Author : DIAMOND LADY Category : Taskar Novels
ya shafa daga bisani ya buɗe closet nashi.
Cikin mintuna ƙalilan ya kammala shirin nashi, so masha Allah, ƙaryar mace ta gan shi tace zata
kauda ido, kyau kam ba'a magana ga kuma wani fayau da skin nashi yayi.
Turaruka ya fesa masu yawan gaske nan da nan ƙamshi ya buɗe ɗakin kamar kogin turare, har
ya juya zai fita ya dawo ya buɗe closet nashi tare da ɗauko wani ɗan ƙaramin kwali.
Ya salaaam! Turaren nan mai suna _Majesté impériale_ wanda ni gaskiya ban taɓa arba da
wani mai amfani da shi ba saboda tsananin tsadar shi, ko a ƙasashen Turai da wuya ka samu
masu amfani da shi sai waɗanda suka jiƙe da ruwan Kuɗi.
Yana fitar da turaren wani mayetaccen ƙamshi ya bayyana wanda yayi sanadiyyar disashe
ƙamshin turarukan da ya shafa. Kaɗan ya fesa daga nan ya jawo trolleyn shi ya jefa turaren.
Briefcase nashi ya ɗauka tare da trolleyn shi janye a ɗayan hannun ya sauƙa downstairs. A
nutse yake takawa har ya fito daga parlour.
Kamar jira suke ya fito kuwa suka amshe both trolleyn da kuma Briefcase nashi suna sara mishi
saying
“Good morning” in chorus.
Bai ko kalle su ba ya nufi motar da take tsakiyar convoy da suka shirya kamar dai yadda yazo,
yana shiga suka figi motocin sai airport.
Suna isa aka fitar da trolleyn nashi, sojan nan da ya ɗauki Briefcase ranar zuwan shi still yanzu
ma a hannun shi yake, hakan ya tabbatar min da cewa shi ɗin amintacce ne gare shi.
Sunayen da aka fara kira ne yasa ya nufi steps na Flight ɗin tare da shigewa, sojan ya bi bayan
shi. Without much time wastage Flight ɗin ya ɗaga yayi landing a jahar Adamawa, Yola.
*ADAMAWA STATE*
*YOLA*
*SHAGARI ESTATE*
Tunda suka nufo cikin ESTATE ɗin kowa ya tabbatar da cewa yaron General ne ya iso saboda
yadda ƙarar jiniya ke tashi.
Dai-dai wani ƙerarre kuma babban gida motocin suka yi horn, Babu arziƙi gate man ya wangale
gate ɗin.
Dai-dai parking lot ɗin su da ke ɗauke da wasu zuƙa-zuƙan motoci suka yi parking, bai bi ta kan
kowa ba ya fice don ko Briefcase nashi bai samu ta amsa ba.
Part na farko ya nufa, bai sha wahalar danna doorbell ba tunda ƙofar a buɗe take, kamar wani
na bin shi haka ya shiga da sauri.
Kai jama'a, anya kuwa wasu na tunanin mutuwa?, Makeken parlourn da na shiga ɗauko report
ne yasa na tuna da hakan.
Masha Allah kawai baki na ya furta, tsayawa bayani da kuma siffanta tsaruwar parlourn ma ɓata
lokaci ne ku dai kwatanta shi cikin zukatan ku.
Wani babban frame da naga wanda ke ɗauke da picture na wata kyakkyawar mata cikin shigar
indiyawa ya bani tabbacin Mom ce tare da Daddy. Sai wani frame ɗin mai ɗauke da hoton wasu
kyawawan samari da kuma iyayen su, tashi ɗaya na gano gwarzon maza kuma soja marmari
daga nesa wato _Hamma Zaki_ sai kuma ɗan uwan shi wato Hamma Saleem.
Ɗaya frame ɗin kuma dukkan su ne har da wata kyakkyawar yarinya wacce ta buɗe baki tana
dariya sai kuma Mom, Daddy, Hamma Saleem sai kuma Hamma Zaki da auta Fauzah.
“Mom, Mom, First love” (nace dama wannan yana magana haka ne?). Jin shiru bata amsa ba
ya kwaɓe fuska kamar zai yi kuka, cike da mamaki nace anya wannan kuwa HAMMA Zaki ne?.
Hanyar kitchen yayi yana ƙara ƙwala ƙiran
“First love, where are u?”
Kamar daga sama taji Muryar gudan jinin ta kuma mafi soyuwa cikin zuciyar ta. Ajiye cake ɗin
da take baking tayi tana yiwa Laraba alamar ta ƙarasa, daga nan ta fice da sauri.
Arba suka yi a dai-dai dining area ai kuwa da sauri ta ƙarasa tayi hugging nashi ta baya.
“Oyoyo My Son, so you wanna surprise us shiyasa ka shiga da wuri, Daddyn ka yace zuwa
yamma zaka shigo”
Murmushi yayi yana juyowa tare da facing Mom dake ta zuba murmushi kamar an mata kyautar
Aljanna. Peck ya manna mata a cheek nata sannan yace
“Common first love, ai gashi na baku mamakin”
Maƙale da juna suka dawo parlourn ta zaunar da shi kan sofa tana kallon shi tana murmurshi.
He can not afford to reject this saboda haka shima ya buɗe baki sai murmushi yake.
Sun shafe more than 5minutes kafin Mom tace
“Oya lemme get u some refreshments now” har ta fara tafiya ta juyo.
“Do You know what?”
Kai ya gyaɗa tare da zaro ido.
“Na yi baking favourite naka”
Ɗauke da tray ta fito, sai da ta tsiyaya mishi drink ɗin ta miƙa mishi, sai zuba take cikin Hausar
ta da kana ji zaka ɗan ba cikakkiyar bahaushiya bace.
Yana gama sha ya miƙe saying
“Mom, lemme fresh up please”
Duk irin gayu na Mom tana mamakin son nata, duk uban ƙamshin da yake yi wai let him fresh
up, mutum sai kace kifi. Ta faɗa a ranta.
Steps ɗin ya ɗale, yana isa bedroom nashi ya shiga.
Kai jama'a wannan guy fah he's addicted to white color, everything there is white ga kuma wani
makeken frame Mai ɗauke da photon shi shi kaɗai cikin wasu jahilan English wears daga gani
a wani beach yayi.. kyawun fuskar shi ba'a magana a picture ɗin.
Irin wannan shi ake kira da *NAMIJIN NOVEL* (Littafi na na gaba kenan)
Da sauri yayi wanka ya sanya jallabiya tare da feshe jikin shi da turarukan shi masu daɗi.
Yana fitowa ya nufi ƙofa, part ɗin Uncle Suraj ya shiga, bayan sun gaisa da Nenne matar uncle
take sanar da shi uncle Suraj baya nan.
Daga nan ya wuce part ɗin Uncle Bello, sun gaisa cike da girmamawa ya taho zai fita yaji
Muryar Salma cikin shagwaɓa kamar wata ƙaramar yarinya
“Mommah don Allah yau kam ki barni naje shopping ɗin nan kinga su Rumah da su Ayra duk
yau zasu je ko so....”
Bata kai ga ƙarasawa ba taci karo da Hamma Zaki da ya juyo ya zuba mata ido.
Haɗiye maganar tayi ta fara rarraba idanuwa tana ƙarasawa kusan shi. Cikin cracking voice
tace
“Good morning Hamma Zaki”
Ba tare da ya amsa mata ba ya watsa mata tambayar
“Meh ya hana ki zuwa school?”
Cikin Muryar inda-inda tace
“Uhm...eh..aaaa...damah ba...bani..da...lafiya ne”
Da ƙyar ta kai ƙarshe saboda irin kallon da yake jifan ta da shi kuma sarai ta san ya gano ƙarya
take.
“Shine kike tambayar fita shopping ko?”
“Eh...ah... I'm sorry Hamma Zaki....i”
“Shut ur mouth up”
Ya daka mata tsawa
“In na ƙara ganin baki je school ba ranki sai ya ɓaci, stupid girl”
Nan da nan jikin Salma ya fara rawa ganin hakan yasa ya wuce abun shi.
Mommah kuwa dariya tayi tana faɗin
“Alhamdulillahi, naji daɗin hakan, tunda dodon ku yazo ai zamu samu salama yanzu kam”
Bai zame ko ina ba sai part ɗin tsohuwa mai ran ƙarfe wato granny.
Tun daga bakin ƙofa ya fara jiyo ɓaɓatun ta tana faɗin.
“Yo ni AISHATU ina ganin ikon Allah, bari anjima Salamatu ta zo ta saka min ƙiran wayar nan
dai”
Sallamar shi ce ta dakatar da ita daga maganar.
“Ah soja marmari daga nesa, soja mazan fama an baro ƙasar nasara kenan?”
Dariya yayi sai a lokacin na ƙara gane cewa shi ƙarshe ne a kyau.
“Tsohuwa mai ran ƙarfe, nayi zaton ai in nazo zan tarar kin bunga ne”
Zaro ido Granny tayi tace
“Bakin ka ya sari guntun kashi ɗan baƙin ciki kawai, yo Ina dalili ni anya kai jinin Muhammadu
ne ma?. Kai to bari kaji in gaya maka in ma mutuwa ne ubanka da uwar ka ne zasu fara
mutuwa kafin ni, ja'iri kawai”
Dariyar sa yake babu ƙaƙƙautawa can yayi shiru
“Haba Uwar gidan Alee mazan fama kuma uwar Muhammadu, ai ba zaki mutu yanzu ba ko
bakya son ganin matar jikan naki ne”.
Goron da ta gutsira ta cire tana murmurshi sannan tace
“Ba shakka kuwa ammah kai anya ma akwai wacce zata aure ka, abu kamar kututturen ice ga
kuma fuska babu fara'a, wallahi duk wacce ta aure ka ma jaraba ta aura”
Hamma zaki yace
“Lallai ma tsohuwar nan, ni ne kututturen icen ko? To sai anjima”
Ya faɗa yana miƙewa zai wuce.
“A'ah haba Maigida duk kishi ne dai irin nawa kasan bana so kayi min kishiya ai”
Murmushi mai sauti Hamma Zaki yayi yana ficewa.
“Daga baya kenan, zan dawo Granny”.
Around 12:00pm wata babbar mota ta danno hanci cikin gidan, bayan tayi packing wasu ƴan
yara suka fito su shida.
Fauzah da kuma Yesmeen kan su ɗaya, Najma da Ra'eesa kan su ɗaya sai Rumah da Ayrah
suma kan su ɗaya.
Fauzah part ɗin su ta shige, Yesmeen da kuma Najma suka wuce nasu haka Ra'eesa da Ayra
suma suka wuce nasu part ɗin.
Ɓangaren Baffi yana ɗaga wayar yayi sallama sai dai ko amsa sallamar Principal bai yi ba ya
fara masa bayani.
“Baba gaskiya kazo ka ɗauki ɗiyar ka don ba zamu ci gaba da zama da ita a nan ba, hak kawai
a yau ta illata fiye da mutane bakwai”
Baffi yace
“Ka dubi darajar Allah Misbahu, duk wanda ya taimaki wani Allah zai taimake shi, kada laifin ta
yasa aikin ladan da kayi niyyar yi ya wargaje”
Da ƙyar dai Baffi ya shawo kan Principal ya amince Ƴar Iya ta ci gaba da karatun a makarantar.
★★★★★★★★★
*ƳAR IYA POV*
Cikin ƙanƙanin lokaci Ƴar Iya ta yi sabo da Ajiram, ƴan room ɗin su kuwa mamaki suke yadda
Boss ɗin nan ke taɗi da Ajiram.
Lokacin Sallah nayi Ajiram ta saka Ƴar Iya gaba kan su je suyi sallah.
“Hamrah, tashi muje muyi salla”
Da kallon mamaki Ƴar Iya ke kallon Ajiram tana tuna wai ma meyeh sallar ne. Ƙara maimaita
mata tayi
“Ki tashi muje muyi sallah”
“Bana yi” abinda ta tsinci Ƴar Iya na faɗa.
Zaro ido Ajiram tayi, na ta saka ta gaba ala dole sai sun je sun yi. Yadda take threatening Ƴar
Iya yasa ta miƙe ta bita.
Da ido ta bita gani tana alwala, ita fa bata taɓa yin salla ba tunda Innar ta haifeta. Haka dai ta
jiƙa fuskar ta da hannun ta matsayin Alwala. Bayan sunyi suka wuce mosque don yin sallah.
Ƙememe Ƴar Iya tayi ita wallahi bata iya ba kuma bazata yi ba. Da Ajiram ta takura mata sai ta
fashe da kuka.....
JAMA'AH KUN JI MUTUNIYAR YAU HAR DA KUKA??
TO AKWAI ƘURA FA!
MENENE SILAR FARA SAUYUWAR ƳAR IYA?
A TUNANIN KU SAUYI NE YA FARA SAMUWA?
ANYA ƳAR IYA ZATA IYA KARATUN NAN???
MUJE ZUWA ƳAN AMANA KU CI GABA DA ZUBO COMMENTS INA ZUBA MUKU UPDATE!
Oum Zainab ce
Garkuwar Nazari Writers.
[5/1, 1:14 PM] Diamond Bhatool:
NAZARI WRITER'S ASSOCIATION
[Marubuta masu aiki da zallar fasahar zamani tare da bin ƙa'idojin rubutun Hausa cike da
kyakkyawan nazari don kawo sauyi cikin Al'umma]
*__KYAWAWAN NAZARI DOMIN AL'UMMA__*
ƳAR IYA
(MAI HANNUN ƁARNA)
[Labari/Rubutawa]
FADIMATU ADAMU HASSAN
DIAMOND LADY
{GARKUWAR NAZARI WRITERS}
★__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart
touching love __★
I DEDICATED THIS BOOK TO NAZARI WRITER'S ASSOCIATION.
BOOK 0️⃣1️⃣
PAGE 1️⃣9️⃣▶️2️⃣0️⃣
Da Ajiram ta takura mata sai ta fashe da kuka. Ganin hakan yasa ta ƙyale ta tare da ɗumbin
tambayoyi a ƙasan ranta.
Yinin ranar haka ya Ƴar Iya ta shafe shi tare da sabuwar ƴar uwarta Aunty Ajiram ba tare da ta
ƙara shiga sabgar kowa ba.
★★★★★★★★★★★
*ALEE POV*
A nutse ya koma part ɗin su ganin Sarah a parlourn duk sai yaji gidan ya fita a ranshi. Sarah
ɗiyar uncle ɗin shi ne haka kawai yarinyar bata burge shi musamman saboda rashin kamun kai
irin nata. Har ya juya zai koma part ɗin Nenne tunda can akwai extra room da aka ware don shi
kasancewar shi ɗan ɗakin ta.
Step ɗaya yayi ya jiyo Muryar Daddy da a lokacin ya fito daga bedroom ɗin Mom.
“My son Ina kuma zaka je?”
Babu yadda ya iya haka ya juyo yana sakin murmushin yaƙe don sam baya son ganin Sarah.
“Sweet Daddy zanje mu gaisa da Granny ne, I don't even know u're back”
Ya faɗa tare da shigewa parlourn. Side hug yayi wa Daddy tare da manna mishi peck a kumatu.
Ita dai Sarah idon ta ƙyam akan Yaya Zaki ganin irin wani kyau da ya ƙara ga kuma girma da ya
ƙara yi a zuciyar ta take faɗin har ya so ya fi yayan nashi ma girma. Ganin yayi wa Daddyn shi
peck yasa ta saki wani murmushi, kiss is normal to her tunda su gaisuwa da kowa in zasu yi
haka suke a India to ammah wannan ɗin yafi burge ta musamman da taga Daddyn nashi
Nigerian ne amma kuma wayayye. Ji take kawai ina ma ita ta samu wannan dama Yaya zaki ya
sumbace ta.
“Baka ga Sarah bane, jiya tunda taji labarin ka dawo Nigeria ta bi ta dame su sai da suka barta
ta taho nan, she'll stay with us sai ka tashi tafiya ita ma ta koma”
Ran shi ne ya ɓaci a lokacin, don meyasa zata zo saboda shi, shifa ya tsani mutum maras
kamun kai more especially mace.
“Good morning brother” faɗin Sarah tana wani smiling as if tana tare da boo nata ne. Banza yayi
mata sai ma ƙara haɗe fuska da yayi.
“Kayi shiru son, ain't u happy to see her here?”
Sai a Lokacin yayi murmushin gefen baki wanda ba lallai ka fahimci yayi shi.
“I am” kawai yace tare da miƙewa.
“Son....wait where are u heading to?”
Narkar da face nashi yayi kamar wani ƙaramin yaro saying
“Zan je na gaisa da Granny kafin tace na zo banje ba” ya ƙarashe cike da ƙosawa. Coz shi bai
son yin magana a gaban yara musamman wannan good for nothing cousin sister ɗin tashi.
“Alright son, we'll have time da dare coz I'll be attending Quranic Memorization walimah of a
friend's daughter, and gobe da safe ina son zuwa Bauchi.
Murmushi Yaya zaki yayi tare da kissing Daddy a cheek daga nan ya fice ya bar Sarah Baki a
wangale.
Directly part ɗin Nenne ya wuce bai tarar da ita a parlour ba kawai ya wuce kai tsaye izuwa
bedroom nashi na part ɗin.
Wayar shi dake aljihun jallabiyar ce tayi ƙara, da sauri ya fito da ita yana kwantawa bisa
makeken bed ɗin shi. Picking call ɗin yayi ya kars a kunnen shi.
Daga ɗaya ɓangaren aka yi sallama kafin ya amsa
“Buddy ba kada kirki ko kaɗan, yanzu har ka shigo Nigeria bazaka sanar da Ni ba ehh?, Ka
kyauta”
A hankali cikin Muryar sa ta jaruman maza yace
“Sorry Man, ɗazu isowa ta gida and na so kiran ka sai na manta”
Kamar an sa shi dole haka yayi maganar.
“Alright zan shigo zuwa yamma”
“Ohk” daga haka bai jira me za'a ce ba ya katse ƙiran.
Yusuf da ke office nashi a asibiti ya janye wayar daga kunnen shi yana ƙare mata kallo cike da
mamaki ya furta
“He'll never change, zan so naga lokacin da zaka faɗa soyayya, u'll suffer” ya faɗa yana cije
leɓe.
Yusuf kenan, aminin Hamma zaki ne, Abbien Yusuf abokin Daddy ne ƙut da ƙut haka Amma
maman shi suna shiri da Mom sosai. Unlike Hamma Zaki Yusuf mutum ne mai fara'ar gaske ga
kuma kirki uwa uba barkwanci irin nasa. Ta yadda halayen su ya banbanta kenan sai dai duk da
haka suna matuƙar ƙsunar junansu.
Bacci ne ya ɗauke Hamma Zaki ba shi ya tashi ba sai around 11:30am. Toilet ya faɗa ya wanko
fuskar shi ya dawo. Wayar shi ƙirar Samsung Galaxy S24 ya ciro wacce tunda ya diro Naija ban
ga yayi amfani da ita ba. WhatsApp ya shiga don ganin messages ɗin da ya tara. Yana kunna
data kuwa suka fara zubowa kamar babu gobe, ganin sunyi yawa yasa ya ajiye wayar. Kusan
10 minutes messages na shigowa tukun ya ɗauki wayar don fara reply.
Daga can ƙasa Hamma Saleem me yayi mishi magana, “Hi brother, please when you're going
home text me so that I can book flight to spend the holiday with u”
Emojij surprise ya tura sannan yayi typing “Sorry Dear, I'm already home, banga ni da wuri ba”.
Haka yayi ta replying messages ɗin da yaga suna da muhimmanci saurann kuma yayi ignoring
coz mostly Ƴan mata ne ke mishi safe journey sun ƙira wayar shi bata tafiya, wasu kuma neman
soyayyar shi suke yi. Shi har mamaki yake yadda mace zata zubar da mutuncinta ta tunkari
namiji wai tana son shi abun haushin ma wasun kamar Mayu...duk da baya buɗewa bare ya
gani amma yakan ga subject ɗin.
Tsaki yayi shi kaɗai jin hayaniya kamar ana faɗa.
Rashin son hayaniyar yasa ya fito saboda ya