MAJANUNI BOOK 5 BY BINTA UMAR ABBALE.txt

Author :  Binta Umar Abbale Category :  Home Of Novels

Chapter   14 / 15

39K to 42K   out of 44.5K words

fuskata a murtuke! bana tsammanin zan d'auki wani raini.

Ya zaune kan kujera cikin farar jallabiya mai karamin hannu. kamar ko da yaushe idonsa sakaye da farin gilashi. amma kallo daya nayi masa ban sake marmarin sake kallonsa ba, saboda yanda fuskarsa take a had'e! da alama har yanzu da sauran 'bacin ran d'azu.

Ba tare da na saki fuskata ba na zauna kan kujera amma ban ce komai ba, sai dai na tsirawa bakinsa ido domin na fi fahimtar maganganunsa.

"Duk lokacin da a ka kawo min 'korafi a kanki na kan 'karyata saboda ina miki kallon mutuniyar kirki, sai ga shi yau nima kin gwada min halinki." Ya ja numfashi kafin ya cigaba da cewa; Ni na baki umarnin d'auko yarinyar nan ki zo da ita domin ki samu sasaauci na daga irin jarrabawar da Allah ya yi miki. watakila ri'konta Allah yasa kema ki samu na ki, sai ga shi tun ba'a je ko'ina ba abubuwa marasa dad'i suna faruwa, wanda har da ni suka shafa, saboda haka ina ganin ki mayar musu da 'yarsu, idan kuma ba haka ba, zan d'auki wacce za ta yi rainonta har ta yi wayo idan ya so sai ki 'karba."

Kallonsa na yi na ce" Ba mu yi haka da uwarta ba, yarinyar nan amana ce a gurina, kuma na kar'ba tsakanina da Allah ba na duba ta hanyar da aka sameta, kuma kafin hakan ta faru sai da na nemi shawararka ka amince, amma me yasa yanzu za ka sanja magana. to gaskiya in dai ka ce dole na mayar da ita za mu tafi tare domin nima na ga ji da wannan zaman wahalar, idan ya so sai ka auro mai haihuwa.

Idonsa ya tsira mini da zallar 'bacin rai a cikinsu!

Ni kuwa ban ji nauyi da shakkar furta masa maganar ba, domin na ranste da girman Allah ba zan mayar da yarinyar ba, mutukar kuwa ya ce sai na mayar da ita to zan bar masa gidansa


Karaf! sai ta ce."To Alhaji Habu tunda matar gidan ta yanke hukunci ai shikkenan. sai mu ta shi mu yi gaba domin dai nima nayi rantsuwa da Allah ba zan zauna da najasa a gida d'aya ba.'


Raina ya dungunzuma! na tsani na ji tana danganta yarinyar nan da najasa ina jin haushi mutuk'a!
A fusace! na ce" A'a Hajiya ki daina kira na da matar gida, nan gaba kad'an za ki kawo masa mace mai haihuwa, kamar yanda ki ka ci alwashin raba tsakanina da shi, to bukatarki za ta biya amma fa ki sani za ki je ki tarar da sakamako a lahira!

Fashewa ta yi da kuka! ni kuma ban yi aune ba kawai na ji saukar lafiyyan mari a kumatuna, abinda bai ta'ba faruwa ba tsakanina da shi!

Ido na tsira masa wanda suka bushe! da zallan b'acin rai da takaici! na nuna ta da yatsa da fadin" Ka ga wannan tsohuwar ba za ta ta'ba barin ka ka zauna da mace ba. ni kuma nayi imani cewa; a zamantakewa ta daku ban zalince ku ba, amma cikinku duk wanda ya zalince ni dai-dai da second d'aya na bar shi da Allah.
Gabadaya na gama kashe musu jiki.

Ban jira komai ba na hau sama na harhad'a kayana cikin akwati, ikon Allah har lokacin ban ji alamun kuka ba, zuciyata ta gama bushewa!

Na sauko cikin shirin barin gidan hannuna janye da akwatin kayana, suna zaune a falon har yanzu suna mayar da magana, ko kallonsu ban yi ba, na shiga na kira Walida muka fito a tare.

Zuwa ya yi ya 'kwace akwatin dake hannuna, be ce min komai ba sai dai na hango tsantsar damuwa cikin k'wayoyin idonsa! jijiyar kansa duk ta ta shi.
Ido ya tsira mini kawai yana kallo. na fashe! da kuka da k'arfi na ce" Yau babu wanda ya isa ya hana ni barin gidan nan, na gaji da wannan bala'i."

Na kai hannu ina jan akwatin hannunsa yana ja ina ja!! su kuma duk sunyi cirko-cirko! Hajiya tayi kalar tausayi kamar mutuniyar kirki! ita kuwa Walida kukan take ta ya ni. yayin da Shukura take ji kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha saboda farin ciki.
Ganin ya ki ba ni akwatin yasa nayi gaba da cewa" Walida shige mu ta fi ko a kafa za mu kai kan mu gida."

Bai ji kunyar kowa ba ya rungumeni tare da yi mini wani irin ri'ko! wanda na rasa yanda zanyi na k'waci kaina, dole haka na ha'kura na kwanta a jikinsa, a lokaci wasu azababbun hawaye masu tsananin zafi suka fara gararanba! a farfajiyar fuskata.
[2/7, 1:31 PM] Bintu: 130
'Kokarin zarmewa yake domin gabad'aya hannuwansa sun kasa tsayawa guri guda, sai yawo suke a sannan jikina, jin haka ya sanya da sauri na cire jikina na matsa gefe ina bin falon da kallo. babu kowa sai ni da shi, ina tsammanin ganin abinda yake faruwa ne ya sanya suka gudu. lallai an tafka abin kunya.
Kallonsa na yi yana tsaye kamar wanda aka dasa a gurin, ya yi mini 'kuri da idanuwansa da su ka k'ank'ace! babu abinda ke damunsa sai fitina, domin duk lokacin da ya shiga irin wannan yanayin ina fahimta, kuma idan na shiga hannunsa sai abinda Allah ya yi.
Hannu nasa zan d'auki akwatin ya janye. ya matsar da ita gefe tare da kusantata, yana ta wani lumshe idonsa, wasu lokutan idan yana wasu abubuwan har mamaki yake bani, ni na tabbatar da cewa; yaro d'an shekara ashirin ba zai nu na masa iya soyayyah ba.

'Kugu na ya kamo ya sake matsani a jikinsa da fad'in." Kina so na rasa rayuwata ko ?"

Kuka na fashe! da shi tare da sake yunk'urin ture shi! ya ri'ke gam! yana ta cusa fuskarsa a jikina.
Na ce" Na ga ji wallahi. don Allah ka yi aure ko kuma ka sake ni, don gaskiya ba zan iya ba, Hajiya ta takurawa rayuwata, kuma ka san hakan, amma ka kasa daukar mataki! har sai da aka 'kure ha'kuri na, mutukar cin zarafi zai wuce kaina ya je kan iyayana ba zan lamunta ba."

Fuskata ya rik'e da hannuwansa. sai da ya daidaita yanayinsa tukkuna ya ce." Ba zan sake ki ba, kuma ba zan yi aure ba. wannan maganar na sha nanata miki! saboda haka kada ki sake min irin wannan maganar.
Yanda yake maganar babu wasa yasa na tsira masa ido da cewa" Ni kuma ba zan iya mayar da wannan yarinya ba, haihuwa kuma Allah shi yake bayarwa ba wani mahaluki ba.

Ya kai minti biyu yana kallona kafin ya ce." Za ki koma daya d'aga cikin sashen dake cikin gidan nan, wanda dama tun farko hakan na so, ki ka ce ke kin fi bukatar zamanki anan, abinda ya sa na yanke wannan hukuncin saboda a samu maslaha a tsakaninki da Hajiya, itama ina so na cika mata rantsuwarta, wannan yarinyar kuma na 'karba bisa amana, Allah yasa sanadin hakan mu samu namu rabon."

Ajiyar zuciya na sauke ina jin sasauci a cikin raina. lallai hakan shine mafita a gare mu bakid'aya. Na ce" Shikkenan hakan ya yi Allah ya ta ya mu ri'ko."

A kasalance ya amsa da "Ameen" ya ja hannuna muka hau saman. abinda ya faru a lokacin yana da wuya da tsayawa a rai! wata irin zazzafar soyayya mai tsayawa a rai ce ta gudana a tsakaninmu. domin ban ta'ba sanin haka ya mutu! a kan k'aunata ba sai a ranar! ya dinga zubar da hawaye wanda na rasa ko na menene! ko da ya ke ni kaina na san na gwane gurin iya sarrafashi a shimfida, shiyasa yake rasa control d'in kansa, ya haukace! da sambatu! da shiririta, abin ya yi ta ba ni dariya da tausayi, hakika kamar yanda ya sha fada min cewa; ko ya yi wani auran ba zai iya adalci ba, na yarda saboda kwata-kwata baya gajiya da ni, kullum kira na yake da sabuwar amaryarsa.


***
Hankalina ya kwanta sosai na koma b'angarena na mussaman, wanda aka sake shirya shi da ababen jin dadi da more rayuwa, domin har ya fi wancan sashin da na bari kyau da tsaruwa, ni da Walida muka sake muna rayuwa cikin kwanciyar hankali. ga Baby Nanah dake samun kulawa, ta yi gwab'i tubarkalah! yarinya kyakykyawa suma sunkuf a kanta ba'ka mai kyau da 'kyalli, shi kansa Maigidan baya nuna k'yama a kan yarinyar, duk lokacin da yake gidan ya kan sanya na d'auko masa ita ya yi mata wasa. tare da yi mata addua irin ta iyaye.


Wannan abu da ya faru ya tsayawa Hajiya a rai! mutu'ka! sai da suka tabbatar da cewa; baya gari ya yi tafiya, sannan suka tattara kayansu suka tafi jibia.

Ni dai na je da safe domin gaisheta kamar ko yaushe tun bayan bari na sashen, sai na samu Baba Marka ita kad'ai a falo tana goge-goge, muka gaisa cikin mutunci da karamci. na tambayeta ina Hajiya. nan take sheda mini cewa; ai sunyi tafiya. ban kawo komai a raina ba, nayi mata sallama na ta fi.

Sai bayan ya dawo da kwana biyu sannan ya ya nufi jibia domin jin abinda ke faruwa, ni dai ko da wasa ban yi gangancin ce masa komai ba, ko da ya tambayeni sai na ce'' Wallahi nima ban sani ba, na san dai watarana na je gaisheta Baba Marka take sheda min cewa sunyi tafiya. shiru ya yi be ce komai ba, amma yanayinsa gabad'aya ya nuna 'bacin rai, wanda ni hakan bai mini dad'i ba, dalili na riga na san da cewa; ba shi da 'koshin lafiya 'bacin rai na iya tayar masa da ciwonsa, shiyasa na dinga lallabashi, tare da kokarin yi masa duk abinda na san zai faranta masa ransa.

Ko da ya sauka a garin bai je da sassauci ba, domin dai yana so a yau din a yi ta ta k'are, ya lura idan bai yi wa tufkar hanci ba Hajiya na iya dagula masa lissafi, ta dauki karan tsana ta dorawa a kan yarinya da ba ita ta hallici kanta da lalura ba, ba zai taba manta irin wahala da gwagwarmar da mahaifiyarsa ta sha a hannun Hajiya ba, to yana ganin tarihi ne zai maimaita kansa akan matarsa wanda yake ganin shi ba zai iya jurewa ba, domin kuwa shi kadai ya san irin wuyar da ya sha kafin ya sameta.

Wannan karon ma a gidansa a ka zauna. Baba Audu da Auta cikinsu dai babu wanda ya yi wata magana, Hajiya ce take ta sababi kan cewa; lallai ya mayar da Fatima domin samun zuria, idan kuma yana ganin ba zai mayar da ita ba, to dole fa ya yi aure muddin yana bukatar ta cigaba da zaman gidansa.

Sai da ya gama sauratanta tsaf! sannan ya ce." Wai shin Hajiya ba sai da lafiya ake aure ba?"

Kallonsa su ka yi da mamakin furucinsa.

Sai ya cigaba da cewa" Na farko dai ni tuntuni na riga nayi rauni, matar da nake zaune da ita a yanzu hakuri kawai take da ni, domin sai nayi wata biyu zuwa uku ban bata hakkinta ba, dalili ba ni da wadataciyar lafiya, bayan haka kuma bana zama a gari. wannan shine dalilin da ya hana samun cikin da ki ke bukata, kuma ita Fatiman da ko da yaushe ki ke magana a kanta sau nawa tana zubar mini da ciki? watakila wannan adadin da ta zubar shine rabona a duniya."

Fatima ta kalleshi tana jin wani kuttun takaici a ranta, ta san duk wannan maganar da yake fadi karya ne, kawai ya yi hakan ne domin ya kare kansa, ta san halinsa ba tun yau ba, yana da k'arfin sha'awa da kuma kuzari, kuma shekarunsa basu kai har ya tashi daga aiki ba, kawai bashi da ra'ayin mayar da ita kamar yanda ya sha fad'a, ita kanta ta zauna tayi karatun ta nutsu ta lura cewa; ko da Allah ya kaddara ya mayar da ita din wahala za ta sha, domin ta lura wannan kurmar yarinyar ta gama dashi, baya kallon ko wace mace da mutunci kamarta.


Ta ce" Idan duk jikina kunne ne wallahi ba zan yarda ba, kawai ka fadi hakan ne domin ka kare kanka, ai shikkenan ni dama tuntuni na ha'kura! har na fara duba wanda ya cancanta a cikin masu k'auna! saboda haka mutukar a kaina a kayi wannan zaman to na janye."

Shukura ta rushe da kuka da cewa; Mommy ya haka kuma? don Allah kada ki janye ki dawo auran Daddy domin ni ke ce uwata babu wata banza da girmama."

Dama tana zaune a kusa da shi, aikuwa ba ta yi aune ba ta ji saukar mari a fuskarta! a fusace! ya ce." Nima daga yau na bar zama dake ki bi uwar taki idan yaso sai ta sauya miki uba."

Ta 'Kara rurucewa da kuka tana wani irin abu.itama Fatima ido cike da 'kwalla ta ce" Wace irin magana ce wannan kuma? Hajiya kuna jin abinda yake fadi ko? wai na sauya mata uba bayan shi ya haife ta."
Cikin reshin kuka ta kai karshen maganar.

Baba Audu ya ce." Alhaji Habu kasan irin maganar da zaka dinga furtawa wannan maganar ba ta cancanta ba.

Shiru ya yi bai ce komai ba amma gabadaya yanayinsa ya sauya da bacin rai mai tsanani!

Ita kuwa Hajiya tunaninta gabadaya ya ta'allaka gurin ganin ta nemo masa magani, domin dai ita har ta yarda da maganarsa, kuma tana so kafin ta mutu ta sake ganin wasu daga cikin 'ya'yansa, halin da su Fatima suke ciki sam bai dame ta ba.


Shiru falon ya dauka kowa zuciyarsa babu dadi mussaman Baba Auta da tunda aka zauna be ce komai ba, ransa in banda zafi babu abinda yake, watakila yana ganin bacin rai da takaicin yaron shi zai zama ajalinsa, tunda duk 'yan kadarorinsa ya daga ya sayar, duk a kokarinsa na ganin malamai da bokaye sun shawo kansa ya mayar da 'yarsa gidansa, anan yake ganin zai fanshe! abinda ya lalatar, to sai dai abin mamaki! aikin ake ana zubar da jini amma a banza domin dai kullum yaron gaba yake arzikinsa yana ha'baka, duniya tana cigaba da suturtasa da rigar arziki. wannan tunane-tunane sune suka zautar da shi, ya yi tsiru a kan kujera sai zare ido yake.

Lokacin Shukura ta tashi ta buga wani uban tsale a tsakiyarsu, ta yi zaman 'yan bori! wasu abubuwa ta shiga yi tana furzar da yawu, tasa hannu ta cire d:ankwalin kanta tana walagigi a falon.

Gaba'daya hankalinsu ya ta shi. Baba Audu ya dinga yi mata tofi! amma kamar k'ara zugata! yake ta dinga yin iskanci samfur-samfur, don har na wannan lokacin ya fi na baya, duk ta hargitsa musu tunani, Hajiya Fatima sai kuka suke sunyi cirko-cirko a tsaye!


Duk yana zaune a kan kujera yana kallon abinda ke faruwa, cikin ransa ya ce yau ko sarkin aljanu ne akan yarinyar zai sauke mata shi.

Sama ya hau ya dauko wata murtukekiyar bulala! ya nado ta a hannunsa! yana zuwa ya fara zabga mata a jiki da dukkanin k'arfinsa!

Ihu! ta tsala! a guje! ta tayi yunk'urin ta shi ya mayar da ita ya cigaba da zabga mata yana fadin." Za ka yi magana ko ba za ka yi ba." Ya fada lokacin da ya lafta mata duka a gadon baya!..

Ta zabura! jiki na makyarkyata! ta ce" Daddy kayi hakuri don Allah wayyo Allah na shiga uku "

Ya k'ara zabga mata da cewa" Shukura ce ko ba ita ba?"


Tana wani irin kuka kamar za ta shid'e ta ce" Ni ce wallahi Daddy ni ce kayi hakuri."
Bai san lokacin da ya kifa mata wani lafiyayyan mari ba, wanda gabadaya ji da ganinta suka dauke, jini ya billo ta hancinta, sai kawai ta bingire! a gurin ta fadi ta suma.
Ba tare da ya ce komai ba ya jefar da blet din ya zauna kan kujera yana wani irin numfashi.

Hajiya Fatima jikinta duk ya yi la'asar, alamun rashin gaskiya ya bayyana a tare da ita.

Hajiya tare da su Baba Audu hankalinsu bai kwanta ba sai da Shukura ta dawo hankalinta sannan. falon ya yi tsit! sai sautin kukan Shukura dake fita a hankali a hankali.


Ya kallesu da fadin." Wannan shine abinda nake fad'a muku, na tabbatar da cewa; abinda yarinyar nan tayi da sanya hannun uwarta a ciki. ni na san wacece Fatima da halayenta" Cikin tsantsar bacin rai ya kai karshen maganar yana sake jin tsanar Fatima a cikin ransa.

'Bangaranta kuwa tun ba a je ko'ina ba yanayinta a nu na cewa bata da gaskiya ta yi tsamo-tsamo!

Baba Audu ya ce " Shukura don Uwanki aljanu ki ke sha'awa! da har za ki dinga burgima kina tumami! da iface-iface! ashe baki da hankli dama ?"

Hajiya ta ce" Ga babbar mara hankali nan a zaune ai tunda duk abinda yake faruwa da sanya hannunta wallahi ni kaina nayi mamakin ganin Shukura tana iskokai, tunda a gaba ta girma bata ta'ba nuna wata alama ba sai da lamarin nan ya bijiro. amma Fatima kin bani kunya wallahi. wato ashe tuban muzuru! ki kayi? ni ina ta balo'ko'ko! a mayar dake ke kuma kin shirya mugun abu "

Shukura na kuka ta ce." Wallahi duk Mommy ce ta tsara mini komai. wai saboda ta lura Daddy yana sona ta ce mu gwada wannan hanyar ko za a dace ya mayar da ita nima na san watarana dole asirin mu zai tonu."


Sai ta fara borin kunya da fad'in" Kausasan! maganganu! Baba Auta ya fitar da hannu ya tsinka mata mari! zuciyarsa na tafarfasa! ya ce." Yi mini shiru munafukar banza da hofi."

Kallonsa ta yi tana mamakin furucinsa! yau ita yake kira da munafuka bayan duk abubuwan da suke faruwa da sanya hannunsa a ciki, yanzu da ya ga ta kwa'be shine zai cire kansa, wallahi don dai ubanta ne kawai amma da sai ta tona masa asiri.
Tana share hawaye ta dauki jakarta ta bar gidan tare da yanke shawara cewa; ko maza sun kare a duniya ta bar Dangaske har abadah.

Ko da ta fita babu wanda ya bi ta kanta illah shi

14 / 15