MAKIRAR MACE COMPLETE BY Yellow .pdf

Author :  Yellow Category :  Hausa Ebooks

Chapter   5 / 6

12K to 15K   out of 18K words

hijabi na, na zaga gidansu Dauda domin
tayashi murnar ƙaruwar mota da yasamu, anan ne yake sanar dani cewa ai wannan mota yasamu
kyautarta ne sanadiyata a wurin Alhaji Usama Ɗan Gari. Sakamakon kamar yanda kikasani cewa tun a
yarinta bakida masoyin da yafi Usama, mutum ne mai tsananin sonki, kuma Usama ada chan ɗan gaye ne
wanda ba ayi kamarsa ba a kaf garin Kandahar. Kamar yanda kikasani matsala ɗaya ce da Usama yasamu
daga iyayen mu, wanda tasa aka hanashi aurenki. Matsalar itace, lokacin muntaso Usama bayason noma
kuma bayason zuwa Kiwo, wannan yasa a wanchan lokacin iyayen mu suke kiransa da malalacin yaro,
sakamakon shi kullum yana Bamako. Tun Usama yana yin wanka kawai yatafi yaje yawo yadawo, batare
da yanayin komai a Bamako ba, har aka kai matakin da Usama yafara yin aikin, tonon Dutse (Kuza). Tun
yanayin leburanci ana biyansa, har yadawo yana iya siyan wuri da kuɗinsa, yagwada tono ko Allah zaisa
yadace da samun Dutsen. Cikin ikon Allah sai Usama ya kasance tamkar mai wankin ido a ɓangaren
wannan harkar, ankai matakin da har ana iya ɗaukansa yaje yaduba wuri ko za a iya samu, kafin a fara
tonon wurin, kamar wasa sai Allah yahorewa Usama. Lokaci guda, Allah ya yarje masa yabuɗe wurin niƙa
dutse nasa na kansa, dalilin haka daga garirruka da dama ake kawo niƙa dutse kamfanin Usama, harkarsu
ta Mining kuma gashi ta kasance a yanzu tana daga cikin harkokin da suke kawo kuɗi a duniya. Wannan
shine dalilin da yasa, Usama ya zama hamshakin attajiri, amma har kullum abinda ya kullewa kowa kai
shine, shi dai Alhaji Usama rufin asirin duniya Allah ya horemasa, amma kuma gashi bashi da mata.
Kullum in an tambayeshi ya akayi har yanzu yake zaune bashi da aure? Sai yace shifa tun akan soyayyar
Halimatu ya gama duk wata soyayyarsa, wannan yasa shi kwatakwata har yanzu bayajin son wata acikin
ransa. Daga ƙarshe Dauda yaƙara dacewa, kuma maganan da Usama yake faɗa akan soyayyarki gaskiya
ne, domin tunda akasa ranar aurenki da Junaidu da Usama yasa ƙafa yabar garin nan yakoma Bamako
baiƙara dawowa garin nan ba. A lokacin da Dauda yagama faɗamin haka sai nace masa, Dauda ni kaina

abaya naso Usama kamar zan mutu, bugu da ƙari kuma na shaƙu da Usama yanda baka tunani, amma
duba da irin ganin darajar iyayena da nakeyi, yasa da sukace sun badani a Junaidu sai bayimusu tawaye
ba. Nayi biyayya ga umarninsu, amma ko ta mafarki bantaɓa kakowa araina ba Usama bane mijina,
amma daga ƙarshe Allah bayyiba. Don haka a yanzu babu abinda zance sai dai nace Allah yayimana zaɓi
da duk abinda yafi alkhairi agaremu. Daga ƙarshe kuma inayi maka fatan alkhairi akan kyatar mota da
kasamu, Allah yatayaka riƙo. Dauda ya buɗi baki yace amin ya rabbi nagode sosai. Anan muka rabu
nadawo gida. Bayan anyi haka, a satin da nagama idda, sai Umaru na kan Tudu yaje Bamako yaƙarayin
albishir wa Alhaji Usama Dangari kan cewa ai nagama idda ta. Kamar wasa shima ya bashi tukuicin motar
naira miliyan biyar, a wanchan lokacin, bayan Umaru yadawo gari yaƙara ruɗewa, washagari kawai ina
zaune acikin barandar Baabata, sai na hangi wata babbar mota kirar jip tayi parking a kofar gidan mu.
Bayan wasu ƴan mintuna kawai sai ga yaro ya shigo wai Alhaji Usama yana sallama da Halimatu a waje".
By Sagiryellow✍️08060616515.
MAKIRAR MACE
19."A take nace da yaron to kace tana zuwa, daga nan natashi na shiga cikin ɗakin Baabata na tadda ita
tana kwance akan gadonta, batare da nace da ita komai ba, kawai taga nafara kintsawa, ta tambayeni
Halimatu wani wuri zakije ne naga kina kintsawa? Nace mata bawani wuri zanje ba, Usama ne ya aiko
yana kirana, Baabata tabuɗi baki ta ce, to Allah ya kyauta. Daga nan nafito, natarar da babbar mota kirar
jeep mai launin baƙin fenti, glass ɗinta na ɗauke da tinted, ni dai kawai sai natsaya naja birki ina kallon
ikon Allah, ganin hakan yasa Alhaji Usama ya zuge glass ɗin ƙofar gefen mai zaman banza, sannan yace
min kibuɗe kishigo mana. Cikin sanyin jiki na ƙarisa nabuɗe ƙofar motar nashiga, naja ƙofar motar na
rufe, daga nan nikam ai nakama kallon ƙauyanci kuma a cikin motar. Da Alhaji Usama yalura dani yace
dani uhm Halimatu, na amsa, sannan na gaishe shi, bayan mungaisa sosai, ya tambayeni kingane ni? Na
ɗanyi shiru nace masa eh, yacemin to waye niɗin? Nace Usama, yayi ajiyar zuciya, fiskarsa cike da annuri
yace baki ƙarisa ba kuma, Usama masoyin Halimatu zakice. Daga nan yacemin to yanzu dai a gurguje,
nazone naƙara jaddadamiki soyayyarki da take cikin zuciyata, kamar yanda kikasani a baya ni masoyinki,
ina mai tabbatar miki da har ila yau babu abinda yachanja acikin irin son da nakemiki sai ma abinda ya
ƙara hauhawa. Don haka na riga dana samu labarin duk abinda yafaru, bana buƙatar duk wani bayani
daga gareki, ni dai tun da kikayi aure Allah bai nufa nayi aure ba. Sannan kuma a yanzu harkar Mining ɗin
Dutsin (Kuzza) nakeyi, nikuma tanan Allah yayi arzikina yake, saɓanin ƙalubalanta ta da iyayen mu
sukayitayi abaya akan ni malalacine a ɓangaren noma da kiwo. To a yanzu dai ina mai yimiki albishir da
zanbiya mana kujerar Makka domin muje muyi aikin Umara, ki roƙi Allah akan lamarin aure na dake, in
mundawo abinda duk kikaji yafi kwanta miki sai kisanar dani ko? A nan ne, nabuɗi baki nace masa, to
Alhaji Usama naji dukkannin bayananka kuma, na gamsu dasu, nima na'amince ɗari bisa ɗari ina sonka,
kuma insha Allah zamuyi aure badajimawa ba. Amma sai dai wani hanzari ba gudu ba, maganan
tafiyarmu Umara tare inaganin kamar hakan bayyi tsari ba, tunda bamuyi auren ba tukun, kaga ko
Baabata ba lallai ta amince da hakan ba. Alhaji Usama yace hakane kam, to yanzu kawai abinda za'ayi zan
biyamiki ke da Baaba sai kutafi tare, idan Allah yasa kundawo lafiya, sai mu ɗaura aure. Nace masa to
shikenan. Daga nan yacemin to mushiga cikin gidan muje yagaida Baaba, nace to, muka shiga suka gaisa
yayi mata alkhairi sosai, daga ƙarshe yayi mata albishir da zuwa Umara, ranar dai Baaba farin ciki har sai
da ta rasa inda zatasa kanta. Bayan Alhaji Usama yatashi ya tafi, a satin Allah yayi tafiyarmu Umara, kafin

mudawo kuwa, muka dawo muka samu Alhaji Usama, ya saye gidajen makwabtan mu, ya haɗesu da
gidan gabaɗaya yasa an rusa su ya gina mana gidan beni. Daga chan gefe kuma, yasa angina Masallacin
Jummu'A, wuri dai yayi kyau sosai gabaɗaya ya chanja kamar ba wurin ba, abinda yafi jan hankalin
mutane akan duk ayyukan kuma shine, sunana da nasa da sayawa masallacin jummu'an, Halimatu
Usama Masjid. Bayan mun dawo da sati biyu, kuwa Allah yanufa aka ɗaura aure na da Alhaji Usama,
natare nan wannan gidan nasa na Bamako, ita kuma Baabata yasa aka nema mata ƴan aiki da masu kula
da ita. Bayan munyi aure, muna zaune lafiya, babu wani wanda yakejin kan mu, domin dama chan mun
shaƙu da junan mu, sannan kuma kusan kowa yasan halin kowa a cikin mu. Wani ikon Allah kuwa
shekarar mu ɗaya dayin aure Allah ya azurtamu da samun haihuwar ƴa mace, wacce muka samata suna
Nana, amma muna mata laƙabi da (Nancy). Wanda idan da kun lura da kuka shigo a chan car park da
zakuga wata mota fara Convertable, a fake mai dauke da flate number Nancy. Kasancewar yanzu Nancy
tana makaranta a ƙasar England tana Oxford University, amma dai yanzu haka suna dab da yin hutu suma
insha Allah, daga kan Nana kuma bamuƙara haihuwa ba. Daga ƙarshe Hajiya Halimatu ta ce, da Guburo
da Suhaima, to kunji wannan shine abinda yafaru dani bayan rabuwata da ku a ƙasar Nigeria a takaice, ni
dai har kullum banida abunda zance sai dai nayi godiyawa Allah kawai".
By Sagiryellow✍️08060616515.
MAKIRAR MACE
20.Buɗan bakin Guburo yace "tabbas, ya tabbata duk wani hani ga Allah baiwa ne, sakamakon rabuwata
dake ya zame miki alkhairi". Hajiya Halimatu ta ce, "wannan haka yake fatan mu dai shine Allah yasa
mucika da imani". Daga ƙarshe Hajiya Halimatu ta ce, "yanzu dai bari naje nayi magana da Daddyn Nana,
yafito kugaisa ko"? Guburo yabuɗi baki yace "a'a Halimatu kibarshi kawai nikam yanzu ma zan tafi".
Halimatu ta ce, "miyasa zakace haka"? Guburo yace "a gaskiya ina kunyar Usama, domin bana mantawa
lokacin muna samari kuna tsakiyar soyayya dashi. Ya fito majilasa, sakamakon naji maganan za abani
aurenki a gidan mu, yasa nake cemasa aure fa bana ragwaye bane, idan yaro yana son aure to sai
yajajirce akan noma da kiwo anan ne zai zama namijin gaske daga bisani sai asamu mai bashi ƴarsa. A
wanchan lokacin mutanen majalisarmu sukaita ihu a Usama, har takaiga mukayi kacha kacha dashi a
wurin, anan muka rabu akan bani bashi har abada. To yanzu kuma taya za ace gani a gidan Usama? Idan
yazo ai duk matakin daya ɗauka akaina nina jawa kaina". Hajiya Halimatu ta ce, "yanzu kam ai wurina
kazo ka a gidan nan, don haka kuɗan jirani ƙaɗan minti biyu". Daga nan Hajiya Halimatu tafita tabarsu
acikin falon nata, bayan wasu ƴan mintuna ƙaɗan sai gata gaba da baya tare da Alhaji Usama. Suka ƙariso
har daf da Guburo da Suhaima, Alhaji Usama yayi musu sallama, bayan sun amsa, Hajiya Halimatu ta ɗan
juya taga Daddyn Nana cikin annashuwa ta ce, "my dear waka gane acikinsu"? Alhaji Usama yace "hm
haba Darling Haleemcy, wannan fa, abokina Junaidu ne, babban abokin takarata da ya bugani da ƙasa
akanki, kuma taya zan manta dashi"? Alhaji Usama ya juya, ya bada hannu a Junaidu sukayi musabaha,
sannan ya zauna a gefensa, daga bisani kuma yace "wannan kuma ai da anganta ba buƙatar sai an
tambaya, domin abinda ya ban bantaki da ita shine, ke kina da kwale ɗaɗɗaya a fiskarki ita kuma batta.
Amma duk sauran surarki irin natane, kama daga kan karan hancinki, da hushiryarki, da gwalagwalan
idanuwanki, da baƙin labbanki, haka kuma yanayin dirinku, itama matsakaicin tsayine da ita, haskene dai
kadai kika ɗan fita haske". Hajiya Halimatu ta ɗanyi murmushi, sannan ta ce, "lallai Daddyn Nana", daga
nan taƙara dacewa "kasan lokacin da aka haifi Suhaima fa tafi Nana fari yanzu ne dai kawai da ta haɗu da

jarabawar rayuwa". Cikin mamaki Alhaji Usama yace "wani irin jarabawar rayuwa kuma"? Hajiya
Halimatu ta ce, "Hm, wato Suhaima da kake gani tsawon shekaru ta kwashe tana aikatau a gidan wani
Alhaji a Nigeria, kalubale kala kala tagani". Alhaji Usama yace "yaaa salam, a garin yaya to, ina Junaidun"?
Anan ne Hajiya Halimatu taƙirgewa Alhaji Usama duk abinda yafaru tunda farko har zuwa yanda akayi
Suhaima da Abbanta sukazo nan garin Bamako. Buɗan bakin Alhaji Usama yace "innalillahi wa'inna ilaihi
raji'un"! Sannan yaƙara dacewa "amma gaskiya Tasallah taci amana matuƙa, kuma a duk inda take a
faɗin duniyar nan itama amana zatacita insha Allah. Don haka Junaidu ka ƙara hakuri akan wanda kayi
abaya, domin innallaha ma'assabirin, (shi Allah yanatare da masu haƙuri), don haka yanzu zuwa jibi zanyi
mana booking fly domin muje Nigeria ku kaimu wajen mutanen da kukayi zama dasu sukayi muku
halacci. A matsayin mu na ƴan uwanku yakamata muje muyi musu godiya ko ya kukagani amma"? Jin
hakan yasa Guburo yafashe da kuka, cikin firgici Alhaji Usama yace "Junaidu miya saka kuka kuma"?
Guburo yace "natuna da wani abune". Alhaji Usama yace "kayi hakuri dan Allah kamanta da komai
kashare hawayen ka". Daga ƙarshe, Alhaji Usama yace da Hajiya Halimatu "ni yanzu zamu tafi side ɗina
da Junaidu, don haka kiyi magana Tanko yau ya yanka mana ɗawisu naman ɗawisu nake sha'awan ci".
Hajiya Halimatu ta amsa dacewa "to"! Daga nan da Alhaji Usama da Guburo suka tashi suka wuce
ɓangaren Alhaji Usama, a chan sukaje suka zauna sukaita hirarsu data shafi yarinta, har aka kammala
farfesun naman ɗawisun da aka dafamusu. Bayan ankawo sunci sunsha, haka dai suka kasance anan har
zuwa washagari, anan ne sukatashi da tafiya gidan Hajiya Baaba, mahaifiyar Hajiya Halimatu, domin
yimata bankwana tafiya Nigeria.
By Sagiryellow✍️08060616515.
MAKIRAR MACE
21.Wannan yasa Lubabatu ta shirya abun karya kumallo tunda wuri, bayan sun karya, daga bisani sukayi
wanka Mummyn Suhaima ta ɗauko wasu kaya daga cikin kayan Nana ta bata domin ta sanya ajikinta. Shi
kuwa Guburo Alhaji Usama shima yaɗauko kaya daga cikin suturarsa yabashi, duk kanninsu suka sanya
kayan suka fito fes abunsu. Daga nan kuma suka tashi suka fito harabar cikin gidan domin tafiya gidan
Hajiya Baaba, batare da ɓata lokaci ba, Alhaji Usama ya umurcesu dasu shiga wata mota kirar Toyota
High Landa, wacce tajima a ajiye batare da anfita da ita ba. Aranar Alhaji Usama ne da kansa ya tukasu
zuwa Kandahar, a yayin da Guburo yashiga gaban motar Suhaima kuwa da Mummynta suka shiga baya.
Alhaji Usama ya tuƙosu a hankali, har suka isa, batare da sun shiga da motar ba, suka parker ta daga
waje, sannan suka shiga da ƙafarsu, har cikin falon Hajiya Baaba, suka taddata ta ɗan kishingiɗa kaɗan a
kushin. Da sukayi sallama, cikin mamaki Hajiya Baaba ta amsa, sannan Suhaima taƙarisa da gudu taje ta
rungume Hajiya Baaba, Suhaima ta ce, "ni tsohuwar nan idanunki suna gani makuwa"? Hajiya Baaba ta
ce, "hmm keɗin yanzu har akwai abunda zaki nunamin ne"? Duk kansu suka fashe da dariya, daga nan
Alhaji Usama yafara gaida Hajiya Baaba, bayan sungaisa Guburo ma yadurƙusa ya gaisheta. Alhaji Usama
ya buɗi baki yace "Hajiya dama munzo ne domin musanar dake munaso gobe idan Allah yakaimu zamuje
Nigeria, sakamakon akwai buƙatar muje muyi godiya a mutanen da suka zauna da Junaidu da Suhaima.
Daga nan kuma idan Allah yasa mundawo lafiya, itama Suhaima sai naturata chan ƙasar England taje tayi
karatu tare da ƙanwarta Nana, shi kuma Junaidu zan bashi jari domin shima ya farayin wani abu". Buɗan
bakin Hajiya Baaba ta ce, "maganan ƙudirinka akan Junaidu daidai ne Allah yabaka ikon bashi jarin kuma
yasa albarka acikin kuɗin. Amma maganan tura Suhaima karatu England a matakin shekarunta a yanzu ba

dai dai bane. Sakamakon mu muslimai ne, yakamata mukasance masu fifita sha'anin abinda yashafi
lahirar mu akan abinda ya shafi hidimar duniya, don haka abinda yafi dacewa da Suhaima a yanzu shine
ta fidda mijin aure". Falon yayi tsittt! Har na tsawon wasu ƴan daƙiƙu, daga bisani Alhaji Usama yace "to
shikenan Hajiya maganan naki za abi, insha Allah da zarar mundawo daga Nigeria har itama Nana hutun
da zata dawo duk za a haɗasu a aurar dasu". Duk kansu suka haɗa baki sukace "to Allah ya tabbatar
mana". Daga nan suka buƙaci zasu koma gida, Hajiya Baaba ta ce "to", sannan tayi musu addu'oi sosai,
suka miƙe, tunda ganan kuma ita dai Suhaima jikinta da sanyi tabi bayan Mummynta sukatafi. Basu tsaya
ako ina ba, sai a gida, bayan sun koma ne sukaje suka ƙarisa gudanar da ƴan shirye shiyensu na tafiya,
wannan yasa washagari da sassafe suka tashi da tafiya Nigeria, suka kammala kintsawa tunda wurwuri,
driver yadaukesu zuwa air port. Da isarsu, sakamakon booking fly sukayi yasa dama jirginsu yacika, batare
da ɓata lokaci ba, suka shiga kawai jirgi yatashi. Bayan wasu ƴan awanni sai gasu sun sauƙau a filin jirgin
tarayyan Nigeria Abuja. A nan ne suka ƙara hawa jirgin Borno kaitsaye, kamar wasa cikin awa ɗaya sai
gasu sun sauka, a filin jirgin Maiduguri, daga nan sukaɗau taxi daga cikin air port zuwa babbar tasha,
domin hawa motar karamar hukumar Dambuwa. Suka shiga taxi driver yafito dasu daga air port, sun hau
hanya sunfara tafiya kenan, sai ga wata mota kirar Toyota Prado da wani matashi aciki yana tuƙawa, tayi
musu overtaking, wucewar da zatayi sai sukaga motar naɗauke da plate number mai suna, GUBURO
KONDUGA 001.
By Sagiryellow✍️08060616515.
MAKIRAR MACE
22.Cikin firgici Guburo ya buɗi baki yace "subuhanallahi", sannan yaƙara da cewa "driver maza muyi sauri
ka tsayar mana da motar chan". Drivern ya amsa da cewa "to"! A take kuwa sai yakara taka motar,
matashin da yake jan pradon gudu yakeyi suna bin bayansa da taxi, har sai da sukazo wani junction, trafic
suka tsaidashi. Suna taka birki, cikin gaggawa Guburo ya buɗe kofar taxi din ya fita, yaje ya tadda
matashin a cikin motar, ya kwankwasa masa glashin motar, ya sauke glass ɗin, daga nan Guburo yace da
matashin "ina mai motar"? Matashin ya buɗi baki yace "kamar ya ina mai mota kuma"? Yaƙara da cewa
"kai kuma malam daga ina"? Guburo yace "kai ya ina tambayarka kana min irin wannan tambayar"?
Kawai matashin yayi yunkurin taka motar zai tafi, daga nan Guburo yayi sauri yasha gaban motar, lokaci
guda hankalin mutane yadawo kansu, wannan dalilin yasa ɗaya daga cikin Trafic ɗin ya ƙariso ya samesu.
Da farko yafara tambayar "wai miyake faruwa ne"? Buɗan bakin Guburo yace "officer wannan motar
mota tace, inaso ne sai naji a inda yasamo motar nan yau", wurin lokaci guda yacika da mutane,
hayaniyace kawai take tashi a wurin har mutum baya iya fahimtar mi ake fadi. Wannan dalilin yasa
Ɗansanda ya shiga gaba mota pradon ya buƙaci matashin yaja motar sutafi zuwa Maiduguri Devision,
batare da matashin yayi tangarɗa ba, yaja motar suka nufi Devision din, sukuwa Guburo suna bin
bayansu a taxi. Har suka isa, sukayi parking suka shiga ciki, kai tsaye suka wuce offishing DCO police ɗin
dayazo dasu yamika case ɗin a hannun DCO, daga nan shi sai yakoma aikinsa. Shikuwa DCO daga nan
yabukaci yaji daga bakin Guburo, "minene dalilin da yasa yace motar nan motarsa ce"? Guburo yabuɗi
baki yace "na farko motar tun lokacin da na siyota, nasa akamin plate number da sunana Guburo
Konduga, sannan kuma takardun motan idan aka duba za asamu da sunan Suhaima aka sayi motar, daga
ƙarshe kuma Guburo yafaɗi chasis numb motar". Kafin DCO yabuƙaci mashin yayi magana yace dasu
sutashi sufita zuwa wurin motar, da sukaje DCO yayi umarni a matashin da yabuɗe motar, sannan ya

sashi ya ciro takardun motar, ƙarshe dai duk abinda Guburo yazayyana akan motar ya kasance gaskiya ne,
wannan dalilin yasa DCO yabuƙaci sukoma cikin office

5 / 6