TUDU A KWARI BOOK COMPLETE BY (LEGENDS PEN).txt

Author :  Legendspe Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   11 / 13

30K to 33K   out of 36.3K words

sunan Nawfal da tagani yasata tsayawa.



Wani irin tausayin sa ne yakamata, tabbas zata gayamasa ya dakata da lamarin Ummi a yanzun.



D aga wa tayi tare da fad in

 Assalamu alaikum.



Daga can b angaren nashi amsawa yayi da  Barka da Safiya fatan ban tashe ki ba.



Dariyar yak e tayi sanan tace

 Katashi lafiya ya mutan gidan?.



 Lafiya klau Asiya mutan gida na lafiya ya naku.



 Lafiya klau suke wallahi.



 Masha Allah. sanan yad ora da cewa.



 Asiya nayi magana da Mahaifina d azu da safe kam suzo su nema mun auren Ummi.



Daram haka kirjin Asiya ga buga, idan akace mata Nawfal yaji yanda kirjin ta yabuga bazatayi mamaki ba.



 Naam Nawfal ke kace.



 Nace nayi magana da Abbana yau da dadare zasu zo tambayamum auren Ummi, ko da matsala ne?.



 Eyh A ah.



 Mene Eyh A ah kuma?.



 Nawfal da bakayi gaggawa ba.



 Haba Asiya wace Gaggawa kuma duk jiran da nayi shine zakice nayi gaggawa.



 Bahaka nake nufi ba Nawfal amma da kasani kasanar da ita.



Shiru yayi dan a maganar Asiya ya fuskanci akwai matsala.



 Asiya zan iya samun a gida.



Shiru tayi na yan mintinan daga bisa ne tace.

 Yes.



Bayan sun kammala wayar ne ta danna lambar Ummi sai dai taji alamun tana wyaa ne, tashi tayi tare da Hijab din ta ta nufi gidan nasu.



 Hajiya na zaune a tsakar gida tagaisheta tare da fad in.



 Hajiya Ummi na ciki.



Kallon tara saura Hajiya tayi mata sanan tace.



 Kajimun yarinya da kinibibi idan tana nan aikin sani idan batanan ai kinsani.



 A ah Hajiya nakira wyaarta ne naji bata tafiya.



 To tana ciki.

Hajiya tafad a tare da cigaba da Abinda take, tashi Asiya tayi tanufi d akin, kwance ta sameta waya a kunne tana magana k asa k asa.



 D aka mata duka tayi tare da cewa bakiga nahsigo bane.



  Zan kiraka anjima Asiya bazata barni nayi wayar nan ba.



Ummin tafad a murya can k asa, Asiya bataji abinda kace ba sai Ummin da taji tace.



 Bye love you.



 Ke da ubanwa kike waya haka Ummi?.



 To uwata da ubana nake waya.



 Ke banason iskanci bawanan ne yakawo ne ba.



Gyara zama Ummi tayi sanan tace.



 To meya kawoki har zaki katsemun waya da masoyina.



 Ummi Nawfal ne yakirani tare da fad an mu wai yayi magana da mahaifin sa kan zasu zo wajen Abb anjima.



A furge ce Ummi ta tashi tare da fad in.



 Me yake damun Nawfal haka ne?.



 Ummi zauna kiji.



Asiya tafad a tare da kamo Ummi ta zauna.



 Relax wanan abun fa muma da namu laifin sabida bamu sanar dashi komai ba kan dawowar master.



 Amma kuma Asiya yasan koda wasa bantaba cewa ina sonshi ba ko hirar soyayya bantaba dashi ba kuma yasan akwai baiko akaina.



 Hakane Ummi yanzu yace zai zo ya sameni kawai ina ga kifito ayi duk maganar da za ayi ta k are.

  

 Kinga fa yanzu wayar da muke da Mukhtar kan gobe yau da daddare zaizo gaida Abba.



Sallamar da suka jiyo a tsakar gidan ce ta katse musu maganar da suke.



Hajiya ce ke fad in.



 Wanake gani haka kamar Affan.



Har rige rige ake tsakanin zuciyar Ummi da Asiya wajen bugawa kafin suka maimaita sunan.



  Affan.



 Chab.  

Ummi tafad a tare da ficewa wajen dai dai lokacin da zai zauna.



Bai kai ga kallon ta ba Asiya taja ta cike tare da fad in.



 Ke Ummi me yashiga kanki, tijara zakije kiyi masa ko me?.



 Wallahi zagen sa zanje nayi nasa shi yafita daga gidan tunda bana ubansa bane?.



 Shikenan kina numai kinji haushin watsar dake da yayi.



 Bangane ba Asiya.



 Nitsu ki fahimce ni, ai tunda kika yazo bayan yadawo to da alamun akwai abinda yakeso, to da wanan zakiyi amfani kici uban shege sanan ki watsar dashi.



 Taya bangane ba?.



Ummi ta tambayi Asiya.



 Kinyi wanka ko bakiyi ba?.



 Nayi.



Ummi tabata amsa baki asake kamar sha sha sha.



 Tashi ki d au wanka d an ubansu nima aramun doguwar riga.



Tashi Ummi tayi ta d akko musu kayan cikin yan mintuna suka shirya, sun tsala uban kyau ko wacce rik e da jaka suka fito.



Hajiya dake zaune ce takalli tare da cewa.



 Ni Saliha ina kuma zaku haka?.



Affan da tunda suka fito idan sa ya sauka kan Ummi,  a hankali k asa k asa yake kallonta.



Asiya ce tayi saurin cewa.



 Zamuje Gidan anty nafisa ne zancen anko.



 Ankon wa kuma?.



Hajiya ta tambaya dan ita bata harbu jirgin su ba.



Dariya sukayi mai cike da aji ba tare da sunce komai ba.



 Ummi wai bakiga Affan ba.



Anzo wajen da Asiya ta fad awa Ummi, kallonshi tayi sanan tace.



 Waye shi?.



Kama baki Hajiya tayi sai yanzu ta d ano jirgin nasu.



Shikam Affan jin maganar yayi kamar saukar aradu wai tambaya take waye shi.



 Dr Affan fa.



Hajiya ta k ara fad a, Asiya ce tai saurin cewa.



 Oh wai Doctor Affan d inan.



 Shi Asiya har kun mantashi kenan.



Dariya sukayi sanan Asiya tace.



 like wanda kace anmasa Engagement da Ummi ko?.



 Like.



Affan yafad a a ranshi yana k ara mamakin irin girma da kyan da yan matanan sukayi sanan gashi ko ganeshi ba suyi ba ita gwanar tashi ma ko magana bata iyawa



Dariyar Ummi ce ta dawo dashi daga tunanin da yake sanan tace.



 Dr Affan how far me yakawo ka kuma?.



A hankali ya furta.



  Tafiya da Matata.





Page [41&42]



Dariya suka tuntsire gaba d aya dai dai lokacin kuma wayar Ummi tayi Ringing, d agawa tayi tare da fad in.



 Hello Babe.



Da sauri Affan ya runtse idonsa domin ji yayi kamar ta buga mai abu akansa.



 oh you re outside already.



tak ara fad a sanan kuma tace



 okay gamu nan.



wanan duk shirin Asiya ne wanda kuma suna da tabbacin komai yayi yanda yakamata.





 Hajiya sai mundawo.



Ummi tafad a batare da sun jira cewar ta ba suka fice.



Da gudu suka shige gidan su Asiya sabida kar tsautsayi yasa ya biyo su yaga inda suka shiga.



 Hajiya zan huce.



 Tun yanzu Affan?.



 Eyh Hajiya daman nazo na gaida ki ne.



 To shikenan Affan nagode Allah yayi albarka.



 Amin ya Allah ga wanan tsaraba ce.



yafad a yana mik amata tulin kayan da yazo da su.



Ko a waje bai gansu ba hakan ya tabbatar mai da Saurayin nata yatafi dasu,ko da yakoma gida bai boyewa Hajiya Balki komai ba  da yafaru a gidan.



 To yanzu Affan komene yafaru laifin kane, yarinyar nan bawani sonka take ba tunda akayi muku baiko kaita hulak anta ta, to yanzu gashi har ta tsayar da wani kuma kasan ta da taurin kai tun tana k arama ba abune mak sauk i zaisa ta karb i auren ka akaro na biyu ba.



 Amma Mom nima da bana sonta sai yanzu kuma ai already anyi mana engagement.



 Affan engagement fa ba aure bane, ana iya sokeshi ko wane lokaci.



Tashi yayi ya huce office d in Abban shi.Sai da yasan yayi duk yanda zaiyi wajen tunzura daddyn shi akan maganar auren sanan yabar office d in.



************



 Gaskiyya Asiya bansan brain d inki yafi nawa jaa ba sai yanzu Wallahi Allah.



Dariya Asiya ta fashe da ita sanan tace.



  To Ummi ai da nabarki naga hauka kike shirin yi mana to ina dalili.



Kirani Nawfal ne ya shigo wayar Asiya, da sauri taja wayar tare da cewa



 ke ya zamuyi da Nawfal.



 Ni Wallahi Asiya bansaniba kawai mu fad a mai gaskiyya.



 Gaskiyyar me Ummi wace k arya mukai mai?.



 To ni bansaniba.



Ummi tafad a tana cire kayan jikin ta, daukan wayar Asiya tayi tare da karawa a kunne.



 Ranki ya dad e na iso fa.



 To shiknan bari nazo.



tafad a tare da kashe wayar sanan ta kalli Ummi.



 Idan nakiraki sai ki fito.



 To kifara dubawa kiga wancan d an rainin hankali yatafi dai ko.



 Ni kinga har na ma manta.



Asiya tafad a tan ficewa bayan tasa Hijab domin a ganin ta wanan kwalliyar bata kamata taje masa da ita ba.



Tsaye yake jikin motar shi tasame idon shi a rufe,  k arasawa tayi tare da yin Sallama, amsa ma ta yayi tare da cewa.



 Ban takura ki ba ko?.



Murmushi tayi sanan tace



 Wace takura kuma?.



 Nasaki fitowa akan damuwa ta.



 Uhm ba wani nan.



Dogon numfashi yaja sanan yace.



 Asiya dan Allah fad amun gaskiyyar komai karki boyemun.



 Duk abunda zai fito daga bakina zallan gaskiyya ce sai dai ba lallai tayi maka yanda kakeso ba.



 Ina jinki Asiya.



 Nawfal tun a farko ka nuna kanason Ummi Amma bata amince ba, ganin yanda kake nuna soyayya yasa nake k ok arin nuna mata kyawawan halayenka ko Allah zaisa taso ka, to kasan so shiyake ganin guri bawani ke gane mai ba.



 Hakane Asiya go straight to your point.



 Nawfal har a yanzu Ummi bataji zata iya baka ragamar rayuwarta ba, bawai dan baka da kyawawan hali ba ko kuma baka kaiba, kawai har yanzu zuciyar ta bataji zatayi naam dakai ba.



Shiru yayi for atleast 10mins sanan yace.



 Shikenan Asiya nagode sosai da sosai, Nasan kinyi duk abinda yakamata Nakuma gode Allah yayiwa Rayuwa albarka yabaraki kema da Mansur.



Dariyar yak e tayi sanan tace.



 Amin tho amma ba mansur d in ba.



 Oh shima bakiji zaki iya bashi ragamar rayuwar ki ba?.



 Nawfal Ummi fa ba iya ta tace bazata iya baka ragamar rayuwar ta ba, nice naga haka, sanan shi Mansur ai akwai dalilin daya ja haka.



 Asiya ai bakice mun Ummi ta fad a ba sanan shima mansur d in zan iya jin dalilin.



Shiru tayi alamun bazata iya fad a ba.



 Tom shikenan Asiya nagode.



 Shikenan Nawfal Allah yasaka da Alheri.



Daga haka ya shige motar shi ya huce, itama ta koma gida, gaba d aya takwashe duk abinda yafaru tasanar da Ummi sanan ta d ora da cewa.



 Wallahi Ummi bakiga yanayin sa ba abun tausayi.



 Nasani Asiya Amma meyasa baki fad a mishi dalilin rabuwar ku da Mansur ba? kika sani ko sonki yake.



 Allah ya kyauta.



Kawai Asiya tafad a domin batasan me zatace ba.





*****************



Yau ne Ranar da za ayi wa Zainab Babbar tiyata wacce take sirad in ko rayuwa ko mutuwa.



  Gaba d aya Tun safe Master yakasa zaune yakasa tsaye,  yana zaune kusa da zainab akan gadonta.



Zainab ce ta kalleshi ya sunkuyar dakai alamun yana wani tunanin sanan tace.



 Mijinaaa.



A hankali yad ago kai yakalle ta batare da yayi magana ba.



  Dan Allah ko bayan Raina na dinga kasancewa cikin ranka, kar kamanta dani da huri.



 Zainab ki daina fad in haka ba mutuwa zakiyi ba Insha Allahu zaki tashi.



 Kasani idan namutu a yanzu ba laifi na bane Allah ne ya amshe ni dan Allah ka kula da Abinda ke ciki na domin nasan ba lallai bane shi yatafi sabida a yanzu yakai wata 7.



Azabure ya d ago ya kalleta tare da rik e hannunta.



 Zainab daman na fad amiki ciki ne dake daman amma kika ki yarda kikace dani ciwon ne.



 Nima sai a zuwan mu asibitinin Dr Shiraz yasanar dani kuma yace za acire d an cikin kafin ayi aikin.



 Zainab insha Allahu zaki tashi za afito dake lafiya.



 Ya maganar tura iyaye wajen Mahaifin Ummi.



Damamaki yabita da Kallo sanan yace.



 Zainab wai bakya ta lafiyar ki ta zancen Aure na kike, Zainab zan hakura da turawa har sai amfito dake daga theater munsake magana.



 A ah yaballabai katura.



 Zainab bazan turaba nagama magana.



Shiru ne yabiyo baya na tsahon mintin kafinan yatashi yashiga toilet.





Page[42&43]



B angaren Ummi kam tun safe take jiran kiran Master Amma shiru m, har suka zo tafiya airport tawowa da Yaya Umar.



Gaba d aya hankalin ta baya tare da ita yanaga Tunanin Master har suka k arasa cikin airport d in.



Bawani jira sukayi ba jirgin su Yaya umar d in ya sauka, dukkaninsu suka nufi wajen fitowar su kowa fuskar shi d auke da fara a.



Kyakyawan matashin dake tawowa, ya d auki hankali duk wata mace dake wajen, kallo ya koma kanshi hatta su Ummi da Asiya ido suka zuba mai.





 A hankali yake taku cike da nutsuwa, gayu da kuma izza, taku yake na cikakkun maza, masu kwarjini.



 Duk irin kyawun Master dasu Ummi ke fad a bai kama ko k afar wanan matashin Saurayin ba.





 Nikam Ummi wanan kamar yaya fa.



Asiya tafad a tana kallon yanda yake tunkarusu.



 Ni banga kama ba amma dai gashinan yana yin inda muke.





Murmushin da Yasakar musu ne yasa Asiya daka uban tsalle tare da fad in.



 Yayahhhhh.



Tayi kanshi da gudu tare da rungumeshi, shima kuwa ya rungume ta tare da fad in.





 I missed you lil.



Cikin sasannayar murya dake fitar da kowanne harafi na turanci.



 i Missed you more Yaya.



Cigaba da  tawowa yayi hankalin yan mata nakasan su Mussaman da sukabi Asiya tace Yaya, dawasu har sunfara jin haushin ta sunyi tunanin Saurayin tane ko mijin ta.



A haka yak araso har inda Ummi take, Kallon ta yayi sanan yace.



 Masha Allah yara duk kungirma, ina mai gidan nake.



Dariyar yak e Ummi tayi domin tun zuwan shi wani abu ya mak e mata arai sanan cikin rawar baki tace.



 Batare muke ba.



Dariya Asiya tayi sanan tace.



 Ni baka tambayi nawa mijin ba?.



 Ke ai nasan bakiyi Aure ba.



Yafad a suna cigaba da tafiya zuwa inda motar su take.



 To ita wayace maka tayi Aure?.



 Ai da zantafi nasan tana relationship da Master yake kowa and nasan is hardly su rabu bayan wanan soyayyar.



 Basu rabu ba Yaya amma har yanzu basuyi Auren ba.



Asiya tafad a dai dai lokacin da take bud e masa boat domin su sa akwatin shi.



Kallon Ummi yayi sanan yace.



 Ummi gaskiyya tafad a.



Ummi data kasa sakewa ce ta gyad a kai alamun Eyh.



Sai da suka shiga motar sanan yak ara cewa.



 To yanzu yaushe ne Auren.



 Yaya kacika tambya ko so kake a had e da naka auren.





 Kawai ina mamaki ne, amma i know definitely something happened.



 Nothing happened yaya gashi ta koma ma kamar kurma da sai tabaka labarin.



Ummi dai batasan meke damun ta ba, hakan yasa ta zab i yin shiru, har suka k arasa gida.



Mutane sun hallara A Gida anata murnar dawowar Yaya Umar, Ummi dai tarasa meke damunta, amma ta lak ana hakan da rashin jin Mastet da tayi tun safe.





A hankali ta salub e ta koma nasu Gidan,sanan tasamu kiran Master dake zaune bayan shiga da Zainab d akin theater.



Yana ganin wayar amma yakasa d auka gaba d aya tausayin Zainab yacikashi, yana ganin kanshi mai butulci, wanda yayi watsi da rashin lafiyar ta ya shiga neman Ummi.



Haka taita kira baisami d auka ba ganin tayi masa kira sama da biyar, sanan ta hak ura tare da kwantawa.





*********************





   Affan nayi magana da Mahaifin yarinyar nan amma yanuna baisan da wanan magana ba, wai su sunjanye baikon su.



Hajiya Balki ce tayi saurin cewa.



 Toh Amma Alhaji haka zaka tsaya, bazaka nuna mishi power ba?.



Murmushi yayi sanan yace.



 Hajiya naso nayi haka amma Alhaji idi yahanani sakamakon ko da anje kotu basu da wani abu da za a iya, tunda basuyi auren ba.



 But Daddu gaskiyya ni inason ta.



Affan yafad a, kallon shi Abban yayi sanan yace.



 Kana sonta ka tafi kabarta na tsahon shekara Hud u?.



 Dad komene yafaru ya riga yafaru kawai ni kayi magana inason ta.





 Daman fa Alhaji zance a hak ura bai taso ba ainaga bamu amshi kud in auren ba ko?.



Hajiya Balki tafad a domin ita duk abinda d anta keso tofa tana sonshi.



 Hajiya ni nagama magana, kuyi duk yadda zakuyi idan wani abu yataso sai ku nemi ni.



Abba yafad a tare da tashi, Affan ne ya matso inda take tare da cewa.



 Mom yanzu mene abun yi please?.



 Affan karka damu yau zanje nasamu mahaifiyar ta.



 Okay Mom please.





******************************





 Hinin ranar Ummi bata samu Master a waya ba, abinda ya matuk ar tayar mata da hankali tare da sama damuwa, baya ga yanayin ta datake ji badai dai ba.



  Asiya ce dake zaune gefe tace.



 Wai yanzu Ummi mene abunyi ko tashi zakiyi muje mune meshi.



Dariyar yak e Ummi tayi sanan tace.



 Lallai Asiya sai kace yarinta zan koma neman master, ai sai dai yadawo da kashi.



 Dariya Asiya tayi sanan tace.



  Lallai yanzu nasan kinzama mutum.



 Au da ba mutum bace.



Ummi tafad a tana nuna kanta, dariya Asiya tayi sanan tace.



  Eyh da muna mutum ce yanzu kam nasan ko da Master yak ara tafiya ba abinda ake fata ba, bazaki damu ba, ko shiga wani hali.



 Dariyar tayi sanan tace.



 Uhm ayi sha ani kawai, amma banjin zank ara zurmawa a soyayyar har na k arasa Kuskuren yin TUDU AKAN KWARI wanda har yanzu yake bini shekaru Sama da biyar.



K arar shigowar text a wayar Asiya ne yakatse musu hirar tasu, dauka Asiyan tayi bayan tagama karantawa sanan tace.



  Ummi bansan mai Nawfal yake nema ba fa, wai yanaso muhad u muyi magana.



 Uhm koma mene zamuji amma nasan Nawfal sonki yake.



  Ummi tafad a tana d aukan wayar ta tare da kunna data ko zata sami messages daga Master.



 Sona fa, shi yanzu har yayi healing daga rashin ki.



 Ummi bakisan ana iya canja so daga wanda kakeso zuwa wani dayake kusa dashi ba?.



 Bansani ba sai a bakin ki kuma banyarda ba.



Dariya suka fashe da ita sanan Ummi tace kice masa yazo yau, kinga ko ma mene sai kiji.



Danna wayar tayu tamayar mai da reply.



************************



 Anfito da Zainab daga theater kuma ana saran samun nasara.



 Dr Shirza ne ya kalli Master dake zaune a cikin office d in shi.



  Mr Mukhtar Inaso kafad amun komai dake

11 / 13