Author : Aisha JB Mrs Danshuwa Category : My Hausa Novels
buÉ—e booth. Da harara na raka bayanta domin haushi ni kam take ba ni idan ta yi
magana ba ta kira sunana ba.
Ina cikin gyaran bayan mun kammala girki da dare na ji tana ƙwala mini kira. Ɗan dakatawa na
yi ina sake sauraro don sake tabbatar da ni É—in ce ake kira ko kuwa, "Zinariya... "Na'am madam
Salima ga ni zuwa." Bayan na je ta kalle ni tare da faɗin. "Ki shirya gobe ƙarfe shida za mu yi
tafiya." Zaro ido na yi waje ina faÉ—in. "Tafiya ina? O'o ni dai a kaini gidanmu ba ni zuwa ko'ina
wallahi." Banza ta yi da ita tare da haurawa sama, "Ni wallahi kar aje a sayar da ni ma a sa na
daina ganin Innarmu... Cak Salima ta tsaya tare da juyowa ta yi mata wani irin kallo tana faÉ—in.
"An ce miki ko na sayar da ke kuÉ—i zan yi? 'Yar talaka da ke har kina da bakin da za ki ce kar a
je a sayar da ke? Ke ba abin farincikinki ba ne a ce za a keta hazo da ke? Karki kawo mini
shashanci." Tana kawowa nan ta yi shigewarta.
cikin ɓacin rai na gama gyaran kitchen na koma ɗaki na ɗau waya zan kira Innarmu na ga ba ni
da kati kamar na fashe da kuka saboda baƙinciki ga shi dare ya yi babu ta inda zan fita a gidan
bare har in samu kati. Haka na kwana cikin ɓacin rai ina idar da sallar subahi na ji wani mugun
ƙararrawa na ƙara kamar za a ta shi kaina, saboda neman fitina kaya kala uku kawai na saka a
leda sai himar É—ina guda biyu, shi kayan ma doguwar riga ce kawai na saka guda biyu sai fallen
zani É—aya da T-shert ina isowa ta yi mini nuni da wata mota gidan baya na buÉ—e na shiga nan
na ga drive ne sai wannan baƙuwar, ita kuma tare da mijinta suke a mota ɗaya.
Gaisuwa ce kawai ya haÉ—a ni da matar dan ita ma na ga alamar irin madam Salima ce ba ta da
sakewar fuska, haka har muka iso airport nan muka iske wata babbar mata dan za ta iya kai wa
sa'ar Innarmu duk sai na ga suna gaisheta, har shi mijin madam Salima wanda iya bayan rigar
shi kawai nake iya kallo, ni kam ina rakuɓe a gefe rumgume da 'yar leda ta ina kallon su, haka
na ga madam ta shiga jirgi da mijinta baƙuwarta ma ta shiga, ya saura daga ni sai matar nan. Ai
tsayawa na yi na ce yau zan ga ikon Allah da gaske ne matar nan so take lallai sai ta sayar da
ni, zaman 'yan bori na yi tare da kurma ihu ina faÉ—in. "Wayyo Allah Innarmu! Wayyo na shiga
tara na lalace... "Subhanallah! Ƙalau kike kuwa 'yar nan?" Wannan babbar matar ta faɗa tare da
É—ago ne. "Wayyo ni ku bar ni, ni wurin Innarmu zan tafi ni a kaini gidanmu." Kururuwata ya sa
security suka nufo wurin suna tambayar ba'asi, nan take sanar musu da babu komai. "Yarinya ki
nutsu babu wanda zai sayar da ke. Mu je jirgin zai ta shi." "Wallahi ba zan je ko'ina ba..." Jama'ar da ke wurin suka tsaya kallon ikon Allah, da ƙyar aka ja
ni zuwa cikin jirgi ina ihu ina fisgewa, duk na haÉ—a gumi da majina. Zaunar da ni ta yi a kujera ta
jikin window kafin ita ma ta zauna kusa da ni ta saka min makari, lokacin da jirgin zai ta shi na
kuma kurma ihun da ya sa mutanen toshe kunnuwansu ita kanta sai ta ta ce. "Kai ohooo!
Wacce irin yarinya ce ke da babu nutsuwa tattare da ke haka?" Ajiyan zuciya na dinga saukewa
ina jan sheshsheka. A haka barci ya yi awon gaba da ni, yaya B kuwa sai jinjina yarinta irin na
Zinariya take yi. Har jirginmu ya sauka a Egypt ina barcina sai da matar nan ta taɓa ni don ta
tashe ni nan ta ji jikina da zafi alamun zazzaɓi. Buɗe idanuwana da suka yi mini nauyi na yi da
ƙyar ina jin jikina na rawa saboda sanyi-sanyi. Motar da zai kai mu masauki ne ya zo ya kwashe
mu duka cikin motar kuwa ina kwance jikin matar nan don na lura duk ta fisu kirki so É—aya muka
haÉ—a ido da madam Salima shi ma ba wani kallon arziki ta yi mini ba. Hotel É—in da muka je a
É—akin matar da na ji suna kiranta da Aunty B, na zauna ita kuma madam tana tare da mijinta
baƙuwarta kuma ɗakinta daban. Ko abinci ban iya ci ba, ruwan zafi na sha nan na dinga kwara
amai, hankalin Aunty B ya tashi nan ta kira Salima ta shigo É—akin. "Ko dai yarinyar ta kwaso ciki
ne na zo ina yawo da ita?" Wannan mummunar kalmar ta yi mugun dukar zuciyata, duk da
ƙarancin shekaruna na san kalmar cikin shege mummunar kalma ce, kallonta na yi da jajayen
idanuna da suka rine dan bala’i na ce mata. "Ni ba 'yar iska ba ce." Salima ta ce. "In ke ba 'yar
iska ba ce amaye-amayen mene ne kike yi wa mutane? Ke ni ba za ki saka ni a masifa ba
akwai jirgin da zai juya wallahi zan saka ki mayar da ke inda kika fito." Aunty B ta ce. "Haba ya
isa Salima wacce irin magana kike faÉ—a haka? Yarinyar nan dai mai aikin ki ce, a gidan ki take
zaune ta yaya za ta yi ciki bayan kuna cikin gida É—aya?"
"Na sani ko tana biye-biye da dare?" Ni tun da uwata ta haife ni ba'a taɓa faɗa mini mummunar
kalma irin wanda madam Salima take yaɓa mini yanzu ba. "Ni ba 'yar iska ba ce wallahi, ni ba
'yar iska ba ce. Allah sai ya saka min... Ko rufe baki ban yi ba wani aman ya sake ƙwace min
salati da sallallami suka É—auka. "Kin gani ko Aunty B? Ni dai wallahi ba za a saka ni a uku ba,
gwara tun wuri ta koma inda ta fito." Ni dai tun da na miƙe da niyar barin ɗakin hajijiya ta ɗibe ni
ban sake sanin inda kaina yake ba sai farkawa na yi na ganni kwance gadon asibiti.
Littafin Zinariya na kuɗi ne, za ku tuntuɓi wannan Number ta WhatsApp domin mallakar naku.
₦500.
09079740079
Maman Faruk.
[30/11, 3:49 pm] à¼ºí µí°˜í µí°’í µí°‡ í µí°‰à¼»: *...ZINARIYA*
_Romantic_
®
AYSHA JB
Farin Jini Writer's Asso..
5&6
Yunƙurawa na yi da niyar tashi nan na ji ni shakaf, zaro idanuwa na yi da sauri ina ƙoƙarin
miƙewa da ƙarfi dan na ji wani abu mai ɗumi yana bin tsakanin cinyoyina. "Na shiga uku na! Me
zan gani? Wayyo Allah an yanka ni! Wayyo Innarmu an sayar miki da Zinariya." Ihu nake
kurmawa da iya ƙarfi na, dukkaninsu suka shigo ɗakin a rikice A'isha tana faɗin. "Ke dalla
rufewa mutane baki duk kin cika mana kunne... "An yanka mutum sannan a ce kar ya yi kuka?
Na rantse da Allah sai an dawo min da jinin jikina tare da naman da aka ɓantala a cinyata, na
rantse ba zan yarda da wannan muguntar da ake shirin yi mini ba." Na ƙarasa maganar ina
hararan su tare da murguÉ—a baki. "Iko sai lillahi, ke kuma Salima wacce aka É—auko miki kenan?
Allah shi kyauta." Cewar Aunty B, Salima da shigowarta kenan ta ce. "Ba naman cinya ba, kanki
za a cire mayya da idanuwa kamar na mujiya, yarinya duk ta ishi mutane, ni da na san haka
kike da hauka ina zan É—auke ki aiki? Ai wallahi ki sauko ki zo ki wuce dan daga nan za a mayar
da ke inda aka É—auko ki."
"Na rantse da Allah babu me ƙarfin halin da ya isa ya cire mini kai, kuma sai an biya ni kuɗin
albashina na wannan watan dan Innata ta ce ba a tura musu kuɗi ba. Ko a ba ni kud’ina ko
kuma wallahi na hana mutum sukuni." Tsaki ta yi tare da barin É—akin, Aunty B, ta ce. "Ke da'alla
bar shashancin nan, girma ne ya zo miki... "Girma? Wane irin girma ne bayan kuma wannan
girman da nake da shi? Ke ki kalleni ɓakutuwa na ciko ta ko'ina... Tagumi Aunty B ta yi tana
kallon Zinariya, ga abin dariya amma takaicin halinta ya hanata darawa. Hannun Zinariya ta
kama suka shiga toilet ta ba ta auduga tare da nuna mata yadda za ta yi, da yatsu biyu ta É—aga
audugar tana mishi kallon mamaki. "Eyye! Iko sai Rabbu! Wannan bala'in kuma daga ina? Ni ce
zan saka wannan a jikina kalan aje a mini satan kayan hanjina? O'o wallahi ba ni iya wa da
wannan abar." Riƙe da haɓa Aunty B ta ce. "In ba ki saka ba haka za ki yi ta yoyo... "Yo me ye a
ciki? Ba gwara jinin ya yoye ba da in tara da wannan abar a zo a yi mini warwason kayan hanji."
"Ke fa da kanki za ki yi floshing É—in shi idan kin gama.. "Fulo me? Eh lallai yadda za a ji daÉ—in
kwashe 'yan hanjin kenan." Da Aunty B, ta ga ji da shirmen Zinariya fita ta yi daga toilet É—in. "Ni
na rantse ba zan saka wannan abar ba." Ta ƙarasa maganar tare da yin wurgi da shi.
ÆŠankwalin kanta ta cire tare da rabawa biyu ta cusa É—aya tare da mayar da É—ayan kanta, tana
murguÉ—e-murguÉ—en baki ta fito. Ko da ta yi arba da abinci ba ta tsaya tambayar na waye ba ta
ɗauka ta fara ci, Aunty B, ta miƙo mata magani tana gamawa suka bar asibitin zuwa
masaukinsu. Da yamma suka É—unguma zuwa asibitin da za a yi wa Salima aiki inda likita ya yi
mata gwaje-gwaje tare da É—ora ta a kan maganin kafin nan da kwana biyar za a yi mata aiki. Ita
dai Zinariya an barta da yatsine-yatsine saboda warin asibitin ya ishe hancinta. Da lokacin sallar
magariba ta yi ta je ta yi za ta yi sallah, Aunty B ta ce. "Babu fa halin yin sallah 'yar nan."
Sheƙeƙe Zinariya ta kalleta tare da haɗa kai da wuya tana faɗin. “Kamar ya babu halin yin
sallah? Kafurta ni kike son yi?" Aunty B ta ce. "Ai ba maraba, duk wanda yake cikin wannan
yanayin bambancin shi da kafiri kaÉ—an ne... "Yanzu kina nufin na fita daga musulunci ko?"
"Shakka babu." Riƙe haɓa Zinariya ta yi tana faɗin. "Taɓɗijam! Lallai sai na yi shari'a da duk
wanda ya yanka min cinya." Zama ta yi shuru tare da rafka tagumi da hannuwa biyu tana
tunanin hanyar da za ta bi don ta koma gida, ita gaskiya ba za ta iya ci-gaba da zaman wannan
wurin da aka kawota ba. Tana zaune tana mita cikin ranta har ta fara barci a zaune, Aunty B ce
ta tashe ta ganin yadda take gyangyaÉ—i. Bayan kwana biyu ta samu tsarki a cewarta ba za ta
fara sallah ba sai ta yi wankan shiga musulunci, haka kuwa aka yi domin sai da ta yi wankan
kafin ta fara sallah. Yanzu ta tsiri fita farfajiyar hotel É—in ne don ta ce ba ta iya zaman wuri É—aya,
saboda baƙin hali irin na madan Salima haka take saka ta wanke musu toilet da gyaran ɗaki
bayan kuma akwai ma'aikatan da suke gyarawa, amma haka ta hana su ta ce ita tana da mai
aikinta.
"Dan baƙin hali a yi ta saka mutum aiki bayan ga su nan da ma'aikatan su, ko abinci ta ci sai dai
ta saka mutum ya zo ya kwashe kwanuka ya fito da shi." Zinariya ke magana tana tafiya har ta
fito wajen hotel ɗin, lokacin ƙarfe tara na dare ta tsaya gaban wani shago tare da harɗe
hannuwa tana kallon yanda mutane ke ta harkokinsu ba mai shiga sabgar wani.
Gefen shagon ta je ta tsaya tana kallon wuta mai launi da ke juyawa yana haskawa ilahirin
kayan shagon, tsawon minti uku tana nan tsaye ba ta ankare ba sai ji ta yi an fisgota da ƙarfi
tare da toshe mata baki aka tura ta cikin mota, mutsu-mutsu take yi tana ƙoƙarin ƙwacewa daga
riƙon da aka yi mata amma ina, ji ta yi an shaƙa mata abu a hanci wanda tun da ta shaƙa ba ta
sake sanin inda kanta yake ba sai bayan kwana uku da aka watsa mata ruwa masu sanyi ta
buÉ—e idanuwa a firgice da ihu, na tsinci kaina cikin wani É—aki mai girma da faÉ—in gaske. A
lokacin da na yi arba da yara tsarata da waÉ—anda ba su kaini ba cikin mummunar shiga hankali
na ya yi mugun tashi, ina kallon yanda ake yage kayan jikinsu ana duba halittar su, nan na ji
cikina ya sake ɗurar ruwa, "Shi kenan ta faru ta ƙare! Ta tabbata dai wannan matar sayar da ni
ta yi, wayyo Innata..." Gabaɗaya sai suka juyo suna kallona, matar da na ga tana duba ƙirjin
yaran na ga ta nufo inda nake tana É—aga hannu alamar me ya faru? Kafin ta fara magana da
harshen da ba zan iya cewa ga abin da na tsinta cikin maganganunta ba. Mannewa na yi jikin
bango yayin da jikina É—auki mugun kakkarwa.
"Innalillahi ina aka kawo ni? Ina ne nan?" Tambayar da nake ta yi kenan cikin ihu da hayagaga,
amma duk cikin waÉ—annan matan babu wacce ta yi zarrar ba ni amsar da nake son ji, ita tana
nan tana wasu yarukan da ban gane kansu ba, yayin da ni ma nake yaren da na fi ƙwarewa
akanta, ina kallon yanda ake yi wa yara 'yan ƙananu yara alluran da ban san ko na mene ne ba.
Ɗirka-ɗirkan mata ne guda biyar masu ji da ƙarfi suke finciko yara tare da danna musu allurori,
idan kuwa ka ƙi ba da haɗin kai da duka ake haɗawa, yau ni na ga bala’in da ban taɓa gani ba
tun da nake a rayuwata. Ina kallo da zaran an gama tsikara musu allura zubewa suke yi a ƙasa
suna ihu da birgima wanda daga ƙarshe sai su ɓingire da barci daga haka sai a ɗauki yaran a
fita da su zuwa wani ɗaki inda nan ne za a kula da su a dinga ba su cimar da zai ƙara musu
lafiya ya sake fitowa da halittar jikinsu. Cikin sati biyu, kafin a fita da su zuwa wani gida inda a
nan ne za a baje kolinsu kowa ya zaɓi wacce ranshi ya yi masa.
Cewar matashiyar da ke zaune a gefe na, cike da razani mai haÉ—e da É—umbin mamaki nake
kallonta sannan na matso kusa da ita ina faÉ—in. "Ke Bahaushiya ce?" Ture ni ta yi da hannunta
tare ta sunkuyar da kanta ƙasa tana faɗin. "Idan kina son kanki da lafiya karki yarda ki zo kusa
da 'yar'uwarki ko ki nuna jin ƙai da tausayinki gare ta." Idan kuwa aka fahimci mun san yaren
juna ko wata shaƙuwa ta fara shiga tsakaninmu shi ma wannan wani hukunci ne mai zaman
kansa. Dan haka za a wurga ki a ɗakin gardawan maza su yi miki wulaƙancin da sai kin kai
wata kina jinyar kanki, gwara ki ci gaba da yi musu yaren da kika iya kafin ki fahimci nasu
yaren." Shuru na yi ina juya wannan mugun lamarin cikin zuciyata. Sai da mata suka fita kafin ta
ɗago kai, nan na ƙare mata kallo, ita ma dai yarinya ce amma za ta kai 19 zuwa 20. Ga ta fara
tass kyakkyawar Bafulata, saɓanin ni da nake nan baƙa.
"Yau kwananki biyar kina cikin barcin da aka saka ki, ke kuwa wane ganganci ne ya kawo ki
wannan duniyar da take cike da zalunci haÉ—e da son zuciya? Kin san rashin imanin da ake
nunawa 'ya'ya mata kuwa musamman mu da muka fito daga Nigeria? Me ya kawo ki Japan har
da za ki faÉ—a harkan karuwanci... "Ya Subhanallah! Karuwanci? Ni da nake Egypt me ya kuma
nake yi a nan? Ni fa daga tsayawa a bakin shago na ji an toshe min baki tare da fisgoni ban
sake fahimtar komai ba sai yanzu da na buÉ—e idanuwana na tsince ni a nan."
Wani irin dariya ta yi tare da faÉ—in. "Sayar da ke fa aka yi, kamar yadda ake safara daga Nigeria
haka ke ma aka yi miki... "Ba shakka wannan muguwar matar za ta aikata kamar yanda ta
faÉ—a."
"Wace ce?"
"Madam Salima, matar da nake yi wa aiki, mun zo ne da sunan za ta karɓi magani ne ko za a
mata aiki ne ni ban sani ba, wato shi ne wannan matar za ta yi safarata zuwa nan, shi ne za ta
buga mini tambarin da har na mutu na bar wa dangina da zuri'ata mummunar tabon da ba zai
taɓa goguwa ba kenan? Wai mai ya sa imani ya yi wa mutane ƙaranci ne?"
"Ba ki da iyayen da za su tsaya miki ne?"
"Ni da nake 'yar talaka, daga dangin uwa har na uba, Innarmu ke É—awainiya da mu domin
babanmu ba ruwan shi da sauke nauyin iyali, Innarmu ke fita ta nemo mana abin da za mu ci a
haka ta saka mu makaranta mu huÉ—u, kin san hannu É—aya ba ya É—aukar jinka, dole dukanmu
karatun ya tsaya daga Firamare, yayuna mata kowa na neman kuÉ—i don a taru a ruwafa juna
asiri wannan dalilin ya sa ni ma na fara aiki fa duk don abin ya yi wa Innarmu sauƙi, Innarmu na
son mu, haka ma babanmu ba ya ƙaunar wani abu ya taɓa mu amma hakan fa ba shi zai sa ya
saya miki ko da takalmi ba ne idan sallah ta zo, duk ya bar É—awainiyar kan Innarmu. Ban san
halin da za