lafiya tare da imani ka kuma kare su daga sharrin waɗanda
Basu Son kawo cigaba, Amin).

★★★★★★★★★★

*ƳAR IYA POV*

Rikicin da ta tayar ne yasa Aunty Ajiram ɗaukar da suka wuce office ɗin Principal.
Jin batun Ƴar Iya yasa ranshi yin wasai ko ba komai yasar da wannan ƙwallon mangwaro zai zo
da sauƙi.

Baffi bai iso ba sai wuraren yammacin ranar basu wani ɓata lokaci ba saboda yadda Ƴar Iya da
kan ta ta nuna tana son tafiya. Aunty Ajiram kuwa kamar ta tsala ihu haka ta je ta kwaso Bagco
na Ƴar Iya bisa umarnin Principal.

Bayan ta kawo ta ja hannun Ƴar Iya gefe ta sanya mata wani zobe mai kyan gaske sannan ta
riƙe hannun ta. Idanuwa Ƴar Iya ta zuba mata yayin da zuciyar ta ke mata wani iri ammah
kewar Iya yasa dole zata bar Aunty Ajiram.

Hawayen fuskar ta ta goge sannan ta fara magana cikin sanyin murna
“Aishatu, ga wannan zoben na baki kyautar sa kasancewar bani da wani abun da zan baki
yanzu, kimin alƙawarin kasancewa da zoben har zuwa ranar da Allah zai ƙara haɗa fuskokin
mu. Ki gaishe da Iya”

Tana kaiwa nan ta goge hawayen da ya ƙara zubo mata sannan ta saki hannun Ƴar Iya ta juya.

Daga nan babur ɗin su Ƴar Iya yayi horn, juyawa tayi ta ɗale kamar yadda suka yi a zuwa daga
nan mashin ya tashi sai Gallara.........

*WANNAN SHI AKE ƘIRA KOMA BAYA, BAHAUSHE YA CE WAI GA CI GA KWANAN
YUNWA, TOH ƳAR IYA, SADUWAR ALKHAIRI, IN DA RABO KUMA WATA RANA KI ƘARA
HAƊUWA DA AUNTY AJIRAM ƊIN KI.*

*MU HAƊU GOBE DON JIN YA RAYUWAR ƳAR IYA ZATA ƘARE A GALLARA, SAUYIN DA
TA FARA SAMU KO ZAI TAFI OHO...*

*INA INNA ZALIHA NE?*
*DUK AMSOSHIN KU NA TARE DA ALƘALAMIN DIAMOND LADY * *KUCI GABA DA
BIBIYAR ALƘALAMI NA*


*COMMENT AND SHARE FISABILILLAHI!*


[5/3, 7:23 PM] Diamond Bhatool:


NAZARI WRITER'S ASSOCIATION

[Marubuta masu aiki da zallar fasahar zamani tare da bin ƙa'idojin rubutun Hausa cike da
kyakkyawan nazari don kawo sauyi cikin Al'umma]

*__KYAWAWAN NAZARI DOMIN AL'UMMA__*



ƳAR IYA
(MAI HANNUN ƁARNA)
[Labari/Rubutawa]
FADIMATU ADAMU HASSAN
DIAMOND LADY
{GARKUWAR NAZARI WRITERS}

★__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart
touching love __★



I DEDICATED THIS BOOK TO NAZARI WRITER'S ASSOCIATION.

BOOK 0️⃣1️⃣
PAGE 2️⃣7️⃣▶️2️⃣8️⃣

*[Gare ki ƴar uwa, ko kin san cewa na ɗaya daga cikin dalilin da yasa mata suka yi rinjaye cikin
wuta butulcewa kyautatawar da mijin ki ke masu?*
*Matso kiji ƴar uwa, butulcewa kyautatawar miji kamar dai yadda mata yanzu muka ɗauki abun
kamar hali ..kowa tana da shi.*
*Mijin ki zai jima yana ɗawainiya dake yana ƙoƙarin kyautata miki ammah da an samu matsala

na rana ɗaya sai ki butulce kina faɗin _me ka taɓa yi min a rayuwa?_*
*Wannan abu yanzu mata sun ɗauke shi sun yafa har wani tinƙaho suke yi...TOH maza ƴar uwa
tun kina da sauran lokaci maza ko yada wannan ɗabi'ar domin kasancewa cikin ahlul jannah*
*Allah Ubangijin yasa muna da rabo baki ɗaya*.



Daga nan babur ɗin su Ƴar Iya yayi horn, juyawa tayi ta ɗale kamar yadda suka yi a zuwa daga
nan mashin ya tashi sai Gallara.

Tunda suka ɗauki hanya take famar zare ido tare da juya zoben da Aunty Ajiram ta bata yayin
da wani ɓangare na zuciyar ta ke jin babu daɗi.

Har ƙofar gida Shayibu ya kai su, daga suka dire. Ƴar Iya bata samu damar shiga da Bagco
nata ba tayi ciki da gudu.

A zaune ta tarar da iya bisa kujerar tsakar gida, da gudu ta faɗa kanta tana sakin kuka.
“Iya ta bakiyi kewa ta ba neh?” ta faɗa bayan ta tsagaita da kukan da take yi.
“Haba shalelen Iya ni ɗin ne kuwa nayi kewar ki, kullum sai nayi hawaye ina tunanin shalele na”

Murmushi tayi tare da sakin Iya
“Iya birni babu daɗi, akwai mugaye a sukul ɗin mu”
Zare ido yayi tayi tace
“Miye sukul kuma shalelen iya?”
Dariya da shewa Iya ta saki lokaci guda.
“Ayyiriri nanaye....lallai Iya na manta ashe fa ke ƴar ƙauye ce” ta dakata tana wani fari da ido
kamar wacce ke gaban saurayin ta.

Iya kam dariya tayi tana faɗin
“Yo Ni kam ai nan ne iyaka ta sai ƙauyukan kewaye, ban taɓa zuwa birni ba shiyasa naso ke ki
tashi a can kinga wata rana sai ki kai ni”
Ta ƙarasa sounding serious.
Dariya Ƴar Iya tayi tace
“Iya kenan, to Aradu ƴan birnin nan mugaye ne barin ma masu baƙin kayan na, hegu kingan su
ƙataye da su ammah sai da na basu kashi”
Ta ƙarasa tare da kaɗa yatsa.

Cike da ƙosawa iya tace
“Yanzu faɗa min suku ne Kika ce ko sumul?”
“Hhhh..... Kiji Iya wai suku, to ai ba haka ake faɗa ba, in Kika faɗa a gaban ƴan birni to
dariya zasu yi miki” ta faɗa tana wani kaɗa kai ita ala dole ƴar birni.

“Toh ai sai ki gyara min yadda nima in na shiga maƙwabta zanyi musu su san Shalele na taje

birni”
Murmushi Ƴar Iya tayi tace
“Ai kuwa, to Iya ai sukul ake cewa ba suku ba”
“Ayya sukwal”
“Hahhhh. Iya ba sukwal ba sukul”
“Ai to sukul”
“Yauwa Iya ta yanzu dai-dai kika faɗa”
Dariyar farin ciki iya tayi tace
“Toh shi sukul ɗin me yake nufi?”
Ta tambaya cike da ƙaguwa.
Sai da ta juya kai kafin tace
“Makaranta shine sukul ɗin”

Haka suka yi ta shirmen su yayin da cikin gari ya ɗauka ai Ƴar Iya ta dawo. Wasu na farin ciki
musamman A'i wasu kuma har sun fara kuka da kansu.

★★★★★★★★★

*ALEE POV*

Bayan sun isa wurin da suka bar motocin su, kai tsaye suka shige tare da wucewa. Bayan sun
isa waɗanda suka samu rauni aka miƙa su asibitin dake can for effective treatment yayin da
Hamma Zaki yaƙi tsayawa.

Bai samu kunna wayar shi ba ko da bayan sun dawo, saboda haka ya kunna tare da ƙiran
Joseph, cikin mintuna kaɗan Joseph ya ƙaraso yayi driving Hamma Zaki gida.

Tun kafin motar ta gama packing gaba ɗaya mutanen gidan suka iso wurin,p Mom da fuskar ta
ke ɗauke da tsantsan damuwa da sauri ta shige gaba ganin Joseph ya buɗe mishi motar, cikin
zafin nama taje tayi hugging nashi tana sakin wani irin kuka.

Zuciyar shi ce ta karye ganin yadda Mom ɗin shi ke kuka.

Granny ma ba a bar ta baya ba,
“Ku bani waje nagan shi don Allah, lafiya ƙalau yake ai koh?” ta faɗa tana Matsowa kusa da shi.

Ganin raunin da ya samu yasa jikin kowa yin sanyi. Nan take Mom tace su wuce Hospital, bai
iya yi mata musu ba haka suka ɗunguma zuwa Hospital. Bayan an yi treating raunukan likita ya
buƙaci su koma don yana buƙatar hutawa.


★★★★★★★★★

Yammacin ranar kuwa Ƴar Iya tayi wanka har da wanke baki da gawayi da kuma alimun, aka
saka kaya masu kyau ita ala dole an je birni.

Ko sallama bata yiwa Iya ba ta fito abun ta tana taku tana yauƙi kamar wata kuɓaiwa. Kai tsaye
gidan su Aminiyar ta A'i ta wuce, kafin isar ta kuwa duk wurin da ta gifta sai anyi gulmar ta wai
Ƴar Iya taje birni baku ga har sauya

10 / 16