MAKIRAR MACE COMPLETE BY Yellow .pdf

Author :  Yellow Category :  Hausa Ebooks

Chapter   2 / 6

3K to 6K   out of 18K words

Mai Dawa Sudani tare da Goggon Affan, duk kansu sukayi addu'a na fatan alkhairi sosai.
Wanda hakan yaƙarawa Affan ƙarfin gwiwa sosai akan cigaba da zuwa yana kaiwan zuma gidan Alhaji.
Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa, suka samu shaƙuwa, wanda har takai idan dai Alhaji baisamu zuma ba, to ko
da nawa za'a sai zuman Affan bazai siyar ba. Haka Affan ya kasance yana cika alkawari duk sati yana kai
zuma gidan Alhaji, har watarana yakai zuma da yaje yatarar Goje bayanan, ya tambayi Suhaima ta ce, "ai
Goje yaje ganin gida ne, sakamakon asalinsa ɗan karamar hukumar Manguno ne. Duk bayan lokaci zuwa
lokaci yakan, zuwa garinsu yayi kamar sati ɗaya yaga 'yan uwa yadawo". Affan yace "ayya to Allah
yadawo dashi lafiya". Suhaima ta ce "Amin". Affan yaƙara dacewa "amma iya yau kaɗai har naji badaɗi
da banga Goje ba". Suhaima ta ce, "kaine kaji badaɗi ko ni? Ai ni nafi kowa kewar Goje, tunda shine nake
gani a matsayin ɗan uwana na Jini". Affan yace "kina zaune a gidanku a gaban Babanki da Mamanki,
amma kice wai iya Goje ne kaɗai yake ɗebemiki kewa"? Suhaima ta ɗanyi ajiyar zuciya, sannan ta ce, "eh
kasan rayuwa ai kowa da gwaninsa".
By Sagiryellow ✍️08060616515.
MAKIRAR MACE
5.Affan yace "hakane magananki, to nikam zantafi sai in Allah yakaimu wani sati, kafin nan idan ƙauran
mata yadawo sai kigaishemin dashi, kafin nazo karɓar tsarabata". Suhaima ta ce, "to badamuwa Allah ya
kaimu". Affan ya fita yakama hanyar komawa gida, wasa ne gaske ne, chan la'asar liss tukun Affan ya
samu isa gida. Da shigarsa gida, yatarar da Mai Dawa Sudani ya kamo Dila, dashi da Goggo sunata gyaran
nama, cikin annushuwa Affan yayi sallama. Goggonsa ta amsa, "wa'alaikumussalam", sannan taƙara da
cewa "ka dawo"? Affan yace da Goggo "eh sai yanzu Allah yayi", buɗan bakin Mai Dawa Sudani ya
tambayi Affan, "minene sunan mai gidan dakake kaimusu zuma"? Affan yaɗanyi shiru, yace "gaskiya
nibansan asalin sunansa ba, ni dai kawai naji suna kiransa da Alhaji". Mai Dawa Sudani yace da Affan,
"yanzu fa ba irin wannan zamanin bane, babu tayanda za ayi haka kawai, rana a tsaka kabi jiro wata

alaƙar da dachan babu ita kaɗaura, yanzu kaiba yaro bane, yakamata ace kadaɗe da sanin wannan".
Affan yace "hakane Kaka, amma dai ina kyautata musu zato, shi Alhaji mai gidan, nafahimci sanannen
mutum ne, ina da yaƙinin mutumin kirki ne". Mai Dawa Sudani, ya ɗanyi ajiyar zuciya, sannan yace "kai
dai kaga mutum kawai Affan, rayuwa yanzu duk tawuce tunaninka, don haka nayi maka iyaka da gidan
daga yau". Affan, yayi shiru, sai chan yace "Kaka banƙi taka ba, na amince zan daina zuwa, amma kabani
dama nacika musu alkawarin dana ɗauka musu nacewa zankai musu sati mai zuwa, daga nan iyaso sai
nayi bankwana dasu".Jin hakan yasa Mai Dawa Sudani yace "to Allah yakyauta", sannan ya umurci Affan
da ya hura wuta domin su fara ɗaura naman, Affan yace "to"! Mai Dawa Sudani yacigaba da yanka nama
Goggo tana rike masa, haka dai suka kasance sunata aikin naman Dila har tsawon kwana uku, daga nan
ne wayewar garin rana ta huɗu Affan yashiga cikin Jeji domin ɗebo zuma, duba da irin yanda zuman ta
taru dayawa, yasa washagari ma Affan yaƙara komawa yaɗebo. Sannan ya shirya tsaff yana jiran wayewar
gari yatafi cin kasuwa. Wayewar garin ranar talata, da sassafe Affan yatashi yashirya, bayan yakammala
komai Affan ya shiga ɗakin Goggonsa domin yaɗibawa Suhaima da Goje irin naman Dila. Goggon Affan
tamiƙe ta ɗauko wata babbar leda daga cikin ledodinta datake sokewa ajikin azara, ta buɗe ledan
tasakawa Affan naman sosai yanda yadace. Affan ya karɓa yana mai godiyawa Goggonsa. Anan suka rabu
suna masu shauƙi, Affan yatafi cikin gari, da Affan yaje gidan sai yayi dace yatarar Goje yadawo daga
garinsu. Goje da ganin Affan yataho da gudu yatari Affan, yana farin ciki, suka ƙarisa suka zauna a bencin
Goje, Affan yafara dacewa "ƙauran mata kasha hanya", Goje yace "gaskiya kam", Affan yace "ai ranar
nazo kawai sai Suhaima takecemin bakanan, shine tafiya ko sallama babu"? Goje yace "kayi haƙuri
shafa'a nayi". Affan yace "bakomai, to yanzu dai ina tsarabarmu to"? Goje yace "iyale sunyi yawa a gida
bansamu na riƙo muku komai ba". Affan yace "amma gaskiya baka kyauta ba indai hakane, kaga kuwa
irin yanda 'yar Alhaji take kewarka da bakanan, yanzu ace bakariƙo mata komai ba"? Goje yace "wacce
'yar Alhaji kuma"? Affan yace "Suhaima mana". Goje yaɗanyi ajiyar zuciya, sannan yace "Suhaima dakake
gani fa ba 'yar gidan nan bace, wanke wanke da shara da sauran wasu ayyuka takeyi a gidan nan. Bata da
wata alaƙa ta kusa, balle ta nesa da mutanen gidan nan, kuma ta ɗauki tsawon lokaci tana aiki a gidan
nan, amma abinda zai baka mamaki shine, tunda take bata taɓa zuwa ko da ganin gida garinsu ba,
ballema wani yasan wani ɗan uwanta. Abinda zai ƙara baka mamaki kuma bazaka taɓaji koda a wasa
Suhaima takawo maka taɗin gidansu ba. Daga ƙarshe Goje yace bugu da ƙari kuma shine, Suhaima ta
kasance tana da farinjinin samari, sam, wani abun mamaki batason maganan abinda yashafi soyayya ma,
balle har akai ga maganan aure. Sakamakon bana mantawa akwai P.A na Alhaji, wanda yanuna yana
matuƙar ƙaunar Suhaima da aure, amma taƙi, kuma mutum ne wanda bashi da wani aibu, mutumin
kirkine abinda ya bayyana mana a zahiri". Jin hakan yasa Affan har sai yakasa cewa komai face, dogon
numfashi kawai daya Jaa! Sannan Affan yace "minene aikin mai gidan nan"? Goje yace "mai gidan nan
Justice ne, sunansa Justice Bakura, shikuma P.A sa daya nuna yana son Suhaima Barrister ne, shine
Barrister Hayatu". Affan yace "amma ita Suhaima bata taɓa faɗamaka dalilin da yasa ta ƙishi ba"? Goje
yace "ta ce, wallahi har cikin zuciyarta bawai taƙi Barrister Hayatu, sabida wani aibunsa bane". Affan
yakara tambayar Goje, "amma akwai wanda ita takeso ne tun a baya"? Goje yace "ita dai tanada farin
Jinin samari harma da manyan mutane, amma kowa yazo sai tace yayi hakuri. Wannan yasa har watarana
nake bata shawarin cewa, ya kamata tagane shi lokaci baya jiran mutum, yanzu ne lokacin da ya kamata
ace kin tsaida mijin aure tunkafin a wayi gari kowa yadaina zuwa wurinki. Sai Suhaima tabuɗi baki
tacemin, itafa ta tsani aure kwatanta arayuwata, bataso taji kuma ana alaƙanta ta dashi ko kaɗan". Cikin
firgici Affan yace da Goje "haka kukayi da ita"? Goje yace "tabbas haka mukayi, amma bansani ba ko

wasa takemin, don kasan wani lokaci kamar kakanta take ɗauka na". Affan yace "hakane Kam, amma dai
ba lafiya ba, akwai wani abu dole zan san tayadda zanɓullo mata nasha cikinta naji koma miyene"?
By Sagiryellow ✍️08060616515.
MAKIRAR MACE
6.Goje yace "a gaskiya, abune mai wuya Suhaima tafaɗama dalili, sakamakon Suhaima ta kasance bata
ɓoyemin komai, amma a wannan fannin sai kyaleta kawai nayi, domin nafahimci bazata faɗamin ba".
Affan yace "aini akwai abunda nake hasashe ne yanzu haka, akan shine matsalan Suhaima". Goje yace
"minene hasashenka"? Affan yace "Ina tunanin zata iya yiwuwa aljanine ya aureta, domin kasan idan
aljani ya auri mace to da zarar wani yazo mata da maganan aure ma faɗa zasuyi, koda kuwa abaya suna
mutunci sosai". Jin hakan yasa Goje yace "kuma fa maganan ka akwai ƙamshin gaskiya a cikinta, sabida
haka bari naje na kirata domin katabbatar da hasashenka". Kawai Goje ya tashi ya shiga cikin gida, bayan
wasu 'yan mintuna sai ga Goje yafito tare da Suhaima. Tana ganin Affan ta ce, "mai pure honey ka iso
kenan"? Affan yace "eh!" Suhaima ta ce, "to sannu da zuwa". Affan yace "yauwa", sannan yaɗauki
naman Dila da yazo dashi a leda yamiƙawa Suhaima yace da ita "gashi naman Dila nazo muku dashi, ki
karɓa sai kirabamuku". Suhaima tasa hannu takarɓa, ta ce, "aikuwa kayi dabara da bakamiƙawa Kura fiɗa
ba, domin inda kabawa ƙauran mata, to da sai dai naji labari". Buɗan bakin Goje yaja tsaki tswwwwww!
Sannan yace "dallachan, kece baƙuwar cin naman Dila, da ni ba a sati banci naman Zaki ba, lokacin ina
tsakiyar fita farauta Daji". Da Affan da Suhaima dukkansu sukayi dariya suka haɗa baki sukace "Chauuu!
Sa'A dai ƙaura Jaa Yaki!" Goje yaɗan haɗa hannayensa yace dasu "AHA Sa'A dai!" Daga nan sai Affan yace
"yauwa, Suhaima nazo miki da wani shawari ne yau". Suhaima ta ce, "na miye haka"? Affan yace "na
alkhairi ne". Suhaima ta ce, "to Alhamdulillahi! Ina jinka"? Affan yace "wani mai gida nane yacemin yana
buƙatar matar aure, shine naga yadace na miki magana ko zaki bashi dama yazo kuga juna"? Suhaima ta
ce, "wani mai gidan ka kenan"? Affan yace "customer nane, kuma gaskiya bawan Allah ne bashi da laifi,
inaso kibani dama sai muzo dashi kiganshi". Suhaima ta ce, "a'a nibana buƙatar ganinsa, domin niba aure
zanyi ba". Affan yace "to Suhaima yanzu a shekarunki inbakiyi aure ba, to mizakiyi"? Suhaima ta ce, "ni
kawai na zaɓi na mutu banyi aure ba a rayuwata". Affan yace "subhanallah, sabida mi kika zaɓi haka"?
Suhaima ta ce, "ni kawai natsani maganan aure ne a rayuwata". Affan yace "dama chan Suhaima kintaɓa
yin aure ne a baya"? Suhaima ta ce, "ni ban taɓayin aure ba, sannan kuma ni bantaɓa sanin wani ɗa
namiji ba". Affan yace "to indai hakane, nafahimci akwai irin fahimtar da kikayiwa aure wanda kuma ba
hakatake ba, sabida haka ya kamata kigane cewa shi aure Ibada ne, yazo mana a shari'a sunnar Manzon
Allah ne (s.a.w) wannan yasa duk wani ɗan Muslimi yake burin yaga yayi aure. Domin raya wannan
Sunnar da kuma samun tarin falalar da yake cikinsa, sannan kuma mutum yaga ya samu 'ya'yan da
zasuna yimasa addu'a, ko da bayan ya rasu. Rayuwar duniyar, duk kusan akan wannan muketa faɗi tashi,
domin kowa yaga yacimma irin manufofin nan, amma taya Suhaima ke zakice bakya ƙaunar maganan
aure"?
By Sagiryellow ✍️08060616515.
MAKIRAR MACE

7.Suhaima tabuɗi baki ta ce, "bazan iya baka amsa akan wannan tambayar ba". Jin hakan yasa Affan yace
"to amma zaki iya faɗamin ke mutumiyar ina ne"? Suhaima ta ce, "ni haifaffiyar garin Konduga ce, dake
nan jihar Borno". Cikin mamaki Affan yace "anan kusa kike ma ashe, to amma yanzu haka iyayenki suna
zaune a chan"? Suhaima ta ɗanyi shiru! Chan ta ce, "iyayena tunda jimawa Allah yayi musu rasuwa,
sannan ni kuma nataso ne, a hannun yadikkona (kishiyar Mamana), tun ina yarinya, har nakai matakin da
nafara mallakar hankalina, ma'ana nafara amsa sunan Budurwa. Daga nan ne, na yanke shawarin barin
garin mu, watarana batare da nayi shawari da kowa ba, nahaɗa ƴan kayan sawana acikin gari yayi zafi
nafita a gida, batare da nasan inda zani ba. Cikin ikon Allah kuwa fitowa ta ke da wuya, sai naci karo da
wata motar pure water, wacce tamiƙa nan garin Dambuwa, a wanchan lokacin, zata kawo ruwa, sai nayi
dace kuwa da na buƙaci suragemin hanya, suka ɗauke ni har zuwa nan cikin garin Dambuwa. Bana
mantawa bayan mun iso suka saukeni a bakin kasuwa. nayi musu godiya sosai, suka wuce suka barni a
tsaye a wurin, inata tsaye, sai sake sake kawai nakeyi harna tsawon wani lokaci. Chan bayan rana tagama
takewa, yunwa da ishiruwa sunfara cin jikina, sai nafara tafiya batare da nasan inda na dosa ba, sai chan
na hangi wani layi daga gefen hanya, na nufi layin, tafiya nakeyi chan naga wata baiwar Allah na zaune a
gidin wata bishiya. Tare da ɗan buhunta da robar ta, da alamun dai bara takeyi a wurin, wannan yasa
naƙarisa na taddata a wurin, nayimata sallama, bayan ta amsa, sai naga ashe Kuturwace bara takeyi a
wurin. Na gaisheta, mukagaisa sosai, na nemi wuri naɗan zauna a gefe da ita, sai ta fahimci akwai
damuwa a tattare dani, wannan dalilin yasa ta ce, dani yarinya lafiya kuwa? Nace da ita lafiya qalau
Baaba, taƙare min kallo tace kai ba lafiya ba yarinya, sannan taƙara dacewa ke daga ina ne haka? Na
ɗanyi mata taƙaitachcen bayani akaina, nayi dace kuwa ta fahimceni, daga nan sai ta ce dani to yarinya,
nidai yanzu alfarma ɗaya zan iya miki, sakamakon a matakin shekarunki yin bara baidace dake ba. Domin
nima danake tsohuwa bata hanyar bara nakeci nake sha ba, sakamakon bara haramunne a Muslimci,
amma akwai wani gida a bayan unguwan mu, gidan Alhaji, mutum ne mutumin kirki sosai, yana iya
ƙokarinsa wajen taimakamana. Don haka tunda keɗin da ƙarfinki, idan kin amince sai muje na nemamiki
alfarmar yimusu aikatau, sabida ta wannan hanyar ne, za kici Kuma kisha, kisamu Zanin ɗaurawa ajikinki.
Amma ko ya kika gani? Cikin gaggawa nabuɗi baki nace mata na amince. Kamar da wasa kuwa tamiƙe,
mukatafi tiryan tiryan har nan gidan mukazo da ita, kai tsaye tashige dani har cikin falon Hajiya, ta
tarbemu hannu bibbiyu, anan ne Baaba tagabatar dani a Hajiya. Atake kuwa Hajiya tace bakomai ta
amince, daga nan Hajiya ta tambayeni amma ya sunana? Na buɗi baki nace sunana Suhaima. Hajiya tace
ayya to yayi kyau, daga nan ta zayayyanemin duk irin ayyukan da zannayi, sannan ta tashi ta nunamin
ɗakin da zan zauna. Bayan anyi hakane sai Baaba tabuƙaci ita kam zata koma gida, anan mukayi sallama
tawuce gidan ta, nikuwa tabarni da Hajiya, washagari kuwa natashi da aiki. Affan to kaji wannan shine,
dan taƙaitaccen tarihina wanda zan iya faɗa muku. Kunji dalilin yanda akayi har nafara aiki a gidan nan, a
takaice". Har bayan Suhaima tayi shiru, daga Affan har Goje, dukkansu sukayi shiru tamkar ba kowa, har
sai bayan wasu yan dakikune tukun, Affan yace da Suhaima, "amma miyasa kike ɓoye mana wasu
abubuwan agame da rayuwarki"?
By Sagiryellow✍️08060616515.
MAKIRAR MACE
8.Suhaima ta ce da Affan, "amma miyasa kace haka"? Affan yace "kalamannki sun nuna akwai abinda
kike ɓoye mana". Suhaima ta ɗanyi ajiyar zuciya, sannan ta ce "kai dai kabari kawai", daga nan ta kawar

da zancen, tace "yanzu dai mai pure honey ga naman Dilan nan ka raba mana kawai". Affan ya buɗi baki
yace "a'a nikam aikune ɗaya, don haka kuje kuraba abunku, nikam yanzu ma zan koma gida ne, ina
tunanin kuma inna tafi ba lallai na ƙara dawowa ba". Cikin firgici Goje yaja dogon numfashi, sannan yace
"Affan miyasa zakace haka"? Affan yace "bakomai fa, kawai dai yanzu zuman ne, tafara ƙarewa a jejin,
wannan yasa yanzu farauta zamu komayi a Daji, dani da Kakana Mai Dawa Sudani". Cikin jimami Suhaima
ta ce, "yanzu kenan, kana nufin mun rabu kenan daga yau"? Affan yace "a'a, kusa aranku indai muna raye
watarana zanzo muku, dani da ku aikusa aranku mun zama daya".Daga ƙarshe Affan yace da Goje da
Suhaima "kasancewar mu 'yan Adam ajizai ne, ku yafeni dan Allah". Goje da Suhaima duk kansu suka
haɗa baki sukace, "Affan bakamana komai ba". Atake shima Affan cikin tattausan murya yace dasu "nima
na ya feku". Daga nan ya rungume Goje, ita kuwa Suhaima na tsaye a gefe guda hawaye ne kawai ke zuba
a idaniyarta, Affan ya juya yana mai yimusu bye bye, har yafita a cikin gidan. Bayan Affan ya fita a gidan,
daga nan ya wuce tallen zumansa, wurin sauran customers ɗinsa da ya saba kai musu. Bayan Affan ya
kammala saida zumarsa tsaf ne, yakama hanyarsa ta komawa gida, Affan tafiyarsa yakeyi a sannu a
hankali har ya samu isa gida. Ya tadda Kakansa na zaune a bakin bukkarsa, yanata dakan itatuwa wanda
yake sarrafasu zuwa magungunan gargajiya. Affan yaƙarisa dab dashi yace "sannu Kaka". Mai Dawa
Sudani yace da Affan "yauwa sannu Affanu" kamar yadda yasaba kiransa dashi, sannan yaƙara dacewa
"kadawo"? Affan yace "eh, Allah yayi, sannan Affan yakara dacewa yau kam nayi bankwana da mutanen
gidan Alhaji, sabida wannan dalilin yanzu inba ranar kasuwa ba, bazanna shiga cikin gari ba, domin dama
ƙarfin shigana shine, ina barin kuɗinane a gidan, sakamakon ba kullum nake samun mai gidan ba. Mai
Dawa Sudani yabuɗi baki yace "tabbas ka kyauta, najidaɗi sosai dajin wannan daga bakinka, sabida haka
Allah yayimaka albarka". Affan yace "amin Kaka". Daga nan Mai Dawa Sudani yace "yanzu abinda zaifaru
shine kashirya idan Allah yakaimu gobe farautar da zanje sai mutafi tare". Affan yace "to Kaka, Allah
yakaimu", sannan ya tambaya "ina Goggo nah Kuma"? Mai Dawa Sudani yace "tana cikin bukkarta, bata
jima da shiga ta ɗan kishingiɗa ba". Affan yace "ayya to bari na barta sai ta tashi kawai". Daga ƙarshe Mai
Dawa Sudani yace da Affan "kafin ka shiga ɗaki, akwai tozali dana ajiye akan saman adakata, ka ɗauka ka
sanyashi yanzu. Tozali ne na wankin ido, sannan kuma katabbatar ka seta barudunka (bindigarka) kafin
zuwa gobe, domin inaso ne zamubi ta chan yankin bakin kogi".
By Sagiryellow ✍️08060616515.
MAKIRAR MACE
9.Affan yace "to Kaka", daga nan Affan yaƙarisa wurin adakar Mai Dawa Sudani, yasa hannu yaɗau
tozalin, ya sanya a idaniyarsa, atake Affan yajishi wasai, ya ɗan juya yace "Kaka shi kuma wannan tozalin
yana jishi daban"? Mai Dawa Sudani yace "wannan tsohuwar ajiyace, sannan kuma labarin dogon labari
ne, don haka kayi maza kashiga daga ciki, domin kasamu ka kintsa yanda yadace a nitse". Affan yace "to"!
Sannan ya shige bukkansa. Washagari asuban fari, Affan da Mai Dawa Sudani suka fito da shirinsu na
tafiya farauta daji, suka ɗan tsaya sukayi addu'oi, sannan sukayi bankwana da Goggo, daga nan suka tafi,
sukabar Goggo a wurin, suka nufi yammacin Dokaddaji. Tafiya sukeyi, tafiya sukeyi, batare da sunga
alamar wani abu mai rai ba, har sai chan dabda magriba, suka iske gaɓar kogi, anan suka tadda tsuntsaye
kala daban daban, Mai Dawa Sudani ya umarci Affan da yayi harbi. Affan yace "to"! Sannan yaɗan risina,
yaɗau seti ya sake bindiga daraaaam! Wani ikon Allah kawai sai ga tsuntsaye da dama sun zube, Mai
Dawa Sudani, da Affan suka ƙarisa, domin ɗiban tsuntsayen, acikinsu sai sukaga wata Shambuwa kwance

Affan ya harbeta a ƙafa, ɗauke da Laya a rataye a wuyanta. Wannan dalilin yasa Mai Dawa Sudani, ya
durƙusa yasa hannayensa yacire Layan da yake rataye a wuyar Shambuwan, ya zaro wuƙarsa a ƙugunsa,
yasa ya yanka ɗinkin jikin Layan, ya warware Layan a hankali.

2 / 6