Author : Saadatu Abdullahi Category : New Hausa Novels 2026
mai haline yana da tarin dukiya sosai shiyasa ita bata aiki sai kawai ta fada harkar kasuwanci, tana fita dubai tana kawo kaya sosai.sai Rabi'atu wadda itama tayi aure amma tana aiki da ma'ikatar lfy ta kano.gaba dayansu kowa yana da rufin asiri daidai gwargwado sbd Alh moda koda yake da kudi bai yarda ya bar yaranshi ba babu ilimin addini dana zamani ba.bayan rasuwar maifinsu ne Alh mado Alh bashir ya koma katsina da zama a inada ya auri diyar aminin babansu Alh garba mai dala.wadda dama suna soyayya dashi wadda hakan yasa iyayensu sukayi masu alkawarin auren junan su kuma Allah ya kaddara.shikuma Alh bashir dalilin dayasa ya koma katsina da zama sbd duk harkokin mahaifin shi suna can to koda y rasu sai ya tattara gaba daya ya koma da zama.yaso ya tafi da mahaifiyasu amma ta nuna mashi tafi son zamanta anan kankiya cikin danginta haka nan ya hakura badon ranshi yaso ba.amma duk satin dunya yana zuwa ya kwana biyu wurin mahaifiyarsa saidai idan baya kasar.kuma yana zuwa da matarsa hjy khadija wadda mace ce mai karamci da nuna kulawa ga yan uwan mijinta shiyasa ta shiga ran kowa na family dinsu Alh bashir .ita kanta hjy hauwa'u tana kaunar sirikar tata sosai bata son taji ance ga laifinta.shikuma Alh bashir ganin yanda take kula da mahaifiyarsa da yan uwansa yasa yake kara ganin darajarta da kimarta.
Kuma yake kyautata mata, itama haka zamansu yake cikin mutunci da girmama juna.to amma duk da haka basa shiri da hjy mariya sbd ita gsky halinta ya sha banban yan uwanta, ita mace ce wadda tasa duniya gaba bata tunanin komi sai son zuciya, sbd tana fita kasashe tana haduwa da kawaye sun zugata tana ganin kowa ma bai isa ba.sbd haka ne basa shiri da Alh bashir yayanta shikam duk harkar wani shashanci baya cikinta.kuma shi mijin nata sbd son dayake yi mata baya iya magana duk yanda take so to haka za ayi Allah ya kyauta.itama mijinta dan katsina ne nan suke zaune a le out.shima Alh bello yana katsina tare da iyalinsa, sai hjy rabi'atu dake aure a kano ita mijinta dan kano ne a nan kundila suke da zama anan take aikinta a ma'katar lfy dake jaha.
Allah ya Albarkaci Alh bashir da haihuwar yara uku aunty zainab ce babba sai yusuf sai kuma Nafisa wadda itace auta.rayuwar farin ciki da kaunar junan su haka rayuwa take tafiya.hjy khadija su uku ne wurin mahaifinsu Alh suleman shine babba sai ita umma sai kuma babana wanda shine kaninta Alh mansir shine mahaifina Allah yayi masa rasuwa ne a sakamakon hadarin mota.daga kaduna zuwa katsina, Allah ya gafarta ma iyayenmu yasa Aljannace makoma Ameen ya hayyu ya qayyum.
To lkcn mahaifina shi yana kaduna ne zaune tunda can yake aiki tare da mahaifiyata wadda dama it yar kaduna ce anan ya aureta alkcn daya rasu an haife ni amma shekareta daya lkcn.sbd haka iyakar zaman danayi da mahaifiyata kenan ana yayeni hjy khadija tace lallai sai an badani haka dai mamana tayi kawai ci sbd karamcin yayar mijin nata ta hakura ta bada ni haka na tashi ina ganin umma itace mahaifiyata tunda koda wasa bansan umma da Abba ba basune iyayena ba tunda ko yaransu ban taba ji abakinsu ba kowa yana sona.nasan dai akwai mamin kaduna tunda haka naji suna ce ma mamana.kuma sai inji suna ce mata mamin yusuf naga kuma yawancin zaman shi acan wurinta ne .na tmby umma sai tace mani ai ita mami itace mamanshi dana dameta da tmby sai tace tashi kibani wuri harga Allah ban kawo komi araina ba.mami tayi aure ta auri wani aminin dad dina wanda shima matarsa wurin haihuwa ta rasu shima mutumin kirkine .amma mami da kyar ta amince da auren shi dayake kuma Allah ya kaddara haka ta auri Alh isma'il shima dan zaria ne amma enginer ne yanzu haka yana Abuja can yake aiki amma nan yabar mami a kaduna sbd tace tafi son zaman kata anan tare da yaranta saidai yarinka zuwa weekend ko kuma wani lkc suje su danyi hutu su dawo
Diyarshi wadda matarshi tabari itace babba wurin mami sai wadanda ta haifa guda uku yaran shi hudu amma baka cewa mami ta haifi ummi ba sai Abdul da khalid da halimatu sune yaran mami
Hjy mariya yaranta biyu jamilace babba sai kanwarta nabila sakamakon tsada haihuwa datayi wai ita bata son ta tara yara kuma su tsaida mata harkokinta nabila ba halinsu daya ba da jamila shiyasa gaba daya basa shiri shiyasa koda yaushe tana gidan umma muna tare ita kuma hjy mariya ta tsani hakan shiyasa ko hidima akaje ta rinka yima umma habaici kenan ita kuma bata kulata.
Masha Allah ku biyoni yawan comment yawan typing π€ͺπ€ͺπ€ͺ takuce sa'ar mataaaaπ€
TUN INA KARAMA ππΉπΉπΉππππ
By sa'adatu Bello saadatu99@gmail.com!
Page 8
...........yaya yusuf da umar cousins ne sbd umar shine babba wurin Alh bello kanin Alh bashir baban yusuf, tare suka taso tun suna yara babu abunda ke raba su sai in yazama dole.ko karatunsu tare sukayi shi india couse dinsu ne ba daya ba shi yusuf permacy ya karanta shi kuma umar Account ne.duk da haka dasuka dawo gida nigeria suna tare acompany daya wanda dama na su ne company babu abunda akeyi cikin shi sai hidimar magunguna sakamakon dama abunda yusuf ya karanta kenan.kuma suna samun kwangila daga gwamnati sbd babu kasar da basu kawo magani kuma masu inganci basu yarda su hada hulda da kasashen da suke yaudarar kasarsu sbd kishin kasa.
Jamila tare suka taso don itama dakadan suka girmeta ko a skul shekara daya ce tsakaninsu da ita itama india tayi karatu tare da su yusuf amma ita kwararra likita ce yanzu haka tana cikin likitocin da ake ji dasu a cikin jihar katsina tana aiki ne da fedaral medical center dake cikin garin katsina.jamila tana son yusuf sosai arayuwarta sbd irin mazan da mace zatayi alfahari dasune.kuma tanada wani hali duk abunda take so to bata boyewa ko jin kunyar nuna mashi kuma tana da son kanta da yawa da son zuciya kamar yadda ta gani wurin uwarta.nidai na taso hannun ummatah da Abbanah wanda su nake ma kallon iyayena da suka haifeni.sbd karamci irin na dangin mamana tunda ko su ban taba jin sunce wani abu ba na dangane dani kawai dai abunda nafara fahimta ina dan kama da mamin kaduna amma bana sawa araina akwai wani abu kuma ina jin ina son matar sosai araina amma tunani nako don tana mahai fiyar yaya yusuf ne.na tashi cikin so da soyayyar yan uwana su aunty zainab.
Haka nayi krtuna primary da secondary anan katsina lkcn dana gama secondary ne ina da shekara 17 kuma ashekarar akayi mani aure da yaya yusuf wanda dama wai jirana kawai yakeyi sbd duk matan dake bibiyarsa baya ma kula su ciki ko harda jamila.bai so maganar aurena yanzu ba amma hakan bata samu ba.
Sbda yaso ace na fara jami'a kwatsam sai gashi ya canza shawara sbd wani dalili nashi.hakan yasa aka gaggauta yin auren mu.
Bana manta wannan ranar da akayi bikin wata cousing dinmu Aisha wanda aranar ne ne komi ya canza a sakamakon wani hoto da da jamila ta hada tare da wani saurayi ta turo ma yusuf shi kuma lkcn yana gida.abunda ya faru, mun shirya nida nabila kanwar jamila zamuje wurin dinner to dama gsky itace kawata sai na nafisa autarsu yusuf tunda duk kanmu daya kuma mun shaku da juna sosai, to nafisa tana wurin aunty zainab a Abuja.mun gama shiryawa muka fito daga dakina muka samu ummah tana zaune tana kallon tashar sunnah tv tana ganinmu ta fadada murmushinta cikin kulawa tace masha Allah kunyi kyau yan matana cikin jin kunya muka rufe fuska tare da isowa kusa da ita muka zauna gefen ta muka sata tsakiya.cikin shagwaba wadda tariga ta zame mani jiki nace ummatah ina yayana?tare da kallon kofar da zata sadaka da sashin shi cikin kulawa tace yaje masallaci amma naga alamar kamar ba zai fita ba, yanzu dai bari in sanar ma Adamu driver ya kaiku tana magana tana kallon wayarta dake caji kafin tayi ta kara mgn na mike na dauko wayar na mika mata.bugu daya ya dauka ta sheda masa abunda zaiyi ya amsa da to hajiya mikewa mukayi tare da yi mata sallama tace kada mu wuce karfe tara komi mukeyi insha Allahu muka ce tare da fita waje muna fita muka ga Adamu yana kokarin fiddo wata katuwar jeep prado blue sai shaning takeyi har inda muka tsaya ya iso ya bude mana muka shiga baya muka zauna tare da gashe shi ya amsa mana cikin walwala baba mai gadi ya bude mana muka fita sai liyafa place inda akeyin dinner .
Fitarmu kenan shikum yusuf ya fito daga masallacin kofar gidanmu yana fitowa ya hangi motar gidanmu ta fita daga get cikin mamaki yace to wa yafita yanzu a wannan motar?cikin hanzari ya shiga cikin get din gidan tare da sallam baba mai gadi ya amsa kafin yace komi yusuf yace baba waya fita da mota yanzu cikin mutunci yace ai yallabai Adamu ne hjy tace yaje ya kaisu autarta wurin biki da yake duk ma aikatan gidan haka suke kira na da autar hjy.ok kawai yace ya shige cikin gidan tare da sallama umma ta dago kai tare da amsa masa sallamar babu walwala a fuskarsa ya zauna kusa da umma yace umma saida kika bar yaran nan suka tafi wurin dinner nan ko?"eh tace ai banyi tunanin zasu dade ba kasan hawwa ma da ba son hayaniya ne da ita ba.ai umma da kin kinkirani sbd darene kuma kin san jamila zataje tana iya yima su hauka tunda sakarai ce cikin damuwa ya karashe mgnar."tace ba komi insha Allahu lfy zasu dawo amma duk da haka shirya ka dawo da su saikace ma Adamu ya taho gida "ok yace tare da mikewa zuwa dakin sa ya canza kaya tunda dama kafin yaje masallaci yayi wanka.yana shiga ya shirya cikin kananan kaya wanda sun karbi jikinsa yayi kyau sosai yana shiri ya na kallon agogon dake manne a dakin.ya dauko perfumes yana fesawa wayar shi tayi kara alamar text ya shigo da kuma hasken da wayar ta karayi.kamar bazai duba ba kuma kawai sai yaji yana son ya duba koda ya dauki wayar sai yaga ashe sako ma na whatsapp ne kuma sunan jamila ne ke yawo akan sakon kamar zai aje wayar sai kuma yayi tsaki mtss ya bude sakon
Innalillahi wa'innailaihin raju'un, haka kawai yake maimaitawa.sakamakon wasu hotona da jamila ta tura mashi na hawwa tare da wani saurayi kamar suna mgn ita kuma hawwa tana dariya wanda ita bama tasan saurayin yana kusa da ita haka ba.
Jikin shi har rawa yakeyi yasa hannu ya dauki key din motar shi a sukwane ya fiti falo babu umma hakan ya bashi damar fita kawai inda yayi parking ya nufa ya shiga motar a rude sbd tsabar kishi.baba mai gadi ya bude mashi get tare da daga masa hannu adawo lfy yace.haba ina ko ji bayayi haka ya fita cikin tashin hankaki da rikicewa hoton hawwa kawai yake gani tana yima saurayin nan dariya.hawwa kina sona kuwa?me nayi maki?
Masha Allah ku biyoni yawan comment yawan typing π€ͺπ€ͺπ€ͺ taku ce sa'ar mataaaa π€
TUN INA KARAMAππΉπΉπΉππππ
By sa'adatu Bello saadatu99@gmail.com!
Page 10
..........cikin sauri na dauki wayar nice zahiri ba karya amma ban san wanene wanda yake kusa dani ba har ina dariya nasan dai fatima kawata nake magana da ita a lkcn amma ya akayi wannan mutumin kusa dani haka.na shiga uku!an bata ambata wallahi yaya ban san shiba asalima nasan na tsaya wurin nan amma bada shi nake maganaba amma ban sanshi ba yaya cikin kuka na karashe maganata tare da jin wani zafi a zuciyata "tunda nafara magana yake kallona yaso ya gasgata maganata amma kishi ya hana yaga hakan tare dani." Ok bani wayata na mika mashi zan kara magana ya daga mani hannu sbd gaba daya kukan da nakeyi har cikin ranshi yake jin shi.kamar bashi yayi maganar ba naji yace hawwa aure kike so?cikin sauri na girgiza kai alamar a'a to ko ba kiso yazama dole sbd bazan iya wadannan abubuwan"walhi yaya banida saurayi bare ince ina son aure to wazan aura?
Bayan nasan bani da kowa kuma karatu nake buri.na cigaba da cewa duk wanda yayi mani sharri bazan yafe masa ba tunda ban aikataba, "batare daya kalleni ba ya tada mota tare da cewa ki cigaba da shirye shiryen aurenki nan da lkc kankani insha Allahu.wayyo Allah !nace shikan shi saida ya tsorata afusace yace kika kara yi mani ihu amota sai na fasa baki.nasa hannu na toshe bakina, ya figi mota muka karasa cikin unguwarmu.muna isa gida cikin get din gidanmu, tun kafin ya gama parking na balle marfin mota na shiga gida da gudu tare sakin kuka mai karfi ummace tare da nabila suna maganar to ina muka tsaya ba iso ba
Ba " nabila tace ma ummah Adamu yace rai bace yaya yazo cikin mamaki tace to koma menene ai sai ya dawo mani da ita gida ko.bata rufe baki ba na fado falon da kuga gaba daya juyo sukayi cikin mamaki suna tmbyta me yafaru?cikin kuka nace umma kada kibari yaya ya fadi Abbanah ina son aure na hade hannuwa na alamar rokonta.cikin rashin fahimtar maganata ta zaunar dani kan kujera nabila kuma ta zauna gefena tare da rike hannuna "ummah tace wai meke faruwa?waye baki so kuma?" Yusuf ne ya shigo tare da sallama amma fuskar nan tashi babu annuri sai ji sukayi yace dama kin daina kuka ki fara shirin aurenki."cikin daga murya umma tace wace by irin mgn kakeyi yusuf?me ya faru ne?"umma ki tmby ta abunda tayi dama ni nace abarta ta fara jami'a to yanzu ra'ayina ya canza zan jira dawowar Abbah tunda ya fara mgn umma ke kallonsa tana nazarin irin soyayyar hawwa tsantsa a idon shi da kishin ta cikin kauda kai umma tace baka isa ba yusuf babu wanda zai takurata da mgnr aure"amma umma ya kamata ki saurareni mana"cikin tsawa tace banda lkcn saurarenka zai kara mgn ta daga masa hannu tare da cewa ya isa haka bai kara mgn ba ya nufi sashensa yana jin wani zafi a zuciyarsa ta juyo tace na nabila tashi ku shiga daki ku kwanta.
Masha Allah don Allah frnds kuyi hkr da typing din nan ba yawa sakama kon ina cikin hidamar biki ne next page zan biya bashi.ku biyoni π€ͺπ€ͺπ€ͺ taku ce sa'ar mataaaaaπ€
TUN INA KARAMA ππΉπΉπΉππππ
By sa'adatu Bello saadatu99@gmail.com!
Page 11
..........( koda ya wuce daki yana shiga ya cire kayan jikin shi ya wuce toleit yayi wanka, wanda ya zame mashi jiki duk idan zai kwanta sai yayi wanka.haka ya gama ya fito daure da towel ajikinsa yana daure da daya yana kuma tsane jikinsa da dayan saida ya gama goge jikinsa sanna ya dauko mai lotion din shi mai dadi da laushi yabi jikin sa ko ina ya shafa sanna ya dauko spray dinsa na jiki ya fesa ko ina haka ya gama shirinsa na bacci ya dauki wasu kaya T shit fara da shot nick yasanya ya dauko lapton dinshi ya dawo falo ya zauna da niyyar duba wani aiki da yake son kammalawa amma abun ya gagaresa gaba daya ji yayi baya iya aiwatar da komi, haka ya tashi yakoma cikin bedroom din sa ya kwanta ba don yana jin dadi ba.tunanin kawai yakeyi aransa ina zai samu mafita?yasan dai umma ba sauraren.gsky dana bi shawarar Abba dayace in fito ayi mani aure da hawwa da haka bata faru ba gashi tun ba'aje ko ina ba abubuwa na shirin lalacewa .naso in barta ta fara karatu domin ta kara samun wayewa ne amma kash, kishinta bazai barni ba ina sonta itace mace ta farko dana ke jinta araina amma bata sani ba ina ganin tayi kankanta da zan nuna mata wacece ita agareni.don har yanzu kallon dan uwanta takeyi mani na jini ba wai ta fahimci sona take ba.gsky nayi kuskure yakamata hawwa ta san tun tana karama nake dakon sonta.
Kuma ai ina nuna mata banbanci tsakaninta dasu nabila da nafisa kuma me yasa dana tafi india kullum mukayi waya sai tayi kuka wai in dawo kuma umma tana fadi mani in rike alkawari kada in yarda wata mace ta shiga rayuwata bayan hawwa don ta lura hawwa akwai soyayyata mai tsanani atare da ita gsky akwai sona ranta saidai bata fahimci sona take ba.haka dole ya samu mafitar cewa mami ce kadai zata nuna ma Abba ya amince cikin sauri ayi auren nan namu.dole ne gobe insha Allahu inje kaduna in samu mami da mgnr.haka bacci barawo yayi gaba da shi.itama hawwa da nabila haka suka shiga daki tare da tunani kala_kala wanda mamaki ya hana su kwanciya kowa da abunda yake tsakawa akan abunda ya faru, haka nabila ta zaunar da hawwa bakin gado itama ta zauna cikin damuwa"ta dafa kafadarta tace hawwa kiyi hkr insha Allahu komi zaiyi daidai amma ki bari kawai koma waye yayi mana wannan abu Allah zai tona masa asiri"cikin kuka nace ni walhi nabila yanda naga yayana ya dauki abun ne tsoro ya kamani yanzu idan har Abbanah yaga wannan pic din ai na shiga uku nabila"nabila tace kema kinsan yaya bazaiyi haka ba kawai dai abunda na lura kishi ne kawai ya ruda yaya, cikin hanzari hawwa ta daga kai ta kai dubanta ga nabila "tace kishi kuma?jinjina mata kai nabila tayi alamar gsky ne " to ni sbd me zaiyi kishina?sbd yana sonki to ai kuma yana sonku A a hawwa yana mana so na yan uwantaka ne amma ke soyayyace tsakaninki dashi."haba nabila ni bai taba cewa yana sona ba ai ba sai yace ba mu da muke tare daku mun gane ai juya wa nayi na kwanta nace bar mgnr nan saida safe.
Haka muka tashi da asuba mukayi sallah da addu'oin mu tare da tilawar alkur'ni mai girma, wanda dama mun saba saida gari ya fara wayewa muka tashi.na kalli nabila nace mata sis zan dan koma in kwanta don kaina