Tun ina karama Hausa Novels by Saadatu Abdullahi.txt

Author :  Saadatu Abdullahi Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   9 / 9

24K to 26.6K   out of 26.6K words

sannan yace shi zai koma sai da safe dare yayi sosai "yusuf yace bros ngd Allah yabar zumunci." ba komi umar yace Allah ya baka lfy sai na dawo da safen haka sukayi ban kwana hawwa ta biyo shi ta rufe gidan shi kuma ya shiga mota ya nufi gida cike da takaici aransa.






.......jamila ko na fita bata zame ko ina ba sai gidansu tana shiga tayi parking ta fito ta shiga cikin gidan bata zame ko ina ba sai part din hjy mariya tana shiga ta sameta sai hada mata magungunan takeyi cikin tashin hankali tace mummy na fasa masa kai.cikin tsoro tace"garin yaya jamila!zakiyi wannan danyen aikin?walhi mummy hanani fitowa yayi shine nima na aikata hakan, "kash!amma ke banza ce to yanzu ai kin lalata komi sai ki zauna mu nemi mafita zuwa safe, " ai dole mummy daddy dai bashi nan ko?don shima yanzu naga kamar ya fara bin bayansu Abban yusuf."ke don Allah kyale shi can da munafurcin su kije ki kwanta bashi gari "to mum ngd.







Hawwa na dawowa wurin yusuf ta zauna tace" yaya bari in hada maka tea kasha kafin kasha magani ko, ta tmbye shi cikin damuwa tausayinta nae fal aranshi yarinya karama amma ana sanya mata damuwa da yawa why ya tmby a zuciyarsa, azahiri kuma murmushi yayi yace"duk yanda kike so sweet heat zanyi, murmushi tayi tace to hak ya kamata tashi tayi ta wuce kitchen ta sanya mashi ruwan zafi tare da warming din kazar da suka zo dashi don su duka babu wanda yaci komi in banda cinye juna da sukayi wanda yasa har jamila tayi masu wannan rashin mutunci.






Haka tayi komi ta dawo ta zauna kusa dashi tana bashi tea din yana sha ita kuma tana ci kadan don ita kanta komi ya fita aranta amma bata so taga yanada damuwa aransa ita dai fatan ta Allah ya bashi lfy kafin tace komi.bayan ta gama ne ta taimaka mashi ya shiga bathroom yayi wanka tare suka gama komi suka fito haka ta shirya shi cikin kayan baccinsa saida ta tabbatar ya kwanta sannan itama ta hau bisa gadon ta kwanta tare da rungume shi ta baya juyowa yayi yana mamakin yanda ta canza duk wannan kunyar ta ta ta cireta shima murmushin jin dadi yayi ya kara rungume abinsa ko ba komi ya samu natsuwa aransa.sai muce Asuba ta gari masoyan juna🤩






......washegari da safe bayan sun gama komi ta bashi magani suna zaune a falo tayi pillow da cinyarsa shi kuma yana wasa da kalabar dake kanta shi kansa wani dadi yakeji aransa yanda yaga bata damu da abunda ya faru ba bare ta tmbye sa me ya faru tsakaninsa da matarsa.ba zato taji yace"littel amma ina ftn babu wanda yasan me ya faru ina nufin su umma.dariya tayi tace"babu wanda yasani, "gud house wife haka ake so mace ta rinka rike sirrin cikin gidanta kuma kada ki damu da abinda jamila takeyi with time kinji ko?" Naji yayana kuma insha Allahu zanyi yanda kace"Allah yayi maki Albarka "Amin dear ta amsa masa tare da kara shigewa jikinsa.






Basu dade ba umar ya shigo duba shi hawwa bayan sun gaisa ne ta tashi taje ta kawo ma shi lemu da ruwa.yusuf ne yace" frnd ina so ka rakani in maido da jamila.cikin razana umar ya mike tsaye yana nuna shi d ya tsa zaiyi mgn sukaji faduwar tiren da hawwa ta dauko da lemu da glass cup din data dauko suka fadi kasa suka fashe sbd jin furucin da hawwa taji yusuf yayi na zuwa dawo da jamila.gaba daya suka juya tare da ganin hawwa bata tsaya ba sauraren komi ba ta juya da gudu tana kuka!!!😨






Masha Allah kuyi hkr na rashin jina kwana biyu walhi na zama busy ne amma duk da haka zaku rinka jina akai kai iluv u fans 💋
Din Tun Ina Karama ina maku ftn Alkairi irin sosai din nan 🥰🥰🥰






Mu hadu a next page takuce sa'ar mataaaa🌹🌹💞🤝



*TUN INA KARAMA 👭🌹🌹🌹💞💝💝💘*

By sa'adatu Bello saadatu99gmail.com!



©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*

_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826

بسم الله الرحمن الرحيم...


Page 27






........tana shiga d'aki tasa key ta fada kan gado ta fashe da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, yusuf binta yayi a kidime yana kiran sunanta amma yana isa kofar yaji ta sanya key, komawa yayi wurin umar wanda tunda yazama kamar an dasa shi sbd mamaki ya zama kamar status.








"Kaga irin abunda nake nuna maka Yusuf, yanzu ace kai bazaka iya hkr da Jamila ba sbd sun gama dakai sun maida ka wani wawa sbd da Allah kanayi ma yarinyar nan adalci kuwa?gsky Yusuf zan fidda hannuna akan wannan badakala taku don bazai yiwu ba kullum problem's yaki karewa tsakaninku kai kuma kullum kalmarka bata wuce revenge zakayi taking ba kuma har yanzu kaki gamawa da al'amarin ba."

"Umar kasan bazan boye maka komi ba arayuwata ba to walhi ban taba son Jamila koda da second daya ne idan ba don asiri ba kuma gaba d'aya mun san haka to Jamila tayi mani abubuwa da yawa arayuwa infact ma ince maka ban taba samun mutumin da ya musguna mani ba arayuwa irin Jamila idan har na rabu da Jamila salun alun to gsky banyi abunda ya dace ba,amma ina so in nuna ma jamila ita bata isa ba arayuwa duk abunda take takama da shi ina so in raba ta dashi in nuna mata ita bata isa ba kuma bazata iya samun digo araina ba na soyayyarta kuma ina so duniya tayi mata kunci, ina so in azabtar da rayuwarta har sai ta wulakanta sannan inyi mata mai gaba daya zan dasa mata ciwo a zuciyarta wanda har ta mutu bazata daina jin sa ba,amma hakan bazata samu ba har sai mun zama clothenings da ita don haka ina so ku bani lkc ku fahimce ni babu komi araina intentionally nayi mgnr nan dama ina so Hawwa taji don inga reaction dinta kuma nagani zanyi handle din komi"ya kara she mgn yana kallon umar sosai.


.......ajiyar zuciya Umar ya sauke tare da jinjina kai alamar gamsuwa,"to amma Yusuf taya ita Hawwa zata tabbatar ba sonta kake ba?"

" Yes ina so Hawwa ta kwaci kanta wurin Jamila tacire tsoron da takeyi mata arai kamar yadda Nabila ta bata shawara kuma naga ta dau hanyar yin hakan, kuma ina so ita Jamila tasan Hawwa ita kadaice macen da nake so a zuciyata duk da ta kasa gane hakan har yanzu zan bita akan asirinta na ta siri har sai nakai inada zamu fara game din daga nan zata fadi kasa warwars daga ita har uwarta."

"to shikenan amma u have very careful about her"insha Allahu frnd ama ba yau ba kaje ka lallashi littel"

"hmm walhi Umar tunda ta kulle daki bazata saurareni yanzu ba"

"to yanzu kasan ya zamuyi?"

"Ban sani ba umar."

"Nabila zan kira tace mata zata zo yanzu na tabbatar bazata cigaba da fushin ba har kasamu ka fahimtar da ita komi cikin hikima."

"gud idea frnd."






Koda Umar ya kira Nabila ya fadi mata ga abunda yake so tayi ta amsa da to kuma bata kawo komi aranta ba sannan yace mata bai so abarta ita kadaine tunda zasu fita da Yusuf ne, koda Nabila ta fada ma Umma sakon Umar na zuwanta gidan Hawwa bata hanata ba don itama tasan Hawwa tana bukatar wani kusa da ita tunda jiya ta koma Umma tace ma Nabila," idan kin shirya ki tafi a motar Hawwa sbd abar mata abunta can nasan ai kun kusa komawa skul?"

"haka ne Umma zan tafi da ita dama key din yana hannuna."


"to shikenan agaisheta amma kada kiyi dare, Umar ya maido ki gida."

"to umma ngd" kiran Hawwa tayi kamar yadda Umar yace ta sanar mata zuwanta Hawwa tana da son boye tsakaninta da Yusuf shiyasa koda Nabila ta kirata bata daga ba saida ta saita kanta sosai sannan ta kirata kuma ita kanta Nabila bata fahimci komi ba.







Suna gama samun mafita Umar yace su fita kada ma tasame su haka suka fito shi Yusuf ga plistar agoshi gidan su Umar suka wuce direct suka nufi sashin Umar batare da sun yarda Ammi ta gansu ba bare ta tmby me yasamu Yusuf din.






Ita ko Jamila tana gida gabanta na faduwa tana tunanin ya zatayi idan kuma an samu wata matsala tsakaninsu amma tayi mamakin yanda har yanzu bataji wani feed back ba kuma tayi tunanin ko Hawwa zata fadi ma Umar komi kuma shima tasan daya sani da yanzu yazo yayi mata hauka amma bari takara sauraren su iyaka kawai tace masu bada niyya tayi ba tsautsayine kawai tana wannan tunanin ne Mummy ta shigo dakin suka ci gaba da kullawa suna kwance wa.




Nabila data zo wurin Hawwa bata fahimci komi ba don bata son daga dawowarta tace ga matsala tana so ta fahimci abunda Yusuf yake nufi da zaman su, haka suka sha firarsu kamar bata da wata damuwa koda Nabila ta tmby ta aunty Jamila cewa tayi ta fita hospital tunda ta na tunanin kamar afternoon takeyi haka suka bar mgnr batare da tunanin komi ba azuciyar Nabila.





Su Umar basu dawo ba sai karfe 4:30 suna zuwa suka iske Hawwa kamar ba abunda ya faru tsakaninsu koda Nabila ta tmbyai Hawwa me yasamu Yaya a goshi cewa tayi koface ta buge shi yayi rauni Allah ma ya kiyaye.Umar najin yanda Hawwa take kare mijinta azuciyarsa yace lallai Yusuf Allah ya baka yar aljannar mata haka Nabila ta jajanta masu sukayi sallama suka rako su har bakin mota suka tafi wurin motar ta ta wuce inda Nabila tayi mata parking.binta yayi da kallo don ita ko sake kallonshi batayi ba tunda su Nabila suka fita budewa tayi ta dauki abunda zata dauka ta rufe bata saurare shi ba ta nufi hanyar shiga cikin gidan binta yayi abaya tana shiga tayi hanyar part dinta cikin sauri ya isa gareta ya rike mata hannu juyowa tayi kafin yayi mgn ta daga masa
hannu dakata,"Yusuf !!"

cikin razana ya bita da kallo don ko da wasa bai taba jin ta kira shi agaban shi ba kai tsaye 🤔






Haka ya tsaya yana kallonta 🤣🤣🤣🤣🤣ran mata ya baci 😡to Yusuf ya ake ciki🤪






Masha Allah ina maku ftn Alkairi masoyan Tun ina karama ngd da kauna da kulawarku.





Ku biyoni next page takuce sa'ar mataaaaa 🥰🥰🌹🌹🌹🤝



TUN INA KARAMA👭🌹🌹🌹💞💝💝💘

©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*

_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826

بسم الله الرحمن الرحيم...



By sa'adatu Bello saadatu99gmail.com!



Page 28



..........mamaki ne ya hana yusuf magana sbd yanda yaga tashin hankali a fuskar hawwa karara, juyawa tayi ta barshi wurin yana tsaye haka ya ganta ta shige part dinta ta rufe.murmushi yayi cikin ransa yace hawwa a hankali zaki fahimceni zakuma ki san ke kadaice araina.azahiri kuma girgiza kai kawai yayi ya shige part din shi shima batare da ya kara binta ba.







Hawwa na shiga daki fashewa tayi da kuka tana cewa meyasa nayi sabo da soyayyarsa dama abunda umma ke gani kenan taso rabamu?gsky bazan iya ganin wannan rashin hankalin ba ace wai mace ta so hallaka ka amma kana cewa zakaje ka dawo da ita alhali ita ko bin ta kanka batayi ba anya akwai adalci cikin wannan rayuwa kuma kace wai kada afada ma kowa, to me kake nufi ne?haka tai tayin tunaninta wanda babu amsa cikinsa hardai ta tashi tayi wanka tayi sallah.bata iya cin komi shiyasa ta dan sha tea kawai ta kwanta shima sakamakon tana da ulcer kada ta samu matsala yasa ta sha.








A bangaren yusuf kuma shima hakan take saida ya gama komi zai kwanta ya tuna da umar cewa yayi bazasu je gidan su jamila ba yadai kirata awaya yace ta dawo.haka ya dauki waya bayan ya gama komi ya kira jamila, zaune take tana chatting awaya kiran shi ya shigo wayarta cikin tsoro da fargaba take kallon kiran har ya katse.tsaki yayi ya kara kira har ta kusa katsewa ta daga cikin karfin hali,"hello tace kafin ta kara mgn yace"come back ur home right now!kafin ta sake mgn taji dif ya kashe wayarsa, cikin mamaki da jin dadi tayi ihu wanda har saida mummy tayo dakin da gudu tana fadin "lfy jamila???





......." Mummy yusuf ne ya kirani wai in dawo gidan yanzu ta fada tare da rungume mummy cikin jin dadi mummy tace "amma fa ya shammace mu amma ba komi tunda dama mun gama komi kawai ki maza ki shirya ki tafi kinsan ance da zafizafi akan bugi karfe " gsky ne mummy bari kawai in tashi to yi sauri kinga 8:30 tayi kije can ki kara shiryawa kinde ji bayanin danayi maki ko?"eh mummy naji amma kinsan nayi mamakin da abunda nayi masa kuma banji ya fada mani komi ba harda wannan dan kazagin nashi banji komi ba.hhh ke wai an gaya maki mu na wasa ne har yanzu ke yarinya ce ai an riga angama komi ke dai tashi dama inata tunanin munyi waya da daddy dinki yace gobe zai dawo dama kada ya dawo ya sameki kuma ya fara fada amma naji dadi tunda anyi haka kuma koda kinje ki kwantar da hankalinki ki bashi hkr kinga dai alamar yana sonki ko?"gsky ne mummy bari ki gani"tasahi tayi ta shiga cikin bathroom ita kuma mummy ta fita don ta fiddo mata komi cikin sauri ta gama komi ta fito ta shiga part din mummy haka suka fito mummy tayi mata rakiya har gaban motarta tare da fada mata yanda ya kamata tayi komi haka ta tashi motarta mai gadi naganin haka yace"ga matsiyaciyar nan bari in bude kafin tayi mani rashin mutunci haka ya wangale mata get.ita kuma dari da tamanin ta fita gidan batare da tunanin komi ba.







Tunda ya kirata bai sake sukuni ba haka ya zauna zaman jiranta, cikin awa daya ta iso gidan shima mai gadin gidan naga ninta ranshi ya baci haka ya bude mata get din ta shiga cikin izza da rashin hankali parking lot ta isa tayi parking ganin duk motocin gidan na nan yasa tayi ajiyar zuciya tace"shegiya neman wurin zama har an dauko mota hmm zanyi maganinki.bude kofar motar tayi ta dauko abunda tazo dashi ta fito ta kulle motar bakin kofar ta isa bell din kofa ta taba sau biyu.tasowa yayi ya bude mata dama tunda yaji zuwanta yana bude mata yaja ya tsaya.ita kuma kakarin shiga takeyi tana tafiya tana cewa y gd ya jikinka"binta yayi da kallon mamaki cikin takaici yace"normal direct part dinta ta wuce batare da ta saurare shi ba.






Shima rufe gidan yayi ya wuce part din shi tare da tunanin hali irin na jamila wato bata ma iya gaishe shi sai wani izza take nunawa lallai jamila kinyi kuskure yanzu za'a fara game din murmushi yayi tare da shafa kanshi ya kara yin balance a kujerar da yake zaune, tabbas kinyi abubuwan daza su sanya in rabu dake amma da sauran lkc.







Ita ko hawwa bata ma ji dawowar jamila ba ta riga har tayi bacci.jamila ko na shiga sashenta ta ajiye magungunanta tayi amfani da wanda zatayi ta boye sauran, tayi imani dama ba zuwa zaiyi ba tashi tayi ta kulle part dinta ta nufi nashi.dai dai falo suka hadu da hawwa ta taso zataje part din shi itama sbd ulcer ta ta tashi kuma maganinta yana part dinsa ka cibus sukayi dai dai kofar shi kalan kallo suka tsaya yi da mamkin juna itadai hawwa bata san t dawo ba ita kuma jamila tana ganin mai hawwa zatayi dakin sa bayan yasan tana gidan?🤔






To masha Allah Ku biyoni next page don jin yanda zata kaya.ina ma masoyan Tun Ina karama ftn Alkairi kuma ina ganin sakon ninku ina gdy sosai 🥰🥰🥰🥰🥰





Taku ce sa'ar mataaa 🌹🌹🌹🤝

9 / 9