Author : Binta Umar Abbale Category : Home Of Novels
lokacin dana bar falon rigima suke a tsakaninsu, nima a raina bana 'kaunar zaman Fatima a gidan, don dai babu yanda zan yi ne, amma akwai damuwa abubuwan da take .
Wanka ya yi ya fito d'aure da babban towel a jikinsa, ya nufi madubi ya dauki man shafawa kafin ya zauna gefen gado, ido muka hada, domin tunda ya fito nake kallonsa, ganinsa cikin damuwa nima duk sai na ji bana jin dad'i."
Magana ya yi min, amma ban ji sosai ba, na dai bi bakinsa ne, wani lokacin hakane yake faruwa idan ban ji magana ba ina kallon bakin mutum a lokacin da yake maganar nan nake fahimtar abinda ya nufi.
'Kasa na sauka lokacin babu kowa duk suna d'aki sai dai amma ina jin hayaniyarsu kamar masu rigima, nayi saurin harhad'a duk abinda nake bu'kata na bar falon, domin bana so wani ya fito ya gan ni saboda gudun zargi.
Kad'an ya iya cin abincin, na kalleshi lokacin yana goge bakinsa na ce" Har ka 'koshi? na ga duk kayi wani iri Allah yasa lafiya?"
Kai tsaye ya ce "Fatima ce matsalata me ya had'a ki da ita har ki ka zage ta?"
Gabana ya buga jin wannan maganar.
Fuska na had'e sosai! na ce."Wani abu ta ce nayi mata to Allah yasa da mutane dai a gurin, kuma duk sharrinta zai koma kanta da izinin Allah! sannan kuma mijina ya yi mata nisa wallahi." Cikin tsantsar kishi da fargaba na kai karshen maganar.
Ta'be bakinsa ya yi, ya d'an murmusa, ba kuma tare da ya ce min komai ba ya haye gado ya kwanta ya ja bargo ya rufe jikinsa.
Hakan ya kara 'bata min rai kishi ya dinga taso min domin na kasa fahimtar inda ya nufa akan tsohuwar matar tasa, hakuri na dinga bawa kaina tare da tausar zuciyata ban bari kishin ya yi tasiri a tare dani ba, na daure na tuttura abincin ina nazarin al'amarin a cikin raina
Babu kuzari nayi wanka nasa kayan bacci sannan na kwanta kusa da shi, lokacin bacci har ya d'auke shi!
Fuskarsa na tsirawa ido a lokacin da yake sauke numfashi cikin nutsuwa yake bacci babu munshari bare buge-buge! ina tausaya masa sosai a raina ban san meye dalili ba, amma can 'kasan zuciyata nake jin wani irin abu wanda ba zan iya fasaltashi ba, kawai dai na bar abin a cikin raina ne, ina adduar Allah yasa na rayu ni kadai a tare da shi.
***
KANO
Talatu taga tujara iri-iri da 'kan'kanci gurin Hujaj! kuka kuwa tayi har ta gaji, duk ta figale ta lalace sakamakon jin labarin auran da zai yi, kuma tun lokacin da surukinsa ya ba shi kyautar gida, ya kwashe kayansa kaf daga gidan Talatu! shi kadai ya tare a sabon gidansa dake rijiyar zaki, a cewarsa amarya ce zata fara shiga domin Talatu zata iya lalata masa gida.
Babban abinda yake sa ta zubar da hawaye a kullum. rashin Hadiza domin dai ta famtsama duniya kusan wata guda kenan rabonta da gida, tana cikin wannan masifar mijin nata ya zo yana sheda mata irin alherin da ya samu yarinyar da ta d'auki karan tsana ta d'ora mata! wai ace kamar Shahida mummuna b'aka kurma(muskiniya) ita ce take auran daya daga cikin attajiran da sukayi suna a duniya, wannan al'amari ya sanya ta zautuwa duk ta sayar da abunda ya rage mata tana yawan asiri akan malamai su raba auran, sannan shi mijin nata a dora masa ciwo ko amaryarsa ta zo ya gagara tsinana wani abu.
Malamai da bokaye duk sun tsiyata ta! ta rasa komai a gidanta, hatta da kwanuka da farantai na cin abinci ta kwashe ta sayar, bata da komai sai tsummokaran da take d'aurawa a jikinta, sai ta fara bin hanya duk gurin da ta ga anyi shanya sai ta kwashe tasa a buhu ta je ta sayar, ta kar'bi kudin ta nufi gurin malami yayi mata aiki akan Shahida da kuma ubanta. har yanzu ta gaza gane annabi ya faku bahaushe yace wanda yayi nisa baya jin kira.
**
To haka rayuwar ta dinga tafiya da dadi babu dadi haka nake ta hakuri, domin kwanan Sadiya biyu da zuwa mai-gidan yayi tafiya zuwa chana domin bud'e sabon kamfanin sarrafa zannuwa! na samu sauki ta b'angaransa! domin idan yana gidan matsanta min yake kullum bani da hutu, a 'kalla sai ya kwanta da ni sau uku ko sau biyu a raina, kuma idan ya fara baya ji baya a ga ni, to tafiyarsa sai na samu sassauci!
Sai dai bana iya sauka kasa na zauna a cikinsu domin ina ganin zamana a cikinsu kamar akwai matsala, tunda har yanzu dai Fatima bata ajiye makamanta ba, duk lokacin da zamu had'u kallon banza ne yake raba tsakaninmu, wannan dalilin yasa nake yin nesa da duk gurin da take, kuma cikin zuciyata nake neman hirji da ita, kuma in sha Allahu mijina yayi mata nisa.
Amma tsakanina da Hajiya da Sadiya babu matsala, cikin girmamawa da mutunta juna muke gaisawa, yaranta kuwa duk mun saba, suna bani girma sosai anti sama anti 'kasa.
Muna gaisawa da juna kullum da mai-gidan, dalilin sabuwar wayar da ya saya min a lokacin da zai tafi, kullum da safe zan yi masa text na gaisuwa tare da fatan alheri. shi kuwa kullum maganarsa, na shiryawa zuwansa domin dai duk abinda yake daurewa kawai yake, amma yana daf da dawowa. saboda haka na shirya idan ya dawo sai na biya bashin dana d'auka!
Dariya abin yake bani duk lokacin da yayi wannan maganar. amma kuma na himmatu da gyaran jikina, kullum sai na hada kankana da madara na sha, sannan na jika kaninfari da yawa, shi ya zama ruwan sha na. a jikina na dinga jin sauyi kuma sa'i da lokaci idan sha'awa ta taso min sai dai na kwanta nayi ta rungume fillo ina tunanin abubuwan da yake min na soyayya a lokacin da muka kad'aice! 'kwarai ya iya sarrafa mace a wannan fage, kuma cikin nutsuwa yake yin komai matsalarsa kawai dogon zango! yana jimawa bai kawo ba, kuma idan ya samu gamsuwa ta farko maimakon ya risina a'a kamar an 'kara masa 'karfi da himma! zai d'ora a inda ya tsaya. wani lokacin har mamakinsa nake idan na dubi shekarunsa na ga irin muzakkaracinsa, sai na godewa Allah da ya azurta ni da lafiyayyan namiji wanda bani da kaico sai dai kuma na kasa sanya abun a raina, kullum idan wata mu'amula zata faru a tsakanina da shi rimi-rimi za a fara dan wani lokacin ma har taimaka masa nake, amma tafiya kad'an zan fara kuka ina ro'konsa ya yi sauri ya gama don na gaji, mussaman idan na samu gamsuwa da wuri gabad'aya sai komai ya fice min a rai, a lokacin da nake wannan rokon shi kuma kamar 'kara masa kuzari ake.
[1/24, 5:39 PM] Bintu: 110&111
Bacci ne ya 'kauracewa idona sakamakon masifar dake damuna, yini nayi a kwance a gado marata sai ciwo take, gaskiya da wuya na 'kara shan wani abu da zai tayar min da hankali duba da cewa; wanda zai d'ebe min kewar baya kusa, kwana biyar da tafiyarsa na ji su Hajiya na fadin zai iya yin sati biyu ko fiye da haka bai dai dawo ba, a lokacin na shiga tunani da nazarin maganarta domin dai sati d'aya ya ce min zai yi, yau ina lissafi kwanansa biyar kenan da tafiya, shiyasa na mayar da hankali gurin gyara jikina dalili na riga nasan yanayinsa. amma kuma abin yana nema ya zame min d'an zani. ga kuma maganar da Hajiya tayi cewa; bai zama lallai ya dawo a lokacin da ya fad'a ba saboda ya saba yin hakan a wasu lokatan zai yi tafiya da zummar yin kwana biyu ko uku amma sai ya shud'e wasu kwanakin bai dawo ba.
Gabadaya nayi saranda na fara tausayawa kaina halin da zan shiga, domin jikina ya riga ya saba da jangwale-jangwale, sai dai ni da kaina na fahimci cewa; ba ni da juriya, domin da tafiya tai nisa nake gajiya, amma kuma da alama inda da sha'awa a kusa.
Waya ta na daura tare da tura masa text Yaushe zai dawo?" sai ya bani amsa da cewa; sai wani satin saboda wasu dalilai."
Ban ji dadin amsar da ya bani ba.
Na sake tura masa da wani sa'kon cewa;
_"Amma dai kai ka ce sati d'aya za kayi don Allah ka dawo nayi kewarka."_
Sai bayan na tura masa text din kuma nazo ina jin nauyi domin ina tsoron kada ya fassara ni.
Ina ta tsumayin amsarsa shiru. a sanyaye na ajiye wayar na sauka daga gadon, band'aki na shiga na sake watsawa jikina ruwa a karo na biyu tun bayan wayewar gari wai a tunani na ko zan samu sassaucin wani abun.
Na shirya jikina tsaf na sauka 'kasa ba tare dana yi kwalliyar fuska ba.
Babu kowa a falon, dama tun safe Sadiya ta sheda min cewa za su zaga gari ita da yara domin mai-gidan yana dawowa za su tafi tasan kuma idan ya dawo ba zai bar su fita ba. ganin babu Hajiya a falon na raya a raina cewa da ita akayi tafiyar. murmushi nayi cikin zuciyata dana tuna cewa; jiya da daddare naji tana kuka da k'afafunta suna ciwo, tabbas da mai-gidan yana nan ba zai bari ba.
Kai tsaye kicin na nufa! Baba Marka tana ta aikace-aikace! muka gaisa cikin mutunci da karamci. na ce"Wallahi awara nake sha'awa ko zaki aikata min, kinga bana jin dadin jikina, amma da ba haka ba da kaina zan yi." Za tayi magana kenan sai gata ta shigo kicin din jikinta sanye da riga da wando masu kama dana sanyi, amma kuma dasu gwara babu domin duk hallitun jikinta a waje suka, babu hula ko dankwali a kanta sai tarin kitson attachment da ta daure da ribbon kamar ba cikakkiyar musulma ba, domin dai ni da ta tsaya a kusa dani ma 'karni na ji tana yi wallahi, ba komai ne ya janyo hakan ba sai bleaching din da take.
Baba Marka ta gaisheta ta amsa kamar ba ta so.
Dama ni tuntuni mun daina magana, domin ko na gaisheta bata amsawa sai dai kallon banza.
Bakinta nake kallo a lokacin da take magana, nan na fahimci abinda take nufi.
"Marka zanyi 'baki saboda haka ki ajiye duk wani aiki da ki ke yi ki fara hidimar shirya musu abinci. kada ki 'bata min lokaci"
Yanda take wa matar magana a tsatstsaye! daga gadara! sai abin ya bani haushi, na kalle ta da cewa; Baba Marka akwai waken suya ko?" da sauri ta ce"Eh Hajiya." Na ce"To ki fara aikin dana sanya ki.''
Sai ta fusata! ta kalle ni da fad'in" Ba ki isa ba kuwa! dole sai ta kammala uzuri na kafin naki".
Na ce"Saboda me?"
"Saboda na isa!" Tafada kamar zata cinye ni.
Dariya ta ba ni, na murmusa kafin na ce"Nan gidan aurena ne, ni nake da umarnin komai koda mai-gidan yana nan, to ballananta kuma baya gari, komai yana hannuna, don haka ban ce kada kiyi abinda ki ke bukata ba, amma ki bari ta kammala uzurina tukkuna ."
"Ke shashasha! rufe min baki anan gurin." Tafad'a tana girgiza.
Na jingina jikin bango ina kallonta tana magana kamar ta tsokane min ido sai kumfar baki take
Na ce"Wai don Allah mai na tsare miki ne? kin d'auki karan tsana kin d'ora min kin san ke baki isa ki kashe min aure ba, amma na fahimci abinda ke damunki idan mijina ya dawo zan rarrashe shi ya mayar dake dakinki shikkenan hankali ki sai ya kwanta ko".
Hannu ta daga zata zabga min mari! na kauce! da sauri ina kallonta idonta yayi jajawur! sai rawar murya take da alama maganata ta 'bata mata rai.
Baba Marka sai hakuri take ba mu, na ce"Baba don Allah ki cigaba da aikinki ki kyaleta idan ta gaji zata bari."
" 'Yar iska muskiniya kawai ke har kin isa ayi abu don ke? to wallahi ki rubuta ki ajiye idan mijina ya dawo hannuna sai kin kwashi kashinki a hannunki da k'afafunki zaki gudu."
Na ce" Ahaf! ai sai da amincewata tsohon mijin naki zai mayar dake, ki lallabani kawai na je na rarrashe shi.''
Cikin dariya nayi maganar domin na sake 'kuntata mata rai!
Aikuwa sai ta rarumi! kofin gilashi zata kwad'a min, nayi gaggawar shigewa kicin d'in ina mamakin al'amarin.lallai wannan bata da hankali.
Hanci ta sha'ka kwalla cike da idonta ta nuna ni da yatsa kafin ta ce" Zaki gane kuranki ne 'yar shegiya 'yar gidan d'an cah-cah!
Na ji kamar ta zuba min tafashashshen ruwa a jikina! ta cigaba da zumdumawa ubana ashar tana ambatar sunansa! da kiransa d'an bariki! al'amarin ya d'aure min kai mutu'ka! nayi mamakin! yanda a kayi ta san sirrina irin haka, shin waye ya fad'a mata asalin mahaifina!
Ban zubar da hawayen ba sai bayan data fita tukkuna, na tsuguna kicin din na rushe da wani irin kukan b'akin ciki!
Baba Marka ta dinga bani hakuri tana bani shawara cewa; ko don gaba da na sake biye mata mu zubar da mutumci, ta ce kuma aikina zata fara sai ta kammala tukkuna ko meye sai ya biyo baya.
Babu 'kwari na fita daga kicin. falo na ganta a zaune tana waya sai kuka take kallo d'aya nayi mata nayi saurin d'auke kaina, sai dai na tsinci wasu maganganun da take kuma da alama da mai-gidan take waya.
Raina ya sake 'baci na hau saman da tunanin matakin da zan d'auka dole idan ya dawo ya zaba ko-ni-ko-ita don wallahi ba zata zauna min a gida ba a rasa gane tsakanina da ita wacece matar gidan.
Kwanciya nayi ina nazarin da tunani akan lamarin. abinda yake bani mamaki shine; cikin labarinsa wanda ya ba ni ya nuna min cewa babu wacce ya tsana sama da ita, kuma a zahiri yana nuna 'kiyayyarta 'karara! to a ya akayi cikin lokaci k'ank'ani! ta janye hankalinsa har yake sauraranta su yi doguwar magana a waya da kuma zahiri? ni wallahi kukan da take yi ma shine yake ba ni mamaki! girgiza kaina nayi da tunanin abinda zai faru idan ya dawo don wallahi ba zan lamunta ba don na ga abin nata babu arziki.
Jin cikina na k'ugi yasa na sauka 'kasan domin duba Baba Marka ko ta kammala.
Suna zaune falo tare da 'kawayenta suna shewa wasu manya mata ne biyu 'yan duniya irinta, gabansu babban tire ne cike da kayan marmari.
Ganin yanda suka tsira min ido ne yasa na soma neman tsari a zuciyata.
Cikin dauriya da jarumta na isa gurin da suke a nutse na ce"Sannunku da zuwa."
Sai naga sun kalli junansu zuwa can kuma suka fashe da dariya suna kallona, raina ya sosu! na san maganata sukewa dariya abinda na tsana a rayuwata kenan!.
" 'Kawata wannan abar fa?" wacce take kusa da ita ke yi mata wannan tambayar.
Ta kalle ni a wulakance kafin ta ce"Ita ce matar tasa."
Suka dinga dariya suna kallona kafin d'ayar ta ce"Allah shi kyautawa Alhaji watakila dai kyawun sura ya duba, amma in ba haka ba meye abin so a tattare da wannan abar, na farko ga ta 'baka mummuna! uwa uba bebiya, wallahi wani cewa zai yi bata da hankali idan ya ga yanda take magana ai sai mutum ya tsorata.''
Bakinta kawai nake kallo a lokacin da take maganar. bayan haka kuma kunnuwana duk sun ji abinda take fad'i a kaina. sosai nayi mamakin furucinta.
Ta ce" Wai nan sai da aka gigita! tunanin mutane sannan aka same ta, domin shi fa a ganinsa daban take da sauran mata! bari ma ku ji wani abu mahaifinta d'an bariki ne mugun dan iska ne duk ina da labarin komai."
Al'amarin da ya fusata ni! nayi tsalle! na dira gabansu! da hannusu na ce" Ku shiga hankalinku wallahi 'yan iska jahilan banza da wofi!" na juya kanta tana zaune tana min kallon mamaki! ina ga ba tayi tsammanin zan iya mayar da martani ba, ido jawur! na ce" Ke kuma wallahi idan ki ka kuskura ki ka sake fadin mummunar kalma a kan mahaifina sai na fasa miki baki! idan kuma kina shakka! ki kara cewa tak! a gurin nan kiga abinda zanyi miki."
Cike da mamaki! take kallona kafin ta ce" Ai ba 'karya akayi muku ba, ko zaki rantse da cewa; mahaifinki ba mutumin banz......bata 'karasa ba na kaiwa bakinta bugu! ban sameta ba dalilin saurin kaucewa da tayi!
Tsaye! ta mi'ke da dumbun mamaki! ni kuma jikina sai tsuma! yake na sake nuna ta da yatsa a karo na biyu na ce" Abu d'aya nake dubawa yasa nake saurara miki, amma zan cire rigar mutumci muddin zaki ci zarafin mahaifina wallahi sai na cire miki iskar dake kanki! ki ji da wai! 'Yar Kano ce ni, kuma haihuwar Jakara! zan iya jure komai amma ba zan lamunci ki ci mutumin mahaifina ba, kuma mijina sai dai gani daga nesa."
Naushi ta kawo min 'kawarta ta ri'ke ta tana bata hakuri! tana fincikewa wai lallai sai ta doke ni, sai zunduma min ashar! take tana yi min cin mutumci, cikin wannan halin su Hajiya suka shigo.
Hajiya ta fashe! da kuka da fad'in "Me zan gani ni Saude! dama wallahi tun a mota gabana yake fad'uwa! wai shin Fatima me yake damunki ne?"
Cikin kuka take maganar tana mamakin al'amarin.
Sadiya ta janye ni daga tsakanin kujerun tana tambayata ba'asi, duk na warware mata komai.
Ta ce"Gaskiya dole ayi wa tufkar hanci domin zamanta a gidan zai haifar miki da matsala, ai iyaye sun fi gaban wasa."
Ashe ta ji lokacin da Sadiyar take wannan maganar.