TUDU A KWARI BOOK COMPLETE BY (LEGENDS PEN).txt

Author :  Legendspe Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   4 / 13

9K to 12K   out of 36.3K words

tayi ba ganin Master inda tabarshi, sai dai wanan karon da yaran sa bashi kad ai bane, a hankali ya k araso inda take sanan yace.



      Asiya zan tambaye ki, ki fadamun duk gaskiyyar da kika sani kada kiyimun k arya, meya faru da Ummi?.



Zama Asiya ta zaiyyane wa Master duk abinda tasani. sanan ta jaddada masa sunan Tsalha domin ita fa duk sabon da sukayi tsoron Master take.



    Daga nan kai tsaye gida Asiya ta nufa, tana Allah Allah ta shirya ta nufi gidan su Ummi domin tana son su gama duk wata shawara a yau, da sallama tashiga cikin gidan, sai dai rashin amsawar da akayi mata ya tabbatar mata da Mahaifiyar ta bata nan.



     Anty ce tsakar gidan tana zaune kan turmi, bawani kaya bane a jikin ta d aurin kirji ne, domin anty ba ma abociyar saka ya bace, duk yawon da zatai cikin unguwa da wanan d aurn kirjin sai hijabi, gata irin mai rushe shen jiki ce amma haka take yawo. da anmata magana sai tace ba aure gare taba, indai kaga anty da complete kaya to unguwa ta nesa zata, amma ko gidan iyayen ta ko shiga cikin kasuwa haka take yawo.





     Ke ubanki wakike wa wanan kallon? shegiya mai kama da d inya.



   Anty tafad a tana zabgawa Asiya uwar harara, Asiya bata ce da ita k ala ba ta huce. domin daman Ummi ce ke tanka mata.



   Halima ce tafito daga cikin d akin su tana sanye cikin d inki doguwar riga ta lace da ta kame jikin ta sosai da sosai, ˜afar ta tana sanye cikin uban heels din takalmi, sai uban kamshi turare take yi.



     To kema Umma kya kula wanan shegiyar yarinyar, tana ji gidan ubanta ne kuma sun cinye shi a gado.   Halima ta fad a tana tunkaro inda Anty take.



    ke halima kyaleni inci ubanta, Uwar ta ma haka muka buga da ita ta kyaleni balle kuma yarta.

     

  Dan Allah Anty kyale yarinyar nan, ki kalle ni.   kallon ta anty tayi sanan tace  naganki.



  Zan fita. Ta faWa tana kashe ido  zuwa ina?.

 Nema. Taba ta amsa tana fara tafiya

 to Allah ya tsare hanya. fitowa Asiya tayi zuwa gidan su Ummi.  To gantalalliya. An fice kenan.



 Gantalalliya ba tahuce wacce tafita yawon ta zubar ba. A  gaban Uwarta har tana cewa a tawo mata da tsara ba. Asiya tafaWa  tare d ficewa.   Wallahi sainaci uban ki, shegiyar yarinya mai kama da Winya.







~~~~~ Zaune suke cikin Wakin Ummi. kasancewar Hajiya batanan ya basu damar sakewa suyi magana.  Ummi ki yiwa kanki faWa, ki nema wa kanki sau™i, ki nema mana.  na tambaye ki wani abu mana?. Šaga kai Ummi tayi alamun ina jinki.  Hajiya tasan da Master kika tsaya?. Girgiza kai Ummi tayi.

 Amma tayi miki wanan dukan? to kisani Ummi duk randa hajiya tasan da Master kike tsayawa, wallahi abunda zatai miki sai yafi wanan, karki ga Abba yana supporting nake wallahi ko shi yasan da Master kike tsayawa Ummi zaki ji jiki.



 Asiya kamar bikin sa soyayya ba?.



 Ta ina zan santa nida ban taSa yi ba.



 To Asiya kifita daga lamarin soyayyata dan Allah.   Shiru Asiya tayi domin taga ne gaba Waya Ummi taga ma tafiya akan lamarin Master.

 

~~~~~ Washe gari ma Ummi bata samu damar zuwa makaranta ba. Hajiya ta hana ta haka sukai ta fama har tsawon sati guda.



     Gaba Waya Mukhtar yafi ta haiyyacin sa,ya shiga damuwa, tunani yayi masa yawa, abinda bai tab a ba a rayuwar sa kenan damuwa akan lamarin wani, tun tasowar sa har zuwa girma da rayuwar sa amma gashi ya shiga akan Ummi yashiga damuwar da bai tab a ba, shiga irin ta ba, idanuwan sa kullum zafi suke masa. Ummi kawai suke son gani, Zuciyar shi kullum zafi take masa, Ummi take son gani. A yanzu ko yayi shaye shayen na sama na lokaci kad an ne, tunanin yake dawo wa cikin zuciyar sa. Har takai da ya fara sambatun da kiran sunan Ummi da daddare.

         



     Yau takama monday. Ummi ta sami damar zuwa makaranta, domin yin temprint. Sanyw take cikin bak ar doguwar riga ta abaya, tayi rolling da jan mayafi, tana sak ale da jakar rataye ta zuwa unguwa. Domin sunyi magana da Abba zata biya gidan Anty Nafisa, dan har yanzu Hajiya ba sakar mata fuska take suyi magana ba.



      Asiya ce tafito daga naso gidan itama tana sanye cikin doguwar rigar lace tasa k aramin veil mai kyau, yan mata da sukeji ta tashe da kyau ga ilimi, domin dukkan su ba banza ba suna da k ok ari sosai afanin boko da arabic,

rankayawa sukai suka nufi makaranta, Ummi sauri kamar ta tashi sama domin tabbas tasan yau zata had u da Master nata, Mutumin da ta tabbatar wa da kanta shine mahad in farin cikin ta.

         ki rage wanan saurin karkije ki fad i.

  Asiya duk randa kika k ara cewa na rage sauri akan lamarin Yaya Mukhtar,wallahi sai namiki rashin mutunchi.  

     Ummi taba wa Asiya amsa tana cigaba da saurin ta , tab e baku Asiya tayi sanan tace

    ki kamo gobe ma.





  page[11&12]



      Tsyawa Ummi tayi ganin sun k araso wajen da suka saba had uwa da master, Asiya kam gaba tahuce domin bata da niyar tsaywa,ta cire hannun ta akan lamarin Master da Ummi tunda ta fuskanci kamar Ummi batason tana shiga lamarin

        Asiya ina zaki.

kallon ta Asiya tayi sanan tace 

      Tafiya zanyi mana Ummi mai zan tsaya nayi.

       wai ke Asiya mene haka,sai kitafi ki barni anan?.

        kinga Ummi na fuskanci ba b ukata ta kike akan lamarin ki ba nacire hannuna gaba d aya sai dai nayi miki fatan nasara.

    daga haka Asiya takama hanya ta huce, tsayawa Ummi tayi tabbas bata kyauta wa Asiya da take hantarar ta akan lamarin nan,amma gani take kaman bata son soyayyar ta da Master dane gaba d aya,itakam duk wanda zaiyi tunanin raba ta da Master sai inda k arfin ta yak are, (tana wanan tunanin ne roget yaron Master ya samu damar yi mata way anan hotonan da master ya tura  mata a office)

        bata fargaba sai mutum tagani a kusa da ita, wani lallausan murmushi ya sakar mata,irin wanda kwana biyi yake gani a mafarkin da takeyi. 

     a hankali ta mayar masa da martanin murmushi sanan tace 

       Yaya.

 Meenah i missed you.

       missed you more yaya, dan allah kar ka kara nisa da gani na.

     insha allah, Ummi dan allah kiyi mun alkwari kasancewa tare dani har abada.

     hannunshi ta kama ta d ota a saman nata sanan tace 

     yaya a ko yaushe ka tuna da wanan alk warin dani Ummi ka d auka, duk tsanani duk wuya ina tare da kai,ina tare da sonka.

       murmushi yasake sanan yace 

 nagode sosai Ummi naa, nima nayi miki alkwarin zaka sance bango a gareki, zan kasance t sanin da zaki dinga takawa a ko yaushe, zankasance fitila mai haskaki a ko yaushe, Ummi ina sonki da dukkan rayuwa ta, Ummi kece macen da nafara so a rayuwa ta, banta b awa wani tarihin rayuwa ta ba amma Ummi yau zan baki.

        tafiya suka farayi sanan Ummi tace ina sauraronka

      Da farko sunana Mukhtar Adam Mukhtar haifaffaen garin jigawa,mahaifina d an asalin garin kano ne amma zama yakai shi jigawa inda anan yake aikin shi,mahifiya ta yar asalin dutse ce anan suka had o da mahaifina sukayi aure,haihuwata da kwana d aya allah yayi wa mahaifiya ta rasuwa, inda k anwar mahaifiyata Anty Halima ta k arbe ni, Anty halima itace macen da nafara so kamar Uwa ina sonta a  matsayin mahaifiya duk soyayyar  da d a yakewa mahaifi Anty Halima na keyi wa.

    na tasu cikin gata daga wajen Mahaifina,Anty Halima da kuma Abba mijin anty halima, ina da shekara Uku Allah yayiwa mahaifina rasuwa daman kuma baiyi wani auren ba bayan rasuwar mahaifiya ta, kasancewar a garin jigawa muke bansan wasu dangin mahaifina na nan kano ba haka itama mahaifiyata ita da Anty halima kawai iyayen su suka haifa,family din su ba irin mai yawan nan bane, suma su biyu ne a wajen iyayensu kuma sun rasu, ita kuma Allah baibata haihuwa ba.

     Anty Halima da mijin ta suka cigaba da rik eni yanda suke mun har zuwa lokacin da yan uwan mijin ta suka sashi a gaba sai yak ara aure,Anty Halima ba tadamu ba nima kuma banda mu ba,ana haka Abba ya auro Jummai wata me siyarda awara anan farkon layin da muke, tun shigowar Jummai kasan da tashin hankali ta shigo domin Anty Halima bata kula ta ba,sai taita sababu da surutu dana fito waje zata k wad eni to anan Anty Halima zata kulata itakuma ta sami abinda take so, ana haka Jummai tasame ciki,nan fa Abba ya maida duk wata kulawa kan Jummai duk da bawai ya daina kula da Anty bane amma ya canja yamaida kaso 80 na kukawar shi ga Jummai anty kuma kasu 15,wata rana na shigo d aki na tarar da Anty ta na kuka,ba dinga tambayar ta meyafaru tace bakomai.

       Kukan dana ga Anty nayi yasani a damuwa har nakasa bacci gaba d aya, cikin dare naji Anty tana addu a akan Allah yabata haihuwa,tun daga lokacin nima nafara tayata addu ar ana wanan zaman ne Jummai ta haifi yar ta mace wacce aka sakamata Lahira sunan Maman Jummai ne.

     Abba yad auke kaso 15 din kulawar dayake bawa Anty ya k ara mai da ita kan Jummai ya zamana ni da Anty munzama yan kallo a wanan gidan,tun a wanan lokacin na taso da tsanar Jummai,Lahira har da Abba haka mukayi tazama nida anty har bayan shekara biyu fa haihuwar Lahira .

     Nadawo daga wasa kawai naga Jummai tashiga wani shago Musa mai kayan miya wanda dama mak wafcin ta ne sanda take siyar da awara,lokacin banfi shekara 7 dan haka banyi tunanin abunda suke ba kenan kawai dai a yanayin da tashiga yasa na gane ba abin gaskiyya zasu aika ta ba, ko da nasar da Anty sai tace k arya nake dana dage da rantse rantse sai tace ba ruwana.

    bayan sati biyu naje makarantar dare da mukeyi sau naji yan wasu ajina ana musu bayanin akan bai hallarta mace ta kwanta da namiji wanda ba mijin taba ko tashiga d akin wanj namijin hakan yasa na d auki alwashin sai na tonawa Jummai asiri ko Abba zai rabu da ita yadawo wa da Anty farin cikin ta (ban san cewa zanyi TUDU NE AKAN KWARI  wanda zai tarwatsa duk wani farin ciki a rayuwar da nake ciki ba,wanda zai juya sama ta ta koma k asa)

           Ranar talata da bazan manta da ita ba nadawo daga wanan wajen wasan da nake zuwa naga Jummai ta shiga wanan d aki, kai tsaye na nupi wajen sana ar Abba nace yazo ba lafiya a gida a kid ime ya biyoni shida abokan sa guda biyu sunje nace ba lafiya yasa suka yo mai rakiya dai dai shagon Musa na tsaya nace ya shiga ciki,tsayawa yayi yana cewa  ina ne nan, me zanyi a ciki. gyad a kai nayi sanan nace 

       Abba ba lafiya kashiga ciki.

jin haka yasa d aya daga cikin abokan nasa danna kai yashiga sai dai fitowad da yayi a guje yasa su abba tambayar shi ko lafiya,rike Abba yayi sanan yace 

   bazaka shiga ba kai haladu shiga kagani.

     d aya abokin nasu ne yashiga shima ya fito yana maimaita innullahi wa inna illahir rajiun 

     a kid ema Abba ya fusge ya shiga sai dai shirun da sukaji yasasu ka bi bayan shi.

   a kwance suka tarar dashi alamun ya suma, Jummai kam iyhu ta fashe dadhi da fad in 

     nashiga uku ni jummai na shiga uku. sanan ta nuna ni da yatsa tace 

     yanda kazama sanadin tonuwar Asiri na wallahi sai nazama sanadiyyar to nuwar naka asirin.  

    da k uruciya bangane me take nupi ba aka kama Abba aka fita dashi zuwa chemist,kai tsaye nayi gida domin sanar da Anty sai dai mutane na gani a k ofar gidan sunyi carko carko wasu suna shiga wasu nafita, da gudo nayi cikim gidan sai dai ji nayi anrik e ni.

    wani b akin mutum dogo da alaman d an sanda ne domin nagane shi ana kiran shi da Judge da k arfi na fusge hanuna sai dai ya rik eni da karfi yanda bazan iya k wace wa ba tun ina fushe fusge har na nutsu domin a yanda nake ganin ana fitowa da gidan cikin tashin hankali dole nasan wani abu ne yafaru.

    Ana haka wata k awar Anty tafito,kallo na tayi sanan tace Mukhtar zo nan,cikani yayi natafi tare da cewa 

     Adda me yafaru a gidan mu.

  cikn rauni da sanye ta ce 

      Mukhtari sai hak uri Allah yayiwa Halima rasuwa.

    kamar anbuga min guduma haka naji maganar tata sai dai maganar da naji ana fad a ta dawo dani daga fad uwar da nake shirin yi 

     aka kashe ta dai ko, kai Jummai ce takashe ma Uwa gata can yan sanda zasu tafi da ita.

     ban k arajin komai ba natafi k asa sumamme, sai dare na gane inda nake lokacin har abinne gawar anty ita kuma Jummai yan sanda sun tafi da ita, gida ya rage dagani sai Abba.

     Bayan kwana uku da kashe Anty Abba yafara wata rashin lafiya sakamakon Musa yagama fad an duk wata gaskiya domin tun kafin Abba ya aure Jummai suke tare har sukayi aure,yarinyar ma da akace yar Abba ce ashe yar wajen Musa d in ce,wanan abu ya k ara tashin ciwon nashi,kwanan sa biyu yana jiya Allah yad auki ransa sai dai kafin ya mutu sai da ya damk a amanata a wajen d an sanda abokin sa wanda shine sanadiyar duk kasancewa ta a wanan hali,Ummi nasha wahalal rayuwa mai yawa a hannun wanan mutumin,nasan zafin maraici a hannun wanan mutumin,naga mummunar rayuwa a hannun wanan mutumin,Ummi k arshe nina kashe wanan mutumin.

     juyowa Ummi tai ta kalleshi inda shikuma ya d aga mata kai alaman eyh

     to garin ya? kuma wace kalal azabar rayuwa kasha a wajen sa.

       Ummi zan k arasa miki amma ki gama da makarantar nan,inda zamu tafi sai na baki.

     toh kawai tace sanan takama hanya ta shige cikin makaranta,zuciyat ta fal da tunani kala kala a game da rayuwar Master,wanda ya k arawa soyyayarsa girma da k arfi a cikin zuciyar ta.

     Ummi ba su gama da makaranta bs sai wajen k arfe 04 hakan yasa bata samu biya gidan Anty nafisa ba,kai tsaye gida suka dawo tare da Asiya wacce tabata duk wani labari da Master ya bata, sosai tausayin Master ya shiga zuciyar Asiya itama a wanan karon, a haka suka k araso gida inda ko wacce ta shiga nasu gidan.

     kamar ko yaushe da sallama Ummi tashiga cikin gida, tayi mamakin kin amsa sallamar da Hajiya tai mata duk da tasan bawai sakar mata fuska take ba saidai tana d an amsa sallamar ta da gaisuwar ta,d aki tashiga jiki ba k wari ya hau canja kaya, sai dai sallamar Goggo da tujiyo ya matuk ar tsorata ta a fili tace.

     Me yakawo wajan jarababbiyar matar kuma.

 Goggo kam fad i take 

     Sahura ina yarinayar nan,.

   Tana fa ciki Goggo itama yanzu ta shigo daga yawon zancen nata.

     Hajiya ta bawa Goggo amsa, Zama Goggo tayi sanan tace 

     Bari shi yazo idan tsoron ta yake mu ba tsoron ta muke ba,ta turo shi yaron yazo ayi musu aure.

      Zai dai fi Goggo,tunda yarinyar nan ba tsoron baccin ran mu take ba, duk kwanakin da na d auka bana mata magana a banza, yau tana fita sai da ta tsaya a wajen sa.  

       innullahi wainna illaihi rajiun.

Ummi ta fad a tare da d ora hannu akanta,wanan wane irin mai sa ido ne yake mata wanan mummuna binciken?

      ba kyajin Goggo tazo ne, ko ita zata shigo ta gaisheki rik ak iyya?.

       Hajiya ta fad a daga nan tsakar gidan

 kaya nake cirewa.  

Ummi tafad a a ranta tana cewa kamar Hajiya ce yar Goggo sabida yan da halin su yazo d aya.

     jiki ba k wari ta gama cire kayan sanan ta canja zuwa riga da wando kasancewar yanayi zafi da ake fama dashi, haka ta fito tsakar gidan kamar mara laka a jiki,daga nesa ta tsugunna k asa tare da cewa

     Goggo sannu da zuwa,ina wuni.

 ke za ai wa sannu,uhm uwar masoya. Googo tafad a tana tab e baki,kallon ta Ummi tayi a ranta tana cewa wanan tsohowa da kinibibi take, kitchen Ummi tashiga ta zuba abinci, tana cikin ci Abba yashigo gidan sakamakon kira da Goggo tasa Hajiya tayi masa, sai da suka gaisa da Hajiya sanan tace

        Kaga Kamalu a matsayina na mahaufiyar ina baka Umarni akan cewa maza maza yarinyar nan tafito da miji ayi mata aure,domin bazan zauna ka zuba mata ido ba tunda ta zab i kule kule maza.  

       aure kuma Goggo duka duka yaushe Ummin ta ta girma.

    Abba yabata amsa cikin tausasawa 

 to indai bazaka yi mata aure ba inaso a yanzu a gabana ka haramta mata kula kowanne namiji,fita indai ba muhimmiya bace.

    daman wanan shine plan d in da suka shirya da Hajiya

    gyada kai Abba yayi sanan yace

   toh Goggo.

Ummi ce ta tareshi da cewa 

  a ah Abba nazab i ayi mun auren.

kallon ta sukayi gaba d ayan su, Hajiya cikin t sananin tashin hankali tace

      Ubanki Ummi nan zaki zo kiyi mana maganar banza.

       Hajiya akan kuce zaku rabanj da Yaya Mukhtar gwanda kuyimun auren kawai.

      Au har yazama yayanki? wace uwar ce ta haifa masa ke?.

     Abba ne ya katse Hajiya da cewa

  Saliha me kikeyi hakane?. sanan ya juya ga Ummi yace

       kinsan abinda kike fad a kuwa?,Aure ba abu bane na wasa Ummi, sanan ba a kowane mataki ake yiwa yarinyar aure ba,bikiga yayarki Nafisa ba, saidai ta kammala diploma a k aramar jami ah,sanan akayi mata aure,kuma bikiga wanda ta aura ba?, mutumin arziki duk sanadiyar tayi ilimi ne.

           Abba nima

4 / 13