MAKIRAR MACE COMPLETE BY Yellow .pdf

Author :  Yellow Category :  Hausa Ebooks

Chapter   4 / 6

9K to 12K   out of 18K words

aure a
Tasallah? Halimatou ta ce, ni dai inhar ka amince to kabarmin komai a hannuna, ni nasan mizanyi, na
ɗanyi shiru, chan nace mata to, Allah yasa mudace, Halimatou tace amin. Bayan munyi haka da sati uku,
sai ta sameni da maganan angama komai fa, yanzu kawai ni akejira akan maganan auren Tasallah, ni dai
har a wanchan lokacin ma jikina da sanyi, sai taƙara ƙarfafamin gwiwa tace min haba Yaya nah, yanzu
duk irin wannan tarin dukiya da Allah yabaka, baza kayi koyi da sunnan manzon Allah (saw) ba. Domin
idan irin ku da Allah yahore muku bakwa ƙara aure, to tayaya sauran mata da suke gidajen iyayensu zasu
auru? Sai nace mata to, yanzu ya kikeso ayi? Ta cemin, yanzu dai kawai maganace ta ɗaurin aure, domin
ba buƙatar sai tazo da wani abu gidan nan, tunda komai akwai, kuma kaima mai yimata kayan ɗakine ko
da wani daban zata aura. Nace mata hakane kam, anan muka yanke ranar ɗaurin aure sati ɗaya,
Halimatu tana murna taje tasanar da mahaifiyar Tasallah, da sati ya zagayo aka ɗaura aure. Bayan
Tasallah ta tare da wata biyu sai Allah yasa aka haifeki na samiki mai sunan mahaifiyata Hadiza, amma
muke kiranki da Suhaima. Daga nan dai sai abubuwa suka fara chanjawa tsakanina da mahaifiyarki,

ƙarshe dai a satin da ta yayeki bana mantawa na kwaceki a hannunta, sannan nayi mata korar kare, ke
kuma na nema miki mai raino har zuwa lokacin da kikayi wayo, nasaki a makaranta, har Allah yasa kika
kammala karatun matakin secondary, ni dai iya wannan shine abinda nasan zan iya tunawa na abinda
yafaru abaya atakaice".
By Sagiryellow✍️08060616515.
MAKIRAR MACE
14.Bayan Guburo Konduga yagama rufe baki ne, Suhaima ta ɗago kanta tana mai hawaye, ta buɗi baki ta
ce, "Abba indai hakane to akwai buƙatar ka kaini garin ku, domin a channe nake ganin kamar zamu iya
samun labarin inda mahaifiyata take". Buɗan bakin Guburo Konduga yace "wannan ba shine abinda
yadace mufara ba, abinda yadace shine, idan Allah ya kaimu jibi zanzo mutafi garin Mangono tare dake,
amma yanzu haka zamu koma Dokaddaji ne, sakamakon Affan ya tabbatarwa Mai Dawa Sudani bazamu
daɗe ba". Suhaima ta buɗi baki ta ce "to, Allah ya kaimu jibin", sukace "amin". Daga nan Guburo
Konduga da Affan suka fita, suka tafi Dokaddaji kai tsaye, da isarsu sai suka tarar da Goggo tare da Mai
Dawa Sudani, suna zaune a gaban bukkokinsu, sunata hira. Bayan sunyi sallama suka amsa musu
"wa'alaikumussalm!" Suka ƙara dacewa "sai yanzu ake ganin idonku, amma ya akayi kukaje kuka jima
haka"? Affan yace "wallahi yau wani babban abun al'ajabi muka gani", da sauri Goggo ta ce "abun al'ajabi
kuma"? Affan yace "eh sosai ma kuwa, sakamakon shigan da mukayi cikin gari ya zama sanadiyar
haɗuwar Guburo Konduga da ƴarsa Suhaima". Goggo ta ce, "Affanu ban fahimce ka ba"? Affan ya fara
zayyanewa Goggo da Mai Dawa Sudani bayanin duk abinda yafaru daga farko har ƙarshe, bayan ya
kammala tsaf ne, Mai Dawa Sudani yabuɗi baki yace "lallai Tasallah tacika Makirar Mace". Sannan yaƙara
dacewa "amma bakomai, ita daɗin wannan rayuwar duk abinda mutum ya shuka shi zai girba, don haka
Guburo Konduga kaƙara hakuri, domin shi Allah yana tare da masu haƙuri ako da yaushe". Guburo
Konduga yace "ba komai Baba fatan mu dai shine Allah yasa mudace", sukace "amin". Daga nan Mai
Dawa Sudani yace da Affan "zuwa jibin in Allah yakaimu acikin kuɗin zuman naka sai ka ɗauki adadin
kuɗin da kasan zai ishesu na mota dashi da ƴar tasa ka bashi". Affan ya amsa da cewa "to Kaka". Daga
nan duk suka watse, washagari suka tashi da sauƙar alqur'ani mai girma, suka saukeshi tsaf a Guburo
Konduga da ƴarsa Suhaima da niyar Allah ya karesu. Bayan ankammala komai da gari yawaye, Guburo ya
tashi da tafiya, a yayinda yaje yin sallama da Goggo tare da Mai Dawa Sudani, Guburo yayi musu godiya
sosai, tare da addu'oi na alkhairi, anan sukayi bakwana tare da umurtan Affan da ya tabbatar yaraka
Guburo har gidan da Suhaima take. Bayan sun fito a gida, suka kama hanyar cikin gari, babu abunda
sukeyi akan hanyarsu banda sauri da suke bugawa ba, duk dan gudun kar lokaci yaƙure wajen samun
motar Konduga, cikin ikon Allah kuwa sai gasu acikin garin Manguno. Da isarsu kai tsaye suka miƙa gidan
Alhaji, suka isa suka tarar da Goje zaune akan benci, Guburo yace da Goje, "Assalamu'alaikum"! Goje ya
amsa, sannan yace "kash! Gashi kunzo kuma Suhaima tana gidan wannan Tsohuwar". Affan ya buɗi baki
yace "to inaga ta manta da batun maganan tafiyar tasu yau ne". Goje yace "a'a fa, bawai ta mantaba ne,
domin itama sai da ta shirya tsaf, sannan ta tafi gidan, kawai zallan tausayin matar Allah yasawa Suhaima
acikin zuciyarta. Domin kafin tafita a gidan nan ɗazu har kuka sai da tayi, tana cewa yanzu idan ta tafi,
waye zatana kulawa da wannan baiwar Allah"? Ana cikin haka sai ga Alhaji yafito, duk kansu suka durƙusa
har ƙasa suka gaisheshi, bayan Alhaji ya amsa, ya tambaya "wannan ne mahaifin Suhaima"? Goje yace
dashi "eh shine". Alhaji yace "naji ance yau zakuyi tafiya, amma lafiya har yanzu banga Suhaima tazo

tamin sallama ba, ko dai kun ɗaga tafiyar ne"? Kafin Guburo Konduga yabuɗi baki yace wani abu, sai ga
Suhaima ta shigo tana kuka, cikin mamaki Alhaji yace "Suhaima lafiya, miyake damunki haka"? Suhaima
ta ce, "lafiya ƙalau, kawai ina tunanin in natafi babu wanda zaicigaba da kulawa da Baaba Iyatu ne".
Alhaji yaɗan jijjiga kai, sannan yace "wannan maganartaki gaskiya ne, amma kisaki ranki daga yau zan
ɗauko Baaba Iyatu tadawo gidan nan, tacigaba da zama har iya ƙarshen rayuwarta". Alhaji yaƙara da
cewa, "tabbas Suhaima ke ƴar halak ce, domin bakya manta halacci komin kaɗan ɗinsa, wannan shiyake
nuna cewa kin haihu, sannan kuma kaima Guburo inatayaka murna da Allah yabaka ƴa irin Suhaima,
yarinya mai hankali da biyayya, a iya zaman mu da ita babu wanda zaice ma ga matsalarta. Da wannan
nake muku fatan alkhairi, a wurin Alhaji yaciro damin kuɗi yamiƙawa Guburo yace dashi gashi ai zaku
rage na mota". Guburo yasa hannu yakarɓa yana mai godiya, daga nan kawai sai Goje ya fashe da kuka.
By Sagiryellow✍️08060616515.
MAKIRAR MACE
15.Alhaji yace da Goje "kukan mikakeyi kuma"? Goje yace "tabbas zanyi rashin Suhaima", Alhaji yace
"hm, Allah sarki hakuri zakayi Goje". Daga nan Suhaima ta shiga cikin gida domin yin sallama da Hajiya.
Chan bayan wasu ƴan mintuna Suhaima tafito tana kuka Babanta ma yana kuka ya rungume Affan. Anan
sukayi bankwana duk kansu daga wurin Suhaima da Babanta suka nufi tasha, bayan sun isa tasha
sunɗanyi jinkiri naɗan lokaci, wanda daga bisani, suka samu motarsu ta tashi zuwa garin Konduga. Cikin
ikon Allah suka isa lafiya, da suka sauƙa, suka hau adaidaita zuwa unguwar da gidansu yake, mai
adaidaita ya ɗaukesu yakaisu har ƙofar gida, da yayi birki yatsaya, sukabashi kuɗinsa yatafi, daga nan su
kuma suka ƙarisa sukayi knocking gate ɗin gidan. Sunata knocking chan wata mata tazo tabuɗe, da ta
gansu tace dasu, "wakuke nema"? A yanayin yanda sukaji muryarta dai alamu yanuna cewa yaren
Yoroba ce, wannan yasa Baban Suhaima yace da matar "munzo wurin Tasallah ne". Ta buɗi baki ta ce,
"Tasallah kuma a gidan nan"? Baban Suhaima yace "eh, ina nufin mata mai wannan gidan". Cikin mamaki
mata yoroban ta ce, "ohhh! Nagane, ai ta sayar da gidan a mijina tunda jimawa". Suhaima da Babanta
duk sai suka haɗa baki sukace, "innalillahi'wa'inna,ilaihi raji'un"! Sannan Baban Suhaima yaƙara da cewa,
"amma dan Allah yanzu inata koma"? Matar ta ce, "a gaskiya bani da labari, domin nima bansan ko ina
ba a garin nan, mundawo nan garin ne sanadin Transfer of Service da mijina yasamu zuwa garin nan daga
Ibadan". Jin hakan yasa Suhaima ta ce, "shikenan kawai madam mungode", taƙara dacewa "Abba mutafi
kawai". Anan matar ta juya ta shege cikin gida, tabar Suhaima da Abban ta a tsaye a kofar gidan, Guburo
Konduga yaja dogon nunfashi yace "akwai matsala babba". Suhaima ta ce, "akwai Allah Abba, ka kwantar
da hankalinka, yanzu miye abunyi"? Guburo Konduga ya buɗi baki yace "yanzu anan zuwan mu garin
Konduga kinga abinda yafaru, to haka zalika kuma jikina yana bani ko da munje Kandahar ba lallai
musamu mahaifiyarki achan ba". Suhaima ta ce, "ni dai kawai musa Allah a ran mu, kawai mutafi".
Guburo yace "to ai duk bawan nan bama, tafiya Konduga tafiya ce wanda take buƙatar muriƙe kuɗi sosai
wanda zamuyi guziri, domin in muka tsinci kan mu a garin bamu da wanda zaina bamu abinda zamuci ko
da kuwa muntarar da mahaifiyar a chan, itama nasan yanzu bayanda take achan". Suhaima, ta ce, "ni
indai dan wannan ne, duk ba matsala bane, domin ina da kuɗin aiki na, da ake biyana wanda nake
tarawa, don haka ina tunanin zasu ishemu muyi komai". Abban Suhaima yace "indai hakane to mutafi
kawai". Daga nan suka kama hanya tiryan tiryan har tasha, anan suka hau motar Bamako kai tsaye, kamar
wasa mota ta tashi, tafiya suke har tsawon kwana uku, da wuni guda suka tsinci kansu a babban birnin

Marly, Bamako. Daga nan bayan sun sauka a tasha, sai suka ƙara hawa ƙaramar mota zuwa garin
Kandahar, chan da misalin la'asar ne suka tsinci kansu a garin Kandahar. Bayan sun sauka a mota daga
bakin hanya suka gangara, suka nufi gidansu mahaifiyar Suhaima Halimatu, ruɗanin da suka tsinci kansu
a ciki da sukaje, suntarar da gurbin inda gidan yake dachan, wani katafaren gidan beni ne a gurbin filin
gidan. Gefen gidan kuma wani masallacin jummu'a ne, da aka ƙayatashi sosai, na ɗauke da suna
HALIMATOU USAMA MASJID. By Sagiryellow✍️08060616515.
MAKIRAR MACE
16.Bayan sun ɗan tsaya a dab da masallacin Suhaima ta tambayi Babanta "Abba inane nan"? Guburo
yace "yau ana wata ga wata", Suhaimata ta ce, "Abba mikuma ya faru"? Guburo yace "wannan gidan
benin da kike gani, da chan abaya a gurbinsa ne gidansu mahaifiyarki, to yanzu kuma gashi munzo
muntarar da tamkar ba ataɓayin wani gidan laka a wurin ba". Cikin mamaki Suhaima ta ce, "to Abba
yanzu ya kenan"? Guburo yace "to yanzu kam dai sai abinda Allah yayi kawai gaskiya". Ana cikin haka sai
ga wani yaro matashi yazo wucewa, Guburo yace dashi "yaro dan Allah ina tambaya ne"? Yaro ya ɗan
tsaya, sannan yace "to Allah yasa nasani". Guburo yace "dan Allah wannan gidan benin na waye ne"?
Yaron yace dasu, "wannan gidan Hajiya Biba ce". Cikin firgici Guburo yace "iyeeeee! Amma wata Hajiya
Biba kake faɗa"? Yaron yace "Hajiya Biba mahaifiyar Halimatu". Daga nan kawai Guburo yayi salati ya
sanarwa ubangiji, yace "Allah mai iko kenan, shiyakeyin yanda yaso kuma a lokacin da yaso". Suhaima ta
ce, "wai Abba miyake faruwa ne"? Guburo yace "abun ne da abin al'ajabi Suhaima, akan maganan da
Yaron chan yafaɗamin cewa wai nan gidan Hajiya Biba ce, yana nufin Kakarki kenan wacce ta haifi
mahaifiyarki". Suhaima ta ce, "ai Abba babu abin mamaki acikin iko na Allah, don haka kawai muƙarisa
mu ƙwanƙwasa gata ɗin".
Guburo yace "to"! Suka ƙarisa suka ƙwanƙwasa kofar, mai gadi yazo yabuɗe, da yagansu, ya tambayesu
"daga ina"? Guburo yace "sunana Junaidu, munzo wurin Hajiya ne, ni ɗan Yayanta ne". Mai gadin yace
"tasan da zuwan kune"? Sukace "a'a", mai gadin yace "to kuji rani bari nashiga nafito", sukace "to"!
Bayan ya shiga sai gashi yafito, yace dasu "wai tace kushiga". Suhaima da Abbanta sukasa kai cikin gidan,
sunata tafiya har sukaje gate na biyu anan ne kofofin sukarabu daban daban, wanda suka ruɗe suka rasa
wacce zasubi, ƙarshe dai sukayo kwana sukadawo baya chan wurin mai gadi. Anan ne mai gadi yashiga
dasu har cikin falon Hajiya Biba, suka taddata tana zaune tanata lazimi abunta, da sukayi sallama, Hajiya
Biba ta amsa, sannan ta ce, "Junaidu dama kana raye"? Jikin Guburo da sanyi yace "ina raye wallahi
Baaba". Hajiya Biba ta ce, "to amma dai baka kyauta ba, yanzu shikenan dan mahaifinka baya raye sai
bazaka nemi inda nake ba, wato dan bani nahaifeka bako"? Gabaɗaya kunya ta gama lulluɓe Guburo
dakyar yabuɗi baki yace "wallahi Baaba bahaka bane, daga nan ta ce, "wannan ɗin waye ce kukazo tare"?
Guburo yace "Suhaima ce, ƴar wurin Halimatu, mai sunan marigayiya". Hajiya ta ce " ƴar nan sai yau
Allah yayi nasata a idona tunda aka haifeta, labarinta kawai nakeji, a gaskiya Junaidu bakyauta ba wallahi
kaci amanar ƴar uwanka Halimatu da muka aurama". Junaidu kawai ya fashe da kuka, yafara da cewa
"Baaba na rantse da Allah, dai dai da sau ɗaya bantaɓayin wani abu domin na chutar da Halimatu ba,
Allah yasani naso Halimatu har cikin zuciyata kuma naso zama da ita. Amma sai abun yazo da akasi
wanda naɗaukeshi a matsayin jarrabawace". Daga nan Guburo yaƙirgewa Hajiya duk abinda yafaru

tsakaninsa da Halimatu tun daga lokacin da suka bar Kandahar har Allah yaƙaddara zamansu a garin
Konduga, da duk yanda akayi har suka rabu da Halimatu. Anan ne Hajiya Biba ta ɗan sauko ta jajantawa
Guburo abinda yafaru dashi, tare da yimasa fatan "Allah ya kiyaye nagaba", suka amsa dacewa "amin".
Daga nan Hajiya Biba ta umurcesu dasu ƙarisa dining suci abinci daga nan kuma sai a rakasu gidan da
Maman Suhaima take aure a cikin babban birnin ƙasar Bamako. Jin hakan yasa Suhaima tsabar ɗaukin
ganin Mamanta tabuɗi baki tace "sunƙoshi kawai azo arakasu gidan". Hajiya tanuna sam "bazaiyiwuba
taya zasuce sunƙoshi, alhali su ba baƙi bane". Suhaima dai ta tirje akan sunƙoshi. Itama Hajiya ganin irin
zumuɗin da Suhaima takeyi yasa kawai tayi magana da Direba, akan yazo yakaisu gidan Hajiya Halimatu.
By Sagiryellow✍️08060616515.
MAKIRAR MACE
17.Bayan ankira Bala Direba a Hajiya, Guburo yace da Suhaima "ki bishi kawai kuje ya kaiki wurin
mahaifiyarki". Cikin gaggawa Suhaima tabuɗi baki ta ce, "haba Abba miyasa zakace haka"? Guburo yace
"dalilina shine, bansan ta yadda zan fara haɗa ido da mahaifiyarki ba a yanzu, sakamakon har kullum
nasan amatsayin maci amana zata cigaba da ganina". Suhaima ta ce "Hm, Abba kenan ai inhar kana
tunanin haka acikin ranka to yanzu dama ce, ta sameka da zamuje ka nemi ta yafemaka". Guburo yace
"uhm uhm Suhaima". Daga nan Hajiya ta ce, "wai tsayuwar mikukeyi ne, bakutafi ba"? Batare da Guburo
yaso Hajiya taji mi akeciki ba, kawai yawuce sukaje suka buɗe mota suka shiga, daga nan Bala yayi key a
motar sukatafi. Batare da suntsaya ako inaba, kai tsaye suka wuce Miloniyas Kwatas, dake cikin birnin
Bamako, gida mai lamba na 9.
Da isarsu Bala Direba yayi horn, Security yazo ya buɗe musu, Direba ya shiga dasu yayi parking a car park
ɗin gidan, daga nan suka fito Bala yayi musu jagora har cikin falon Hajiya Halimatu. Suna sallama, ɗaga
idon Hajiya Halimatu ke da wuya, kawai sai taga Guburo tare da Suhaima kamar a mafarki, cikin mamaki
Hajiya Halimatu ta ce, "Suhaima", kawai ta taho da gudu ta rungume Suhaima. Hajiya Halimatu kawai sai
kuka, tana mai cewa, "Suhaima ashe da rabon zan saki a idona"? Suhaima itama sai kuka, ta fara dacewa
"Allah na gode maka da kacikamin burina anan gidan duniya". Daga nan Hajiya Halimatu tabuƙaci su
shiga su zauna, suka shiga bayan sun zazzauna suka gaggaisa sosai, Suhaima tana mai farin ciki taƙara da
cewa, "Mama arayuwa babu jarabtan datakai mutum yatashi bai san iyayensa ba a rayuwarsa". Hajiya
Halimatu ta ce, da Suhaima "hakane kam, amma idan ya kasance haka Allah ya tsarawa mutum
ƙaddararsa arayuwa babu yanda zaiyi, fatan mu dai shine Allah yasa mudace duniya da lahira". Suhaima
ta ce, "amin amin Mama". Hajiya Halima ta juya ta kalli Guburo, sai ta kurewa yaketayi ta ce dashi "Yaya
Junaidu ya kuma ba kuzo da Tasallah ba"? Guburo yace "Hm!" Hajiya Halimatu ta ce, "haba Yaya Junaidu,
aiko ba komai kai ɗan uwana ne na jini, sannan kuma bugu da ƙari ga ƴarmu Suhaima, inaganin ai waƴan
nan dalilin sunkai ace ko bama tare, matarka zatazo wurina". Jin hakan yasa Guburo yaƙara yin ajiyar
zuciya, sannan yace "Halimatu bansan tayadda zanfara neman gafararki ba, amma dai da farko inaso
kisani dukkannin abinda ya faru tsakanina dake bayin kaina bane. Har ga Allah nasoki, domin irinkine
matan da ake kira da mata nagari, to amma sai dai kash! Kaddara tariga fata, na auren Tassalah danayi,
domin Tasallah makirace, kuma taci amanar mu bakiɗayan mu, wanda har yau mamakin da nakeyi shine,
wai minayiwa Tasallah tasakamin da irin abinda ta aikatama na"? Haji Halimatu tabuɗi baki ta ce, "ban
fahimce kaba Yaya Junaidu"? Daga nan Guburo yafara zayyanewa Hajiya Halimatu duk abinda yafaru,

batare da yaɓoye mata komai ba, tsaf, ya zayyane mata komai, bayan Hajiya Halimatu ta gama sauraron
komai daga bakin Guburo. Tafara dacewa "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!" Daga nan Guburo yace "da
wannan nake me neman ya fiya agareki, domin rabuwar mu abaya batayi tsari ba, ina nadaman wannan
al'amarin har kullum acikin raina". Hajiya Halimatu ta ce, "wannan kasa aranka komai yawuce, ai kaima
ba lefinka bane, sakamakon wannan duk yasamo asaline daga shairin makirar mace. Kuma kasancewar
zuciyata ɗaya nake zaune da ita, wannan yasa a wanchan lokacin da mukarabu nadawo gida Kandahar
kaitsaye, nazo natarar da Baabata na zayyane mata duk yanda mukayi dakai, buɗan bakinta sai tace to
Allah yasa hakan shine mafi alkhairi agaremu bakiɗaya, nace amin. Bayan munyi haka da ita, washagari
sai tashiga makwabtan mu take labarta musu cewa ai aure na yamu, a yayin da Baabata take basu labari,
akwai wani matashi mai suna Dauda yana zaune a cikin gidan. Wannan yasa acikin satin Dauda yatashi
yayi tattaki zuwa Bamako, a chan yaje ya iske Alhaji Usama Ɗangari, yayi masa albishir dacewa aure na
yamutu, yanzu haka nadawo Kandahar ina gida. Jindaɗin albishir ɗin yasa Alhaji Usama yaba da kyautar
mota sabuwa gal, wanda kuɗin ta yakai naira miliyan biyar a Dauda amatsayin tukuici".
By Sagiryellow✍️08060616515.
MAKIRAR MACE

18."Bayan Dauda yadawo gida anan ne naji anata zuwa masa murna, akan ya samu kyautar mota daga
wurin Alhaji Usama Ɗan gari. Wannan yasa nima na sanya

4 / 6