Author : Aisha JB Mrs Danshuwa Category : My Hausa Novels
kawai hamida ta yi tana daure
zuciyarta da ke bugawa kamar zai faɗo ƙasa. “Kin yi shuru ba ki ce komai ba, ko har yanzu ban
kai a soni ba? Ban yi miki bane?“ Ya faɗa tare da zama daf da ita. Ɗagowa ta yi da sauri tare da
girgiza mishi kai. “Ni dai na san ba da kurma nake tare ba, ko rowar muryan ake yi min?“
“A’ah“
“To a ba ni amsata, shin kin amince min na zama abokin rayuwar ki?“ Sunkuyar da kai Hamida
ta yi tana jin hawaye na cika idanuwanta, tabbas za ta so hakan ta kasance, da tun farko ta san
Hilal zai faɗo rayuwarta yaushe za ta yarda da auren Mansur? Da ta san za ta samu wannan
kyakkyawan halittar da take tare da shi mai cike da sanyi da nutsuwa yaushe za ta fara gina
rayuwarta tare da Mansur, duk da Mansur na da tarin na shi kyawun amma Hilal ya zarce shi,
kalma bayan kalma yake fitar da shi wanda ya sa ta ji zuciyarta ta nutsu da shi, zuciyarta ta
rabu gida biyu, ga Mansur a tsagin damarta yayin da Hilal yake tsagin hagunta, ta yaya za ta
amsa mishi? Ta yaya za ta karɓe shi har ta fara soyayya da shi... “Ba zan takura miki ba, amma
shurun ki ya tabbatar da na samu karɓuwa daga zuciyarki, dan Allah ki soni kar ki yi wasa da
zuciyar da ta mace kan ƙaunar ki. Ina tsananin sonki Hamida...“
Ƙaramin box ya cire daga aljuhun shi tare da buɗewa ya fito da zoben gwal fari ƙal sai sheƙi
yake yi hannunta ya ce ta kawo sai taƙi tana jin tsoron ya taɓa ta kasancewar da igiyar wani a
kanta. Da ya fahimci ba ta so ya taɓa ta ne sai ya yi murmushi tare da ajiye mata zoben yana
faɗin. “Ɗauka ki saka da hannunki.“ Haka ta ɗauki kyakkyawan zoben ta saka a hannun hagu
yatsar dake kusa da ƙarami aikuwa zoben ya zauna ta kalle shi tare da kallon zoben. “Wow!
Kinga da ya yi miki kyau kuwa“ Ita ma murmushi ne ya suɓuce mata domin tabbas zoben ya tafi
da imaninta tana da tabbaci da kuɗi mai tsada ya saye shi. “Na gode...“ Ta yi godiyar cikin
sanyin murya, murmushi ya yi tare da kama cikin shi cike da zolaya yace mata. “Sai yunwa ta
cinye ni ne za a ba ni abincin?“ Da sauri ta miƙe tana faɗin. “Afuwan!“ Bin bayanta ya yi da ido
yana sauke ajiyar zuciya ganin yadda skert ɗin ya fitar da shape ɗin jikinta sosai.
Abincin ta zuba mishi ya sauko daga kujera ya zauna kan capert yace ita ma ta zauna dan tare
za su ci, babu yanda ta iya haka ta zauna tana tsakurar abincin. Lomar farko da ya yi ya lumshe
idanunwa tamkar yau ya fara cin girkin nata yace. “Gaskiya abincin ya yi daɗi, idan zan tafi a
min na musamman domin na yi guzuri da shi.“ Maganar shi sai da ya sa ta murmusa. “Duk daga
cikin santi ne.“ Hilal yace yabon gwani ya zama dole.“ Duk yanda ta kai ga son taƙaita hirar su
ya ƙi ba ta damar haka, domin a cikin barkwanci yake janta da hira tun tana ba shi amsa a
gajerce har ta saki jikinta suka yi hira da yake ta baya, motar Mansur ne ya shigo take ta Ni
zuciyarta ya buga, nan da nan ta shiga wani yanayi wanda har sai da Hilal ɗin ya so fahimta.
“Da wani abu ne?“ Girgiza mishi kai ta yi alamar babu komai, tabbas Mansur ya ga Hamidar sai
dai bai gane ta ba ganin kwalliyar da ta yi da irin kayan da ta saka dan shi a cikin gidan ya san
da himar take yawo. A falo ya iske Rufaida da Mufeed zama ya yi tare da zuba ruwan sanyi
yana faɗin. “Baƙi kika yi ne a gidan?“ “Eh wallahi, Hilal ne ya zo suke tare da Hamida... Ruwan da ya kurɓa ne ya dawo da shi cikin
tashin hankali yana faɗin. “Wacce Hamidar?“ Rufaida ba ta fahimci mugun yanayin da mijinta ya
shiga ba jin ambaton sunan Hamidar da ta yi sai ma ci gaba da ta yi da maganar cikin
murmushi. “Shi fa wai son Hamida yake yi shi ya sa yake ta sunturi Lagos to Abuja... “Kam
babban buran...“ Bai ƙarasa ba Rufaida tace. “Ka yi mamaki ko? Wallahi ni ma haka nake cike
da mamaki lokacin da ya faɗa min ƙaunar da yake yi wa Hamida kuma auren ta yake son yi.“ Ta
dire maganar ta tare da tura mishi plate ɗin abinci gaban sa ta miƙe da Mufeed ta wuce ɗaki.
Abincin da bai iya ci ba kenan ya miƙe ya yi waje hankali a tashe.
Miƙewa Hilal ya yi yana faɗin. “To Sarauniyata ni zan wuce, ina fatan za ki kula min da kanki da
zuciyarki, sannan ki hana kowa matsuguni a cikinta bayan ni.“ Ya faɗa maganar yana dariya.
“Murmushi Hamida ta yi tare da faɗin. “Kar ka damu, Allah Ya kai ka gida lafiya.“
“Amin Ya Rabbi, mu ƙarasa na ba ki tsarabar da na tawo miki da shi.“ Kallon shi ta yi tare da
faɗin. “Bayan wannan tsadadden zoben har da wani tsarabar ka taho min da shi?“ Murmushi
kawai ya yi mata sannan ya buɗe gefen motar da direba ya ɗauko shi ya ɗauko wani babban
leda yana miƙa mata, hannu biyu ta amsa tana yi masa godiya da fatan alkairi. Tana tsaye
direba ya ja mota ya fita da shi, a hankali ta juyo zuwa cikin falo kiciɓus suka yi da Mansur da
ke fitowa a fusace. “Ke uban wa ya ba ki damar kula wani bayan kin san da igiyar aure na a kan
ki? Ras-ras ta ji gabanta ya faɗi take jikinta ya ƙara yin sanyi ta kasa yi mishi magana dan ba ta
san me za ta ce mishi ba. “Magana nake miki ko kin manta igiyar aure na da ke kan ki ne?“ A
fusace yake maganar kamar zai kife ta da mari. “Maganar me nake ji?“ Rufaida ta faɗa tana
kallon su......
09079740079