Author : Ubeera Category : Hausawa Novels
nuna hakan ya dame shiba.
"Babu yadda banyi da ita ba wallahi taƙi sha gaya can zazzaɓi ya kamata tana ta rawar sanyi"
Hajja ta faɗa tare da share ƙwallar dake zubo mata.
Da mamakin yake kallon hajja wannan wace irin ƙauna take ma waccan yarinyar kosu in suna
ciwo bata ɗaga hankalin ta haka.
Daɗan ɓacin rai ya dubi hajja.
"Ki dena kuka! dan iskanci abata magani a asibiti sannan taƙi sha dan ta rena ki, ina maganin
yake?"
Yafaɗa cikin rashin walwala.
Da hannu ta nuna masa ledar da tunda ya ajeta babu wanda ya ɗauketa.
Da matiƙar ɓacin rai ya sanya hannu ya ɗauki ledar tare da nufar bedroom ɗin hajja wanda
ummul ɗin ke cikinsa a kwance............
Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806
starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400
[8/4, 4:55 PM] ❤️❤️ : *BA SON TA NAKE BA*
{ Tausayi ne }
NA
*AUTAR MANYA*
13
Cikin nutsuwa ya ƙarasa cikin bedroom ɗin hajja murya can ƙasa yayi sallama wadda ta tsaya a
iya fatar bakinshi.
Tsaye yayi a bakin gadon ya zuba mata ido yana kallon yadda jikinta yake rawa ta cikin bargon
data rufa ajikin nata.
Yafi ƙarfin mintuna goma a tsaye yana auna yadda zeyi ya tayar da ita acikin yanayin daya
same ta.
A hankali yaja ƙafafunshi kamar mai tsoron ƙasa ya ƙarasa gaf da gadon ya sanya ƙafa yaɗan
bugi gadon kaɗan A hankali ummul taɗan zabura tare da furta.
"Wayyo Allah! dan Allah karka kuma kayi haƙuri na dena na dena"
Muryarta ke tashi cikin wani irin ƙaraji! rintse idanu yayi alama ta nuna mafarki take wanda
sautin maganar mafarkin nata ta fito fili, ɗan tsaki yaja ya kuma dukan gadon da ƙafarshi
Wannan karon ƙara tasan ya kaɗan tana jan ajiyar zuciya ƙaƙƙarfa.
"Khairy! khairy"
Yake kiran sunanta ahankali.
Cikin nutsuwa takejin saukar muryar wanda batai zato ba acikin kunnuwanta ahankali take dai
dai ta nutsuwarta wadda ta rasa acikin mafarkinta.
Yun ƙurawa tayi ahankali tana rintse idanunta sannan ta tashi daga kwanciyar data yi.
Ganin yana gab da ita ya sanya taɗan ja baya ta matse jikinta acan ƙarshen gadon ta cure
kamar mai jin sanyi wani irin ƙaƙƙarfan kuka ne ya tawo mata batare data shirya masa ba.
Kukan take da iyakacin ƙarfin ta tana jan ajiyar zuciya mai ƙarfi.
Rasa yadda zeyi da ita yayi, se kawai ya tsaya tare da harɗe hannunsa a saman kirjinsa ya
zuba mata dukkan idanunsa yana binta da kallo.
Cikin nutsuwa ya ƙarasa inda ta raɓe murya can ƙasan maƙoshi yake furta mata.
"Ke bani son sha shanci miye aka maki kike faman ɓare baki kina ma mutane kuka?"
Bata bashi amsa ba se cigaba da kukan nata data yi.
Rintse idanu yayi ko kaɗan baya son hayaniya arayuwar shi musamman kukan mace yana
sanya wa jikinsa ya mutu.
Wannan karon a hankali ya bita.
Samun waje yayi can gefenta ya zauna tare da kallonta kaɗan yace.
"Ɗago fuskar ki malama ki dube ni"
Yafaɗa muryarshi adake!
A hankali ta sanya hannu ta goge hawayen dake Zubo mata.
Tare da ɗago fuskar ta data yi jajir ta dube shi batare data iya janye idanunta akan shi ba.
Wani irin sahihin kyau yayi mata wanda take jin dama zasu dauwa ma a haka tana kallon shi.
Yana da wani irin baiwa ta musamman wanda ba kowa ne ze lura da hakan ba seya zauna
dashi Allah ya bashi abubuwa da dama musamman nagarta tare da kyawun zuciya da tausayi.
Baya cikin jerin maza masu mugun kyau! sedai yana daga cikin jerin nagartattun maza
waɗanda kowace mace take burin taga ta mallaka! kyawunsa sassanyan kyaune mai kwanciya
a zuciya.
"Sabida karki sha magani yasa kika dame ni da kuka?"
Muryar shi ta katse ta acikin tunanin data faɗa.
Janye idanunta tayi daga cikin nasa tare da ɗan turo bakinta gaba kaɗan.
"Nifa bana jin daɗi zazzaɓi ke damuna shiya hanani shan maganin"
Tafaɗa tana wani haɗe fuska kamar wadda zatai kuka!
"Hajjah zatai maki ƙarya ne?"
Yafaɗa yana ƙoƙarin saka idanun sa cikin nata.
wasa take da yatsun ta a wannan karon batai magana ba.
Ɗan sassauta fuska yayi tare da ɗan matsota kaɗan.
Duk girmanshi ya cika mata idanu da ɗakin.
Murya can ƙasan maƙoshi ya furta.
"Kiyi haƙuri kisha magani duk wani ciwo in ba'a shan magani wallahi baya tafiya ta sauƙi ki
ɗaure kisha ki shafa wannan cream ɗin shima in Allah ya yarda zuwa gobe zakiji kin warke"
Yafaɗa yana wani mayar da numfashi kaɗan kamar wanda yayi gudu!
Girgiza kai tashiga yi tana zubo da hawaye tasan maganarshi gaskiya ne gareta sedai ita ko
kaɗan bata ƙaunar magani.
Bata kai dayi mai magana ba taga ya miƙe tsaye ya fita daga ɗakin ba jimawa ya dawo
hannunsa riƙe da cup ya dire a gabanta.
Tare da ɓallo mata maganin guda ya miƙo mata babu musu ta karɓa yana tsaye akanta ta
haɗiyi maganin tana wani yamutsa fuska kamar mai shan maɗaci.
Amsar cup ɗin yayi ya fita waje mintuna kusan biyu suka dawo shida hajja abin mamaki da
kanshi ya shiga toilet ya haɗo ruwan ɗumi cikin bawo ya sanya tawul aciki ya fito ya miƙawa
hajja tare da furta.
"Ina falo zan ci abinci kafin ku kammala ke kuma ki mata gardama karki fasa"
Yafaɗa tare da fita falo.
Da ƙyar ummul ta yarda hajja ta taimaka mata wajan gasa wajan ta shafa mata cream ɗin
wanda babu abin da ummul take se kukan shagwaɓa tana matso hawaye!
A haka suka gama hajja takai bawon bayi ta dawo tana mata dariya tana cewa.
"Ke kam ummi raguwa ce ahaka zamuyi wankan jegon lallai duk mai maki wankan jego ze
kwashi takaici"
Tafaɗa tana dariya.
Turo baki ummul dake zaune rashe rashe a carfet ɗin hajja tayi wadda take ta faman zubo da
hawaye kafin tace.
"Allah hajja bakiji zafi ba wallahi Shikam yaci ka mugunta shine ze haɗo ruwan da zafi"
Murmushi hajja tayi tana cewa.
"Ai ni mamaki ma abin ya bani lallai kinci sa'ar Aliko da har ya tsaya ya kula dake! wanda
ƙannen shima in suna ciwo suna kuka zane su yake amman ke ai kinci sa'ar shi"
Hajja ta faɗa tana ficewa a ɗakin.
"Nikam ba wani sa'a se wahalar daya hassasa mini"
Tafaɗa tana mai shafo wajan wanda yade na mata zafin kuma zazzaɓin ma yaɗan soma sauka
ba kamar ɗazu ba.
Ya gama cin abincin ya kunna TV yana kallon labarai hajja tayo sallama falon.
Fuskarshi ɗauke da murmushi yake amsawa hajja tare da cewa.
"Har kun gama?"
Murmushi hajja tayi.
"Da ƙyar muka gama wannan yarinya badai kafiya ba,duk wanda ze mata wankan jego seya
shirya dambe"
Lumshe idanu yayi batare daya ce mata komai ba ya miƙe yana duba wayar shi tare da fiddo
dukkan girman idanunshi waje.
"Hajja 11 ta kusa fa bara na ƙarasa gobe nake son tafiya insha Allahu amman kafin na tafi zan
shigo na maki sallama"
Yafaɗa yana ƙoƙarin fita.
"Amman meya sa bazaka kwana anan ba tunda akwai ɗakuna naga an fara yayyafi"
Murmushi yayi wanda ya ƙara haska kyawun fuskarshi.
Yaɗan shafo kanshi kaɗan.
"Haba hajja ada dai na kwana amman yanzu ina magidan ci ina zan kwana gidan......."
Filo ta kwaɗo mai tana cewa.
"Ni zaka cewa haka to babarka ma nina haifeta bare kai"
Dariya yake wadda tai masa mugun kyau yana mai kallon hajja data haƙiƙance tana ta surfa
masifa.
"Allah ya huci zuciyarki hajja akwai ayyukan dazanyi da system shiyasa zan koma"
Yafaɗa yana mai dena dariyar daya keyi.
"ayyo to shikenan kaje ka ma ummi sallama seka wuce"
tafaɗa tana mai mayar da hankalinta wajan tv dan hajja tana tsananin son kallo.
Ɗan haɗe ran shi yayi kaɗan tare da cewa.
"Miye haɗina da ita hajja wannan ma bada maganin arziƙin ki taci ay"
Yafaɗa yana mai ƙoƙarin ya fice.
"Aliko karka fita kaje kawa ummi sallama ai babu daɗi yarinya babu lafiya ka kasa yi mata
sallama"
Babu yadda zeyi haka ya koma da baya zuwa bedroom ɗin hajja daga Bakin ƙofar ya tsaya
yana kallon ta yadda take ta faman saka hannu ta cikin rigarta tana shafo wajan ciwon.
A ranshi yake ayyana wannan yarinya ta cika raki.
Kafin ya ƙarasa ciki yayi sallama wadda ta bayyana gareta.
A hankali ta amsa mai batare data dubi inda yake ba.
"Ya jikin?"
Yafaɗa kamar an masa dole.
"Da sauƙi"
A hankali tai furucin.
"Zan tafi seda safe don gobe nake son komawa garin mu"
Yafaɗa kamar baya so.
Lumshe idanu tayi kirjinta na dokawa kaɗan kaɗan tace.
"Mai yasa baza ka kwana anan ba dare yayi fa sannan ruwa ake duba kaga window"
Tafaɗa tana mai nuna masa window ɗin da hannunta.
"Kawai sena kwana anan dan baki da hankali ke koda yaushe kin fi son mu keɓe da juna salon
na kwana anan ki lallaɓa ki bini ɗakin dana kwanta ai ko rashin shan maganin ki ma gulma ce
dan kinsan zan zo ne shiyasa kika ƙi sha dan mu keɓe ko?"
Yawani faɗi maganar cike da rainin hankali.
Ɗimauce wa ummul tayi da jin sharrin daya lafto mata.
Shura ƙafafunta take tana faman sakin kuka ƙasa-ƙasa.
"Allah ya saka mini ni wallahi ba haka bane"
Tafaɗa cikin kuka!
Dariya ya saki mai ƙayatarwa tare da saurin ficewa daga ɗakin ya tsincin kansa cikin nishaɗi da
shagwaɓar datai mashi ayan zu.
Bai tsaya wajan hajja ba yayi saurin fita waje.
Wanda hakan yayi dai dai da sanda ruwan ya kuma gocewa da tsananin ƙarfin gaske............
Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806
starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400
Wanna shagon kayan kwalliya ko kayan Gyeran jiki zakaje kayi sayayyar aqalla Naira 32k
sannan su baka kyeutar kayan 19k akan 1500?ko da kuwa sayayyarka ta Farko dasu kenan?
ORIFLEM sun bani garabasar kayan kimanin 19k
Maza kiyi sayayyarki Dan kema ki Samu taki garabasar!wannan Garabasar zata qare a 5 ga
watan nan.
Bata Qare anan ba,Kamfani yace daga nan zuwa 10 ga watan nan Register kyeuta ne,bazaki
biya kudin Register 4490 ba.yar uwa me kike jira????
Maza Danna wannan link na kasa domin Amfana da wannan Kamfanin Mai Albarka.
https://wa.me/message/ARQS3KWKIYKQD1
Ko Number waya
08064400588
[8/4, 4:55 PM] ❤️❤️ : *BA SON TA NAKE BA*
{ Tausayi ne }
NA
*AUTAR MANYA*
GARKUWA WRITTER'S ASS....
*14*
Tun ma kafin yakai ga fita daga cikin gidan hajja ruwan ya gama jiƙe masa jikinshi sharkaf.
Amman sabida tsabar kafiya da taurin kai irin nashi bai juya ya koma gidan hajja kamar yadda
ta bashi shawara ba haka ya shiga cikin motar duk jikinshi ya gama jiƙewa hatta ga saman
kanshi ruwan ke ɗiga.
A haka ya tashi motar ya bar layin tafiya yake cikin ruwan wanda hatta fitilar motar shi seda ta
dusashe sabida rashin wadatar haske sakamakon ruwan dake zuba kamar da bakin ƙwarya.
Ikon Allah kaɗai yakai Aliyu hotel ɗin daya sauka.
Anan ɗinma ruwan da ake tsulawa yafi na wanda ya baro agidan hajja horn ya danna masu
gadi suka tawo aguje cikin lema suka wangale mai ƙaton gate ɗin da sauri ya shigar da hancin
motar shi zuwa cikin parking lot na hotel ɗin ya jima yana saƙa yadda zeyi ya fita waje cikin
wannan ruwa dubarar kiran Abokin shi nas wanda suka zo kano tare suka kuma sauka a hotel
ɗin tare wannan wanda yayi mai magana a tun farkon page ɗinmu na baya, Sedai shi Nas ɗan
sanda ne na farin kaya bincike shima ya kawoshi kano dan haka ma tunda suka sauka basu
haɗu ba, Dan shi nas zeyi wajan sati ɗaya a kano saɓanin Aliyu daya gama aikin daya kawo shi
aranar yau dan banda dalilin gidan hajja ma da tuni ya jima da wuce wa gida.
Wayarshi ya fiddo yana niman numbern nas sedai abin takaici taƙi shiga haka yayita trying
amman wayar taƙi shiga tsaki! yaja mai ƙarfi tare da mayar da wayar aljihun jallabiyar yana
kallon saukar ruwan ta glasess ɗin motar.
Kashe motar yayi tare da fita waje wanda nan da nan ruwan yayi mai caaa akanshi yana dukan
shi.
Da sauri mai kama da gudu yake shiga ciki da gudu ya haye saman benen amman dukkan
jikinshi rawar ɗari yake na rashin sabo dan tun asali Ali bayi son ruwa ya taɓashi dukan ruwa na
saurin yi mai illah.
Da karkarwa yake buɗe ɗakin daya sauka yana gama buɗewa ya tura ƙofar ya shige ciki ya
kunna ƙwai wayar shi ya cillah saman gado da sauri da zafin nama yake ƙwaɓe rigar jikinshi.
Ataƙaice tawul ya ɗaura ya shiga bathroom ya haɗa ruwa mai zafi yana watsa wa ajikinshi.
Wajan mintuna ashirin ya ɗiba kafin ya fito yana zabga atishawa dafe kanshi yayi a galabaice ya
sauya kaya zuwa wata jallabiyar mai ruwan toka.
Wayar cikin ɗakin yayi amfani da ita ya kira ɗaya daga cikin ma'aikatan cikin hotel ɗin ya bashi
umarnin ya kawo mai black coffee, Ba jimawa yaji bugun ƙofar ya buɗe ya amsa ya koma gefen
gado yana kurɓar shi da zafinshi yana kammala wa ya koma bathroom yayi brush ya ɗauro
alwalar kwanciya bacci.
Kwanciya yayi saman gado yana dafe kanshi wanda yake mai ciwo ga atishawar daya ke ta
faman jerawa gaba ɗaya saman karan hancinsa yayi jajir yana fitar da gumi.
A haka wahalallan bacci ya kwashe shi wanda ko kaɗan baya jin daɗin sa..
Hawaye na zuba murmushi na sauka a saman kyakykyawar fuskarta ahaka hajja ta shigo ta
tarar da ita.
Tsaye tayi akan ta tana kallon ta cike da mamaki kafin tai gyaran murya tace.
"Ummi lafiyar ki wannan wani irin shashanci ne kina kuka kina murmushi kamar sakarya?"
Hajja take mata wannan maganar bayan ta nemi guri gefen gadon ta zauna.
Turo mitsitsin bakinta tayi gaba cike da sabo da shaƙuwar da sukai da hajja tace.
"Yaya Aliyu ne"
Tafaɗa tana ƙunshe kanta cikin hijabinta.
Murmushi mai ƙayatarwa hajja tayi.
"Me Baffan yayi miki kike kuka da dariya?"
Ta cikin hijabin tace.
"Hajja inna gaya miki zaki yarda?"
Murmushi hajja tayi.
Tare da cewa.
"Haba ummi mahaifiyarki haifarki kawai tayi amman rainonki duk yana hannuna dan kin san ba
da ban jarabar ubanki ba da babu yadda za'ai kibar hannuna sabida haka komai kika gayan
inna gaskiya ne zan gane inma karya kike zan gane ummi haka kawai Allah ya ɗoran
soyayyarki wadda bana wa jikokina dana haifi uwarsu" Hajja ta ƙare tana dariya.
"Hajja wallahi ban san mai yasa na damu da yaya Aliyu ba tun ma kafin nasan jikan kine naji ina
son shi dan Allah hajja ki roƙe shi ya soni"
Tafaɗa tana dunƙule wa waje ɗaya.
Murmushin dake saman fuskar hajja bai gushe ba ta furta.
"Kema kinsan baffa baze ce yana son ki tafarar ɗaya ba sedai muyi masa shigar sauri"
A razane ta ɗago tana kallon hajja dake jefa goro cikin bakinta.
Murya can ƙasa cike da ruɗani ta furta.
"Daman nima nayi wauta nasan ba kowani namijine ze dubi girman ƙaddara ta ya aure ni ba,
Dan Allah hajja gaya min hanyar da zanbi domin na kankare faitin dake bibiyata kodan Aliyu ya
zama mallakina?"
Tafaɗa tana kuka!
Jan yota jikinta hajja tayi tana shafa gadon bayanta.
"Ummi ba ina jifanki da baƙar magana bane ko ɗaya ni sema daɗin dana ji da kika ce kina son
jinina kuma koda kowa ya gujeki wallahi ni bazan gujeki ba! idan har hafsatu ɗiyata ce ta halak!
Aliyu ɗanta ne na halak to baya da mata seke ummi wannan karon zanyi masa shigar sauri
sedai ko kaɗan bana tunanin Aliyu ze soki sedai yayi maki son tausayi sabida matar shi
shu'umar mace ce, sedai kuma ko wace mace akwai tata kalar kirsar ban san taki baiwar ba
wataƙil da ita ki janyo shi jikinki"
Hajjah takai maganar tana kokarin miƙewa.
"Hajja na haƙura dashi, Ina tsoron kishiya domin naga zahiri akan Bamu dan Allah hajja karma
ki gaya ma Ammi tai masa dole akan ya aure ni bana son yadda mukai zaman boranci
agidanmu agidan miji ma na mai maita"
Tafaɗa tana sakin kuka tare da cusa kanta tsakanin kafaɗun hajjah.
"Aifa tunda kika furta kina son jikana sefa kin aure shi rufe bakin ki babu maiji bare ya gani
zamuyi abun mu cikin sauƙi"
Hajja takai tana dariya.
Turo baki tayi tare da sakin hajja ta koma gado ta kwanta.
Hajja ce ta fice a ɗakin tana furta.
"Munafuka kyayi kya gama"
Dariya ummul ta sanya tana rufe idanunta bata taɓa zaton komai zezo mata cikin sauƙi ba,
Tabbas hajjah mai son ta ce.
Shiko Aliyu koda ze yanka ta gunduwa gunduwa tana son shi zata zauna a haka.
Da wannan tunani bacci mai daɗi ya kwasheta wanda ta jima bata sami irin shiba.
Koda asubahi ma da ƙyar Hajja ta tayar da ita sabida nannauyan baccin daya ci ƙarfinta.
Acikin sujjadar sallarta sosai ta dage tana jaddada neman zaɓin Allah a tsakaninta ita da Aliyu.
Sabida acikin kwana biyun data san shi taji kaf duniya acikin maza masoyan ta bata da gwani
azuciyarta kamarshi.
Anan zaune tayi azkar ta miƙe tahau gyarawa hajja ɗakin seda ta kammala sannan ta wuce
kicin.
Da kanta take sarrafa abin break fast wanda ta kammala komai tsaf ta jere a center table bayan
ta baɗe ɗakin