TUDU A KWARI BOOK COMPLETE BY (LEGENDS PEN).txt

Author :  Legendspe Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   7 / 13

18K to 21K   out of 36.3K words

da sauran yan Uwa duk sun k araso, Hajiya tafita hayyacin ta domin gani take kamar itace ma takashe Ummi ko saka ta a halin da take ciki,sauran mutane kam sunyi jigun jigun domin babu wanda yasan mak asu din rashin lafiyar idan ka cire Asiya.

   Asiya kam a yanzu bata iya bud e baki, domin iya kukan da tayi anan wajen yasa mata mat sanan cin ciwon kai wanda har yakai bata iya ko motsi da kan.

    Umar kam bayan ya samu musu mai mota ya koma gida yayi wanka,shine yatawo da asiya a machine dinshi bayan ya biya ta gidan Anty Nafisa ya sanar da ita



***

    Badoo bai b oye komai ba yasanar daRogeet halin da yaje ya sami Ummi,sosai Rogeet yake mamaki duk da yasan bazai huce mahaifan Ummi sun hana Master bane, shine dalilin da yasa suka kasance cikim wanan halin gaba d aya 

    Yanzu Rooget menene abun yi?.

Badoo yafad a domin yanda yake ganin Master kwance yasan dole sai ya buk aci ganin likita

     Kaga Badoo tun d azu nake ta trying lambar Dr Affan amma baya d auka, inaso nasanar dashi ko shi zaizo gida ya duba shi ko nan asibitin zamu kawo shi.

     To yanzu ka k ara gwada lambar idan batayi ba kawai ku d auke shi dan gani nake wanan kamar ba bacci yakeyi ba.

  k ara gwada lambar yayi amma still bai d auka ba

     Tashi mu tafi asbitin kawai.

Rogeet yafad a yana mik ewa isar su  asibitin yayi dai dai fitowar su Dr Affan, daga d akin da Ummi take ciki

     Dr Affan ne yace da Abba

 Yanzu Alhamdulillah insha allahu zuwa anjima zamu k ara komawa,kawai ku cigaba da Addu a.

   Shiru Abba yayi da duk kansu ma gaba d aya kowa jikin shi ya mutu

    Wucewa Dr Affan yayi zuwa office d in shi, sai dai bai k arasa shiga cikin office d in ba aka shigo da Mukhtar shima kwance kan gado ana faman turashi, Rogeet ne ya k araso inda Dr Affan ya tare da fad in 

     Dr ina ta kiran ka baka samun damar d agawa ba, Master ne gashinan kwance rai a hanun Allah.

    Kallon gadon Dr Affan yayi sanan yace

 Meyasa meshi haka?.

    Wallahi bamu da masaniya.

Bin gadon Dr Affan yayi zuwa d akin dake kusa da na Ummi, basu sha wahala ba akan Mukhtar kamar Ummi ba,sabida shi ciwon shi mai sauk ine.



***

   Sai bayan Azahar Affan ya samu nutsuwa bayan ya koma gida yaci abinci ya sake wanka, Rogeet yakira zuwa office d in shi

    Isa mene ya same Mukhtar?.

 Wallahi Dr bana ce ba amma dai nasan Master yatafi gaida sirikan shi ne.

   Kallon shi Dr Affan yayi sanan yace

 Wane sirikai kuma?.

   Nan Rooget ya hau bashi labarin tun daga soyayyar Mukhtar da Ummi har zuwa kiran da tayi masa akan iyayen ta nason ganinshi gar zuwan da yayi da kuma daowar da yayi sanan ya gaya masa abinda Badoo ya gano da safe gidan su Ummi

     Ummi kace?.

Dr Affan ya tambaye shi d aga kai yayi alamar Eyh 

    Shikenan tashi kaje idan yatashe sai kusan yanda zaku kula dashi.

   Tashi Rogeet yayi yafice shikam Dr Affan tunani yafara tun daga haduwar su da su Master irin taimakon da Master yayi masa lokacin da wani abokin fad an shi na makaranta yasa akashe shi,Allah yakawo masa su Master suka kwace shi, tunda ga wanan lokaci yake taimakon master ta ko ina har zuwa san da yafara aiki.

         Zuwa yamma Master ya samu ya farfad o, amma b angaren Ummi kam abun ba a magana, gaba d aya mutane sun fara fitar da rai da Ummi har dasu likitocin ma, babban dalili bugun zuciyar ta ma k asa yake k arawa lokaci zuwa lokaci, wanda shine kad ai abinda ya ke nuna cewa Ummi na da rai.

    

***

   Washe gari

A yanzu kam za ace jikin Master yayi sauk i domin har abinci yana iya ci sai dai gaba d aya tun da ya tashi babu zancen da yake sai na

     Ummi na tuba,Ummi zancanja hali.

 Dr Affan ne yasashi a gaba ya tambayeshi wace Ummi,wand tuba yayi.

    Master bai b oye masa komai ba yagaya masa tun daga soyayyar shi da Ummi har abinda yafaru last

    Dr Affan tun a lokacin yagane Ummi itace patient dinsa domin sai da yak ara tambayar Mahaifiyar shi bayanai akan Ummi.

    Hajiya Balki kam ba shiri ta bud e baki tafara zayyana mai domin ita a tunanin ta yafara tausayin yarinyar ne.

      Domin alak warin dasu kayiwa juna ita da Saliha na auren yaransu, amma gaba d aya yaran suna neman karya musu alk wari.

      Dr Affan yaji dadin yadda Master yafara tunanin canja hali, sanan a ranshi yad auki alk warin indai Ummi ce Master sai ya aure ta

       B angaren Ummi kam haka za ace gwanda jiya akan yau,domin gaba daya jikin nata k ara saki yake.

   

***

     Oh ni! kai cona kai con rayuwa ta, nasa jika ta a masifa sabida son duniya.

    Goggo dake zaune cikin taron mutanen dake cinjiyar Ummi take fad a

    Babu wanda ya kulata domin gaba d aya a yanzu kowa yayi sanyi ba mai iya magana.

    Jin shirun da sukayi yasa Goggo dagowa ta kallesu Hajiya ta had a uban tagumi, Anty Nafisa na zaune ta had e kai da gwiwa, Mama na zaune tana jan carbi, Asiya na zaune tasa kanta a jikin Mama.

    Bud e baki tayi da niyar yin magana,mai kawo abinci daga gidan Hajiya Balki yayi sallama tare da k araso wa wajen.

       Sannu d an nan da k ok ari baka gajiya da wanan hidima ta kawowa ita ma Hajiyar bata gajiya,kullum sai ankawo sau uku to allah yayi albarka.

   tafad a a jere kamar mai wak a

     Amin.

  yafad a mata a dak ile sanan ya kalli sauran yace

    ya mai jikin?.

 Da sauk i Musa.

Mama tafad a domin a zuw yanzu kowa yasan sunan shi sabida yawan kawowa da yake

     Allah yak ara Afuwa.

yafad a tare da hucewa bai ko kalli goggo ba

     

Page(21&22)





   Da daddare Dr Affan ya salmi Master sanan ya bashi shawarwari akan yadda zai gyara rayuwar shi da yan kud ad e.

   Haka suka koma gida, Master yakasa hakuri zaije ganin Ummi ko da gobe ne.

  Daga d akin su Master kai tsaye d akin Ummi yahuce domin duba ta.

    Sai dai yanda yaganta ya d aga mai hankali domin gaba d aya bugun zuciyar tata ya tsaya, babu wani abu dake nuni Ummi na da rai.

  A gigice yake duba duk wani abu da ya kamata amma ina abu yaki gaba yaki baya,

   Tabbas Ummi ta mutu.

   yafad a afili amma ta ina zaifara sanar da iyayenta, waya da dauka ya kira Mahaifiyar sa yasanar da ita sanan yakara da cewa

    Mom i m scared, bansan ta inda zanfara fad awa iyayen ta da yan uwan ta ba.

   cikin kulawa da tausayawa tace

 My son claim down kaji, kasa nurse takira maka Maman Asiya ko Nafisa insha allah zasu san yadda zasuyi, nima i m on my way.

    okay mom.

yana tsaye wata nurse tazo hucewa yasata ta kira mai ko maman asiya ko anty nafisa.

    Duka su biyun su ka zo cikin yan mintina

Mama na gani Ummi jikin ta yabata ita kam Anty Nafisa cewa tayi.

    likita gamu ta warke ko?.

yanayin rud ewar ta kawai yagani yasashi cewa.

    Ban dake fa Maman Asiya kawai akan rashin lafiyar Asiya ne.

    To ai nima rashin lafiyar Asiyan ta tab ani, baka ganin tare muke da mahaifiyar tata tun zuwan mu.

    Anty Nafisa tafad a,kallon Mama yayi sanan yayi mata alamu da ido akan ta kori Anty Nafisa.

    Kinga Nafisa jeki, barni nayi magana dashi.

  tashi Anty nafisa tayi tafice, kallon Mama Dr Affan yayi sanan yace

    Mama ga Ummi nan babu rai.

A razane ta kalleshi

     Me hakan ke nupi?.

 Mama nasan ke zaki fi fahimta yasa na kiraki, Ummi sai dai ayi hakuri.

    Innullahi wa inna illahir rajiun.

Mama tafad a tare da samun waje ta zauna.





    A hankali take takowa,kana ganin yanda take tafiya kasan tana cikin wani hali ko wata damuwa, a haka ta k araso inda suke zaune.

   

    Anty Nafisa da tadawo ta daga masu hankali ce tace

       Ku ga yanda take tafiya! kuga! Wallahi Hajiya wani abu yafaru.

  

       Nafisa dan Allah ki nutsu ki bari ta k araso mana.



Wata k awar Hajiya tafad a, kallon ta Goggo tayi sanan tace

       Ke Tsibatu banason shishigi! wace nutsuwa zatayi yar uwarta na kwance asibiti.

   Daman Goggo haushin natar take ji tunda tazo ta k i tabarta ta d ibi abuncin da takawo wanda yaji uban nama

         Sahura lafiya dai ko?.

Hajiya tafad a domin tabbas yanda taga Maman ya matuk ar tsorata, Mama ba takai ga bud e baki ba suka jiyo muryar Hajiya Balki wacce Affan ganin kamar Mama ma tashiga tashin hankali yasa shi k ara kiran Mahaifiyar tasa, inda tace masa tana dab da shigowa asibitin domin tabbas tasan halin da Sahura xata shiga idan tasamu labarin cewa Ummi ta mutu.

     K arasowa inda suke tayi tare da cewa

 Sahura samu waje ki zauna, ko me za a fad amiki ai ba zai kamata a fad a miki kina zaune.

      

      Dan allah Balki mene ne? Sahura mene yafaru dan Allah?.



    Hajiya tafad a tana kallon su duka, Hajiya Balki ce taje ta rik e ta tana cewa



    Saliha dan allah ki zauna ki nutsu, ko ma menene ai zakiji ko.



ihun da Anty Nafisa ta saki tare da zubewa k asa ne ya dawo da hankalin su kanta,dai dai lokacin da Asiya ma ta zube tare da fashewa da ihu.



   Wai ashe aljanin su ne suka zo yi musu jaje



 Innullahi innullahi, subhanallahi subhanallahi, auzubillahi auzubillahi.

    Goggo tafad a tana mik ewa tsaye 

 Wallahi yarinyar nan mutuwa tayi tunda kika ga wanan yaran sun zube kamar rak umai, bana manta sanda babban mutum ya mutu wanan yarinyar ita tafara wanan ihun. tafad a tana nuna Anty Nafisa

      Nanfa asibiti ya rud e da koke koke har wasu ma mak waftan su su ka taya su zubewa kun san aljanu da kara=ØÞ>Ø-Ý

    Dai dai lokacin dasu abba suka samu k arasowa cikin asibitin, zuwan su Abban ne yayi k ok ari wajen saita su har aka samu aka fara tafiya dasu gida kafin sukayi cike cike a tafi da gawar Ummi.

     Bayan sallah magriba kafin isha i wanan abu duk yafaru, kafin lokaci k ank ani labarin mutuwar Ummi ya karad e unguwa gaba ki d aya, sanan Anty tashiga gida gida tana bada ba asi wai.

     yarinyar ce takeson wani gagurumin d an daba shine Hajiya tayi mata duka har ta mutu.

   Kasancewar itama bata da tabbaci domin jita jita taji, amma mutum mai sharri, sai da tabi kowa tana fad amasa.

   A dai dai wanan lokacin labarin Mutuwar Ummi ya riske su Master,

   Innullahi wainna illahir rajiun, wata mummunar faduwa daMaster   yayi zuwa k asa, sai kayi tunanin kwakwalwar sa ta bugu,a sume ya k arasa k asa.



     Hakan wanan dare ya kasance daren kuka ga kowanne b angare gidan su Ummi da b angaren su Master.



   Washe gari akayi haka kowa ya tashi duk da basu samu bacci ba, sunyi kukan har sun gaji, ko magana basa iyawa har zuwa lokacin da akayiwa gawa wanka ka aka ajiye ta.

   WANAN SHINE ABINDA YA FARU







Page[23&24]





    To ai yanzu sabarni na aure wanda nakeso ko?.

  Ummi tafad a tana kallom Asiya bayan ta gama bata wanan labarin.



    Ummi ba wai ba ason ki auri Master bane dan ba a sanki, idan ta soyayya ce za a barki ki aure shi Amma Ummi ko tarbiyar yaranki a halinki.



  Anty Nafisa da tashigo yanzu ta fad a, 



Ummi bata ma kalli Anty Nafisa ba balle ta kula da Mutanen dake bayanta, ta bud e baki tace



    Daga sanda na Aure shi ya zama a halina,

    rayuwa ta, abunda ya shafe ni ba ku ba.



jikake taff! Hajiya ta k wad e Ummi da mari cikin fushi tace.



    Yanzu Ummi akan soyayya, akan saurayi kika zab i kigayawa iyayen ki magana,



 kigayawa yar uwar ki kwaya d aya da allah yabaki Ummi kinja tunani.



   Hajiya tafad a cikin kuka. Anty Nafisa kam tasowa tayi zuwa wajen Hajiya ta rungume ta tare da fad in.

   

   Kiyi hakuri yajiya, yarinta ce ke damun ta.



 Ba wata yarinta da ke damuna, nasan abinda nake, ku ya kyaleni da rayuwa ta tunda ta wace, banason shishigi ban shiga rayuwar mutum ba kar yashiga tawa.



     Wai Ummi mene ke damunki haka ne baki da hankali.



  Asoya tafad a cikim fushi da fusata



 Dalla malama fita daga sabgata kema banason shishigi rayuwar ku ce?.



   Ummi ta katse Asiya cikin nuna matuk ar fushi da jin haushi.



   Ba rayuwar mu bace amma Ummi muna da hakk in fad a miki gaskiya a kowanne lokaci.



   Rik e gaskiyyar ki Asiya, kifita daga rayuwa ta kibarni.

   

   Shiru Asiya tayi sanan daga baya ta mik e zata fice.



   Tabbas ko bakiyi nadamar fad amana bakak en maganganu ba a matsayin mu na iyayenki, zakiyi nadamar fad awa Asiya a matsayin ta na aminiyar da tazama yar uwa a gareki.



   Hajiya tafad awa Ummi lokacin da Asiya ke ficewa, Duk irin b acin rai da damuwa da Ummi ke ciki tabbas taji na dad i kan abinda tayiwa Asiya.



 Asiya kam nafita gidan su tayi kai tsaye tafad a d akin ta ta kwanta tare da fashewa da kuka.



 Haka Hajiya ta fice Anty Nafisa ma ta fice, Abba dake tsaye jikin d aki duk jikin shi ya mutu.



 Goggo ce ta kalli Ummi ta tab e baki sanan tace.



   Ke kam wanan yarinya kingama asara duniya da lahira.

  

   Mitcheww. Ummii taja dogo  tsaki



 Tsaka ma tayi ta gama.

Goggo tafad a tana ficewa.



Haka wanan gida gaba d aya suka kwana cikjn b acin rai da damuwa ,

mai makon su kasance cikin farin ciki.



  Washe gari tun safe Asiya ta gama had e kayanta tsaff, zatahe kaduna gidan k an war Mama kafin lokacin fara jarabawar su ta Waec.



    Wai yanzu Asiya bazaki je kiyi sallama da matar nan ba? itace tayi miki abu?.



   Wallahi Mama banson k ara shiga gidan a rayuwa ta.



Asiya tabawa Mama amsa bayan ta takura kam taje tayi sallama dasu Hajiya.



  Kinga Asiya tashi kije kiyi Sallama dasu kafin ranki ya b aci.



 HHaha daman duk wanda ya hau motar k wad ayi, karshe a tashar hulankaci zai sauka.



 Anty dake cikin d aki tafad a



 Yoo daman anty ai k arahen alewa k asa.



Halima tafad a itama daga cikin d akin



 Karshen bariki kuma da nasani.



Asiya dake zaune tabasu amsa, ai kamar kububuwa Halima tafito daga d akin tayo kan asiya tana fad in.



 Ke wallahi tallahi idan kina cin k asa ki kiyayi ta shuri, ni ba sa ar ki bace yanzu zan sa a b ab alla mun ke.



Mama bata ko kallesu ba, domin tasan a tanzu Halima ba fad awa Asiya magana zatayi tai mata shiru ba dole sai ta dama, dukane kuma wanan ba ta isa ba tunda dai ita tashiga sabgar ta.



   Aou Ashe badad i kenan?.



Asiya tafad a cikin sigar rashin kunya, 



 To k arya akayi miki da zaki ce ashe ba dad i.



Anty dake fitowa daga cikin d aki tafad a cikin hargowa.



   To nima k arya nayi?! ba k arshen bariki da nasani bane.



 Ya isa Asiya tashi kifice.



Mama ta dakatar da ita



 Tashi Asiya tayi tafice tana gunguni a ranta tana sanye cikin doguwar rigar lace tayafa k aramin blue d in mayafi.



 Atine nasha fad a miki kifita sabgar yarinyar nan kunk i ko to zanyi maganin ku.



 Kiyi maganin namu gida ne ko, insha allahu mun kusa tashi mubarmuki tsiyar ki.



Anth tafad a tana jan hanun Halima suka shige.



 Halima ki takura wa wana mutumin yabaki gidan nam mu koma ko masa mu mu huta da gori.



Anty tafad awa Asiya cikin k asa kasa da murya.



 Ai Anty yau ko gobe.





  A soro Asiya  ta cika karo da Yaya Umar, Kallonta yayi sanan yace.



   Yanzu Auta kin dage yau zaki tafi, baza kijira gobe muyi sallama ba?.

  

   Yaya ai yanzu ma munyi sallama, sanan kai zaka kaini har tasha.



  Asiya chaina fa zantafi, ba tafiyar kasuwanci ba tafiyar karatu, a k alla sai nayi shekara hud u zuwa biyar, lokacin fa duk kunyi aure da yaran ku.



  Dariya tayi sanan tace 

  Gaskiyya dai yaya, amma bari naje nayi sallama dasu Hajiya nadawo.



 Da haka tafice, tafi minti biyar a soron sanan tayi sallama a hankali, Ummi dake kwance cikin d aki ce ta tashi zaune, tabbas ko a iya jiya tasan tayi kewar Asiya, jiran shigowar Asiyan take sai da tajiyo muryata suna magana da Hajiya.



   Hajiya ina kwana?.



    Lafiya k lau Asiya mun kwana lafiya?.



 Alhamdulillah Hajiya, daman sallama nazo yimuku zan tafi kaduna gidan, Anty Larai.



Durum Dum Dum! Ummi taji gaban ta yafad i,

Anty Nafisa da tafito daga d akin ta ke zaune kasancewar har yanzu bata tafi gida ba ce tace.



   A ah Asiya me yayi zafi haka?.



 Bakomai Anty kawai ina son samun canjin waje ne da wasu abubuwan.



   Hakane Asiya amma ai da ko gida na kin bini amma Kaduna yayi nisa.



Dariya kawai Asiyan tayi sanan tace.



 Baba faa?.



  Hajiya ce ta amsa mata da cewa.



 Yana waje amma k ila ku had u.



Tashi tayi tsaye tare da cewa.



 Tom Hajiya, Anty nahuce, sai nadawo.



 Allah yatsare hanya Asiya.

Anty nafisa tafad a itakam Hajiya cewa tayi.



 Allah yayi miki albarka Asiya.



 Da amim ta amsa tafice, A zaure ta ci karo da Abba nan ma suka gaisa tayi masa sallama.



Hajiya ce tace da Anty Nafisa

 Wallahi ko a haka Ummi tayi rashin Mutanen arzik i.

  

  Bari hajiya abun har ba a magana wallahi.



Daga cikin d aki kam Shiru Ummi tayi tabbas bata kyautawa Asiya ba, ko kuma bata kyautawa kanta ba.



   Dai Dai sanda yaya Umar ya saka ta a motar da zata kaita kaduna, idanun ta suka sauka akan master dake zaune

7 / 13