MAJANUNI BOOK 5 BY BINTA UMAR ABBALE.txt

Author :  Binta Umar Abbale Category :  Home Of Novels

Chapter   7 / 15

18K to 21K   out of 44.5K words

sai ta koma kanta da zagi! da fad'in" Sai ta ga wanda zai fitar da ita daga gidan.

Itama Shukura ta goyi da bayan uwarta suka dinga yi wa Hajiya rashin kunya! wai sune bata k'auna! komai su kayi lefi ne.

Hajiya dai barin gurin tayi. Yayin da 'yan iskan 'kawayenta suka d'auki jakukkunansu suka tafi babu wata damuwa a tare dasu duk da fitinar da suka haddasa!


Duk sona da awarar da 'kyar! na iya cin uku! na gabatar da sallar magariba na kwanta kan dadduma ina tunane-tunane.

Sadiya ta shigo dakin da sallama a bakinta

Zaune na tashi ina kallonta har ta zauna a kusa da ni.

"Hakuri na zo na baki Antina." ta fada tare da rike hannuna.

Na ce"Wane irin hakuri kuma 'kanwata?"


Ta ce"Kan abubuwan da Hajiya Fatima keyi min don Allah kiyi hakuri kuma kada kisa damuwar komai a ranki, akwai dalilin da yasa take hakan, ni kuma na san duk abinda za ta yi yayana ba zai sake zaman aure da ita ba."


Na ce"Meye hujjarki na fad'in hakan?"

"Saboda babu wacce ya tsana kamar ta."

Murmushin takaici nayi na ce" Da kenan! a yanzu dai ta janye hankalinsa akwai yuwuwar ya dawo da ita dakinta, tunda yana iya sauraranta a waya ko a zahiri, ni ganau! ce."


Ta ce"Kada ki manta 'yar uwarsa ce! kuma uwar 'yarsa, ina ganin wannan ala'kar ce ke sanya ya shiga huruminta, amma bana tsammanin zai cigaba da zaman aure da ita."

Dariya ta bani ganin yanda take kare shi, na ce"To shikkenan tunda kin ce haka, amma ni idan ya dawo zan zauna da shi, tilas ya fada min dalilin Fatima na zama a gidansa, idan kuwa babu k'wa'kwkwaran hujja! to zai za'ba ko-ni-ko- ita don mutane su bambance! wacece matar gidan a tsakaninmu.

Ta ce."Kema kina da hujjah antina, amma don Allah a sassautawa dattijo kinga shekaru sun fara hawa kansa, bayan haka ga zirga-zirga da hatsaniyar neman halal! a gurinki kawai zai samu sassauci! kada ki tsawwala masa da yawa.

'Yar dariya nayi na ce"Nayi miki al'kwarin ri'ke miki dan uwa bisa amana. ki taya ni addua."

Ta ce."In sha Allahu. zan taya ku adduar zaman lafiya tare da samun zuria masu albarka domin babban burin Yayana kenan."

Murmushi kawai nayi ina kallonta. cikin zuciyata na amsa da "Ameen" domin har ga Allah ina so na haihu domin tabbatuwar farin cikinsa tare da cikar burinsa.
[1/25, 10:08 PM] Bintu: 112&113
Sadiya ta jima a tare da ni duk a 'ko'karinta na ganin ta kwantar min da hankali dangane da irin abubuwan da suke faruwa a gidan, ganin yanda ta damu da al'amarin ne yasa na nuna mata cewa; komai ya wuce a gurina, hakan yasa ta kwantar da hankalinta, muka jima muna hirar duniya, yanda take fahimtar maganata da yanda take mu'amula da ni sai ka rantse da Allah cewa; mun jima a tare, sosai take gane maganata fiye da tunani na, hakan ya kara mata matsayi a cikin zuciyata, domin ni a rayuwata ina so naga wanda ya iya mu'amula mai kyau! kuma yake fahimtata a koda yaushe idan nayi furuci! bai kyare ni ba, bai kuma nuna gazawarsa ba.

Da kanta ta kawo min abinci da duk abinda zan bu'kata, tana ta yi min hidima tare da tsokanata da fad'in" Yau ta fanshi d'an uwanta!

Dariya kawai nayi na girzgiza kai. gaskiya na yabawa k'o'karinta, kuma ta yi nasarar gusar da kashi hamsin na 'bacin ran dake damuna, haka da muka kasance cikin tsokanar junanmu irin na wasan kanin miji.

Sai wajan goma da rabi na dare tayi min sallama ta sauka 'kasa


Ni kuma na shiga band'aki domin watsa ruwa a jikina.

Tsaf na shirya cikin kayan bacci masu taushi na gyara gashin kaina wanda yake ta wani irin kumburi dalilin mayukan da nake shafawa, gashin ya cika ya yi laushi da ba'ki sosai gwanin sha'awa, manya ribbon nasa na daure sannan nasa hula, na nemi guri na kwanta da tunanin abubuwa da yawa a cikin raina


Wayata na d'auka ina dubawa nan naga text d'insa yana tabbatar min da dawowarsa gobe.

Dubawa nayi amma ban bashi amsa ba, kawai na ajiye wayar ina tunani a akan dawowarsa, tun dai kafin faruwar hakan, da bakinsa ya ce sai wani satin saboda wasu dalilai to amma na fi zargin ya samu labarin hatsaniyar da ta faru shine dalilin dawowar tasa bagatatan! na san kuma ba kowa ne zai sheda masa ba sai ita fitinanniyar.

Addu'a nayi sosai kafin bacci ya d'auke. cikin ikon Allah ban farka ba sai asubahi, nayi baccin dana jima ban yi irinsa ba.

Bayan na idar da sallar asubahi. sai na sauka 'kasa domin gaisawa da mutanan gidan kamar koda yaushe.

Ina shiga d'akin Hajiyan na same su gabad'aya har da shi a zaune da alama bai jima da sauka ba, kuma a dakin ya yar da zango. Na ji wani iri a cikin raina kuma na tsargu! mussaman ganin irin kallon da suke min. yanayinsu ya nuna suna tattauna muhimmiyar magana ne, ita Hakimar ma tana zaune a kusa da shi, kuma babu wata sutturar arziki a jikinta, kayan bacci ne, duk ga nononta nan a waje da shattin cinyoyinta.

'Bacin raina ya sake nunnukuwa! amma ban nuna a fuskata ba, nayi k'okarin danne damuwa na gaishe da Hajiya kamar koda yaushe ta amsa cikin kulawa. na kalleshi lokacin ya tsira min ido kamar wanda yaga sabuwar hallita, na daure zuciya da fadin" Yallabai sannu da hanya ka dawo lafiya?"

Da sauri ya amsa min yana 'kokarin tashi tsaye da jakarsa a hannu.

"Antina ina kwana." Sadiya ce take gaishe ni. na amsa fuskata a sake kafin na yi ya'ki da zuciyata gurin kallonta da Cewa; Anti Fatima mun tashi lafiya?"

Ta amsa ba tare da ta kalle ni ba sai wani cin magani take.

Tsaye na mi'ke da niyyar fita, sai kawai ya biyo bayana muka fita daga dakin a tare, al'amarin da ya basu mamaki! kenan, mussaman wacce ta assasa zaman! ranta ya 'baci ainun! ganin yanda ya dauki jakarsa ya bi bayan matarsa daga shigowarta duk ya rikice! ana magana da shi rimi-rimi! amma ya tashi ya fita. wasu hawaye masu ciwo suka ciko idonta, tana ganin dole sai ta tashi a tsaye gurin ganin ta farra'ka tsakaninsu! yarinya 'kan'kanuwa ta rikita babban mutum irin wannan! ba zata iya jure wannan takaicin ba.


Tun da muka fito daga dakin yake ta kallon fuskata! ni kuma naki yarda na kalleshi, na dai yi namijin kokarin kar'bar jakar hannunsa nayi sauri nayi gaba ba tare da nace masa komai ba.


Yana shigowa d'akin ya zo ya zauna kusa da ni. idanuwansa kawai na kalla na gane abinda yake da akwai, abu biyu suka dame shi, sha'awa da kuma damuwa! gabad'aya ba a nutse yake ba sakamakon tayar masa da hankali da Fatima tayi, wannan dalilin yasa ya d'auko hanya babu shiri, duk da cewa bai kammala uzurinsa ba, sai da ya bar komai gurin amintattun abokansa da yaransa.


"Me ya faru bayan tafiyata?" Ya fad'a tare da rike hannuna.


"Me ta fad'a maka ya faru?" Nima nayi masa tambaya irin wacce ya yi min.


Ya d'an 'bata ransa da cewa; Ya ina tambayarki kina maimata min irinta."

Na ce"Ai dole na tambayaka nima."

Tsira min ido ya yi na 'yan mintina kafin ya ce." Me ya had'a ki da Fatima har kina kiranta da karuwa! kuma kina 'ko'karin sheganta Shukura."

Gabana ya fad'i! kallonsa nayi da mamakin furucinsa! fuskarsa babu walwala yake kallo na.

Sai kawai na fashe da kuka! na ce"Sai Allah ya saka min wannan sharrin wallahi. kuma akan wannan matar zan iya barin gidanka muddin ba kayi wa tufkar hanci ba."

Ya ce."Ni ba wannan na tambayeki ba, dalilin da yasa ki ka fad'i wannan maganar. saboda na baki labarin rayuwata, shi yasa ki ka samu makami! gurin tozartani a idon duniya, idan kin kira Fatima Karuwa, kin sheganta Shukura mijinki ki ka zubarwa da mutumci! me yasa za ki yi min haka."


Hawaye na kwaranya na ce" Ka ga kawai kayi shiru tunda dai baka iya yanke hukunci ba, ya za a yi kawai daga zuwa ka fara tuhumata akan abinda ban aikata ba, sosai nake ganin girma da mutuncinka kada wannan ya janyo maka zubewar mutunci a idona."


Ya ce."Mutunci wane iri kuma bayan wanda ki ka zubar min! Shahida ina miki kallon mai hankali me yasa zaki 'bata rawarki da tsalle?"

Hawaye na goge na kalle shi ina ayyana abubuwa da yawa a raina , wato ina ganin idan ban fito masa a mutum ba, zai cigaba da raina min hankali ne, na lura hawayen da nake zubarwa sam! bai dameshi ba, ya zauna yana so ya tarwartsa min zuciya!


Na ce"Ai dama ka saba yaudara! to akan wane dalili zan yarda da kai? duk maganganunka k'anzon kurege ne! ka saba sanja suffofinka tare da kalamanka a duk lokacin da ka so hakan."

Ya zuba min ido da mamakin furucina a tare da shi.

Na ce "Kana ta wani abu! ko ka d'auka kidahuma ce ni? to idan kana da burin dawo da ita gidanka ban damu ba abinda dai na sani shine ranar da ka dawo da ita ni kuma a ranar zan bar gidanka don ba zan zauna ana min yawo da hankali ba."


Cike da d'umbun mamaki! ya ce."Ke kina da hankali kuwa?"

Na ce"Sosai kuwa! kayi magana ne na baka amsa daidai da wacce kayi. Ita kuma wacce tsohuwar guzumar mai kama da arna sai ta gane kuranta wallahi. zata san ni take shiryawa wannan sharrin."


Ya dinga kallona kamar babu gobe, ni kuma ina zaune turmin danya, ko gezau! kuma ban yi nadamar magana ta ba. yanda ya tsira min idonsa nima haka na tsira masa nawa, da kansa ya janye nasa ya tashi ya shiga band'aki babu wani karsashi a tare da shi, kwata-kwata bai ba ni tausayi ba saboda tsabar haushin da ya ba ni.


Ina zaune ya fito daga band'akin da towel a jikinsa, fuskarsa na kalla sai naga kamar bai ta'ba dariya ba, jijiyoyin kansa sun fito, jikina ne kuma ya yi sanyi dana tuna cewa bashi da cikakkiyar lafiya, kada wannan damuwar tasa ciwonsa ya ta shi.

Ina zaune ina kallonsa ya shirya cikin sabulwar jallabiya fara tas! ya fesa turare kamar koda yaushe, ya zauna kan Sofa da wayoyinsa a hannu. a lokacin duk ya kunnasu kira ya dinga shigowa tare da sa'kkoni!


Kallona ya yi, a lokacin da nake kallonsa, sai nayi saurin d'auke kaina ya bud'e murya da bani umarnin kai masa kwamfiyutarsa (loptop) dake kan dirowar gado.

Babu 'kwari a jikina na d'auka na kai masa kafin na shiga band'aki domin yin wanka.

d'aure da towel mai girma na fito daga band'akin, wai ni a dubura ta kada ya hangi wani abu na jikana, ashe nayi a banza, domin tunda na fito yake bina da kallo, gabad'aya yanayinsa ya sauya ya ture loptop din dake gabansa, ganin ya nufo gurin da nake tsaye duk sai na diririce! ni nake da muradin kasancewa da shi, amma 'bacin ran dana kwana dashi ya haddasa ficewar komai daga raina, sha'awar ma ta d'auke! sai 'ko'karin ganin na samu hanyar warware matsala.

Hannu nasa na sake d'aure! towel din dake jikina na zuba masa ido har ya iso ya tsaya daf da ni hucin numfashinsa na dukan fuskata.

Ido na lumshe sakamakon yanda na ji wani irin 'kamshi ya bugi hancina, hucin bakinsa ma abin kwantace ne. mutum ne mai tsabta da kula da komai na jikinsa.


Hannuwansa biyu yasa ya rike k'ugu na da kyau! ya manne kirjinsa da nawa, ya cire hannu daya tare da kokarin kwance towel din dake daure a jikina.

Jin haka yasa na d'an ture shi tare da kokarin kaucewa abinda yake shirin yi.

Da sauri na matsa daga kusa da shi tsigar jikina duk ta tashi.

Ya jima yana kallona kafin ya sauke zazzafar a jiyar zuciya ya koma ya zauna kan Sofa, amma ya gagara aikata komai sai aukin kallo da yake min, duk motsina akan idonsa har na shirya jikina na iske gurin da yake ba janye idonsa ba.


Rashin abin cewa yasa na ce."Ko zaka ci abinci?"

Kai ya girgiza a nutse ya ce."Zauna ina son magana dake." Ganin babu alamun wasa a tare dashi yasa na zauna a gabansa, amma na kasa kallonsa.

Ya yi magana da sautin da zan ji "Shahida ni ki kayiwa rashin kunya ko?"

A sanyaye na ce"Kayi hakuri raina ne ya 'baci wallahi.

Ya ce." Ki yi min bayanin abinda ya faru bayan bana gari.

Na ce" Ni kam ba za ka ji komai daga bakina ba, amma ka ajiye a ranka cewa; ba zan ta'ba tozartaka ba, sannan kuma nayi al'kawarin ri'ke amanarka a gabanka da bayan idonka, amma kuma ina neman alfarma guda daya a gurinka, don Allah kada ka boye min gaskiya ka fada min, meye amfanin zaman Hajiya Fatima a gidanka?"
Na kai karshen maganar idona a tsaye a kansa.

Murmushi ya yi kafin ya ce." Fatima 'yar uwata ce kamar yanda ki ka sani, ban da wannan ala'kar babu wata, a can baya dai nayi zaman aure da ita, amma yanzu babu wannan a tsakaninmu, kuma bani da ra'ayin sake zama da ita, hujja ta biyu kuma Fatima na sauka a gidana ne a duk lokacin da tayi tafiya ta dawo to a nan zata sauka idan baki manta ba ita din 'yar kasuwa ce, tana da gidan kanta wanda ta gina, sai dai zamanta a gidan ita kad'ai akwai had'ari! wannan dalilin yasa na amince da ta dinga sauka a nan, bayan haka babu wata alak'a ta soyayya a tsakaninmu.

Na ce" To yanda na fahimta ita ta d'auke ni kamar kishiyarta, kuma idan baka sani ba a yanzu babban burinta ka mayar da ita d'akinta, tunda duk ta nuna alamu, bayan haka kuma bana tsammanin zan yarda da hujjarka domin dai na gani da idona har sau biyu tana waya da kai a duk lokacin da ta bukaci hakan, bayan haka kuma zata zauna kusa da kai cikin shigar banza, shin wannan daidai ne a gurinku?"


Shiru ya yi yana nazarin maganata kafin ya kalle ni da cewa; Kina zargin wani abu na shiga tsakani na da ita kenan?"

Girgiza kaina nayi na ce" Ba na zarginku amma ai akwai shaid'an zai iya shiga tsakaninku, mutukar zaku ke'bance! kana kallon suffofin jikinta a waje! mai yasa ba za ka tsawatar mata ba, ko da yake na gane abinda kake bukata kenan."


Dariya maganar ta ba shi, ya ce." In banda abinki ni mai zai burge ni a tare da Fatima! ke kad'ai kin ishe ni domin kin tara duk abinda nake bu'kata matsalar kawai kin kasa sabawa da ni, kullum cikin tsorana ki ke, wannan kad'ai shi yake damuna dake, amma ni babu ruwana da Fatima."

Yanda yake maganar yana dariya sai ya ba ni haushi, na tamke fuskata da cewa; "Bana ra'ayin kasantuwarta a cikin gidan nan, muddin ina da hakki a kanka, kuma idan duk jikina kunne ne to ba zan amince da maganarka ba, ina so Fatima ta koma gidanta da zama idan ba haka ba to ni zan bar mata gidan sai ta maye gurbi na tunda dama haka take muradi"

Ya gyara fuskarsa da fadin" Yanzu ya ki ke so ayi kenan?"

"Fatima ta fita da sabgata, sannan kuma ina so ka ja mata kunne ta daina cin mutumcin iyayena domin ban san a ina ta samu labari ba, bayan haka kuma ta yi gaggawar yin nesa da ni, idan ba haka ba to kai zaka kasance cikin damuwa da tashin hankali."

Ya jima yana kallonta tare da ayyana abubuwa da yawa a ransa, ya lura yarinyar nada zafin kishi! kuma sai da so ake kishi! amma damuwarsa yanda zai hana Fatima zaman gidansa, ko babu komai akwai zumunci, bayan haka akwai zuria a tsakaninsu, wannan sune manyan dalilan da ya sanya yake jin nauyin yi mata wani abu na tozarci, idan ta lalace! dole a zage shi a duniya, dama kuma ya lafiyar kura! da yawa jama'a suna yi mata wani bahagon kallo. zamanta a gidansa a duk lokacin da take gari, shine rufin asirinsu bakid'aya. to amma ya san ta inda zai 'billo mata.

Ya ce."Shikkenan ranki ya dad'e abinda ki ke so za a yi, amma kema kada ki sake biye mata kuyi abinda bai dace ba kin jiko, sannan maganar cin mutuncin iyaye zan dauki mataki a kai in sha Allahu.

Ajiyar zuciya na sauke tare da jin sassauci a zuciyata, ina ganin hakan shine samun salama a gare mu bakid'aya domin ni sam ban yi tunanin abinda zai je ya dawo ba.
[1/26, 10:37 PM] Bintu: 114&115
Ina da bu'katar abinda zan ci." ya fad'a yana d'aukar babbar wayarsa dake ajiye a gefensa.

Tashi nayi na sauka k'asan da zummar cika umarnin mai-gidan, abun mamaki! Hajiya Fatima da Shukura suna zaune a falon su kad'ai, Hakimar ta she'ka ado wanda ya ba ni mamaki! sai ka rantse da Allah cewa ita ce matar gidan, abinda ya sake d'aure min kai shine yanda gabad'aya hankalinsu yake kaina a lokacin da nake kokarin saukowa, sai muka shiga kallon-kallo a tsakaninmu, wani bahagon kallo suke min, yayin da ni kuma nake masu kallon mamaki! yanda na fahimta gabad'aya babu alheri a zuciyoyinsu. shiyasa na gyara fuskata, ban kuma yarda na bi ta kansu ba ballanatana wata magana ta had'amu kai tsaye kicin na nufa, a jikina kuma na ji cewar ba su janye idonsu daka kaina ba.

Wainar shinkafa da miyar tantakwashi! tare da kunun gyada Marka tayi na karin kummalo. lokacin dana shiga kicin din ta kammalla komai sai k'amshi ne yake tashi. Marka tana da tsabta da kula, kuma

7 / 15