Author : Saadatu Abdullahi Category : New Hausa Novels 2026
ya shiga ya nufi part din shi yana shiga ya nufi bedroom dinsa sai yaji kamar motsi cikin sauri ya karasa tare da bude kofar daga ita sai towel daure jikinta ganin mutun yasa ta saki wata irin karaaa!wadda saida shikanshi yayi saurin juyawa a sukwane ya rufe kofar gammm!!!
Wannan page din naku ne kuyi yanda kuke so dashi mum iliham shatuu tare sis shamsiyya Allah ya bar zumunci😘
Masha Allah ku biyoni frns inayin ku walhi takuce sa'ar mataaaaa 💃💃💃🤝
TUN INA KARAMA 👭🌹🌹🌹💞💝💝💘
By sa'adatu Bello saadatu99gmail.com.
Page 16
..........cikin sauri ya juya tabbas hawwa ce amma me takeyi haka a dakinsa dama yana mamakin ganin part dinsa bude amma bai tantance ba saida ya ganta, dawowa yayi falon ya zauna bisa kujera yana jiran yaga ikon Allah.hawwa komawar da yayi ya rufe kofar shine ya bata damar sanya key ta rufe kofar cikin tsananin tsoro tare da zama bisa gadon ta dauki turarukan da zatayi amfani da su ta cigaba da shafawa tare da humrar da zatayi amfani da ita.cikin fargaba da tsoro takeyin komi acikin ranta tana cewa dama bata biye ma su nafisa ba da suka bata shawarar zuwa part din shi ta shirya sbd mutane ko ina amma babu wanda yayi tunanin dawowar shi yanzu tunda ansan shi ba mai son hayaniya ba.zaune yake yana tunanin koma ya tashi ya tafi gidansu umar ne.amma bari ya jirata yaji me ya kawota ne?tana gamawa ta dauki rigarta ta sanya ta dauko hijabinta ta sanya ta hada komi nata ajakar data shigo da ita ta zura takalminta ahankali ta tako bakin kofar kamar munafuka haka ta sanya hannu ta murza key din kofar ya bude ganin shi datayi zaune a falo yasa jikinta kyarma cikin dauriya ta karasa fitowa batare data sake kallon inda yake ba shiko kallo daya yayimata yayi tasbihi ga Allah gaba daya yarinyar ta canza mashi tayi wani irin kyau ga jan lallen nan ya zanu ajikinta.rabawa tayi zata wuce shi batare datayi mashi mgn ba cikin sauri ya tashi ya rike mata hijabi saurin juyowa tayi tana kallonsa a tsorace murmushi yayi mai kayatarwa yace me kikeyi adakin mijinki?tmbyr tazo mata abazata cikin inda inda tace mutanene adaki na shiyasa naxo in yi wanka anan bansan zaka dawo yanzu ba amma kayi hkri."sbd kinzo dakin mijinki kike bani hkri to amma hawwa ko ki kirani kice kin iso bakiyi ba, ta lura son janta yakeyi da magana "yaya ai ni tunda muka iso kaina ke ciwo bacci nayi yanzu ma tashi na kenan nazo nan.murmushi yayi" yasan fadi kawai tayi cikin hikima ya sakar mata hijabi sbd yaji yanayinsa ya fara canzawa ok shikenan yanzu kin gama komi kika fito ya tmbyeta saurin daga masa kai tayi alamar eh sbd a takure take sbd wani irin kallo daya keyi mata are u show?yasake tmbyrta?"yes tabashi amsa ok jeki sai na fito tom ta amsa tare da saurin fita daga dakin kallonta ya tsaya yi yana dariya kasa kasa don yaga yadda take hade step.
Tana fitowa ta yi wata ajiyar zuciya tare da gode ma Allah don gsky taji kunyar ganinta dayayi wai har yana cewa tazo dakin mijinta kai yaya yusuf shi baima jin komi haka yake sakin mgn ba ruwansa da wannan tunanin ta shiga part din su.bayan ya shiga kamshin daya rikita shi ajikinta shine a dakinsa kota ina wai yaushe littel ta canxa turarene haka masu dadi da kamshi lallai zan sha kamshi ya furta tare da nufar toleit don yin wanka shima ga magrib na shirin gabatowa wooow ya furta yanda yaji toleit din ya na tashin kamshi towel din datayi wanka ya dauko ya rike tare da rungume shi a kirjinsa yana wani lumshe ido kamar hawwa ce ya rungume hhhhh kaji su yusuf sabon shiga 🤭nidai fitowa nayi na bashi wuri don naga abun nashi sai a hankali🤣🤣🤣
Hidima akeyi ba kama hannun yaro ta ko ina yan uwa da abokanin arzuki suna ta fasowa ta ko ina hawwa sun gayyaci kawayensu inda da yawa sun halarci bikin nan yusuf ya kashe kowane party sai dinner kadai sbda yace walhi shidai yana kishin matarsa itama dinner sbd abokaninsa wadanda suka zi daga kasahe daban daban ne kada suga bai kyaut a masu ba shiyasa umar yace lallai yayi hakr ayita amma anyi walima tsakanin mata kadai kuma abun yayi kyau sosai gwanin ban sha'awa anyi wa'azi akan zaman takewar aure kuma da nasihohi sosai abun dai masha Allah.rana bata karya saidai uwar diya taji kunya ayau ne aka daura auren yusuf Bello mado da amaryarsa hauwa'u Bashir mado haka speaker babban masallacin dake GRA ta gauraye da fadi an daura auren akan sadaki mafi karanci naira dubu hamsin wanda Alh bello ne ya biya kowa yaji dadin hakan duk da suna da kudi amma basu nuna alfahari ba.to fah yaufa yusuf baki bai rufuwa yasamu abunda yake so tun tana karama me zaiyi banda gdyr ubangiji bayan angama daurin aure ne suka wuce hotel din da bakin su suke domin yin resption.
Biki kam yayi ashe da dangi muka kuriii💃💃💃gidan Alh Bashir babu masaka tsinke cike yake haka gidan Alh Bello mutanen kankiya sun cika shi kai sai inda kake so zaka zauna su nabila da nafisa kuwa basa ma ganuwa haka aunty zainab ga aunty Rabi atu ta kano autarsu Abba kowa yana cikin farin ciki in ka cire hjy mariya sbd tana cikin hdimar amma ta ciki na ciki hakama jamila sbd hjy mariya tace ta saki jikinta itama lkc kadan ne indai yusuf ne a hannunta yake shiyasa ta fita ta warware ta shiga anayin komi da ita amma kasan ranta kamar ta kashe hawwa ta huta takeji.ummah kam cikin ranta fes alkawarin Allah ya cika Addu'a kadai takeyi dftn zaman lfy atsakanin yaran nata mami kuwa har kuka tayi sbd farin ciki.tun ranar da suka hadu a part din yusuf bai kara sanyata ido ba sbd gaba daya barin gidan yayi shima umar barin gida yayi suka koma hotel da abokansu kasan cewar ba kamun kai jamila take dashi ba takan zo hotel din wurin wasu data sani da sukayi karatu tare kuma ko don tazo taga yusuf ko bazai kulata ba shiko kamar ya shaketa yakeji yana tir da hali irin nata, haka nan taji tana son jin muryar yayan nata cikin sanyin jiki tace "nabila dauko mani wayata ki kunna mani nasan yaya fushi yakeyi dani tunda na kashe wayar nan murmushi nabila tayi " tace kyaji dashi yarinya idan ma zaki cire kunyar nan ki rike mijinki hannu biyu biyu to tun wuri kisan abunyi don akwai kuraye ta karashe maganar tana dariya tare da dauko mata wayar tana mika mata.amsa tayi ta bude wayar batare da tunanin komi ba ta danna kiran yaya yusuf .yasanya wayar caji a falon dakin daya ke ya shiga yayi alwalla ita kuma shigowarta kenan zata shiga wurin frnd dinta ta lura da wayar yusuf na neman agaji cikin sauri ta duba screen din wayar my angel taga ni yana yawo tabbas hawwa ce murmushin mugunta tayi ta daga wayar hawwa sallama tayi cikin sanyi murya.murmushi jamila tayi"tace to ke banda abunki tunda kinyi nasarar auren shi mu kuma ai sai ki barmu mu huta dashi kafin mu mika maki sauran.cikin tashin hankali tasaki wayar kasa gaba daya ta tarwatse shikuma daidai da fitowarsa yana gyara hannun rigarsa ya jamila rike da wayarsa tana kallon wayar tana murmushi mai hade da mugunta.😨
Masha Allah Aunty uwani ina gdy sosai Allah ya bar zumunci🥰🥰🥰 masoyan littafin TUN INA KARAMA ina ma kowa ftn Alkairi ngd sosai da kauna😍💖🌹🌹🌹ku biyoni page na gaba takuce sa'ar mataaa💞🤝
TUN INA KARAMA 👭🌹🌹🌹💞💝💝💘
By sa'adatu Bello saadatu99gmail.com!
Page 17
..........cikin azama ya karasa wurinta tare da fisge wayarsa a hannun jamila wani mugun kallo yayi mata wanda sai da zuciyarta ta buga sbd tsoro amma cikin dakewa ta ce masa"daga na taimaka na amsa maka ma shine zaka wani karya mani hannu, "uban wa yace ki daga mani waya?yusuf ya tmbyta cikin tsawa da hasala ke dai walhi baki da hankali baki san ciwon kanki ba am last waning kika kara shiga hurumin da ba naki ba sai na ci ubanki nonsens fita yayi batare da ya kara saurarar ta ba.cikin jin zafin abun ta juya itama ta bar wurin.yana fita ya duba yaga angel ce ta kira cikin sauri ya dalling number ta amma swittch up ya kira yakai sau biyar amma shiru mamaki yakeye Allah yasa ba wani mummunan abu ta fada ma littel ba haka ya kara sa masallaci yayi sallah.nabila cikin sauri ta kara so wurin hawwa tana tmbyrta lfy me yasamu yaya?zubewa kasa tayi batare da tace komi ba hawaye ne kawai ke zuba a idonta matsawa nabila tayi tana girgizata hawwa gaya mani don Allah me ya faru kallon nabila hawwa takeyi cikin kuka " hawwa tace nabila yaya ya cuceni ashe yana da yan mata awaje wadanda ya ajiye yanzu cikinsu ne wata ta daga wayarsa bata boye mata komi ba ta fada mata cikin rashin fahimta nabila ta bude baki zatayi mgn wayar nabilace tayi kara gaba dayansu dubansu yakai ga screen din wayar sunan yayane ya baiyyana a wayar nabila.cikin sauri ta daga tare da sallama bai tsaya amsa gaisuwarta ba ya tmby ina littel?"yaya ban san ya akayi wata ta dauki wayarka ba ta fada mata mgn gashi can kuka takeyi kuma ta jefar da wayarta ta fashe.abunda yake zargi ya tabbata "cikin damuwa ya ce walhi nabila caji nasanya na shiga inyi alwalla jamila ta daga mani waya kuma ke kin san jamila bata da hankali ." nabila cikin mamaki tace aunty jamila?tabbas zata iya amma menene ribarta in tayi haka?katse mata tunani yayi da cewa ki hadani da hawwa, to yaya ta amsa tare da mika ma hawwa wayar wadda tunda suka fara mgn take saurarensu amsa tayi tare da sake fashewa da kuka bata yi mgn ba shikam jin kukanta yakeyi tamkar saukar wuta a zuciyarsa cikin damuwa yace littel nima kukan kiso inyi ne?"ya tmbyt cikin rauni girgiza masa kai tayi kamar yana kallonta ya cigaba da cewa don Allah littel kiyi hkr walhi ban san komi ba shirin jamila ne kuma walhi zanyi maganinta plsss my sweety nah kada kowa yaji wannan mgnr ku barta daga ke sai nabila plssss ya kara she mgn cikin sanyi murya "cikin damuwa tace ni yaya ban san me nayi ma aunty jamila ba ta tsane ni haka?amma ya dace ta fada mani wannan mgnr me nayi mata?ta kara she mgn cikin yanayin damuwa harga Allah baya jin zai kyale jamila sai ya wulakanta ta kamar yadda taso ruguza mashi farin cikin sa na yau amma zai rama shima haka yaci gaba da lallashin matarsa har hankalinta ya kwanta sannan yace mata ta fadu irin wayar datake so ya kawo mata " cikin jin kunya ta ce duk wadda ka saya mani inaso yayana."cikin jin dadi yace kin yarda da choice dina kenan?"yes ur choice is my choice my dear husband tsunkulin kansa yayi wai ko mafarkine yakeyi kafin ya kara mgn yaji dif an kashe wayar.bin wayar yayi da kallo yana smile, ita ko dariya takeyi nabila ma dariya takeyi suka rungume juna nabila na jin dadin yanda hawwa take daukar shawararta akan lkc kuma tana tir da halin yayarta na son zuciya.
Haka suka warware babu wanda yasan abunda ya faru tsakanin su .suka gyara jikin su suka fito wurin kawayensu cikin jin dadi.haka shima yusuf yaji dadin yanda littel ta fahimce shi kuma ta yafe masa iluv her ya furta tare da fita daga cikin motar tunda dama ya yanke shawarar zuwa gidan ne idan har hawwa bata fahimce shi ba to ya gode ma Allah da shedancin wannan makirar baiyi tasiri akan su ba Allah ka shiga tsakaninmu da ita nima Amin nace yusuf🙏haka abubuwa suka kasance har dare karfe 7:30 motocin kai amarya sun cika unguwa hawwa ta sha kwaliya da wani less sky blue komi na jikinta sky blue ne abunka ga farar fata abun sai wanda ya gani.gAmin👏kya suna falon Abba aunty zainab ce rike da hawwa ummah na zaune kusa da Abba sai mami dake gefe sai hjy kaka da itama tana kusa da Abba yusuf ne jikinta sai aunty rabi atu da itama tana wurin hakika yau naji abunda ya girgizani na bani tarihin rayuwata ashe mamice mahaifiyata ummah mahaifyar yusuf gsky na shiga rudani asheni marainiyace wanda ban taba sanin maraici ba gsky ina jinjina ma Abbah da ummah da yan uwan mami da ita kanta mami shima kuma yusuf ya cancanci a yaba masa kuka nakeyi wanda babu mai iya tsaida mani shi ashe pic din danke gani adakin ummah shine mahaifina Alh mansir kanin ummah da akace ya rasu?tashi nayi na fada jikin ummah ina kuka mai tsuma xuciya wanda kowa na wurin saida y share kwalla.Abbah ne yayi gyaran murya yace to haka Allah ke nashi ikon don haka kai yusuf ban baka aure ba don kana nawa a a cancanta na gani walhi da baka can canta ba ni zan nemo mata mijin da ya dace da ita amma tunda Allah ya hada kanku bani da bakin gode masa ina maku ftn Alkairi tare da zaman lfy da hkr da juna ka rike amanar da Allah ya baka kuma ka tausaya mata amatsayinka na shugaba sbda kowa yazama sheda bazan raga maka ba natsawar zaka cutar da matarka."Abba yace zo nan littel cikin rashin kwari hawwa ta matsa kusa da Abba ya kama hannunta yace ma yusuf taso nan shima ya taso kusa dashi kanshi na kasa Abba ya kama hannunsa ya hada dana hawwa yana murmushinsu na manya yace ma yusuf rike matarka ina maku ftn mutuwa ce zata rabaku gaba daya dakin ya amsa da Amin👏haka yusuf ya rike hawwa gam kamar za'a kwace mashi ita haka kowa ya mike muka fito ina kuka kamar raina zai fita ga rabuwa da ummah tayi mani daci wannan shine dalilin aurena da yaya yusuf
Bayan ankai ni gidansa dake barhin wanda ya tsaru yayi kyau sosai haka daga nan muka shirya zuwa wuri dinner wadda umar ne ya shirya komi su kansu kayan xuwa wurin dinner ya sha banban da namu na nan don komi daga india aka kawu mana kayan da zamu sanya wurin jamila bata san da wannan shirin ba hankalinta ya tashi sosai ganin wannan shirin namu duk sai ta raina kanta mune karshen tafiya umar ne zai kaimu daga ni sai yaya sai umar da ke jan motar zaune muke abaya hannuna cikin nashi yake rada mani akunnena wai idan munje don Allah bai son inshiga da kunyata in ajiyeta baki kofar mota kafin in fita murmushi kawai nakeyi duk abunda mukeyi umar na kallon mu ta madubi dariya kawai yakeyi har suka isa hall din dai bakin kafar yayi parking da sauri ya bude ya fito ya zagayo ya bude masu kofa kama hannunta yayi suka fito tare ai aka shinfida kafet tunda ga wurin motar har zuwa ciki ga masu binsu da flower suna watsa masu ga kida na tashi abun gwanin ban sha awa haka suka isa har wurin da nasu ne na musamman wapre table suna zama kowa ya zauna sai tafi rab rab rab ke tashi nan da nan mc ya fara jawabi babu wanda amarya da ango basu birge ba haka aka kira babbar kawar amarya tabada tarihin amarya wanda kowa sai da yayi dariya haka nabila ta koma ta zauna aka kira umar shima yayi bayanin ango wanda duk mgnr da sukeyi da turanci sukeyinta sbd abokansu da basa jin hausa haka mc ya kira amarya da ango suka shigo fili haba dan da na wuri y kaure da ihu ana tafi umar kuwa tunda ya balle dolars zuba masu kawai yakeyi haka sauran abokanin su suma dolars ce kawai ke yawo wurin cikin hikima jamila ta shiga filin ta fara zuba nata kudin akan amarya da ango da dabara ta kama rigar hawwa tasa reza ta jata ai ko nan da nan bayanta ya baiyyana umar ne kadai yaga abunda tayi cikin azama ya iso ya rike hannun jamila jikake fas fas fas ya dauke jamila da mari jin karar marin sai hankalin mutane ya dawo gare su.
Masha Allah gdy nake kawata sibara madugu present☝️tace masoyan Tun ina karama ina gdy Allah yabar zumunci
Ku biyoni next page daga nan har ranar monday in Allah ya kaimu.taku ce sa'ar mataaaaaa💋😘🥰🥰🤝
TUN INA KARAMA 👭🌹🌹🌹💞💝💝💘
By sa'adatu Bello saadatu99gmail.com!
Page 18
..........kowa ya juya yaga mai ke faru jin karar wannan mari da mutane suka ji "afusace umar yake nunata da yatsa yace kibar wurin nan tun kafin insa a fitar mani dake ummi dake kusa dashi ya jawo gyalen dake jikinta ya mika ma hawwa yace sanya sbd ita tariga taji abunda ya faru da ita jikinta rawa kawai ya keyi yusuf kuwa mutuwar tsaye ya yi sbda ya fahimci komi jamila dafe fuskarta tayi zata bar wurin hankali tashe cikin azama nabila ta jawo gyalenta fuskarta hawaye na zuba a idonta " tace aunty jamila baki ji kunya ba kina jayayya da abunda Allah ya kaddara?agsky ke muguwa ce bayan sharrin da kika hada dazun yanzu kuma kin zo da wani cikin takaici nabila ta girgiza kai tace kaicho da kika zama yar uwata ta jini amma walhi baki iya raba hawwa da yaya yusuf duk makircin ki "umar ne ya jawo nabila yace mata kyaleta sis cikin baki ciki ta sake ta tana kukan takaici " umar ce ma yusuf ya bar wurin da hawwa shi takaici ma ya hana shi cewa komi ita ko hawwa hankalinta yayi mummunan tashi hannun ta ya kama batare da yace komi ba suka bar wurin mutane da ba kowa ya fahimci komi ba kowa sai ya koma hidimarsa yasu yasu ne kawai suka san abunda ya faru cikin family din
yusuf na fita daga hall din wurin motar da suka zo da ita ya nufa ya bude ya zaunar da hawwa wadda ta zama kamar wata status sbd mamakin jamila yana shiga