Chapter 3 Reading ZINARIYA ROMANTIC HAUSA NOVELS BY AYSHA JB.pdf Arewa Novels

ZINARIYA ROMANTIC HAUSA NOVELS BY AYSHA JB.pdf

Author :  Aisha JB Mrs Danshuwa Category :  My Hausa Novels

Chapter   3 / 14

6K to 9K   out of 40K words

su shiga ba idan suka fahimci ba na nan."

Numfasawa na yi kafin na ci gaba da faɗin. "Babanmu ba zai taɓa barin madam Salima ba
muddin ya ji labarin ta sayar da ni, domin kuwa za ta sha terere dan duk inda ya zauna sai ya yi

wannan batun."

Kallon matashiyar na yi jin ta tuntsure da dariya. "Ba fa zai iya shari'a da masu kuÉ—in nan ba,
ƙarshe ma za ta iya cewa ita ba ta ma san wata mai aiki ba ke dai ki yi addu'ar Allah ya fitar da
ke.



Littafin Zinariya na kuɗi ne akan ₦500. Za ku tuntuɓi wannan Number ta WhatsApp domin
mallakar naku.
09079740079



Maman Faruk.
[30/11, 3:49 pm] ༺�𝐘𝐒𝐇� 𝐉�༻: *...ZINARIYA*
Romantic�

®
AYSHA JB

Farin Jini Writer's Asso..

7&8

Gyara zama na yi ina kallonta sanan na ce. "To ke yaya sunanki? Me ya kawo ki nan? Su kuwa
waÉ—annan azzaluman babu hukumar da za ta dakatar da su ne ko ta kama su? Oh ni na shiga
uku, shi kenan ba zan sake ganin Innarmu da babanmu ba? Allah sarki yaya Fadila, Allah sarki
yaya Radiya shi kenan an É—auke muku 'yar auta... "Kina da abin dariya wallahi, bari na ba ki
labarin wannan ƙasar da ta yi ƙaurin suna. A Japan, ana fataucin mutane ne da nufin yin lalata
da bautar da su kamar bayi a ƙasar, Japan ƙasa ce ta asali, wadda ake yawan ziyarta, haka
kuma ƙasa ce da ake safarar 'yammata musamman masu ƙananan shekaru don mai da su
karuwai a yi lalata da su ba bisa son ran su ba.
'Yan ƙasar Japan, musamman mata da ake yin safarar su ta hanyar mai da su karuwai da ƙarfi
da yaji a cikin Japan da kuma zuwa wasu ƙananan ƙasashen waje. Ana safarar waɗanda suke
daga ƙasashen waje zuwa cikin ƙasar japan. Yara kanana, da mutanen da suka fito daga dangi
marasa ƙarfi wato waɗanda talauci ya musu katutu sun fi fuskantar matsalar fatauci. Ana
yaudarar waÉ—anda aka yi fataucinsu da manufar kasuwanci, ana yi musu barazana da tilasta
musu yin karuwanci. Masu safarar mutane
waɗanda suka kamasu suna ƙwace fasfo ɗinsu da takardun banki da duk wasu muhimman
takardun da suka shafe su, ana yawan É—aura musu basussuka don su biya su fanshi kansu
daga halin da suke ciki. Ana raunata su idan suka ƙi amincewa, kina kallon yanda ake dukan
waÉ—annan yaran, to haka suma manyan ake musu, sannan ana yi musu barazanar kisa kuma

da yawa daga cikin waÉ—anda aka yi safarar su suna kamuwa da cututtukan da ake É—auka ta
hanyar jima'i, da fyaɗe, kuma suna rayuwa a cikin yanayi mara kyau rayuwar ƙunci da
wahalhalu. Wasu idan suka samu ceto ma'ana idan suka tsira suka gudu suna fuskantar wariya,
daga jama'a a dinga ƙyamar su. A irin wannan yanayin baƙinciki kan sa har suna yunƙurin
kashe kansu. Akan É—auke su hotuna a lokacin da suke tsirara sai a watsa hotuna a yanar gizo
don muzanta su". Riƙe haɓa Zinariya ta yi tana faɗin. "Bala'i! Lallai ana shege a duniya, abin da
muke ji a labarai yau dai gamu cikin yanayin, to su kuma masu fataucin daga ina suke?"

" Masu fataucin maza da mata a Japan sun fito ne daga wurare dabn-daban. Masu safarar
mutane galibin su membobi ne na ƙungiyoyin masu aikata miyagun laifuka, suna haɗuwa ne su
cure waje ɗaya don samun sauƙi wajen aikata miyagun Laifuka. suna da alaƙa da ƙungiyoyi da
dama, suna da ɗaurin gidi daga fannin manya 'yan ƙasan, domin suna ba su kaso mai tsoka
daga abin da suke samu. Wannan dalilin ya sa suke gudanar da harkokinsu hankali kwance ba
su da haufin komai domin babu wanda zai yi musu shamaki ko karan-tsaye bisa kasuwancinsu.
Hatta gwamnatin ƙasar muryarta ba ta isa ta yi amo ba... "To amma ke mai ya fito da ke? Ki ba
ni labarin ki, yaya sunanki?"

"Hinduu, sanin labari na kuma ba zai ƙare ki da komai ba. Don gudu na yi daga gida na shigo
duniya saboda za a tilasta ni yin rayuwa da wanda ba shi ne zaɓin zuciyata ba, ba nan na fara
zama ba. Sai da na yi rayuwa a Thailand kafin ni ma aka sayo ni zuwa nan." Jinjina lamarin
Zinariya ta yi cikin zuciyarta kana ta ce. "Kuma kema an yi miki allurar ne?"
"Ba ki ji na ce miki sai da na fara rayuwa a Thailand kafin na zo nan ba? Ai tun a can an riga da
an yi mini komai, har ciki na yi aka cire, daga ƙarshe aka yi mini tsarin iyali.. "Aka cire ciki
kuma? Ta yaya? Mene ne kuma tsarin iyali?" Zinariya ta faÉ—a cike da zallar yarinta. "Ina nufin ni
na yi mu'amula da maza ba so É—aya ba ba so biyu ba har na samu ciki na haihuwa, sai aka
zubar da shi, aka kuma yi mini allurar da zai hanani É—aukar wani cikin." Shuru Zinariya ta yi
domin duk ba ta fahimci abin da Hindu ke magana akai ba. "Aka yi miki ciki haka na haihuwar
yarinya, kuma se aka zubar da cikin?" Ta faÉ—a tana dafe cikinta tare da É—ago hannu tana
kwatanta yadda ciki yake idan ya yi girma ya fito. "Oh ni Zinariya ko yaya ake yin cikin oho"
Kallon Zinariya Hinduu ta yi sosai domin ta lura har yanzu ba ta ma gane kan maganar da take
mata ba. "Ba ki san yanda mata da miji ke kwanciyar aure ba?" Girgiza kai Zinariya ta yi alamar
a'a, "Kin je islamiyya kuwa?" Zinariya ta ce. "Wannan ai tambayar raini hankali ce, ni tun ina
shekara sha biyu na yi saukar allo." Dariya Hindu ta yi sannan ta ce mata. "Okay."

Zinariya ta ce. "Yawwa na tuna."

Hinduu ta ce mata. "Me kika tuna?" Zinariya ta ce. "Kin ce an miki allura a can Telan yake ko
ina? Kuma nan É—in ma sai an yi miki wani allura?"

"Duk cikin maganar iya abin da kanki ya iya riƙewa kenan?" Gyaɗa mata kai na yi, "Ai nan za su
duba kafin su yi min. Idan suka fahimci ni ba cikakkiyar budurwa ba ce, ma'ana na yi sex da
wani na miji, za su kaini É—akin 'yanci ne kawai a yi mini gyaran jiki sai su fita da ni zuwa inda za

a zo a É—auke ni... "Me ye six kuma? Idan aka É—auke ki ina za a kaiki?"

Hinduu ta fahimci Zinariya ba ta san ma komai ba a harkar, wannan dalilin ya sa ta yi shuru
zuciyarta cike da tausayin Zinariya, dan ta san muddin ta shiga hannun mazan garin Japan fasa
ta za su yi, ba su iya bin mace da sauƙi ba.

"Kin yi shuru...

"Shh! Yanzu za a kawo mana abinci." Aikuwa tana rufe baki sai ga shi an buɗe ƙofar tare da
shigowa da abinci, aka ajiye ma kowa na shi. Ga dai abinci lafiyayye amma ko burge ni bai yi
ba. "Ki dai ci abinci, dan in kika ƙi ci haka za ki zauna da yunwa." Cewar Hinduu, kaɗan na
tsakuri abincin na ture sauran.
Na so mu ci gaba da hira amma sai Hinduu ta ce barci za ta yi, haka na ƙyale ta, washegari ma
haka wannan gardawan matan suka zo suka É—ibi yara kusan goma dan gaskiya muna da yawa.
Ranar da na cika sati cikin yaran da aka É—iba har da ni, lokacin da aka zo É—aukar sunana
zuciyata ta tsinke, hankalina ya yi mummunar tashi domin na tsani yanda suke yage rigar
mutum suna duba ƙirjinshi, cike da tsoron na kalli Hindu kafin a zo ɗauka na murya na rawa na
ce. "Na shiga uku ina za a kaini?"

"Za ki shaƙi iskar 'yanci mana, ke kam ki kwantar da hankali za mu haɗe ne in sha Allahu da
zarar na fito." Daga haka Hinduu ta É—auke kai ba ta sake min magana ba. Da suka zo É—aukana
na fara turjewa aikuwa matar ta É—aga hannu da niyyar kwaÉ—a mini mari, nan na tsura mata
idanuwa tare da tamke fuskata na tsuke baki ina jiran saukar mari, amma sai na ga saɓanin
haka, cikin zuciyata na ce wallahi da kin mare ni kin ga yanda ake hauka. Yage himar É—in jikina
aka yi wanda tun da na zo da shi nake nanuƙe a jikina, ko wanka na yi ba na yarda na cire shi.
Ina ji ina gani aka barke rigar jikina, nan suka ga ƙirjin sulum ba komai sai ɗan kan da ya fara
tasowa. Kallon juna suka yi suna yare ga dukkan alamu sun yi mamakin ganin babu komai a
ƙirjin. Haka suka danna mini allura har guda biyu, na daɗe ina jijjiga tare da jin gaɓɓai na suna
sakewa kamar wanda ake kwance mini su kafin wani wani masifaffen barci ya yi awon gaba da
ni. Sai tsakiyar dare sosai na farka nan na tsinci kaina cikin wani ƙayataccen ɗaki inda na ga
'yammata bila adadin suna ta harkokinsu, ina ta kallonsu ganin yadda suke É—aure da É—an
ƙyallen ƙirjinsu yayin da suke sanye da wani ɗan mitsitsin siketi, tagumi na yi ina kallon galewar
rayuwa dan wallahi ko gama saukowa cinyarsu siketin ba ta yi ba. Wani irin lafiyayyen abinci
aka kawo min wanda tun da nake ban taɓa ganin irin shi ba, nutsuwa na yi na ci sosai ina karon
'yammatan ɗakin, wata mata ce ta zo ta riƙe hannuna zuwa toilet nan aka shiga wanke ni ba ji
ba gani, kusan sati biyu ana min wani irin masifaffen gyaran jiki tare da wanke ni da ruwan
turaruka. Gashi na da yake tufke aka warware shi, nan shi ma aka gyara min shi duk da ba wani
yawa ne da shi ba amma yana da tsayi dan ya sauko har kafaɗata. Ƙirjina kuwa saboda fitinar
shi da aka yi da shafe-shafen mayuka da magungunan dole ya fara fitowa har kana iya ganin
shi ta cikin riga saɓanin da ba a iya ganin komai.

Ni kaina ƙaunar kaina nake yi wallahi ganin yanda na yi masifar kyau, jikina har wani sulɓi yake

yi, sai kallon kaina nake ina sake latsa fatata da ta murje ta yi fresh sai ka ce baƙar baturiya. (Ni
kuwa na ce su Zinariya an samu na yi, sai a yi ta latsa jiki) Da dare ina zaune bayan na gama
cin abinci na É—auki wani riga mai É—an mutunci daga cikin kayan da aka ba ni na sakawa ina
ƙoƙarin sakawa sai ga matar da take yi mini gyaran jiki ta shigo ta karɓe rigar tare da miƙo min
wasu kaya, buÉ—e kayan na yi na kalla tare da kallonta. "Me ye wannan? Me zan yi da ita?" Da ta
fahimci abin da nake faɗa sai ta karɓi kayan tana gwada mini yanda zan saka. Innalillahi na ce
ganin irin mugun kayan da ke jikina wanda ba shi da maraba da gidan sauro. Tsirara ziryan,
dafe ƙirji na yi tare da kallon madubi ina faɗin. "Na shiga uku ni Zinariya, yau kuma haka na
zama?" Jan hannuna matar ta yi zuwa waje inda aka saka ni cikin wata mota.
****
Egypt.
Neman duniyar nan a yi wa Zinariya amma ina, babu ita babu labarinta. Hankalin Salima ya
tashi sosai amma da ta tuna Zinariyar ba zaman Egypt É—in take so ba sai ta lauya zancen tare
da faÉ—in dama can ba son zaman take yi ba shi ya sa ta gudu. Da wannan kalaman ta share
batun Zinariya. Aunty B kuwa cewa ta yi. "Amma Salima sai yau na sake tabbatar da ba ki da
hankali da imani, ta yaya 'yar mutane za ta ɓata sannan ki zauna hankalin ki kwance? Me za ki
cewa iyayenta?" Salima ta ce. "Me kuwa zan ce musu wanda ya wuce na faÉ—a musu 'yar su
guduwa ta yi, ni na ɓatar da ita? Dan Allah Aunty B ki ƙyale ni da wannan maganar." Mamaki ya
cika Aunty B ta kasa yin wata magana, daga ƙarshe haka suka dawo bayan gama aikin da za a
yi wa Salima.

Dawowarta ba jimawa ta sa aka kawo mata 'yar aiki, amma ko wata ba a rufe ba ta kore ta
saboda rashin kamun kan yarinyar, a haka ta dinga canja masu aiki ta kasa samun ƙwaƙƙwarar
da za ta mata aiki ba tare da sun samu saɓani ba. Wani lokaci ta kan tuna Zinariya, duk da tana
shiririta amma a hakan take mata aikin da ranta yake so, sai da babu ita take jin takaici, da
zarar kuma ta tuna irin rashin kunyar da ta dinga yi musu sai ta ji gabaÉ—aya haushinta ya rufe
ta, take kuma take kore tunanin Zinariyar daga zuciyarta.
****
Uwaisu Sadi, wanda ake yi wa laƙabi da Malam Uwaisu haifaffen garin alƙaleri ne da ke jihar
Bauchi, wanda tun fitowarshi cin rani bai sake waiwayar gida ba, yana da ilimin addini da na
zamani wannan dalilin ya sa ake kiran shi malam Uwaisu kasancewar wani lokaci har bugun
ƙasa yake yi kafin ya yi aure, bayan auren shi da Mardiyya sai ya daina da ya fahimci ba ta son
sana'ar. Nan ya shiga 'yan buge-buge yana samo musu abin da za su rufawa juna asiri
kasancewar ita ma iyayenta ba masu ƙarfi ba ne, amma duk da haka suna tallafa mata
musamman da suka lura da ba wani aiki Uwaisu yake yi ba. Ita ma ba ta zauna haka ba, inda
take sai da kayan miya a gida, a haka suka fara tara iyali inda hidimar ta fara yin yawa wanda
daga ƙarshe Uwaisu ya zare hannu ya barta da ɗawainiyar yaran. Tsakanin Fadila da Radiya
tazarar shekara guda. Fadila shekararta 19, Radiya 18, sai mai bi mata Zinariya mai shekara
16, kafin Ahmad wanda suke kira Madu shi kuwa shekarar shi 12. Yaran sun taso da farin jinin
jama'a.
Zinariya da Madu sune tsagerun gidan, hatta 'yan unguwa ba su bar su ba, ga shaƙiyanci da
zolaya domin kuwa in suka saka mutum a gaba da zolaya haka za su mayar da shi mahaukaci,
ga shegen kafiya da naci idan ka taɓo su. Malam Uwaisu na ƙaunar Zinariya sosai dan wani

lokacin yakan saya mata abu ba tare da ya saya wa 'yan'uwanta ba. Wannan dalilin ya sa ba su
jituwa da Madu, dan kishi yake muddin Baban su ya yi wa Zinariya abu bai yi mishi ba. Cikin
haka watarana Zinariya ta ce lallai za ta fara aiki tun da su Radiya su ma suna gidan aiki, amma
sai Innar su taƙi, tana ganin Zinariya ta yi ƙankanta da aiki, da ta dage lallai sai tana so ne ya sa
Innar su amincewa.

Ajiye wayar Inna ta yi tare da ƙwalawa Madu kira. "Je ka duba in babanku ya dawo ku taho
tare." Bai kai ga ƙarasa fita ba suka ci karo da juna. "Yawwa baba da ma Innarmu ce take
neman ka."

"Ya labarin Zinariya? Ka je gidan ka duba ta?" Hannu Malam Uwaisu ya saka cikin aljihun rigar
da ke jikinshi tare da tatare rigar ya zauna yana faÉ—in. "Ke kin ji maganar banzar da matar ta
turo mai gadi ya faÉ—a min ne a lokacin da na je neman Zinariya?"

"Me ta ce?"

"Cewa ta yi wai wacce Zinariya ake nema? Shi ne na ce kamar yaya? Wai ai tun watanni uku da
suka wuce Zinariya ta gudu daga gidan.... Zubur Inna ta miƙe dafe da kirji tana sallalami.


Littafin Zinariya na kuɗi ne akan ₦500. Za ku tuntuɓi wannan Number ta WhatsApp.
09079740079




Maman Faruk.
[30/11, 3:49 pm] ༺�𝐘𝐒𝐇� 𝐉�༻: *_ZINARIYA...�_*

Farin Jini Writer's Asso..

*For you Ishaq Nasir Abdallah Nasrulla 💔�*

9&10

"Ai ki kwantar da hankalinki Mardiyya ƙariyar iskanci suke ji, ba taƙamar su dukiya ba? Na san
matakin da zan É—auka dan wallahi sai sun fito min da 'yata, in ma sun je sun sayar da ita ne duk
za mu sani amma wallahi Zinariya sai ta fito ba za ta salwanta ba, ai mai kamfanin S.S ne uban
gidan nata." Zama Innarmu ta yi tana yarfe hannuwa tare da fashewa da kuka tana faÉ—in.
"Wayyo Zinariya, wayyo 'yata, Allah ka dawo min da ita lafiya, Allah ka tsare min 'yata." Fita
malam Uwaisu ya yi yana kaÉ—e babbar rigar shi bai zarce ko'ina ba sai police station, bai tsaya
ina nan ba ya nemi masu watsa labarai nan aka dinga É—aukar shi yana jawabin abin da ya faru,
take gari ya ɗauka lungu da saƙo zancen ɓatar Zinariya ya baza ko'ina, nan 'yan jaridu suka

buga labarai tare da ɗora hoton Zinariya da S.S. Inda ake zargin shi da ɓatan mai aikin gidan
shi. Iyayen Zinariya na cikin damuwa da ƙunci musamman da hukuma suka wanke S.S daga
zargin da ake yi mishi saboda rashin ƙwaƙƙwarar hujja dan ya ce bai san batun ɓatan wata 'yar
aiki ba. *** **
Zare gilashin idanunshi ya yi tare da miƙewa da laptop a hannunshi ya nufi ɗakinta daidai ta fito
daga wanka tana ɗaure da towel ta ji an turo ƙofar ɗakinta. Waigowa ta yi da murmushi tana
faɗin. "Saifu yau kai ne a ɗakina... Shuru ta yi ba tare da ta ƙarasa sauran maganarta ba ganin
ya nufi kan bed ɗinta tare da ajiye laptop ɗin ya harɗe hannuwa a ƙirji yana binta da kallo
fuskarshi a haÉ—e. "Wani irin shashanci ne wannan Salima? Akan wani dalili ne za a dinga yaÉ—a
hotona a social media ana faÉ—an wasu maganganu? Girma kike amma kullum cikin jawo min
magana kike, kullum case É—inki da masu aiki, abin bai tsaya ina nan ba har ya zo kaina yana
shirin shafan kasuwanci ne? Ita yarinyar da ake maganar na ɓatar

3 / 14