Author : DIAMOND LADY Category : Taskar Novels
ya hana ta sukuni, zata ga Sweetheart ɗin ta, babu abunda ke
tashi sai sautin waƙar India tuni ta manta duniyar da take.
Dai-dai Gate ɗin gidan General Muhammad Naira suka yi horn, gateman ya buɗe, sai da suka
kai dai-dai parking space suka yi parking motar. Ba tare da sun fito ba suka tsaya ƙarewa
motocin dake wurin kallo, ga kuma tsarin gidan da tuni ya tafi da su.
Pretty da ta tuna mai ya kawo ta ta ce “Babes wanne part ɗaya zamu shiga ne?”
Fauzy tace “Mu shiga na farkon idan ma ba nan bane ai za'a tura mu wani”
“ƙwarai yadda Fauzy ta faɗa haka za'a yi” Sumy ta amsa mata.
A gadarance cike da yauƙi suka fito daga motar tare da nufar entrance na part ɗin. Ganin door
ɗin a buɗe yasa suka kutsa kayuwan su ciki. Ƙamshin da ya daki hancin su kaɗai yasa su
lumshe ido, bisa latsa-latsan kujerun suka yiwa kansu masauƙi.
Ganin babu wadda ya ko gifta yasa Ishy faɗin “Pretty wai zaman me muke yi ne?, Letz just get
in mun tsaya a nan babu mai fitowa fa” Sumy kam da kallo ta busu don tuni gidan ya matuƙar
burge ta, sai taji inama ace tana da wata alaƙa da gidan. Su Fauzy ma dai zuciyar nan a
cunkushe ana bawa ido abinci.
“Assalamu Alykum” sallamar Fauzah da ta doki kunnuwan su yasa su waiwayowa don ganin
waye”
Mutuwar tsaye taso yi ganin baƙi a parlourn Mom, baƙin ma Christian, sai da ta hango Sumy
tukun taga ita kamar musulma ce. A hankali ta ƙara sa tare da faɗin “Ina yinin ku”
Murmushi duka suka yi mata tare da faɗin “lafiya ƙalau a tare”
“Bari na sanar da Mom tayi baƙi to”
Daga haka bata jira amsar su ba ta wuce bedroom ɗin Mom.
“Good evening Mom.... I'm back oh sorry u've visitor outside”
Cike da mamaki tace “Visitors kuma Fauzah, su waye”
“I don't know them but it seems like Christians ne, suna jiran ki” ta ƙarashe tare da nufar hanya
zata fice.
“Wait Fauzah, ask Laraba to bring something for them, Ina fitowa”
“Ok Mom”
Kamar yadda Mom ta umarce ta haka ta wuce ɓangaren su Laraba ta sanar da ita saƙon Mom
kafin ta wuce bedroom nata ta cire uniform tare da yin wanka. Sai da Mom ta ƙara kusan five
minutes ta fito sanye cikin kayan al'adar su, sari ce blue wacce tayi matuƙar ƙara bayyanar da
kyau da kuma izza irin ta Mom ga kuma kyakkyawar kwantacciyar baƙar sumar ta da ta zubo da
ita ta baya.
Jin takun takalmi yasa duka suka waiwayo..... idanuwan su suka zaro tare da sakin baki kowa
na ayyana abun da ke zuciyar sa. Cike da mamaki ganin duk ciki babu wanda ta sani yasa ta
ƙara ƙure su da ido ko zata tuna su. Su kuwa kallon da Mom ke jifan su dashi ya sauƙar musu
da shakkar ta na lokacin.
Tana ƙarasowa ta zauna tare dayin murmushi. Ganin kamar ba kansu ɗaya ba yasa Mom fara
gaida su.
“Ƴan mata ina yinin ku?”
Cikin ƙiƙina suka amsa babu kunya da
“Lafiya Mom,”
Mom! Mom ta ƙara nanata sunan cikin zuciyar ta, “Ikon Allah, wai mom ko wace Mom ɗin rai?”
ta faɗa a ranta a fili kuma tayi murmushi tare da faɗin
“Sannun ku da zuwa, sai dai ban gane ku ba fah”
Sumy ce tayi ƙarfin halin faɗin
“Laa Mom yaranki ne ai”
Ishy ta cafke da faɗin
“Mun zo wurin Captain ne Mom”
Mom kam sun ɗaure ta da abun mamaki, ita dai iya sanin ta Son nata baya ma kula mata bare
yayi mu'amala da waɗannan masu kama da Ashawos ɗin nan, murmushi kawai tayi tace
“Ku ƙira shi kuce kuna jiran shi parlourn”
Jin hakan yasa fitsararriya Pretty faɗin
“Ji rainin wayo...” bakin ta Ishy tayi saurin rufewa da hannun ta tare da fatan Allah yasa Mom
Bata ji ba, sai dai aikin gama ya gama.
Fauzy ce tayi ƙarfin halin faɗin “Ki bar zancen ku da Sulaiman ya wuce mana Pretty, na san
shine har yanzu a ranki” daga haka ta kalli Mom dake mamakin Pretty tace “Kiyi haƙuri Mom
kada kiyi tunanin dake take, tana da rashin lafiyar maimaita abu idan ya faru da ita, ga bata iya
mantuwa” Murmushi Mom tayi tace “babu komai”
Ganin shiru babu wacce ta ɗago waya ta ƙira Hamma Zaki yasa Mom tace “Ku ƙira shi manah,
ni zan wuce ciki”
Cike da duniyanci Ishy ta kaɗa yatsar ta “Wayyo Mom, Kinga saboda saurin da muke na har
mun mace wayoyin mu a gida”
“Shikenan bari na wuce, zan ƙira shi”.
Bedroom ɗin ta ta koma tana mai juya maganganun baƙin Hamma Zaki. Bayan ta sanar da shi
ta hanyar kiran shi a waya ta faɗa tunanin su waye waɗannan, ko suwaye da gani babu alkhairi
a tattare da su, yara sam babu ɗaa bare girmama babba.....
“Hmm to Allah ya kyauta, amma tabbas tana son sanin abu game da su.
Kwance yake yana latsa wayar sa kasancewar bai jima da dawowa daga wurin aikin shi ba. Ya
miƙa wayar zai ajiye gefe yaji ringing na wayar. Kamar ba zai yi picking ba ya na tsani tare da
ɗagowa, ganin Mom yasa ga zare idanuwa tare da picking.
“Sweetheart...” ba tare da ta barshi ya faɗi me zai ce ba ta katse shi da faɗin
“Kana da baƙi a waje, suna jiran ka a parlour”
“Parlour?” ya faɗa cikin sigar tambaya coz Basu yi da Dr. Faruq zai shigo ba ko wani friend
nashi.
“Who Are they Mom?”
“Get down and see” daga haka ta katse ƙiran.
Kamar baya so ya buɗe ƙofa tare da fitowa, shi ba mutum bane mai son gulma ba hakan yasa
bai dubo daga can ba. Black jallabiya be jikin shi, kamar koyaushe ƙamshin daddaɗan turaren
shi ke tashi. Sam ko kaɗan bai sa a ranshi matan nan ne baƙin shi ba hakan yasa ya miƙe zai
je Bedroom ɗin Mom. Cak ya tsaya jin an riƙe hannun shi. A hanzarce ya waiwayo don ganin
waye wannan. Dum! Ƙirjin shi ya buga, shi bai yi magana ba sai wani kallo da yake aika mata
cikin ranshi kuma yana faɗin (This girl again?”.
Ganin hankalin shi na kanta yasa ta marairaice fuska “Please Sweetheart, no sau ɗaya ka bani
damar nan, wallahi ina son ka shi yasa na baro Abuja takanas saboda kai, Please ko sau ɗaya
ka bani lokaci”.
Ba tare da yace mata komai ba ya janye hannunsa ya wuce zuwa bedroom ɗin Mom wondering
why yarinyar nan ta ƙara dawowa gare shi. Tun shigowar shi Mom ta tare shi “Kun gaisa da
baƙin ne?”
Kai ya gyaɗa yace “Mom, why are they here, ban san su ba” Mom tace “Ban gane ba, baka
sansu ba fa kace?”
Cike da ƙosawa yace “Is ok”
Daga haka ya fito, fitowar shi yayi dai-dai da shigowar Sarah daga bedroom ɗin ta.
“Good Evening bro”
“Evening” daga haka ya wuce zai haye stairs ɗin.
Ganin zai wuce yasa Pretty miƙewa da sassarfa tabi bayan shi, babu tsammani taji an riƙe
ƙugunta ta baya. Juyawa tayi don ganin waye ke shirin yi mata shamaki da abun son ta.
Cikin sanyin murya Sarah tace “You again?, What brought u here?” ta faɗa tana pointing Pretty.
Cikin son danne fushin ta don ita kanta ta fara tabbatar wa cewa Sarah matar Sweetheart ɗin ta
ne ko da ganin mahaifiyar Sweetheart ɗin nata tace “Rabu da Ni ba rigima nazo yi ba”
“Then me ya kawo ki?” jin tayi shiru yasa tace “Idan ma saboda shi ne ki sani baki kai ya soki
ba, mata masu daraja kaɗai ke samun matsuguni a zuciyar shi, hope I'm clear!”
Cikin jin haushi Pretty ta janye jikin tare da nufi bedroom ɗin da taga Mom ta shiga ɗazu, babu
sallama tace
“Mom!” mamaki ya hana Mom ko da amsawa ne sai jin Muryar Pretty tayi tana faɗin
“Mom na zo ne don furta soyayya ta ga ɗan ki Captain, da farko i thought zai yi sauƙi kamar ke
but ashe kawai hasashe ne iri nawa, don Allah Mom let him Know that Ina son shi. Gobe zan
wuce gida Abuja, amma zan ƙara dawowa”
Daga haka ta fice tare da yiwa su Ishy da ke cikin mamaki da ɗimuwa alamar su fito. Babu shiri
suka miƙe suna makawa Sarah harara tare da ficewa.
★★★★★★★★★
*ƳAR IYA POV*
Sana'a Ƴar iya ke yi babu kama hannun yaro, ciniki kuwa sosai baa magana, da zarar kayan
sana'ar ya ƙare zata ɗebo ta ƙara busarwa taje gidan Arɗo ta daka abun ta.
Samun da take yi bai hanata yin halin da ta saba ba, gashi bikin A'i sati mai zuwa ne, hakan
yasa Ƴar Iya bada himma wurin sana'ar ta, kullum tayi ciniki zata kawowa Halima ta ajiye mata.
Safiyar yau tunda Ƴar Iya ta tashi take jin shiga hancin mutane, hakan yasa ko karyawa batayi
ba ta fice sai gidan Inna Zaliha. Inna Zaliha da aka ce wai ciki gare ta abun yayi wa Ƴar Iya daɗi
don yadda ta san wannan kwaɗayayyiyar to dole zata ji daɗi musamman da ta tuna duk zuwa
gidan da zata yi sai ta tarar da abun daɗi.
Tana isa lokacin Inna Zaliha ta shiga bayi ga kuma tukunya bisa murhu ƙamshi na tashi. A
hankali cikin sanɗa ta ƙarasa wajen murhun tana lashe baki.
“Wayyo Ni Ƴar nan, yau akwai burauba, bari na samu na fice kafin mayyar nan ta fito.”
A haka ta ɗaga tukunyar daga kan murhun tare da lallaɓawa ta fice abun ta. Tana kaiwa hanyar
waje ta ajiye don ganin menene a ciki. Ido ta zaro tana faɗin
“Shegu ai yau kam mun haɗu, Aradu kun daina ci ku kaɗai”.
Dahuwa ce ta kaza wacce daddawa taji a ciki, ga romon jajir da shi kamar me.
Bata tsaya ɓata lokaci ba ta arta a guje sai gidan Iyar ta.
COMMENT PLEASE