Tun ina karama Hausa Novels by Saadatu Abdullahi.txt

Author :  Saadatu Abdullahi Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   3 / 9

6K to 9K   out of 26.6K words

ke dan ciwa ok ba damuwa tace ki kwanta ki huta ni zanje in taya Asabe break.to shikenan nace na koma na kwanta.nabila tana shiga sashen umma ta shiga dakin tare da sallama.umma tana hada wasu kaya da zatayi amfani dasu ta juyo ta amsa ma nabila sallam cikin fara' da kulawa nabila har kasa ta tsugunna ta gaishe da umma bayan sun gama gaisawa na ta tmby hawwa ko lfy nabila ta amsa da bacci ne ta koma ta kwanta"umma tace to ba damuwa kema ki koma ki kwanta mana a a ummah zan taya Asabe ne break to shikenan ki sameta kichen din.yaya yusuf koda ya tashi da asuba yaje masallaci ya dawo ya gama abunda yakeyi ya shirya tsab tunda ya gama yanke hukuncin tafiya wurin mami kaduna.bayan ya gama ne ya fito ya wuce part din ummah ya shiga dakinta tare da sallama ta amsa masa ba yabo ba fallasa bayan sun gaisa ne yake sheda mata tafiyar da zaiyi kaduna .hmmm kawai tace tare da fadin Allah ya tsare hanya yasa a adawo lfy.Amin ya amsa mata tare da jin dadin addu'arta gareshi, sbd duk fushin da ummah tayi bata fasa yima yaranta addu'a haka ya tashi duk da baida wata walwala amma yaji ranshi ya fara sanyi.bayan ya futa ta girgiza kai aranta tace zan nuna maka darajarta kafin in tabbatar maka da aurenta bazan bari ka rasata don ita ta dace da rayuwarka insha Allahu.bayan ya fita yaje wurin motarsa tare da budewa ya saka jakar lapton dinsa ya shiga motarsa tare da Addu'a yayi rivos ya nufi get baba ya bude masa tare da ftn alkairi ya amsa da amin






Yana fita bai zame ko ina ba sai wurin umar.to frnd dama shiyasa nace maka indai har zaka saurari jamila to zata samu galaba akanka yanzu kai ka yarda da wannan pic din?da har zaka tada hankalinka?umar yace ni dai ban yarda ba walhi amma kuma auren naku shi zafi tun wuri kafin wannan shidaniyar ta lalata komi ya kamata ka baiyana ma hawwa tun tana karama kake kaunarta simple.yusuf ya sauke ajiyar zuciya tare da kallon agogon hannunsa yace yakamata mu wuce ko?"umar ya daga kai alamar eh haka suka fito daga part din umar inada suka samu Ammi a falon gidan su umar suka gaisheta cikin girmamawa Ammi tace yusuf yasu hjy ya amsa da lfy klau Ammi "to masha Allah Allah ya taimaka suka amsa da Amin suka mike tsaye zasu tafi umar yace Ammi zamuje kaduna sai yanda ta yiwu to ba komi Allah yasa adawo lfy amin suka amsa suka fita tabi su da kallo tana jin dadin alakarsu sosai haka suka shiga motarsu suka fita umar na tuki sai kaduna garin gwamna sai muce Allah yasa a dace yusuf.






Bayan na tashi wurin karfe 10:30 sbd babu wanda ya tasheni saka makon umma tace abarni in huta.ina tashi da addu'a bakina tare da salati na mike na shiga toleit bayi wanka na fito na shafa mai ajikina tare da spray masu dadi ina cikin bude drawer ne in dauko rigar da zan sanya sai wata leda ta fado ina kai hannuna zan dauka gabana ya yanke ya fadi cikin sauri naje wurin window na yaye labulan inda yake parking babu motarsa ya salam!ina ka tafi bayan kace yau zamu bude wannan ledar yaya?why why kayi avoiding me?






To fah🤔 yanzu aka fara wasan fa menene burin jamila yaya hawwa zata dauki aurenta da yusuf?wace irin kalubale ke tare da rayuwarsu?to koma me kenan mujira dawowar Abba, ngd da kauna masu biyoni a pc suna nuna mani soyayyarsu da littafina mai suna tun ina karama👭insha Allahu nima ina tare daku don jin dadinku 🌹🌹🌹masha Allah sai mun hadu a next page takuce 🥰🥰🥰 sa'ar mataaaa🤝


TUN INA KARAMA 👭🌹🌹🌹💞💝💝💘






By sa'adatu Bello saadatu99@gmail.com!






Page 12






........( ban san lkcn da hawaye suka zubo mani ba nayi sauri na nasaki labulen na koma wurin drawer na maida ledar da ban san menene ciki ba nace nima bazan bude ba har sai idan ya daina fushi dani haka na shirya cikin doguwar rigata ja mai stone agaban ta na dauki vell dinta na saka powder kawai nasa batare danayi make up ba haka na sanya takalmina simple na fito nasame su su duka gidan suna falo ummah da Asabe da nabila Asabe mai aikinmu ce amma mun dauketa kamar kaka sbd shakuwa dakuma kirkin matar shiyasa ta zama tamkar yar uwa ta jini da yanda ta dauki umma shiyasa umma ta jata ajikinta sosai gani na kowa da murmushi a fuskarsa umma ko cikin ranta cewa tayi masha Allah yayi hallita wurin plss🙏 le ne yusuf ya tashi hankalinsa don hawwa mace ce kyaunta yanzu yake kara fitowa sosai isowa nayi na zauna kusa da ummah na dora kaina bisa kafadarta shi ya dawo da ita tunaninta nace ummatah ina kwana lfy klau ta amsa tare da cewa ya ciwon kan naki ya bar ciwo ko?na amsa da eh ummatah ya bar ciwon kafin mu kara mgn nabila tace ai sai ki tashi kije kiyi break kike ta wani shishigema ummah na dan harareta to yar sa ido.






Dariya su ummah sukayi mana na kalli Asabe nace kakas ina kwana daftn dai kinyi mani kunun gyada kwarai kuwa autar hjy nayi maki , "ummah ta kalleni cikin kulawa tace tashi kije daning kiyi break dinki ke dai dama ya rage na amsa to tare da mikewa tsaye na nufi daning ina zama na zuba abunda zanci na gama na dawo cikinsu hira sukeyi ina jefa nasu baki jefi jefi amma bawai don ina fahimtarsu ba hankalina gaba daya yana wurin yaya yusuf tunda ya saba mani idan har zai fita bai ganni ba to zaiyi mani text " kamar haka sleeping girl in kin tashi ki nemi yayanki yana son jin muryar littel din gidan su.na kanyi dariya in kirashi ya gama tsokanata mu rabu cikin annashuwa sbd yusuf mutum ne mai son tsokana.to amma yau shiru kuma banji ummah tace komi ba.hmm nasan fushi yakeyi dani.amma fa duk mai son hadani da yayana bazan yafe masa ba.






Duk abunda nakeyi nabila na lura dani kuma tana tausaya mani tunda naki yarda da cewa soyayyace tsakanina da yaya yusuf, lkc nata ja naji shirun tayi yawa wajan 11:30 kawai na yanke shawarar yi mashi text haka kuwa akayi"sweet bros don Allah kadaina fushi littel sis dinka plss🙏haka kawai nace masa na tura masa ina gamawa na dora wayata akan kijina na lumshe idanuwa na kamar mai bacci






Dai dai zasu shiga jaji wayar shi yaji alamar shigiwar text ya dauka ya duba sai umar yaga yana murmushi cikin zolaya umar yace littel dince ko?ya jinjina kai alamar eh , umar yayi dariya bai dai ce komi ba.reply ya bata kamar haka.(sorry littel sis ummanki tana sonki da yawa bazata bari in rinka fahimtar dake gsky ba don haka nina tafi kaduna wurin mamita sai Abba ya dawo zan dawo gidanku an good luck all ur best littel imiss u too)idona lumshe kamar mai bacci naji shigowar sako cikin hanzari na bude amma abunda nagani ne yasani mikewa tsaye tare da fadin what!da karfi na fashe da kuka cin ta shin hankali kowa ya ya taso gareni walhi umma kadunanan🤩 bazan zauna ba nima yaya yace ba zai dawoba nima can zan koma ya za'ayi a rabani dashi umma ya zaki barshi yabar gidanmu baki hana shi tafiya ba.tunda na fara magana cikin kuka kowa kallona yakeyi suna ma kasa cewa komi.nabila ce ta matso ta dafani tace wai hawwa me ya farune haka?ki sakeni nabila nima binshi zanyi umma bata sona tunda har ta barshi ya tafi wayyo Allah zan mutu.ran umma yayi mugun baci da jin kalamin dake fitowa daga bakina hankalinta ya tashi wai bata sona yau ita hawwa take fadi ma haka lallai dole ta koya mata hankali don gaba.bata san lkcn da ta daga hannu ba ta dauketa da mari ba ta sake dauke ta da mari akaro na biyu, kowa na wurin saida suka tsorata ni ko wata juwa nagani tana dibana wanna shine tarihin arayuwata wanda umma ta dora hannunta akaina







Ban san lkcn dana daina ganin komi ba saidai jina akayi jim a kasa warwas cikin tashin gaba daya sukayo kaina suna salati umma cikin rudewa ta kamani tana girgizawa cikin rudewa take kiran sunana hawwa ki tashi walhi bazan yafe ma kaina ba idan wani abu yasameki .nabila ma kuka takeyi Asabe ce dabara ta fado mata ta nufi wurin frige ta dako ruwa mai sanyi ta balle gorar ruwan ta watsa mata cikin hukuncin Allah tayi ajiyar zuciya umma tace ma Asabe su kamani su dora ni bisa kujera nabila ta zauna kusa dani umma ta dauko wayarta ta nemi layin amma a kashe ta nemi na umar shima akashe cikin ranta tace lallai yusuf dani kake mgn bazan saurara maka ba.yanda Asabe taga umma cikin damuwa tace"hjy ki kwantar da hankali tunda tasamu bacci data tashi zata warware.






Umma tace Allah yasa Amin suka amsa gaba daya shi kam yusuf yana gama tura mata text din ya kashe wayar shi cikin hikima ya amshi wayar umar shima ya kasheta batare da umar ya fahimta ba.koda suka shiga kaduna basu tsaya ko ina ba sai unguwar sarki gidan mami suna zuwa saka makon suma yan gidan ne mai gadi ya bude masu get suka shiga sukayi parking gaba daya suka fito daga mota suka nufi cikin gidan, mami na kichen taji kamar muryar yusuf na sallama cikin sauri ta fito zuwa falo tana shiga ta gansu zaune cikin fara'a tace aaa bakin nan kun iya bazata daga ina haka cikin jin dadi yusuf ya ce mami daga gida umar yace mami dan lelenki ne yace ya sai yaga maminshi.nima yana raina nan ta zauna suka gaisa cikin girmamawa tare da tmbyr yan gida.bayan sun gama gaisawane yusuf yace mami coffe za a bani tace to ba matsala bari in hada maku kalaci kafin in gama abincin rana dama nasan wanan tafiyar ai bakuyi break ba umar yace ai mami bai bari ba mun yi break tana dariya ta tashi ta nufi kichen ta hada masu komi ta dawo daning ta shirya masu.bayan su gama ne suka dawo wurin inda take zaune umar yace mami da dawata mgn muka zo maki mami tace haba koda naji to ina saurarenku ya akayi?umar ya gaya mata komi yusuf kansa na kasa don kunyar mami yaji sosai






Mami tace ba damuwa barima in kira Alh ku kwantar da hankalinku komi zaiyi daidai insha Allahu.mami ta daga waya ta kira Abba bugu daya ya dauka mami ta gaishe shi cikin girmamawa sannan yace maryam lfy dai ko?cikin girmamawa tace yaya lfy klau dama wata yar alfarma nake nema wurinka game da yarona yusuf takarashe mgn cikin dariya cikin kulawa yace kamar me fa ki fadi ba abunda zai gagara ai in sha Allahu .nan mami ta zaiyyana mashi komi cikin fahimta kuma ya fahimce ta tare dayi mata alkawarin next week zai dawo daga malesiya in ya dawo za'ayi komi agama insha Allahu ta gaya ma yusuf yafara shirye shirye shi ma da yan uwanta aba kowa hakkinsa, mami tace ngd yaya Allah ya kara girma ya amsa da Amin sukayi sallama.






Bazan fasa gdy ba gareku masoyan wannan littafi nawa na tun ina karama ina jin dadin yanda kuke nuna mani kauna nima ina yinku irin sosai da sosai din nan🤩






Masha Allah takuce 🥰🥰🥰sa'ar mataaaaa🌹🌹🌹🤝



TUN INA KARAMA 👭🌹🌹🌹💞💝💝💘






By sa'adatu Bello saadatu@gmail.com!






Page 13






........Bayan mami ta ajiye waya ta daga kai ta kalli yusuf wanda tunda ta fara waya da Abba yake kallonta zuciyarsa cike da fargaba"mami ce ta katse masu shirun da cewa to yusuf ina fatan dai iyakar matsakar kenan ko?kuma kunji yadda mukayi da Alh ko?to kawai abunda ya kamata kawai kaje ka fara shiri tunda kaga komi yazo cikin sauki in sha Allahu ni daga ban garena banida matsala kuma babu abunda zai gagara kuma idan kana neman wata shawara ko gudunmawa ko kuma wani abunda ya shige maka duhu to kofa a bude to kofa a bude take don ni ba surikarka bace bare kace zakaji kunyata ni uwace diya ba tawa bace ba ga uwarta can itace surikarka wadda naga alama sai kayi da gaske zaka rabata da abunta ta karashe maganar tana dariya cikin zolaya tunda ta lura ya fara nuna mata surutaka ita kuma tafi son yazama free da ita.






Cikin jin dadin maganganun mami gaba dayansu sukayi murmushi umar yace mami godiya muke Allah ya kara girma yasa kifi haka mami gaba daya suka amsa da Amin, yusuf tashi yayi yaje har gaban mami inda take zaune ya durkusa ya dora hannuwansa kan gwiwarta tare da kwantar da kansa yana jin wani irin son mami a ransa tare da kaunarta a ransa yadda take nuna masa karamci bashi da bakin gode mata sai yanzu yake jin kulu-kulun dake cikin zuciyarsa yake fashewa hawayen farin ciki ne kawai ke zuba daga idanuwansa yana jin wani rahama na sauka aransa mami kasa cewa komi tayi sai ma daga masa kai tayi tana share masa hawayen dake zuba daga idanuwansa tana jin wani tausayin sa da kaunar sa tana kara shiga cikin ranta tana ganin soyayya amma soyayyar yusuf da hawwa






Tun tuni yayi mata wuri na musamman arayuwa gaba dayansu birgeni sukeyi kuma yusuf yana son hawwa fiye da tunanin mai karatu haka itama hawwa anata haukan na kuriciya kawai yan uwan taka ne, cikin karfin hali mami tace my own son ina son kazama namiji tsayayye bana son ka kara zubar da hawayenka akan matarka wadda itace zabinka bazan so inga mace tana sanya yarona kuka ba gsky bazan lamunta ba sbd haka kada in kara ganin haka my son.cikin yanayin damuwa ya amsa da to mami insha Allahu na bari amma mami ina son hawwa kowa ma ya yasani amma ummah kullum nuna mani take zata iya rabani da hawwa kuma ni a tunanina babu wanda ya dace da ita kamar ni indai har tana son kwanciyar hankalin mu ni gsky bazan iya hkra da ita ba itace mace ta farko dana ji ina kauna tun ban san cewa sonta nakeyi ba sbd haka ina ftn zama da ita arayuwata na har abada.






Kallon ikon Allah umar yakeyi masa tare da tausaya abokin nasa don ya daina bashi mamaki tausayi yake bashi wanda tun tuni ya fada tarkon son hawwa amma yanayi da irin taurin kai irin na abokin nasa yasa yakasa tantance hakan, duba da yanda yanmata ke bibiyarsa amma yana avoiding dinsu lallai so daban ne Allah bamu masoyan gasky Amin.mami ce ta ka tse mas ushirun su wanda kowa da abunda yake kitsawa karka damu yusuf ummanka tafi kowa son zamanka da hawwa don na tabbatar babu wanda zata sallama ma kowa hawwa idan ba kai ba don haka ka kwantar da hankalinka babu wata matsala insha Allahu umar ya nisa "yace hakane mami nima abunda nake nuna masa abi komi a hankali haka dai suka ci gaba da maganganunsu da mami da cewar sun bar mata komi tayi masu jagora daga karshe suka tashi suka nufi part din yusuf da yake mallakinsa ne a gidan.







Sbd shima dan gidan ne suna shiga ko ina a gyare tsab ga kamshi yana tashi ko ina na kusuwar dakin sbd mami ba daga baya ba wurin tsabta koda yusuf ba zaune yake ba amma kullum cikin gyaran shi take ko ta gyara da kanta ko kuma su fatima su gyara sbd tace a koda yaushe yana iya shigowa suna shiga umar ya wuce bedroom bai tsaya yin komai ba ya fada toleit yayi wanka yana fitowa kwanciya yayi akan gadon dakin don ya gaji bai dade kwance ba bacci yayi gaba da shi.shi ko yusuf dama bai shiga ba falo ya tsaya ya zauna kan kujera sai yanzu ya tuna cewa ya kashe masu wayoyinsu cikin hanzari ya yasa hannunshi aljihun suit dinshi ya dauko wayoyin ya kunna don yasan rigima na can sunayi ita da umma kuka kam ya tabbatar ta sha shi har sai ta ba umma haushi kuma sai yaji ba dadi bai kyauta ba bari ya kunna wayar ya kirata ko kara zolayarta yayi







Yanayin dalling din no ta bugu biyu aka daga amma yayi mamaki idan dai har itace bazata daga ba har sai ta katsaye ya sake kira kafin ta dauka indai tana fushi dashi sallamar nabila ta katse masa tunani cikin fargaba nabila ta gaishe shi tace bacci takeyi yaya cikin damuwa yace bacci nabila?ki fada mani gsky fa yasake tmbyrta?cikin tsoro nabila ta baiyyana mashi komi duk abunda ya faru tace yanzu haka tunda abun ya faru batayi ma kowa mgn.cikin tashin hankali yace wasa nake mata fa?yanzu ina ummah ya tmby ta?umma tana part dinta taje ta dauko wani abu cikin hanzari yace to kada ki fada mata munyi waya ma insha Allahu i am my way to katsina.nabila ta amsa da to yaya itama hawwa kada ki sanar da ita daga haka ya kashe wayar yana dana sanin abunda ya aikata "nabila ta sauke ajiyar zuciya taji dadin hakan ko ba komi yar uwarta zata warware ta samu sauki indai yaya ya dawo na tabbatar zatayi kwanan farin ciki batare da damuwa bedroom din ya shiga yasamu umar har ya fara bacci cikin damuwa ya tashe shi tare da sanar masa katsina zasu koma sbd hawwa ba lfy cikin damuwa umar yace littel ba lfy me yasameta shima ya tambya cikin rudewa yana kokarin tashi.sai alkcn ne yake fada masa abunda ya aikata.cikin fushi umar yace walhi yusuf baka da tausayi saida ka kara sanya mata wata damuwa wai kai wane irin mutum ne?kullum a irin damuwar sanya ta ciki to ni gsky bazan yarda ba arinka yin wannan dani ba.







Walhi kuma wannan izzar dake bisa kanka garaka sauketa ka tarairayi abunda tuntuni shine zabinka to kana ji kana gani zakayi asara ka daina ganina kowa yana bayanka haka umar ya gama

3 / 9