MAJANUNI BOOK 5 BY BINTA UMAR ABBALE.txt

Author :  Binta Umar Abbale Category :  Home Of Novels

Chapter   13 / 15

36K to 39K   out of 44.5K words

san gidanmu."

Murmushi ta yi da cewa." 'Kawata ce ta yi min kwatance sai na ga ashe ma muna kusa da juna, shine na ce bari na shigo na yi miki gaisuwa kafin ki tafi, duk da yake nima cikin satin nan nake koma saudiya.

Jin haka yasa na gazgata abinda nake zargi, wato a gurinta Hajiya Fatima ta samu labarin komai, wanda ta samu damar cin zarafin mahaifinta.

Shiru na yi mata ban ce komai ba, amma na lura fakaice take yi min wani irin kallo.
Wanda ya sanya gabad'aya na tsargu! 'bata fuskata na yi nayi bala'in shan kunu! don gabadaya matar bata kwanta min a rai ba.

Sai ta yi 'yar dariya da cewa; Allah sarki Hadiza Allah ya gafarta mata ya raya abinda ta bari."
Na amsa da ameen'' kamar na gaura mata mari saboda takaicin abinda take.

Ta mik'e tare da d'aukar jakarta da cewa; to Allah ya kara hakuri." Anti Murja ta ce" Ameen ya rabbi Allah ya bada lada."
Tana 'kokarin sanya takalminta take amsawa.
Tana fita na ja tsaki da fadin." Anti na lura da yawa mutane gulma ce take kawo su wallahi. wannan shine dalilin da ya sanya yau-yau din nan zan bar garin nan wallahi".
Ta ce" To ya za a yi da sha'anin mutane! kin san yanzu jama'a sun fi zuzuta! sharri! a kan alheri Allah dai ya rufa asiri."

Na amsa da "Amen dai Allah ya sa mu dace."

****
Cikin gajiya na fito daga cikin motar, lokacin ana ta kiran sallar magariba. Walida ta fito goye da babyn a bayanta wacce muka mayar mata da sunan mamanta sai muka yanke shawarar kiranta da Nanah! lokacin da na shirya tafiya ne na nemi alfarma gurin Babanmu ya ba ni Walida. ba don komai ba sai dan ta d'ebe min kewa ta kuma taimaka mini da rainon yarinyar. haka nan ba don ransa ya so ba ya amince ne kawai saboda baya son 'bacin rai na, amma maganar kyautar da Hadiza ta yi mini ta tafasa bai ce ba balle ki sauke, kawai ya ja bakinsa ya yi shiru, yanda na fahimta ma kamar hakan ya yi masa dad'i yarinyar tayi nesa da shi.


Da sallama muka shiga falon, Shukura ce kawai a zaune da waya a hannunta

Wani irin kallo take mana na san tana mamakin ganin Walida ne da kuma yarinyar dake goye a bayanta tana tsala ihu!

Na daure na yi mata magana da cewa" Shukura ya gida? ina Hajiya?"

Da k'yar ta bani amsa da cewa" Ta shiga sallah.

Ban sake wata magana ba na fara hawa saman domin babu abinda na fi bu'kata a yanzu kamar na watsawa jikina ruwa.

Walida ta biyo bayana tana jijjiga yarinyar dake wani irin kuka da alama dai akwai abinda ke damunta .


Hajiya ta fito d'aga daki tana fadin" Kukan jarirai na ke ji a cikin gidan nan".

Shukara ta bata amsa da cewa" Eh mana matar gidan ce ta dawo ina jin ta je gidan marayu ta dauk'o mana jangwam!

Ta zauna kan kujera da fadin" A'a to ba a gidan nan ba, domin mafi akasari duk yaran da suke gidan marayu shegu ne an rasa yanda za a yi da su aka kai su can aka aje."


Shukura dai ta'be bakinta ta yi ta cigaba da danna wayarta ita dai babban burinta mamanta ta dawo gidan.

Ina 'ko'karin shiga wanka kawai na ga mace ta shigo dakin. fuskarta kawai na kalla na gane cewa; ba alheri ne ya shigo da ita ba.

Na ce" Hajiya sannu da gida, na dawo ai Shukura ta ce mini kina sallah.

Ta shiga bin Walida da kallo wacce take kokarin cirewa babyn pampas.

"Wannan jaririyar fa?" ta fada idonta a tsaye a kaina.

Na ce." 'Yar gidan Hadiza ce, na san kuna da labarin mutuwarta ko?"

Ta ce" A'a mu ba mu da labari. to yanzu da ki ka dau'ko ta kina da nonon da za ki bata ne?"

Na ce" Hajiya wannan ai duk mai sauki ne akwai madara da likita ya dora ta akai.

Wani irin kallo ta yi mini kafin ta ce." Kin d'auko nauyi kin kawo mana cikin gida ita kuma wannan fa?" ta fad'a tana nuna Walida dake zaune.

Na danne 'bacin raina na ce" 'Kanwata ce ita ce 'karama a cikinmu."

Tsaki! mai tsayi ta ja kafin ta ce" Allah ya kyauta! ai na d'auka gidan marayu ki ka je ki ka d'auko mana jaraba! domin dai duk shege ne a gidan."

Gabana ya fad'i da jin abinda ta ce. ina jin tsoron ta san asalin yarinyar ban san wane irin tashin hankali ne zai faru ba.

Na yi namijin 'kokarin fadin." A'a Hajiya ba duka suke shegu ba, don Allah ka da kiyi wa al'amarin mummunar fahimta, domin wasu kaddara ce take kai su gidan, kuma shegen da ki ke magana a kai ai yana da uba, domin dai mace ita kadai bata iya haihuwa, kuma dukkansu Allah ya kaddara hallitarsu ta wannan hanyar.

Uffan ba ta ce mini ba, sai mummunan tsaki da ta ja min ta kama hanya ta fita.

Ajiyar zuciya na sauke tare da shiga band'akin da tunanin abinda zai je ya dawo.

A gurguje na yi wankan na fito, dalilin kukan da yarinyar take tsalawa, dama kwana biyu abinda ke damunta kenan koke-koke! rashin kwanciyar hankali ya sa ba mu kaita asibiti an dubata ba.

Walida na tsaye da ita a kafadarta tana jijjigata ta ce." Anti anya ba wani abun ne yake damun yarinyar nan ba, ina kokarin sanya rigata na ce." Na fi tunanin cikinta ne ya kumbura tunda kinga tunda aka haifeta ba ta yi kashi ba, tun bayan wanda suke a ranar da aka haife su''

Cike da alhini ta ce."To anti yanzu ya za a yi?"

Hannu nasa na kar'be ta da cewa; Kada ki damu in sha Allah likita zai zo har gida ya duba ta, ke dai je ki yi wanka ki d'auro alwala ki fito.

Ta amsa da ''To" ta ta shi ta nufi band'akin!

Iskar bakina na dinga hura mata a kunne har Allah ya sa tayi shiru jikinta ya saki alamun baccin ya dau'keta, a hankali na kwantar da ita. na hau kan dadduma na gabatar da sallah.


Sai da ta idar da sallah tukkuna na kalleta da fadin."Kina jin yunwa ko Walida?"

Murmushi ta yi da cewa" Ba sosai ba, amma Anti ina da tambaya idan babu matsala."

Ido na tsira mata ina sauraranta.
Ta ce" Da alama ba kya jin dadin zama da mutanan gidan nan, duba da irin kallon banza da su kai mana, maganganun da matar nan ta yi, sun tsaya min a rai."

Murmushi na yi na ce" Walida al'amarin sai dai addua kawai, amma na ajiye abinda yake faruwa a matsayin ibada, kin san shi aure hakuri ya fi rinjaye, ke ma ina so ki kawar da kanki a kan dukkanin abinda za ki ga yana faruwa a gidan nan."

A sanyaye ta ce" Shikkenan Anti Allah ya ba ki hakurin da juria." na amsa da "ameen" kafin mu sauka kasan domin nu na mata masaukinta

Akwatin kayanta na
can a jiye a bakin kofa! na ce." Ki dauko kayan ki biyo ni."
Dakin dake kusa da Shukura na nufa. da mukkuli a jikin kofar ina murzawa ya bude, muka shiga tare, komai a akwai a dakin, sai dai ya yi datti! yana bukatar gyara, na ce'' Ki gyara abinda ya sawwaka idan ya so da safe sai ki 'karasa. amma ki fito min da kayan Nanah dake cikin akwatinki."
Ta ce"To shikkenan Anti." fita na yi daga d'akin cike da tunani a cikin raina.

To a daran na tura masa text na bayanin duk abinda yake faruwa, na ba shi tabbacin cewa mun dawo gida amma yarinyar tana bukatar ganin likita.

Washe gari da sassafe sai ga likita mace ta zo. na sauk'a kasa da yarinyar a hannuna na shiryata tsaf! muka gaisa da juna, ta kar'be ta na dubata, nan na yi mata duk bayanin da ya dace.
Ta ce." Watakila madarar da ake bata ce bata kar'be ta ba, amma za a sauya mata wata in sha Allahu. sannan akwai magunguna da za a dinga bata za su taimaka mata."
Na ce" Na gode sosai 'yar uwa. yanzu za ku je da Sule sai ki hada masa duk abinda ya dace."
Ta ce"To shikkenan hakan ya yi Allah ya bata lafiya."
Cike da kulawa na amsa da "Amen."

To cikin ikon Allah yarinyar ta samu lafiya sakamakon madarar da aka sauya mata da kuma magungunan da nake bata a kan ka'ida, ta dai na kuka yini take tana bacci, sai dare ya yi ta hana ni yin nawa, k'arshe k'asa na sauko na tare a masaukin Walida muna renon tare.
Wani lokacin kuma Baba Marka ta kan taimaka mana domin idan ta kammala ayyukanta, yini yarinyar take a bayanta, a lokacin muke samun dama rama bashin baccin da muka tara.
Hajiya kuwa kallonmu kawai take duk d'auki ba dad'in dake faruwa ci kanku ba ta ce ba.

Cikin wannan halin
Hajiya Fatima ta dira a gidan, tun bayan abubuwan da suka faru ba ta sake zuwa gidan ba sai wannan lokacin. sama-sama muka gaisa, sai dai gani na, ina hidima da jaririya ya sanya ta dinga yi min wani irin kallo wanda sai da na sha jinin jikina, kuma na tabbatar da cewa; sai wani abu ya faru na tashin hankali.
[2/4, 8:41 PM] Bintu: 128&129
Aikuwa dai ina fitowa daga kicin na riske su suna mayar da yanda akayi gani na ya sanya Hajiya
cewa" Shahida ashe wannan yarinyar ta hannunki shegiya ce shine ki ka d'auko najasa ki ka kawo mana gida?"

Na ce" Lallai duk wanda ya fad'a miki wannan magana ya cika ma'karyaci."
Na fad'i hakan ne saboda Fatima domin ina da tabbacin ita ta zo da maganar, tunda ta tura k'awarta ne domin ta d'auko mata rahoto!

Kallona ta yi da cewa'' Ke kada ki mayar da mutane shashashai mana, ko kin d'auka ba mu da labarin abinda ke faruwa? idan Hajiya ba ta san komai ba, to ni a tafin hannuna ki ke?''

Na ce." Oh! shiyasa ki ka tura 'kawarki mai suffar karuwai."

Kallona ta yi kafin ta yi murmushi da cewa" Hajiya Zaliha dai ba ta ta'ba ajiye d'an shege ba ballanatana ki goranta mata, tsiya da fasadi ya tattara a zuriarku masu mugun abun fad'a."
Karaf a kunnan Walida Fatima ta kai karshen maganarta, dama can Walida ba kanwar lasa ba ce, jin irin cin mutuncin da Fatima ke yi ya sanya ta dakatar da ita ta hanyar fad'in" Ga ki nan karuwa! mai bilitin da suffar 'yan wuta!"
Shukura ta zabura! ta mike tsaye tana d'urawa Walida ashar da fadin"Lallai yau sai ta bar gidan."

Na ce" Walida kada ki sake wata magana ki k'yalesu koma meye dai ba zan mayar da yarinya ba tunda gidan mijina ne da kuma amincewarsa komai ya ke faruwa."

Hajiya ta ce" Aikuwa ni zan bar miki gidan. domin kuwa ba zan zauna da najasa a gida d'aya ba."

Shiru na yi mata ban ce uffan ba, na ja hannun Walida muka shiga daki.

Na ce" Walida wallahi akan wannan yarinyar zan iya barin gidan nan, bari maigidan ya dawo na ga ji da wannan masifar."

Cike da alhini ta ce" Anti gaskiya mutanan nan sun matsanta miki da yawa, ke da gidanki sun zo suna takura miki mussaman waccer tsohuwar wallahi na tsaneta.

Na ce" Walida ki bari kawai! ni kadai na san irin takaicin da nake k:unsa a gidan nan, amma Allah zai yi min maganinsu.''

Ta ce" Shiyasa fa wasu basa son auran masu kud'i saboda gudun matsala irin wannan, ga dai jin dadin amma babu kwanciyar hankali."

"Ni ba ni da matsala da mijina domin yana sona mutu'ka, matsalar kakarsa ne da tsohuwar matarsa sune suka addabi rayuwata.'

Ta ce" Anti ki yi hakuri amma ki tsananta da addua in sha Allahu. komai zan wuce."


To a can falo kuwa Hajiya ta sa a kira mata maigidan a waya. ta rushe da kuka da cewa" Babu shakka Alhaji Habu ka kalalace, yanzu a ce da goyon bayanka matarka ta d'auko najasa ta kawo mana gida, to wallahi zan tattara kayana na bar maka gidanka muddin ba za ka d'auki mataki ba.

Sai ya kasa gane inda maganarta ta dosa ya ce." Hajiya wace irin najasa kuma? don Allah ki yi hakuri kina sasautawa yarinyar nan, abinda ke faruwa a tsakaninku baya yi min dadi."

Ta ce" Dama ai da gadara take fad'in gidanta ne kuma miji na ta ne, sai yanda ta yi, to ai babu lefi tunda kai ka bada goyon baya kuma baka hango kuskure hakan ba, zan tattara kaya na bar maka gidanka tunda dai haka ku ke so.

Ajiyar zuciya ya sauke ya ce." Ki yi hakuri in sha Allahi gobe i war haka ina gida sai mu tattauna maganar."

Ta ce." To shikkenan Allah ya kawo ka lafiya."

Wayarsa ya kashe yana girgiza kansa, ya rasa abinda yake damun Hajiya, dama bahaushe ya ce." Idan ka shekara ba ka ga mutum ba, to duk lokacin da ku ka had'u ka tambaye shi halinsa, a lokacin zamansa da Zinaru har tausaya Hajiyan yake, amma da yake 'yar adam ce ta samu yarinyar kirki tana wahalar da ita, maganar dai guda daya ce ta rashin haihuwa har yanzu sun kasa gane cewa; Ubangiji shike bayarwa kuma shike hanawa.

Hajiya Fatima kuwa jin cewar zai dawo gobe ya sanya tattara komatsanta da sassafe ta nufi jibia, domin tana jin tsoron ya dawo ya risketa a gidan, ya kuma samu labarin cewa da sa hannunta a cikin faruwar al'amarin, tabbas ta san cin mutunci ne zai biyo baya, shiyasa ta ware!

To dama tun dare ya yi mini text cewa zai dawo gobe, dalilin da ya sanya kenan na yi 'yan shirye-shirye irin wanda ba a rasa ba, na san dai yana sauka da abin zai fara, shiyasa na shirya jikina.

Sai dai kuma matsalar da a ka samu. baby ta wayi gari da rikici! kuka take na ba gaira ba dalili, tunda babu yunwa a tattare da ita, Walida ta yi ta ga ji ta ba ni ita, na kar'be ta ina ta aikin jijjigata, lokacin kuma Baba Marka tana kicin tana aiki ballanatana ta taimaka mana, cikin wannan halin ya dawo gidan.
Hankalina ya rabu gida biyu, duk na rasa yanda zanyi domin dai kukan da yarinyar take ya fara ba ni tsoro sai nake zargin ko dai ba ta da lafiya! tausayinta ya cika mini zuciya.
Hakan ya janyo na kasa ba shi kulawar da yake bukata, gashi ya dawo da matsananciyar bu'kata! don ko abinci bai ci ba, yake ta 'ko'karin kwanciya da ni, ni kuma na ce lallai sai ya huta gajiya tukkuna ya barwa dare koma meye sai ya faru.
Hakan sai ya janyo min b'acin rai mai tsanani! domin dai fad'a ya rufe ni da shi wanda nima na gaza ha'kuri! na mayar masa da martani ina kuka dama kuma a kusa nake sakamakon irin tujarar da Hajiya take min a gidan ta ishe ni ta gallabeni kuma ya kasa d'aukar mataki, kullum maganar dai guda daya ce na yi ha'kuri, gaskiya na ga ji ba zan iya jurewa ba." Abinda na fad'a masa kenan ina kuka! irin wanda na jima ban yi irinsa ba, domin na riga na tara abubuwa da yawa kukan ne kawai zai sanya na samu sasauci!

Ganin na 'ki na daina kukan ne ya sanya ya ce na tashi na fitar masa a da'ki! yanda ya yi maganar zai tabbatar maka da cewa; a kufule ya ke, ban nemi sulhu ba kawai na ta shi na fita. idona jajawur!
Hajiya da Shukara suna zaune a falo na sauko, gani na cikin rashin nutsuwa ya sanya suka bi ni da kallo. har na shige masaukin Walida ba su janye idonsu daka kaina ba, tabbas na san hakan ba 'karamin dadi ya yi musu ba.


Ko da na shiga d'akin kasa daurewa na yi na kwanta kawai hawaye! na ambaliya a fuskata! Walida goye da baby a bayanta ta tsuguna gabana murya na rawa ta ce."Anti menene? wani abu su ka yi miki ko?"

Shiru kawai na yi mata domin duk bayanin da zan yi mata ba za ta fahimta ba.

Tasa hannunta tana goge min hawaye! yanda lura itama saura kiris ta fashe da kukan, domin kwalla ta kwarmin idanuwanta.


Ganin haka ya sanya na daure zuciyata na tashi zaune na goge hawayen da suka kasa daina zuba na ce" Kada ki yi kuka Walida, na daina nima ka da ki zubar da hawayenki."


Muryarta na rawa ta ce."Anti mutane da yawa suna sha'awarki cewa kina auran attajiri! ashe ke kad'ai ki ka san matsalar dake damunki, wallahi ba na jin dadin ganinki cikin damuwa Anti zan ta ya ki da addua in sha Allahu.

Na ce" Na gode sosai Walida amma ni babban abinda yake damuna cin zarafin mahaifina da akeyi wallahi idan ni kad'ai abin ya shafa zan iya jurewa, amma duk lokacin da a ka fadi mummunar kalma akan Babanmu hankalina yana ta shi."

Ta ce" Anti duk wannan masifa da 'kask'ancin da muke ciki shine sila. domin shi ya zubar mana da mutunci a duniya a can baya yana ganin duk abinda yake aikatawa daidai ne, wannan shine fa dalilin da ya sanya aka fasa auran Jamila, ga shi har yanzu da ni da ita ba mu da tsayyayen wanda zai aure mu.

"Komai yana da lokaci Walida kada hakan ya dame ki, in sha Allahu za ku yi aure idan lokacin ya yi, addua za ku tsananta." Na fad'a cikin kwantar mata da hankali.

Ta ce" Kin ga dai yarinyar nan ta yi bacci. wallahi Anti wani sa'in kawai rigima ce, amma na ga ke sai ki dinga ganin ko ba ta da lafiya ne.

Na ce" Walida kukan yaro ai babu dadi. wallahi duk lokacin da yarinyar nan take kuka sai na tuna Mamanta, hakan sai ya tayar min da hankalina na ga kamar na gaza ta wani fannin shiyasa ki ka ga ina shiga damuwa "

Za ta yi magana kenan Shukura ta shigo babu sallama.
Babu walwala a fuskata na kalleta. Ta ce" Ki zo Daddy yana magana."
Daga haka ta kama hanya ta fita.
Ta shi nayi na bi bayanta

13 / 15