Author : DIAMOND LADY Category : Taskar Novels
abinda ya faru a wurin taro yasa yake ta banko masa
ƙira tun lokacin sai dai shikam yana can garden ma, ko da ya dawo cikin gidan ma bai samu
sukunin taɓa wayar ba.
Lallamin sa shima Hamma Saleem ɗin yayi nan da nan ya sauƙo har da ƴar dariyar shi, daga
haka suka yi sallama yana ce masa zai shigo in Sha Allah.
Bayan sun kammala wayar ne kawai yaji sha'awar hawa online. A nan yaci karo da abubuwan
dake trending, cike da mamaki ya shiga pictures ɗin yana dubawa wasu yayi tsaki wasu kuma
yayi murmushi, kan picture nashi wanda aka yi musu da duka sisters ɗin shi ya tsaya. Ya jima
yana dubawa yana murmushi. Ƙaunar su ce kawai ke yawo cikin zuciyar shi yayin da yake jin
zai iya sadaukar da komai nadhi saboda su.
Daga nan comment section ya shiga, nan fa yayi ta jera tsaki ganin haukar mutane. Ya jima
yana dubawa wani wurin kuma ya yi murmushi. Haka ya leƙa all media handles nashi daga nan
ya kashe phone ɗin tare da ajiyewa.
Wanka yayi tare da ɗauro alwala ya saka Armani pyjamas tare da fesa turare, daga kashe light
ya bar iya bedside dim light, nan ya haye bed ɗin sa tare da janyo blanket, addu'oin baccin sa
yayi tare da kwanciya.
_Annabi tsira da aminci su ƙara tabbata gare shi yace, duk wanda yayi alwala kafin yayi bacci,
ya kaɗe shimfiɗar sa sannan ya kwanta ɓangaren dama tare da karanto addu'oin bacci,
Ubangiji zai sanya Mala'iku su zama dakarun da zasu yi gadin sa har zuwa lokacin da zai
tashi._ Hadisin ingantacce ne.
_Addu'oin bacci_
★Ayatul kursiyy
★Amanarrasul
★Suratul-ilhlas (qul huwallahu ahad)
★Suratul falaq (qul authu birabbil falaq)
★Suratul-Nas (qul authu birabbil nas)
★Bismikallahumma Amutu wa ahya.
COMMENT & SHARE FISABILILLAHI!
[5/18, 10:50 AM] Diamond Bhatool:
NAZARI WRITER'S ASSOCIATION
[Marubuta masu aiki da zallar fasahar zamani tare da bin ƙa'idojin rubutun Hausa cike da
kyakkyawan nazari don kawo sauyi cikin Al'umma]
*__KYAWAWAN NAZARI DOMIN AL'UMMA__*
ƳAR IYA
(MAI HANNUN ƁARNA)
[Labari/Rubutawa]
FADIMATU ADAMU HASSAN
DIAMOND LADY
{GARKUWAR NAZARI WRITERS}
★__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart
touching love __★
SADAUKARWA GA ƘUNGIYAR NAZARI WRITERS, ubangiji ya kula da al'amuran ku tare da
ƙara tsarkake muku alƙaluman ku. Allah ya bar mu tare.
BOOK0️⃣1️⃣
PAGE 3️⃣9️⃣▶️4️⃣0️⃣
Sanyin asuba da ke busawa yayin da alfijir ya keto, Babu abunda ke tashi sai kiraye-kirayen
sallah wanda ake jin sa daga can nesa. Miƙa yayi ɗauke da addu'a a bakin sa.
دمحلاE لله يذلا انايحأ دعب ام انتامأ و هيلإ .Fروشنلا
Sai da ya shafe wasu sakanni kafin ya ziro sawayen shi ƙasa. Toilet ya nufa tare da alwala
sannan ya gabatar da sallar sa. Yana idarwa ya yi azkar ɗin sa na safiya tare da karanta wasu
ayoyi daga cikin Alqur'ani. Ba shi ya tashi daga praying mat ɗin ba sai around 6:00am. Bayan
ya naɗe ta ya haye gado tare da komawa baccin sa saboda har yanzu bai gama cinye hutun da
aka bashi ba.
(*Ko kun san cewa miƙewa tsaye immediately bayan tashi daga bacci ne ahaifar da matsaloli da
dama?, Idan baki sani ba toh daga hau in kin farka daga bacci ki tabbatar kin cigaba da
kasancewa a kwance na wani lokaci kafin ki miƙe domin kiyaye lafiyar ki*)
*PRETTY POV*
Directly Cikin tuƙin ganganci suka fizgi motar sai hotel ɗin ransu a matuƙar ɓace. Bakin kowa
tsit banda sautin waƙar _Rush_ babu abinda ke tashi cikin motar.
Bayan sun isa Pretty ta buɗe musu ɗakin tare da shigewa. Pretty dake wani hura hanci ga
fuskar nan tayi ja jawur kamar an watsa mata ruwan zafi (nace ai kusan hakan, ga marin Sarah
ga na Capt Sulaiman). Kayan dake jikin ta ta fara cirewa. Tas sai da ta cire komai tukun ta
ɗaura towel ɗin dake lanƙaye jikin hanger. Toilet ta shiga ta sakarwa kanta ruwa ko zata ji
sauƙin raɗaɗin da ke damun ta.
Ishy, Fauzy, da kuma sumy suma a lokacin suka tuɓe suna jiran fitowar ta, sai da ta ɗan ɓata
lokaci kafin ta fito, Ishy da Fauzy suka shige abun su a tare yayi da sumy ta tsaya taya Pretty
shiryawa tana lallashin ta. Su biyun tare suka fito sannan sumy ma ta samu ta shiga. Cikin wasu
tsinannun kaya suka shirya waɗanda ko a zaman gida wanda ba kai ɗaya ba bai dace ka sanya
su ba.
Bayan sun shirya Pretty ta ƙira aka aiko musu da abinci.
Sai da suka yi hani'an suka yi brush, batun sallah kuwa babu shi, turare suka fesa tare da
miƙewa suka yi waje.
Motar su suka nufa but this time around Sumy ke driving, duk irin yadda kiɗa ke tashi a motar
basu daina hirar da suka fara ba.
Pretty da kanta ke lafe jikin kujerar motar tace “Guys yau ban san ya zanyi ba, yet zuciya na bai
daina zafi ba”
“Sorry Pretty, yanzu zuciyar ki zata sauƙa for a while, ance Adamawa akwai sweetboys
wadanda suka san harƙa, just relax kiyi mankas muyi rawa abun mu, all this sadness will fade
away.” Sumy ta faɗa tana juyo gefen ta da Pretty ke zaune.
“Uhmm” Pretty ta faɗa tana sakin wani killer smile “Ban jin zan iya mantawa da wulaƙancin nan
da wuri fah”
“Ke dai ki bari” inji Ishy dake sit na baya ita da Fauzy.
Fauzy tace “Just relax babe, ko baki mance ba in mun dawo we'll make u forget it”
“Toh Allah yasa”
Suna isa suka samu wani ɓangare tare da parking motar su. Tun daga fitowar su suka ci karo
da wasu gang ɗin samari suna busa shisha.
“Payo....ɗago kaga wasu hot babes a nan” ya faɗa yana tsaida kallon sa kan su Pretty dake
sanye cikin wasu tsinannun transparent gowns da basu da maraba da babu.
“Bura uba” payo ya faɗa yana muƙewa tsaye “Alquran yau akwai shagali Subato” ya faɗa tare
da miƙa wa subato hannu.
Miƙewa suka yi tare da nufan su Ishy da suke daf da isowa yadda suke.
Kallon banza su Pretty suka aikawa su subato tare da raɓawa ta gefen su suka shige ciki.
Sauran gang members ɗin kuwa dariya suka saka suna musu gwalo.
Directly hall ɗin suka nufa, a daidai entrance door ɗin suka ci karo da wata budurwa samanta
wani ƙato sai haƙarta yake yi (Authubillah ko kunyar ido babu). Raɓa su suka yi sannan suka
shige cikin hall ɗin. Suna zama waitress ɗin ta miƙa musu alcohol Wanda brand ɗin ta ana hana
mutane ta'ammali da ita.
Sai da suka yi mankas daga nan kowacce ta manta yadda take, sautin waƙar dake tashi sai a
lokacin yake ɗibar su, Pretty da Ishy suka nufi stage ɗin suna tangal-tangal. Rawar da sukeyi
kaɗai ya isa ta bawa mutum haushi, su gasu kamar macizai saboda lanƙwashewa amma haka
suka yi tayi.
Payo da ya shigo yaga mutanen nasu sunyi mankas yasa ya janyo hannun Pretty suka shige
room ɗin da ya kama.
Suna shiga ya fuzge mata rigar da da ita Gara babu nan ya cafki boobs ɗin ta ya fara sucking,
tuni salo ya canza aka wuce zuwa wata duniyar.
Ishy kuwa tare da subato suma suka baje tasu hajar. Fauzy da Sumy kuwa dama sun fi
ƙwarewa a fannin lesbian hakan yasa da suka samu partner suma suka shige nasu room ɗin
tare da ci gaba da masha'ar su.
(Innalillahi wa inna ilayhi rajiuun, wannan itace rayuwar da matasan wannan zamani suka ɗauka
a matsayin wayewa, zina ta zama ruwan dare, maɗigo (lesbian) da kuma luwaɗi (homosex) sun
zama jiki a wurin matasan mu. Subhanallah, ayyukan da suke samarda fushin Allah su bayi
suke aikatawa hankalin su kwance?, Ina zamu je ne?, Ina zamu saka rayuwar mu ne?, Shin
mun manta akwai mutuwa ne?, Lallai ya kamata mu farka mu san ne muke yi, ba fa komai ce
wayewa ba! Mu tuna zamu mutu, ya muke tunani idan mutuwa ta riske mu a irin wannan hali?,
Me zamu faɗawa Ubangijin mu?.
Ƴan uwa ya kamata mu san cewa aikata waɗannan abubuwan baya daga cikin wayewa sam
sai dai ma taɓewa, kuma masu aikata waɗannan ayyuka in Basu tuba ba kafin mutuwar su toh
Ubangiji ya tanada musu azaba mai raɗaɗi tun daga mutuwa har zuwa hisabi da kuma miƙa
kowa gidansa na har abada. Allah yasa mu dace).
Su Pretty basu bar club ɗin nan ba sai around 2:00am, lokacin alcohol ɗin ya saki sumy da yake
ita ba wani da yawa ta sha ba, hannun Fauzy ta kama tare da miƙa ta cikin motar su sannan
tabi rooms ɗin da Ishy da kuma Pretty suke, suma ta ɗsuko su ba tare da ta mayar musu da
kayan jikin nasu ba ta miƙa su motar.
A haka ta fuzgi motar sai hotel ɗin su, da ƙyar ta taya su suka shigo ciki saboda har yanzu suna
kan network. Nan duk suka baje wasu ƙasa wasu suka haye bed.
Sai around 10:00am suka tashi, bayan sunyi wanka suke tambayar taya suka dawo. Dariya
sumy tayi tace
“Dole kuce haka babes, irin wannan dare da gani U guys enjoy it”
Su duka suka kwashe da dariya, Pretty tace “Tuni na manta da maganar Sweetheart, sai yanzu
na tuna, hope zaku ƙara raka ni tunda sai gobe mu wuce ko?”
Ishy tace
“Shegiya Pretty dole ki manta da shi mana, kinje kin buɗe xender ya tura Miki bahubali!” ta faɗa
tana sakin dariyar shaƙiyyanci.
Fauzy da har yanzu ke dariya tace
“Babes baku da dama gaskiya, kiji wai xender!” ta faɗa tana miƙa wa Sumy hannu wacce itama
dariyar take tsulawa.
“Ke dai ki bari sumy, ai gwanda xender wai kinji bahubali!” itama ta faɗa suna cigaba da dariya.
Bayan sunyi breakfast kuma suka ja motar su neman pretty's Sweetheart.
★★★★★★★★★★
*ƳAR IYA POV*
Yau tunda ta tashi daga bacci tayi wanka tare da sheƙa kwalliyar ta irin ta Aljanu. Janbaki kamar
zai yi magana haka powder kamar wata dodanniya.
Neman halal ɗin ta ta fita, yau ma dai bata biya ta gidan su A'i ba saboda ita ta a can tana
shirye-shiryen bikinta ne.
Tana fita ta fara zagayawa daga gidan dake maƙwabta da su. Da sallama ta shiga kamar dai ba
Ƴar Iya ba.
“Salamu Alekum, ina mutan gidan ko sun fita ne”
Goggo hari dake cin ɗumamen tuwon dawa tace, “A'ah yau kuma mu aka tuna shalelen Iya?,
Maraba lale iso muci ɗumame”
Zama Ƴar Iya tayi kan taburmar tana sinne kai. “Iy Aradu inna Hari yau ke na tuna, talla na
kawowa sirikan ki, bari na shiga ciki”
“Tallen me kuma shalelen Iya?” Goggo hari ta jefa mata tambaya.
“Maganin mata ne, ku fa tsofin nan kun fiye tambaya, haka iya ma ta sani gaba da tambaya to
Sarkin Aljanu da kansa ya koya min, kuma duk wanda bai siya ba Aradu mijin ta sai ya sake ta”
Ta faɗa tana miƙewa tsaye. Goggo Hari jin ambaton Aljanu da Ƴar Iya tayi yasa ba shiri ta bata
hanya.
“Allah ya kawo kasuwa” Gaba Ƴar Iya tayi abunta ba tare da amsawa ba.
Lirwanu ɗan Goggo Hari na farko ya fito zai fita suka ci karo da Ƴar Iya. Dakatar da shi tayi ta
hanyar faɗin “Mallam ka bawa matarka kuɗin siyan magani”
“A'a shalelen Iya ce?, Ya Iya ɗin tana lafiya”
Katse shi tayi da cewa
“Ba shi na tambaye ka ba in ka damu da Iyar ka je ka gaishe ta ai, mtsss ka bawa matar ka jaka
biyu da rabi kaji”
“Toh toh babu damuwa” ya faɗa tare da bin bayan Ƴar Iya har suka isa, su Ƴar Iya ashe akwai
hankali a bakin ƙofa ta tsaya jira, bayan ya fito ta tambaye shi ko ya bayar, da ya bata amsa ta
barshi ya wuce ita kuma ta kutsa cikin ɗakin.
Ala dole haka tabi sirikan Goggo Hari duk suka siya tukun ta fito daga gidan. Tunani ta fara ina
zata kuma nufa?
“Gidan Baba na!” ta faɗa tana murmurshi. Bata tsaya ko ina ba sai gidansu. A lokacin Inna
Zaliha na zaune a kan kujerar zaman gida tana wanke-wanke tana rera ƴan waƙen ta. Ko
sallama Ƴar Iya bata yi ba ta kutsa cikin gidan sai wani hura hanci take tana ɗaga shi sama,
bakin nan yayi gaba kamar bututu.
Inna Zaliha da fuskar ta ke nuna tsantsan mamaki ta kalli Ƴar Iya tana yatsina fuska
“Ke kuma rasa kunya daga ina?”
Ƴar Iya bata amsa mata ba sai ma ƙoƙarin sauƙe kayan tallar ta da take.
“Wai ba magana nike maki ba?, Me Kika zo yi gidana?”
Duk rashin hankali irin na Ƴar Iya sai da ta tsaya ta maimaita me kike yi a gidana cikin
ƙwaƙwalwar ta. Can ta kalle Inna Zaliha tace “Gidan ubanki ne ko nawa?”
Baki buɗe Inna Zaliha ke kallon Ƴar Iya tace “Eh ba shakka gidan ubanki ne kam..eh babu
shakka haka ne”
Ƴar Iya ta harare ta tace “In baki sa na dawo gidan da zama ba, shegiya mai shegen baƙin hali
da baƙar zuciya”
Inna Zaliha tuni ta tsure da zancen Ƴar Iya tunawa da sharaɗin da Bokan ta ya bata....hakan
yasa tayi murmushi tana sunkuyar da kai.
“Wa ya isa ya hana shalelen Iya guda?, Yanzu dai me ya kawo ki maza ki faɗamin” Ta faɗa cike
da ƙosawa coz zaman ta a tare da su akwai matsala.
Sai da ta gama shan ƙamshin ta tace
“Maganim mata na kawo miki ki saya, ai nasan kina amfani dashi”
“Maganin mata kuma Ƴar Iya?” ta watsa mata tambayar.
“Eh shi dai, ko kin fi so nayi ta maimaita magana kamar jaka?”
“Aah ba sai kin maimaita ba, wane iri ne”
“Irin wadda kike amfani da shi ki mallake min tsoho na har kika raba mu da shi gaba ɗaya,
Aljanu da kansu suka bani wannan maganin bari kiji, Kuma in Kika karɓa bakiyi amfani da shi
ba Aradu sai kin mutu, shegiya mai raba ɗa da uwa”
Cikin sanyin murya Inna Zaliha tace “Nawa ne?”
Ƴar Iya tace “Naira dubu biyu ne babu yawa, kuma zan dawo don kullum sai kin siya Aradu”
Zaro ido Inna Zaliha tayi tana kallon Ƴar Iya
“Dubu biyu fa kika ce shalelen Iya?”
“Eh haka nace!” ta bata amsa a fusace, “Kina amsar fiye da haka ma daga wurin Baba na ki
hallaka a wurin ƙato ai”
“Shikenan yi haƙuri, bari na ɗauko miki kuɗi” ta faɗa tana miƙewa don ta ƙosa Ƴar Iya ta bar
gidan zata shiga ɗakin taji Muryar Ƴar Iya “Ki taho min da dubu ɗaya zan biya na siya burodi”
Kamar inna Zaliha zata yi kuka haka ta amsa da to tare da shigewa ɗaki.
LIKE PLEASE
[5/18, 10:52 AM] Diamond Bhatool:
NAZARI WRITER'S ASSOCIATION
[Marubuta masu aiki da zallar fasahar zamani tare da bin ƙa'idojin rubutun Hausa cike da
kyakkyawan nazari don kawo sauyi cikin Al'umma]
*__KYAWAWAN NAZARI DOMIN AL'UMMA__*
ƳAR IYA
(MAI HANNUN ƁARNA)
[Labari/Rubutawa]
FADIMATU ADAMU HASSAN
DIAMOND LADY
{GARKUWAR NAZARI WRITERS}
★__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart
touching love __★
SADAUKARWA GA ƘUNGIYAR NAZARI WRITERS, ubangiji ya kula da al'amuran ku tare da
ƙara tsarkake muku alƙaluman ku. Allah ya bar mu tare.
BOOK 0️⃣1️⃣
PAGE 4️⃣1️⃣▶️4️⃣2️⃣
Dubu uku cas Inna Zaliha ta ɗauko tare da damƙawa Ƴar Iya tana zuba godiya. A yatsine Ƴar
Iya ta amshi kuɗin sannan tace
“Idan Baba na ya dawo kice masa inji ni ya bani wasu kuɗaɗe za'a yi bikin ƙawata daga nan
kuma nima za'a yi nawa ba daɗewa.
“to to zan faɗa masa, sai anjima”
Harara Ƴar Iya ta Banka mata tare da ɗago daron ta ta aza shi bisa kayin ta, nan ta fice abun
ta tana murna. Ganin tayi ciniki yasa ta yanke shawarar komawa gida ta adana kuɗin ta.
★★★★★★★★★★★★★★★★
*PRETTY POV*
Yammacin yau Laraba Pretty ta shirya kaima Sweetheart nata ziyara bayan ta binciko bayanai
game da shi.
Sanye take ciki wasu expensive English wears, Wanda suka ɗame ta sosai, surar jikin ta ana
gani kamar dai babu. Kitson attachment da tazo da shi ta sa aka sauya duk da ta kashe kuɗi
mai yawa kafin ayi mata, ƙwaƙuyayyen kan nata ta ɗaurawa wata cap na gashin doki tare da
gyara ta tsam, nan sai ka rantse gashin ta ne.
Fauzy ce ta mata makeup wacce ta mayar da ita mutum-mutumi, in ka ganta babu abinda zai
hana ka guduwa, hankali kwance ta fesa uban turare tare da yiwa ƙawayen nata alama da suzo
su wuce, suma da shigar tasu babu gwanda, sai dai ita sumy Abaya ta saka tare da rolling veil.
Cikin motar kuwa Pretty farin ciki