Author : DIAMOND LADY Category : Taskar Novels
ga jiniya wiwiwi....wiwiwi.... Tun daga cikin hostel ɗin su ake jin ƙarar
jiniyar, lokacin da yawa suke saka uniform don tafiya classroom.
Bayan motar tayi packing dai-dai office na Principal, wasu daga cikin Ƴan sandan suka shiga.
Bayan sun gaida Principal suka sanar da shi aiko su da ogan su yayi.
Bai ɓata lokaci ba yace
“Hostel zaku je kuce waye Angel, in ta zo sai kuce tazo zaku kaita wurin Baffin ta da Iya. Kai
tsaye ku wuce police station da ita, ku kaita ɗaki mai duhu sannan ku hukunta ta sosai sai taji
jiki tukun ku ƙyale ta sai ku dawo min da ita nan”
“Alright ur wish is our command sir”
Daga haka suka fito da Principal's office, Basu tsaya ko ina ba sai hostel, a lokacin Ƴar Iya tare
da Aunty Ajiram da ke riƙe da hannun ta suka fito daga hostel ɗin zasu wuce classroom.
Alama police ɗaya yayiwa Aunty Ajiram da tazo Saboda gargaɗin Principal Akan yarinyar na da
hatsari gaske. Bayan Aunty Ajiram da Ƴar Iya sun ƙaraso yace
“Please sisters ku shiga hostel ɗin ku kuce Angel ta zo”
Shaye da mamaki suke kallon police ɗin...............
TOH INA TEAM ƳAR IYA, YAU FA ZAKU HAƊU DA GABAN KU!
KO ME ZAI FARU?
ZA'A TAFI DA ƳAR IYA POLICE STATION, KO A CAN NE ZATA YI HANKALI??
DUK AMSOSHIN KU SUNA A TARE DA ALƘALAMIN DIAMOND LADY .
COMMENT &SHARE PLEASE!
[5/1, 8:11 PM] Diamond Bhatool:
NAZARI WRITER'S ASSOCIATION
[Marubuta masu aiki da zallar fasahar zamani tare da bin ƙa'idojin rubutun Hausa cike da
kyakkyawan nazari don kawo sauyi cikin Al'umma]
*__KYAWAWAN NAZARI DOMIN AL'UMMA__*
ƳAR IYA
(MAI HANNUN ƁARNA)
[Labari/Rubutawa]
FADIMATU ADAMU HASSAN
DIAMOND LADY
{GARKUWAR NAZARI WRITERS}
★__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart
touching love __★
I DEDICATED THIS BOOK TO NAZARI WRITER'S ASSOCIATION.
BOOK 0️⃣1️⃣
PAGE 2️⃣3️⃣▶️2️⃣4️⃣
[Ƴan uwa na masu albarka ina muku nasiha da ku yawaita yin sadaƙa.
Ko kun san irin alkhairin da ke tattare da sadaƙa musamman gare mu mata?.
TOH bari kuji wani hadisi.
Daga Abi Sa'eed Alkudriyyu yace:
Annabi tsira da aminci su ƙara tabbata a gare shi ya fita ranar sallar idi ƙarama ko babba zuwa
wurin sallah, sai ya biyo ta wurin wasu mata daga wurin sai ya tsaya yace:
«Ya ku taron mata, ku yawaita sadaƙa, domin mafi yawancin ku kun kasance ƴan wuta»
Bukhari ya rawaito.
Mai buƙatar ƙarin bayani game da wannan hadisi tana iya yi min magana kai tsaye a nan
WhatsApp +2347061707238].
Shaye da mamaki suke kallon police ɗin da ya basu wannan saƙo. Shiru suka yi su biyun, ganin
sun yi shiru yasa police ɗin faɗin
“Kinga sister ki ƙira mana ita ba komai zai faru ba wurin Baffin ta za'a kai ta”
Jin an ambaci Baffi yasa Ƴar Iya faɗin
“Toh ai gani a gaban ku, Aradu da na fita kilasmum da wuri da bazan ga Baffi na ba, Allah sarki
banda Iya zan gani?”
Ta tambaya tare da marairaice fuska.
Murmushi police ɗin yayi yace
“Har da Iya duk suna jiran ki, maza shigo Mu tafi.”
Ya faɗa yana nuna mata wurin da suke ajiye masu laifi in zasu tafi.
Aunty Ajiram haka nan taji babu daɗi daga nan tayi wa Ƴar Iya sallama.
“Ki gaida min Baffi da Iya kinji A'ishah?”
Kai ta gyaɗa tare da zagayawa don shiga wurin da aka nuna mata.
Ganin polisawa da yawa kusan biyar zaune suna pointing mata wani ɗan wuri a tsakiya yasa ta
Banka musu harara.
“Kutumelesi, Aradu ni ba Ƴar Iska bace da zan shiga tsakiyar ku, sai dai ku koma can ku
cakuɗu in ba haka ba na faɗawa ogan ku”
Ƙasa magana suka yi saboda tsantsar mamaki ganin yarinya ƙarama na tsula musu tsiya son
ranta, ko mutuncin uniform ɗin su bata gani.
A harzuƙe ɗaya daga cikin su ya buga mata tsawa
“Oya get in or else I'll shoot u to death”
Ya faɗa yana saita ta da wata pistol ɗin roba. Ba shiri ganin bindiga ta shige ciki. Cikin ranta duk
tsoro ya cika ta har ta fara tunanin satar bindiga.
“Wannan fah irin bindigar nan ne da ake kashe mutane da ita a TV, kutt, Aradu don wurin Baffi
zasu Kaini amma sai na sace ɗaya saboda ƴan banzan mutane.
★★★★★★★★★
Zaune suke a katafaren dining area na gida, Daddy, Mom, Sarah sai kuma Fauzah. Babu abun
da ke tashi sai ƙarar cokali yayin da na jiyo sautin taku daga staircase na gidan.
Sanye yake cikin wata haɗaɗɗiyar Black suit da farin shirt a ciki sai farin necktie. Sumar Kan shi
ta sha gyara sai wani ƙyalli take kamar wanda ta fito daga rijiyar mai, Black shoe ne a ƙafan shi
sai kuma wani uban ƙamshi da yake yi na turaren _majesté impériale_ wanda tuni ya sanar da
mutanen dake dining ɗin isowar shi.
Mom da tunda ta fara jiyo ƙamshin sa ta daina cin abincin sai sakin murmushi take haka Daddy
yayin da Fauzah taji kamar ta tashita bar wurin. Idon Sarah ƙyam a kan shi yayin da shi kuma
babu abinda yake kallo sai frame ɗin dake kallon shi, fuskar nan a tamke kamar kullum ammah
hakan bai hana kyawun shi fitowa ba.
Yana ƙarasawa dining area kusan Mom ya fara zuwa yayi mata side hug tare da peck a cheek
nata
“Good morning Mom”
Murmushi tayi tana faɗin
“Morning first love, how's your night?”
“Absolutely fine one”
“Alhamdulillah”
Daga nan ya ƙarasa zuwa wurin Daddy, kamar yadda yayi wa Mom haka suka gaisa da Daddy
tukun ya samu kujerar shi ya zauna.
Mom da kanta tayi serving nashi cips and fried egg sai Hot coffee.
A hankali Fauzah tace “Good morning Hamma Zaki”
Ba tare da ya ɗago ba yace
“Morning”
Sarah ma ta gaida shi ya amsa kamar baya so.
Fauzah ce ta fara barin dining ɗin ta ɗauko school bag nata tayi waje, Sarah ma ta miƙe zuwa
bedroom ɗin ta. Ya rage saura Mom da Daddy.
Daddy ya kalli Hamma Zaki ɗauke da murmushi a kan fuskar shi
“Daddy's love jiya na dawo da dare, I was thinking of meeting you a parlour sai na tarar kayi
bacci ma”
Shima murmushin yayi yace
“I'm sorry Daddy, I'll squeeze and have time with u”
Daga haka ya miƙe yana waving hands
“Bye, Mom and Daddy”
Yana fita Joseph ya zo ya amshi Briefcase nashi zuwa mota, daga nan driver ya ja motar sai
Barrack.
Bai dawo ba sai wajen yamma saboda ayyukan da ke gaban shi.
A wahalce ya dawo, yayi wanka sannan ya wuce bedroom ɗin Mom. Saman sallaya ya same ta
alamar sallah tayi. Sallama yayi ya shige daga nan ya samu gefen sallayar ya ɗan kwanta yana
ɗora kanshi akan cinyar ta.
Murmushi Mom tayi tace
“Welcome back Son”
“Thanks Mom”
“Ya aikin dai, da alamu ka gaji da yawa, muje kaci abinci”
Kan shi ya jijjiga saying
“No Mom, Ina cake ɗin da kika yi baking?, Shi nake so sai Hot coffee”
“Ohk ɗaga Ni na haɗo maka”
Kwaɓe face yayi yace
“Nifah Mom ban gaji da cinyar ba, baki ganin ina jimawa ban hau ba...da na hau kuma sai ki
tashe ni”
Murmushi tayi tana jan kumatun shi
“Toh shikenan sai ka zauna da yunwa haka kake so?”
“Auchh..sakar min kunnen mana ko so kike ya cire saboda yafi naki kyau?”
“No yi haƙuri Son Bari na haɗo maka.”
Dining ya wuce ya jira Mom sai gata ɗauke da cakes cikin bowl sai kuma hot coffee a kan tray.
Da kanta tayi feeding sakaltaccen yaron ta daga nan ta kawo mishi batun Sarah coz sun taɓa
magana da Mommyn Sarah ɗin wai tana so su haɗa yaran aure. Mom ɗin Sarah cousin ɗin
Mom ce.
“Son Kun gaisa da Sarah kuwa?, Ta zo ne saboda kai Please ka ke sakar mata fuska”
Fuskar shi ya ɓata yana tura baki
“Wai Ni Mom meyasa kuke son cusa mutane cikin rayuwa ta, bana buƙatar kowa bayan ku don
Allah Mom ku daina zubo mutane rayuwar classic yaron ku”
Dariya Mom tayi coz Bata son duk wani abu da favourite ɗin ta baya so.
“Is ok Son, na daina but ko ba komai Sarah is your sister”
“I know, all I hate from her shine rashin kamun kanta, but if she'll change me too I'll change”
Bayan ya gama ci ya ce ma Mom zai je garden zuwa maghrib.
★★★★★★★★★★★
*POLICE STATION*
Suna isa duk suka dire haka Ƴar Iya ma tayi ganin yadda suka yi. Kallon su tayi tace
“Ina Baffi?”
Banza suka yi mata yayin da biyu daga ciki suka fizgo hannun ta, tana turjewa suna ja har suka
isa ciki. Da yake an riga an musu bayanin me zasu yi tuni suka shigar da ita Cell. Fitowa suka
yi don su nemo abun da zasu hukunta ta da shi bayan sun sakawa ƙofar kwaɗo da key.
Few minutes suka dawo ɗauke da Koboko (Dorina) irin wacce ake jibgar Dawaki da ita, suka
haɗo da bucket cike da ruwan sanyi har wani tururi yake yana fitar da raɓa.
Ƴar Iya da ke cikin Cell hankalin ta baya kan su duk tunanin ta Baffi zasu ƙira mata. Har suka
buɗe ƙofar bata sani ba, babu zato babu tsammani police ɗaya ya janye Hijabin check ɗin ta,
tuni ta fito daga duniyar tunani ta fuskanci duniyar asali. Tana juyowa kuwa ɗayan ya fizge rigar
ta da sauri yayin da ɗayan ya zame wandon.
Tsabar mamaki da ya cika ta rasa me zata yi ma tayi.
“Kutumar Uba, me nayi muku zaku cire min kaya na?, Dama ba gun Baffi zaku Kaini ba ku Ƴan
Iska ne?”
Bata aune ba taji ruwan sanyi a jikin ta...tuni ta fara rawar sanyi, yo ita wankan ma yaushe tayi
shi ballantana ma da ruwa irin wannan. Har abun tausayi yadda take rawar sanyin ammah su
basu ji ba, wani bucket ɗin suka ƙara janyowa suka ƙara tsula mata shi tas.
(Toh fah Ƴar Iya yau kin gamu da gamon ki).
Sai da suka tabbatar sanyin ya ratsa ta suka ciro dorinonin su suka fara sharɓa mata, irin
yanayin da take ci ba zata iya ƙwatar kanta ba saboda zazzaɓin da ya rufe ta lokacin ɗaya.
Dukan ta suke yi su biyu da dorinonin su tun tana ihu har Muryar ta ta dishe ta daina fita da kai.
Duk da haka maimakon su sarara mata saboda ƙarancin shekaru irin nata sai suka ci gaba da
dukan ta har sai da ta daina motsi.
(ALLAH SARKI, ƳAR IYA AN MUTU)
A haka suka fice suka barta. Ta share kusan awa biyu zuwa uku a suke kafin ta farfaɗo, lokacin
kuma zazzaɓin da take ji ya sake ta tana buɗe idon ta ya sauƙa a kan baƙin ɗakin da take, nan
ta fara tariyo abun da ya faru da ita.
Babu shiri ta fara miƙewa, a hankali ta janyo wandon ta da har ya bushe da kuma rigar ta ta
ƙwama, bata ƙara bi takan hijabin ba ta fara ƙoƙarin buɗe ƙofar sai dai ƙyam ƙofa taƙi buɗuwa
alamun akwai padlock jiki. Ba tare da ta damu ba ta fara jan ƙofar da iyakar ƙarfin ta.
Kyawawan ja guda uku tayi lock ɗin jikin ƙofar ya ɓalle, wangalewa tayi ta fito. A reception ta
fara tarar da wasu polisawa saboda haka tayi kansu ba tare da ɓaga lokaci ba. Wani katako ta
gani a gefe ai kuwa ta wawuro shi tayi kan su.
Tsabar mamaki da jin kai irin na polisawa suka ƙame suna jiran ganin ƙarshen iskancin yarinyar.
Gani suke yi kamar ƙaramar mahaukaciya ce shiyasa kowa yayi ƙyam.
Ba tare da wani tunani ba Ƴar Iya ta sa hannu cikin aljihun ta da ta cika shi da yashi ta watsa a
fuskar su. Nan fa suka farga zasu fara guduwa, ƙara ciko hannun ta tayi ta watsa musu.
Sai da ta tabbatar idanuwan su sun raunana ta janyo na baki-baki tare da buga mishi katakon a
ƙafar hagu, ta juyar da shi dama ta ƙara buga mishi nan da nan ya cilla ƙara tare da faɗuwa
yana sowa.
“Wayyo ƙafa ta na shiga uku wayyoh Allah wayyoh shikenan ta karya Ni wayyo”
Jin ihun da ɗan uwan su ke yi yasa suka far lalume zasu buɗe office ɗin da ke kusa sai dai ina
ta riga ta far musu da shiri.
Haka ta ringa bugun ƙafafuwan su da katako tana yasar da su, polisawan da ke bakin Gate ne
suka jiyo ihu nan da nan suka shigo ciki don ganin me yake faruwa.
Kafin shigowar su kuwa ta gano fuskar mugayen da suka buge ta ai kuwa tayi kan na farko.
Hannun sa na dama ta samu ta buga mishi katakon da ƙarfi sannan na hagu daga nan ta buge
masa ƙafafuwa kamar yadda ta bugawa sauran.
Haka ta jawo ɗayan shima ta fara bugun shi kamar yadda tayi wa ɗayan sannan ta bar shi ƙasa
ta dawo gefe tana maida numfashi.
Ganin aika-aikar da yarinyar tayi yasa duk suka fara jin shakkun ta. Kallon su tayi tace.
“In ba zaku kai ni gun Baffi na ba to ku mayar da ni sukul ni wurin Iya ta zan koma Aradu birni
duk mungaye ne”
Kuka ta raushe da shi kamar ba ita ce wacce ta nakasa waɗannan tarin ƴan sanda da sun kai
takwas ba.
A gaggauce suka fara kwasar ƴan sandan suna jera su cikin mota ba tare da sun bi ta kan Ƴar
Iya ba. Kai tsaye asibiti suka wuce a nan aka tabbatar musu da cewa duk sun samu karaya a
ƙafafuwan su biyu biyu sai waɗannan biyun da suka karye a hannayen su.
Ƙiran DPO suka yi suka sanar da shi, nan da nan shima ya tsorata da al'amarin yarinyar yace
su mayar da ita makarantar su kafin ya zo asibitin zasu yi magana da shugaban makarantar su.
Ba musu da suka koma police station suka nemo Ƴar Iya suka saka ta a mota sai
school.................
Ina godiya sosai da addu'oin ku masoya na, masu ƙira da masu tura saƙo duk na gode Allah ya
bar ƙauna. Babu daɗin yadda kuka damu da Ni, ina matuƙar son ku da yawa da yawa.
MU HAƊU GOBE DON JIN YADDA ZATA KAYA.
KUN JI ƘUDURIN ƳAR IYA NA KOMAWA GUN IYAR TA DA BAFFI BAYAN TA KWASHI KASHI
GURIN POLISAWA.
TOH FAH, GA KUMA DAI AN FARA SAMUN SAUYI TA ƁULLO DA TSIYA.
KU CI GAVA DA BIBIYAR ALƘALAMIN DIAMOND LADY DON NISHAƊANTUWA DA KUMA
WA'AZANTUWA.
DIAMOND LADY CE
TOH ƳAR IYA NACE ALLAH YA TAIMAKA.
COMMENT AND SHARE FISABILILLAH!
[5/2, 9:03 PM] Diamond Bhatool:
NAZARI WRITER'S ASSOCIATION
[Marubuta masu aiki da zallar fasahar zamani tare da bin ƙa'idojin rubutun Hausa cike da
kyakkyawan nazari don kawo sauyi cikin Al'umma]
*__KYAWAWAN NAZARI DOMIN AL'UMMA__*
ƳAR IYA
(MAI HANNUN ƁARNA)
[Labari/Rubutawa]
FADIMATU ADAMU HASSAN
DIAMOND LADY
{GARKUWAR NAZARI WRITERS}
★__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart
touching love __★
I DEDICATED THIS BOOK TO NAZARI WRITER'S ASSOCIATION.
BOOK 0️⃣1️⃣
PAGE 2️⃣5️⃣▶️2️⃣6️⃣
[Annabi tsira da aminci su ƙara tabbata gare shi yace: «Akwai wasu kalmomi guda biyu masu
soyuwa wurin Ubangiji, masu sauƙi akan harshe, masu nauyi akan mizani, sune _subhanallahi
wabihamdihi subhanallahil azeem». Bukhari da Muslim suka ruwaito.
Ya ke Ƴar uwa mai albarka ki lazimci furta waɗannan kalmomi da basu da nauyi da wahala
wurin faɗi domin mizanin ki ya nauyaya ranar sakamako]
Ba musu suna komawa police station suka Iya suka saka ta a mota sai school.
Kafin Isar su DPO ya ƙira Principal, ranshi a ɓace bayan Principal yayi picking call ɗin ya fara
magana
“Haba Misbahu, fisabilillahi wa rasulihi me ka aikata haka?”
Kwantar da murya Principal yayi yace
“I'm sorry sir, wallahi an samu matsala ne”
“Matsala kake cewa eh, matsala koh?, To bari kaji in faɗi maka Yarinyar nan ba full mutum
bace”
“Ban gane ba full mutum bace, kaga kofato ne a ƙafarta” Principal ya faɗa yana rarraba
idanuwa.
Jin batun Principal yasa ran DPO ƙara ɓaci yace
“Eh kofato kake magana Misbahu?, Ana maka magana ta aika-aikar da yarinyar tayi kana batun
kofato?”
“I'm sorry sir, kayi haƙuri ka faɗa min me tayi don Allah” Principal ya faɗa yana kwantar da
murya.
“Toh bari kaji na