Ba Sonta nake ba ( Tausayinta nake ) By UBEERA.pdf

Author :  Ubeera Category :  Hausawa Novels

Chapter   4 / 9

9K to 12K   out of 24.5K words

kaɗai zanyi sabida insha Allahu zanyi typing da iya yadda Allah ya
horemin na tunani da basirata insha Allahu littafin baze ɗauki lokaci mai tsawo ba zan gama shi,
sabida haka duk mai son ya biya kuɗinshi don ayi tafiyar dashi ga hanyar biya nan a ƙasa
amman pls bana son katin waya*✍


Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806
starling bank shaidar biya tanan 08142105218

*Fauzarh's Organic Skin Care*

*INSHA ALLAH YAU ZAMU FARA TRAINING ƊINMU DA MISALIN 8:30pm DUK MAI
BUƘATAR SHIGA TAMIN MAGANA NA BATA ACCOUNT NO DA ZATA TURA KUƊINTA.*

_Ina kuke masu buƙatar koyan Sabulai, Creams, Oil, Scrub,?? Ga fa dama ta samu gareku,
da kuɗin ki ƙalilan zaki koyi abubuwa da dama, domin yanzu wannan sana'ar tana ɗaya daga
cikin abubuwan da kasuwarsu ta ke ci, ke dai maza ki garzayo wajen FAUZARH akan farashi
mai kama da kyauta akan dubu ɗaya(1k) kacal za ki koyi abubuwa kamar haka_ *_Da farko zanyi bayani akan skin care, yadda za ki san kalar fatarki da rukunin da take.
Sannan zan yi bayani akan Menene molato. Aikin molato a jikin fata. Yadda ake awo da
muhimmancinsa_*

*YADDA AKE HAƊA SABULAI.*
1- Yadda ake molato body soap.
2- Yadda ake lightening black soap.
3- Yadda ake whitening black soap.
4- Yadda ake Acne/pimple set.

*YADDA AKE HAƊA OIL'S.*
1- Yadda ake carrot oil.
2- Yadda ake coconut oil.
3- Yadda ake molato oil.
4- Yadda ake pink lip balm.

*YADDA AKE HAƊA CREAM'S.*
1- Yadda ake molato body cream.
2- Yadda ake molato face cream.
3- Yadda ake molato scrub.
*BONUS*
Yadda ake haɗa shower gel.
Yadda ake haɗa papaya molato soap.
Sannan zan sanar daku inda zaku samu kayan haɗin duk garin da kuke.

*Domin neman karin bayani a tuntu6eni ta wannan nohttp://wa.me/+2347065012071*
[8/2, 2:10 PM] ❤️❤️ �� : *BA SON TA NAKE BA*
{ Tausayi ne }

NA
*AUTAR MANYA*


HOME OF QUALITIES WRT ASS....

007


Ƙarfe 4:30am ya farka bakinshi ɗauke da addu'ar tashi daga barci ya ziro da santala santalan
ƙafafunshi zuwa ƙasa tare da miƙewa tsaye, yana mai yamutsa fuskarshi wadda take nuni da
baccin nashi bai ma ishe shiba agurguje ya faɗa bathroom ya haɗa ruwan ɗumi ya watsa
ajikinshi tare da ɗauro alwala. Ya fito gami da shinfiɗa darduma ya soma gabatar da raka'atul fijir seda ya duba time yaga
lokacin shiga masjid yayi sannan ya miƙe ya gabatar da asubahi bayan ya idar ya soma rera
karatun alkur'ani mai girma wanda inba tsakanin jiya da yau ba ya ɗauki lokaci mai tsayi baiyi
karatun kur'ani ba kuma Alhamdulillahi tun jiya daya karanta baqrah yaji daɗin azuciyarshi
hakanan yau ma dayake karatun nan baƙaramin daɗi yake jiba.
Seda ya karanta shafi biyu nadaga cikin suratul kahfi sannan ya rufe qur'an appks ɗin dake
wayarshi kana ya soma karanta azkarul subhi, Bayan ya kammala yayi salati ga Annabi
muhammad (s.a.w)Tare da shafe jikinshi kana ya miƙe.
Gaban mirrow ya tsaya yana shafawa jikinshi cream ƙarfe shidda dai dai ya kammala shirinsa
cikin haɗaɗɗun Ash colour suite waɗanda suka amshi kalar fatar jikinshi sukai mai wani irin
kyau ɓarin turare yayi ma jikinshi haɗi da ɗaukar wata ƙaramar baƙar jaka wadda takardune
masu yawa acikinta. Wayarshi ya ɗauka tare da manna baƙin glass a saman fuskarshi ya nufi fita daga dakin yana
zuba wani irin haɗaɗɗan ƙamshi.
Ƙofar ɗakin yayi ma key da sauri yake tafiya yana dannah layin mutumin dasukai magana dashi
ajiya Cikin nutsuwa mutumin ya ɗauka suka soma gaisawa kafin ya sanar masa cewa gashi nan
a hanya.

Direct wajan motar shi ya karasa ya buɗe ya shiga tare da bata wuta kai tsaye hanyar kotun da
zasu fara shari'a ya wuce.
Tafiya kaɗan ya ƙarasa a bakin kotun suka haɗu da mutumin atare suka ƙarasa ciki inda shi ya
wuce wajan alƙali shikuma mutumin ya zauna zaman jiranshi.
Ƙarfe 11:00am aka soma gabatar da shari'a wanda Barrister Aliyu Ali Dikko shiya tsayawa
mutumin dake ƙarar Abokinsa daya cinye mai kuɗinshi wanda ya ranta mai waɗanda kuɗin suke
da mugun yawa cikin nasara suka soma gabatar da shari'ar wanda mutumin bai musa ba sedai
yace aɗan ɗaga mai ƙafa sabida halin rashin da ake fama dashi a ƙasarnan dan haka alƙali yayi
rubutu tare da buƙatar kowani ɓangare su sanya hannun yarje jeniyar biyan kuɗin da mutumin
ya amince zeyi nan da ƙarshen wata.

Alhamdulillahi Anyi shari'a lafiya angama lafiya don Kuwa komai ya tafi cikin tsanaki bayan an

tashi Aliyu sukai musabaha da jama'ar wajan sannan ya hau motarshi yayi gidan kakarshi
kamar yadda Yayi ma Ammin shi alƙawarin zuwa....



Banda rawa babu abin da jikin ummul keyi wanda hakan yayi matiƙar bawa ameerah tsoro
aranta take ayyanah kodai Ummul tana da wata lalurar ne wadda ita bata san da ita ba Babu
abin da take face saurin taje ta sadata da inda ta buƙata saboda gudun kar wata matsala ta
afku duk da har zuwa wannan lokacin bata tunanin acikin Ahalin ummul da wanda yasan inda
take da zama.
Tafiya ce mai shegen nisa kafin su ƙarasa cikin unguwar Tunga wadda anan gidan mahaifan
ummul yake tafiya ameerah take a hankali tana bin yadda ummul ke nuna mata ada idan sunje
har suka ƙarasa cikin layin gidan su ummul wanda ya cika da yara ana ta wasan ƙasa wasu
kuma na ƴar gala gala alamar yawanci yaran basuje makaranta ba sabida anyi ruwan dare gari
duk ya jiƙe.
Tunda motar ta doso layin yaran suka fara ihu! suna bin bayan motar suna shafata kafin
ameerah ta sami waje adai dai bakin wani ɗan madaidaicin gida mai ɗauke da farin gate tai
parking motar tata.
Dayake baƙin glass motar ameerah kedashi yasa na waje baya ganin na ciki dan haka seda
yaran suka gama ihunsu sannan ameerah ta kashe motar tare da fitowa waje.
Itama ummul a hankali ta buɗe nata ɓarin tare da fitowa ta dubi wani ɓaɓurarran gidan ƙasa
dayafi ko wani gida lalacewa a layin ta lumshe idanu tare da nufar wannan gidan mai farin gate
gami da sanya hannu tana kwankwasawa.
Kamar zata faɗi ameerah tayi saurin tarota jikinta ahaka wata ƴar yarinya da bazata fi shekara
goma sha biyar ba tazo ta buɗe musu gate ɗin tare da rabewa ta basu waje suka shiga ƙaramin
tsakar gida se kofar falo wadda ɗakuna da kicin da toilet ke ciki wanda alamu sun nuna gidan
mai komai acikine. A ɗan ƙarami falo suka yada zango saman kujera ummul ta kwanta tana kiran.
"Hajjah hajjah hajjata kina ina?"
Muryarta a hankali tana mayar da numfashi.
Da sauri wata fara jajir ɗin tsohuwa wadda zata kai shekaru sittin a duniya ta fito daga cikin
ɗakin dake kallonsu bakinta ɗauke da far'a take furta.
"wana keji kamar ummi agidan nawa?"
Tafaɗa tana ƙarasowa zuwa gaban ummul ganin ummu kwance saman kujera yasa wannan
tsohuwa wadda ta kira da suna hajjah ta ɗagata da sauri ta ɗora saman cinyarta.
A kiɗime take kallon ameerah tare da cewa.
"Mai ya sami ummi kuma ke yarinya?"
tafaɗa duk hankalinta yana wajan ummul.dake zubar da hawaye.
"Hajja tun jiya take ta zazzaɓi shine yau tace akawota gidan ki"
Ameerah ta faɗa tana mai yaba karamcin tsohuwar.
"To sannu ummi salame zoki kawo mata magani tasha taje ta kwanta daman seda nace karki
tafi ki zamanki anan kika kama hanya kika tafi yanzu wa gari ya waya kin bar ahalin ki cikin
takaici"

Hajjah ta faɗa tare da amsar ruwan da salame ta miko mata.
Tashi ameerah tayi tare dayi ma hajja sallama ta kama gabanta wanda hajja ita kuma ta kamo
ummul jikinta ta bata maganin tasha sannan tace ta kwanta bayan ta kunna mata fanka.
"Yi bacci anjima idan babanku ya fita se a aika akira babar taki, ni bana son ma ki ƙara tafiya ko
ina"
Lumshe idanu ummul tayi tana mai jin hajja da tatsuniyarta amman tafiya kam seta koma

"Bara na koma kicin na ƙarasa girki wannan ɗan rigimar ne ze ƙaraso gidan tunda yayi aure
shekara biyar yaron nan bai ƙara tako ƙafarshi gidana ba se yau"
Tafaɗa tare da nufar kicin.
Gyara kwanciya ummul tayi ba jimawa bacci yayi awon gaba da ita.....

Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806
starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400












_Akwai ingantaccan maganin gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin
zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu
lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya
k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar
sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga
sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya
mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da
wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal
zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI
GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah
duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu
'batawa kai lokaci_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye!
infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula
mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi

amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
[8/2, 2:10 PM] ❤️❤️ �� : *BA SON TA NAKE BA*
{ Tausayi ne }

NA
*AUTAR MANYA*


HOME OF QUALITIES WRT ASS....

009

Lumshe kyawawan idanunta tayi tare da dafe saman kirjinta wanda ya tsananta bugawa tamkar
zuciyarta zata faɗo Ƙasa.
Sake wara idanun nata tayi akanshi wanda ya wani kauda kai tamkar Bai taɓa ganinta acikin
duniyarshi ba.
Kafe shi tayi da lumsassun idanunta tana cigaba da kallon shi tamkar zata lashe shi duk da
ɗaure fuskar dayayi tare da cin magani kamar bai taɓa dariya ba, Ita hakan ma dayayi ba
ƙaramin ƙara dilmiya zuciyarta cikin tafkin kogon son shi yayi ba.
"Hajja ina kika san shi?"
Fitar amon! sautin muryarta ya bayyana cikin tambayar data ke ma hajja.
"Ke ni bani son kankanba da shegiyar tambayarki kamar ta ƴan jarida tashi tsaye naga ina ke
miki ciwo"
Cewar hajja dake ɓallo goron data kunce a gefen haɓar zaninta tana faman garza.
Tura baki tayi gaba cikin shagwabar data kema hajja idan suna tare gami da cewa.
"Nifa hajja bayana da gefen ƙuguna ke faman ciwo amman ina sanya ruwan zafi zanji daɗi"
Tafaɗa still idanunta kafe akan Aliyu wanda yayi kamar bai san da halittar ta a cikin falon ba.
Haushin yadda yayi banza da ita bai nuna yasan da ita wajan ba yasa ta miƙe da ƙarfin dayayi
saura agareta tayi hanyar ɗakin hajja.
Sedai ko taku biyu bata kai ba ƙugunta ya riƙe gam da wani irin sauri take ƙoƙarin juyowa sedai
yadda Bayanta yay mugun kawo damƙa yasa tai wani irin juyi ta zube bisa jikin Aliyu wanda
yayi suman zaune.
Gaba ɗaya baƙon yanayi ya saukar mata ajikinta da sauri take kokarin tashi ya sanya hannu ya
matse ƙugun nata yadda babu wanda ze lura da hakan wata irin ƙara ta sanya wadda hajja tai
saurin tasowa zuwa gareta.
"Haba Aliko kaiko kamar mai zuciyar mutanan farko zuciya a dake kamar ta rodi kaga yarinya
tana ƙarar azaba amman ka saketa ai ka tausaya mata"
Hajja ta sanya hannu ta janyo ummul jikinta da sauri ummul ta mike tana ɗingisawa ta wuce
ɗakin hajja hancinta shaƙe da ƙamshin mayen turaren shi.
Tsaki hajja taja mai sauti tare da kokarin bin bayanta.
Shiko ya sanya hannu ya kamo hajja ya zaunar ta gefenshi cikin tattausar murya mai ɗauke da
rashin Amo! ya fara magana.

"Haba hajja miye na ɗaukar zafin dan Allah karmuyi rabuwar haka dake please matar, Ita ɗin
wacece har zata shiga tsakanin soyayyata dake?"
Ya faɗa yana wani janyo numfashin sa da ƙyar.
Goge ƙwallar dake saukar mata tayi da haɓar zaninta.
"Dole naji babu daɗi idan naga ana nunawa ummi ƙyama na fuskanci tunda ka haɗa idanu da
ita kake jefa mata kallon ƙyamata to bari kaji ummi baiwar Allah ce wallahi kaji labarinta sekai
kuka fatana dan Allah ku rabu lafiya bana son daga jinina inga wani na nuna mata ƙyamata a
sanadin halin data tsinci kanta" Hajja tai maganar tana mai tashi ta nufi cikin ɗakinta inda ummul ta shiga.
Da kallo Aliyu yabi bayan hajja yana mamakin wannan cakuɗaɗɗiyar magana da hajja tai masa
wadda ko fahimtar mai take nufi bai yi ba.


Zaune ta tarar da ummul ta cusa kanta a tsakanin cinyoyinta tana riskar kuka!
Salati hajja taja tare da zama gefenta.
"Bari salame tazo ta siyo aboniki a shafa maki wancan miskilin baze je ya siyo miki ba sannu
ummi ta yaya kika buge?"
Zumɓura baki tayi gaba.
"Nifa hajja ba ciwon bane nagaya miki a ina kika san shi kika hau yimin faɗa bari nayi tafiyata
tunda kema ɗin dana kejin sanyi a wajan ki zaki fara hantarata"
Tafaɗa tana kokarin tashi.
Da sauri hajja ta kamota ta zaunar a gefenta.
Tahau share hawayen daya ke fitowa ta cikin idanunta.
"Bana Son inji kina ƙara faɗin zaki tafi ki barni ina fatan wannan zuwan da kikai ya zama shine
zaman ki na din din din a wajena dama kinga ni ɗaya ce semu sha zamanmu na tabbata babu
wanda zesan kina gidana"
"Shikuma wancan manta shi kikai Aliko ne fa ɗan wajan Ɗiyata Hafsatu dake aure a abuja
wanda yake baki alewa idan kina kuka kin tuna shi lokacin dayazo wani ƙarashen karatu nan
garin a jami'ar bayero har ya zauna a nan gidan"
Hajja ta faɗa mata cikin sigar murmushi.
Ɗan jimm tayi sannan ta ware idanu kamar yadda hakan ya zama al'ada cikin rayuwarta.
"Lahhhh hajja yaya Baffa daman shine amman ya nuna kamar be sanni ba?"
Tafaɗa tana zubo da wani hawayen.
"Ai baze nuna ba kinsan har yau halin shi na nan na miskilancin koda ma can da yake baki
alewar ai wai kukan kine bai so"
Hajja ta faɗi hakan tana dariya.
"Amman ya jima da barin nan tunfa ina yawo ba riga"
Tafaɗa tana kunshe dariya tuno da datai lokacin kuruciya.
"A,a yazo gaf da bikinshi shekara biyar lokacin bakya gida shiyasa baki sani ba,Mace ce ya
haɗu da ita shu'uma marar kirki ta karfin tsiya ta rabashi da kowa hatta uwarsa seya jima bai
leƙata ba"
Hajja ta faɗa cike da tarin damuwa acikin ranta.
Dum!dum!!dum!!! gaban ummul ya bada sautin hakan cikin rawar murya ta furta.

"Hajja yana da mata kuma harta ma haihu kilan?"
Tafaɗa tana mai kokarin danne tsinin mashin kishin daya taso mata.
"Yana da mata amman bata haihu ba se faman zaga ƙasashe suke mukuma muna nan muna
fatan karma ta haihun don irin su matarshi ba'a fatan haɗa zuri'a dasu domin irine na rashin
imani! duk wanda ze raba soyayyar ɗa da mahaifi ka duba tsabar rashin imaninshi"
Fakar idanun hajja tai ta goge hawayenta da sauri kuma ta mike tayi cikin bayin dake dakin
danne kukan dake neman tona mata asiri tayi tare da wanko fuskarta aranta tana ayyana
shikenan yayi mata nisa don ita a duniya tana tsoron kishiya musamman irin matar shi da hajja
ta gama faɗin halinta. A daddafe ta dafo bango ta fito da kallo hajja ta bita kafin ta tashi ta fita minti ɗaya ta kuma
dawowa.
"Ummi zo Aliko ya kaiki wajan masu gyara a duba ki dare ake ji"
Tana gama gaya mata hakan ta koma falo wajanshi wanda yaji wannan haɗasun da hajja tai
tamkar ta ɗaura mai dala da gwauron dutse ne akan sa dan dai kawai baya son tayi ɓacin rai ne
dan haka seya mike tare da daukar keyn mota ya fice.
Ummul kamar wadda aka shuka haka ta tsaya tana auna maganganun hajja kafin ta gyara
hijabinta ta bi bayan hajja zuwa falon.
"Ki bishi baya son jira yana waje"
Babu yadda zatai haka tabi umarnin hajja tabi bayanshi seda ta kare fuskarta da hijabi gudun
kar wani a yaran gidansu yaganta yaje yakai ma babansu rahoto sannan ta nufi motar gaban
motar ta bude ta shiga kusa da shi ta zauna.
Bai ko bari ta karasa rufe kofar ba yaja motar aguje yabar layin a hankali ta dai dai ta zamanta
tana mai tsirama hanya idanu...........
Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806
starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400
[8/2, 2:10 PM] ❤️❤️ �� : *BA SON TA NAKE BA*
{ Tausayi ne }

4 / 9