NUR FIRDAUS BOOK 1 HAUSA NOVELS BY SURAYYAHMS.txt

Author :  SURAYYAHMS Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   42 / 52

123K to 126K   out of 155.6K words

nur ta fashe masa da wata iryar shagwabbaen kuka

Daga haka ya fizgota tsaye dan baison jin kukan nata yatura gaba gaba da fushi a yanayinta tabar gun da sauri tana gudu tana kuka sosai, bin ta yyi da kallo wato ma bazata bashi hakuri ko ta rokesa ya kaita gida bako..tsayawa yay har yaga ta kusan kaiwa karshen titi sai yaga ta tsaya, wasu gayu ne subiyu ya hango tsaye gabanta duk da ba wani haske gun yake daba, atsorace ta juyo xata canxa wani direction wani ya sha gabanta, ashe sune back up din da su fahad din suka kira awaya dazun, jan hannunta yaga suna yi xuwa gun wani mota da alama tasuce abun ya bawa javeed mmki bana kadan ba, kafin ya ankare har sun isa gun motar da ita yana kuma iya jiyo ihunta daga inda yake duk da nisan wajen.

da wani mahaukacin speed yataka motarsa kamar xai tashi sama kafin yaje gunsu har sun jefata a mota yay saurin isowa kusa har yay kusan cinkaro dasu suka razana suka tsaya...yana tsayawa kamar me iska yabude motarsan ya fito daya daga cikin samarin ma ya fito da shirin masa bala'in ya buge musu mota bai ko sauraresa ba ya bude backseat din motar yaga bakinta suka rufe da wani kyalle fixgota yyi daga motar izuwa waje duk samarin suka tsaya kmr dolaye sunafa kallonsa harya bude tasa motarsa ya jefata aciki.

komawa yay wajensu
tanata kallon yadda duka gayun suka tunkareshi yana kama mutum sai kaji ihu har ya karya masa hannu shifa daga yadan rike mutun da dan karfi sai taga ya karyashi kabas duk tarasa wani irin mugun karfine dashi..

harya ciro gun zai daddana musu harbi nur ta zuba masa ihu daga nan cikin motar tafara rokonsa tana cewa pls dont shoot dont shoot...

ya juya yana kallonta ganin ta tsoratane fa sosai sai yadan dakata nan saigama motar hukuma na tunkarosu da speed ta wajen

mayar da gun din yay aljihunsa ya ma gayun kallon she save ur life snn ya koma driver seat dinsa yashiga ya ja motar suka fara tafiya...

banda kuka babu abunda takeyi shikm baice mata uffan ba
sabida tambayoyi yake dashi me tarin yawa aransa akan wann daren wanda yake son tabashi amsarsa ayau din nan.

tafiya yayi me nisa da ita suna daf zasu sha kwanan wata round abt motocin polisawa suka fara bibiyarsu da alaman yan uwansu sunje sunga abunda yama yaran ne suke nemansa.

kawai ji tay ya miko hannunsa jikinta ya dallara mata seat belt
kuma uffan bece mata dama inzeyi abunsa baya neman izini

daga nan bata kara gane komi ba dan tun da suka fara guje guje da polisawan cikin garin abuja babu abunda takey sai kuka sai ambatan Allah.

dan ta lura javeed is doing it for fun kawai de wasa da hanklinsu yakey abanza bawai guje musu yakey ba..

ahaka sanda suka kusan barin garin abuja snn ya jasu cikin wata hanyar da babu coal tar, kamar ance ta bude ido kuwa taga yazare gun din yaran nan yana kallon madubin mirrorsa da left eye dinsa.

wani sabon kuka ta fashe masa dashi ya juyo ya kalleta suna hade ido yace mata "can you drive? da mugun sauri tace masa nooo, pls.. yace good, sai kuma taji ya damke hannunta ya dora akan stiring yace

"kirike nagaji, just hold it"..tarasa comand ya bata ko request..

haka ta rike jikinta na wani irin rawa tana kuka cikin rasa meke mata dadi tarike masa stiring da hannayenta bibbiyu, lkcin motar taji yana wani irin wainuwa dakansa kafin kace wani abu ya seta gun din yaran a kasa ta window ajere ajere ya bikan tayoyin su ya farfasa saida ya tabbata yay cripling dinsu sann ya jefar musu bindivar yaran ya amshi tukinsa a hannunta suka bar wajen..

kanta dake juyawa takife akan cinyarta har sukayi tafya me shegen nisa kafin can taji kamar yayi parking gefen titi tsaban ta jijjigu jitay numfashin ta ya tafi can sama, ya juyo yanata kallonta takife kanta tana jan sheshheka, cikin wata sigar lumshe ido da budewa yace.."i am listening"ya ji tay shiru wani irin muguwar kallo ya watsa mata nn ma yaga bata dago ba yana da hot temper dan haka ya sauka ya bude motarsa ya fito dasauri ya bude seat dinta yadago kanta yaga ashe har taja xucytane ta suma,

mamaki ya cika shi ya dan wara idonta yaga idontan yay wani irin jaaa da hawaye taciki, idontan a lumshe ga lashes dinta kamar andasasu hancinta dogo kamar an xana mata, a hankali ya sauke idonsa kan karamin bakinta daya yay masa kala biyu pink nd black yau

dan dauke kansa yayi sai kuma ya kwantar da ita akan seat din yanata tunanin yanda xai yi da ita ta farka

sai can da sauri ya dagota jikinshi ya kai hannunsa dai dai hancinta kirjinsa na bugawa ya kwanto ahankli yakai soft bakinsa dai dai nata yasa hannu ya bude bakin nata ya dora nasa akai ya shiga hura mata iska, ya kusa five minutes yana haka kafin nan a hankali ta bude ido ta kallesa softness din bakinsa takeji akan nata sai kuma tamike xaune da sauri ta rike kanta dayake juyawa shidai kallonta kawae yake bece mata uffan ba. sauka yaga take son yi dagakan kujerar motar yarike ta yace "stay still..." atsorace Ta fashe da kuka cikin rudewa tana jujjuya kanta tace Where is this place, can you please take me home..dan Allah wallh my head is aching i want to go home
...tafara masa kuka sosai.

wani uban harara yayi mata acikin duhun daren kamar tana kallonsa yace "Wani ya fito da ke yawon dare? Da kyar ta bude murya tana kallonsa da tuhuma muryartan na rawa tace "nace maka yawon dare na fito, yace toh menene?
u sneak out of ur parents house at night, u got ur self in
stupid unnesscry troble with boys...i am sure ur parent dint knw ure out haka ne?

..tana hawaye tana kuma kallonsa tace yes, they dont, But, Dont say things u knw nothing abt kaima ai yawonka fito waye sani agidanku?..

cikin katseta da mamakin tsiwartan yace ohhh you want to turn dis on me after saving ur god damn life, ta zuba masa ido
..ya hade rai girarsa na sama a dage yace 'go ahead, and thank me! ryt now...

muryanta na rawa tace thank you for what?? after you accuse me of sneaking out of my parent house irin banida hanklin innan kenan ko..

ya lumshe ido kadan yace okay enuf..get out of my car ryt now.

jikinta na rawa rawa ta sauka abunta ta kama hanyar titi tana tafiya tafara kuka sosai.

Tsaki yaja ya fara binta abaya har ya cimmata a fusace ya fizgota if u dont tell me the truth i wll take you with me bazaki taba komawa gidanku ba har abada,suwaye wayancan yaran i wnt to knw who they are.

tay kamar zata masa ihu dan ikon da yake nuna mata a muryan sa har yana so yafara razanata"tace i dont knw them. cikn zare mata ido yace i hate 'lies"..da har zata sharesa sai kuma ta hatsala da muryar kuka ta hau gaggaya masa komi daya faru bata boye masa komi ba, wani irin juya mata baya yayi da fuskarsa kamar ma be amice da ita ba wanda hakan ya kara bata haushi sosai..

koma mesa ta tsaya masa bayani oho wani haushin kanta ta fara ji aranta tace shidin wayene da zaina tuhumanta kaman wani ubanta haka

cikin shareta ya koma cikin motar dan yaga inda wayarta ya fadi dazun data tsaresa sai ya dauka ya aje, yana zuwa ya dauko wayar ya dawo dashi yamika mata yace unlock it, hawayenta tashare tabude masa wayar aikuwa chat dinta yana dede kan text message din da aka turo matan da hoton laylan da komi ya bude ya kalla....

yakara fixgota bada karfi ba amma yace come with me...

gaba gaba suka kara sanda suka kai gaban wani waje mai dan tudu sann ya zauna ya daga idanuwansa masu sanyi ya dallara mata tanata kallonsa taga yamika mata hannunshi dacan kamarma bazata taba kulashi ba toh bata san sanda takama hannunshin ba ahnkli yajawota tazauna kusa daf dashi..

tarasa me takeji akansa dan bata taba sakewa da mutum hakanan ba sai shi

yanzu xai bata haushi yanxu saikuma taga tana biye masa.

dan shiru sukayi na wucen gadi kafin nan yace "so, what did u think dos boys want frm you?? da rashin kunyarkin nan kin taba musu wani abune?

dan sunkyar dakai tay wani sabon hawayen taji yayanko mata ahnkli tace mishi i dont knw nifa babu wanda na sani a schl din sai kanwata da kawaye na..i just..
heard dat they are bad boys,And they rape girls.."yace really? dakyar tace mishi umm,ahnkli ya dago ya kalleta da taushin murya yace "toh sorry.
ta kallesa da sauri dan batay tsammnin zai furta mata hakan ba,ganin tana kallonsa yasa yadan lumshe ido muryansa kasa kasa yace kinaji na?
tana kallonsa tace eh,..yace "Dont ever put ur life in danger again, kanta ta sauke kasa again snn tace but i cannot leave my sister over der what if,..cikin katseta yace shushh, listen. ur sister isnt the target, u're..kiyi abunda nace miki kawai do not disobey me.

tay shiru batace masa komi ba...

ya amshi wayartan ya bude sakon ayshan ya ciro nasa wayar ya bude yay scanning din boyayyen lambar da wata application na military intelligence awayarsa aikuwa sai ga lambar aysha sata boye ya fito karara.
yace who is aysha othman? itade tunda wayarta yashiga hannunsa takejin dar dar tambayarsan ya dawo da ita dan tsillin hawayenta tashare da mamaki ayanyinta tace she is my friend..

kai tsaye yace"I dont like her. i don't want u close to her ever...

tana kallon cikin idonsa takasace masa komi sabida tadda taga yake mata magana da iko kamar wani babanta..

can ta turo masa baki gaba tace ."nide i want to go home"..

yay shiru kamar be ji ba..muryanta na rawa takallesa taga yanata famar daddana mata wayarta batama san meyakeyi ba, hawaye take ya cika mata idon tace 'please.. its late..
inason insan ko sister na ta koma gida.

saida ta fadi hakan snn yace "okay" nan
yamike tsaye zai dan jawota tay sauri ta ja jiki dashi tay gaba ya kyabe bakinsa ahankli ya biyota abaya.

tsayawa tay ya zo dakansa ya bude mata seat din gaba ta shiga ta zauna snn ya rufeta, sai da yadau like 5 more mins da wayarta awaje snn ya shigo ciki yana zama ya aje mata abunta ta dauka taga time kusan 4:30pm na asubah.

lumshe idanunta tay ta jingina kanta da jikin kujera tay shiruu
harya ya fara tukasu

tsaban tarasa menene zcyarta yake sakawa tamanta shataf bata masa kwatancen gidan na su ba, tana cikin duniyar tunani dataji sanyin A.C ya gaurayu da wann shgn qamshin turaren nasa sai kawai ta bingira da bacci.

ahnkli ya dinga tukasu time to time yakan juyo ya kalleta yana tuna yadda ta bashi labarin with all the honesty in her voice and eyes

tun ba anan yasan ba karya take masa sam
numfashinta datake saukewa a baccin is soo fragile and serene
like her kind heart harji yake da wani abu ya sameta yau din nan da baisan ya zaiyi da ransa ba.

badon yaso ba amma Dan dolensa ne kawai ya saka Security tracker dinsa a awayrta, he just cant risk it anymore ya lura kamar yarinyar tana da maqiya sosai.. even among her friends..duk da baida niyyar shiga personal life inta amma kusan dole yazame masa ya kare mutuncinta dan yasan yarinyace batay wayon da zata fahince wasu abun ba. he is going to have a spy dat will be watching her movemnt kullum daga zarar tafice daga gidansu dan tanan ne kawai yakeji hanklinsa zai kwanta.


Daga gidansun kuwa layla ta kasa bacci sai jeka ka dawo take agidan tana nadamar sakasu acikin wnn matsalar duk ta gama tsorata sosai da abunda zai iya biyo baya idanunta nakan agogo every time tana kuma kirar aysha akai akai har ayshan tazo ta dena kulata.

sai dataga hudu ya wuce sann ta yanke hukuncin kawai zata canja kaya ta fita neman nur dan bakaramin guilt takeji aranta ba, ta haura sama kenan bada jimawa ba aka kira sallah kawai tay alwala tayi sallahn

ta idar lokcin past five da hijabin sallahn ajikinta ta rarumo wayarta ta sauko kasa da sauri tana daf zata sauka waje kenan tajiyo motsin motar mrs haseena, tsayawa tay jikin flower da mugun tsoro aranta tanajin wani irin tsananin rudewa ta ciki dan batasan ma zata fara ce ma Mrs haseena ba

tay nisa cikin tunanin abun cewar kenan saicaraf haseena ta hangota, da mamaki tace "Auta?? a mugun tsorace layla ta dago kai da muryan kuka tace "mummy" sai kuma ta sauya fuska da shagwaba ta taho da mugun gudu tazo ta rungume jikin mrs haseena tafara kuka sosai

..atake hanklin mrs haseenar ya fara tashi tafara tambayarta tana cewa cmon layla what is wrong?wani abu ya farune agidan
me aka miki????

layla na kkrin budar baki zatay bayani kawai sai sukaji wata bakuwar sallama a bakin gate din gidan

malam liman ne yaje ya bude ya shigo tare da wani hukumar polisawa su biyu..

cikin katse gaisuwar su Mrs haseena tace
ahhhh ahhhh ahhhh meyafaru kuma? how can i help you officers
...

police din ya matso kusa da ita yace sorry maam, bt we have come to question ur kids.

a mugun zafafe mrs haseena tace what!?? akan me...abeg get out of my house bana son iskanci..my kids are good kids officer
..saidan in wani sharrin za'a laka min

dayan police din yace ma'am please we have permission frm head office to ask them few question please.

Da zafin kai hassena tace abt what?

yace, We have information dat ur kids are involved in night party accident wanda ya jawo aka harbe yara bakwai a hannu da wasu civilians dukan su da karaya ajikinsu...

cikin dafa kirji haseena tace hasbinallahu wa neemal wakeel and you think my children have sumting to do with party and shooting? ihun da ta musu yasaka har makota ake jin muryanta..

this must be the work of my dump enemies i am not going to let you drag my innocent girls into this nonsense baseless accusations..

"layla ko kinsan wani abu akai??

da sauri layla ta girgiza kai tace mummy nifa bansan komi ba ni sallah kawai nakeyi..sai kuma ta fashe da kuka sosai..

Haseena ta inda take shiga batanan take fita ba haka kawai zaa zo har gidana ana menan aci min mutunci dan anga mune zamu lashe kujera to wallah ba isa asaka yarana acikin wann makircin ba

you officers u better leave my house kafin yau din nan ku rasa aikin ku..my child has already admited dat she dont knw anything
..dont let me file a case againts you for child abuse and emotional black mailing..she is just 15 uban me zata muku awajen party ehhhh

dayan officer yace toh ina yayarta, ance mana su biyune..

malam liman ne ya tsoma baki yace haba officer, yarinyar data gama ciwo gasar qur'ani dana tarbiya wa Abuja kake tsamnin zaka ganta agidan party, yanxu haka zaka samu tana karatun qur'ani abaya

kallon debar albarka da mrs haseena take musu tana kan latsa wayarta agaggauce yasaka polisawan kawai suka haqura suka yanke hukuncin katse bincikensun agidanta sai bai kara ce mata komi ba dan sun santa sarai yadda tadau zafin nan yanxu zata iya kulla musu sharri ko suji sunansu na yawo a social media..

sallama suka mata akan zasu dawo in akwai bukatar hakan

ta inda mrs Haseena take shiga banan take fita ba ta rakosu har gate tana zazzaga musu buhun bala'i

mama hauwa da maman sa'id tsabar gulma koro koro suka fito waje tsegege daga ita sai mayafi ta tsaya tareda mama hauwa sunata kallo kuma sunajin me ake cewa..

kusan wuce juna motar javeed dana polisawan yay tun akan titi amma dake ahnkli yake tukin ko kallonsa basuyi ba suka bar anguwan..

maman sa'id tay sauri ta tsare haseena ita da mama hauwa nan tafara bawa haseena labari ai jiya anyi kame yara kanana yan makarantar su nur sunje sun hada party maza da mata sunata shaye shaye suna zina shine har aka harbe wasu..

maman seed cikin shan ciki tace hmm To wallahi ni na ji da kunne na tun jiya da dare aka fara case, kuma ance su 'yan makarantar nan ne na icice suka je party nan kuma faaa ana zargin an sha giya wiwi har da zina Kuma shine ace har ‘yayanki ciki?!"

cikin gallaza mata harata mrs haseena tace Allah ya kiyaye,
aniyar kowa yabishi..

mama hauwa tace uhum ni dai na ji wai akwai wata yarinya da akace ta bace ma bayan kowa ya watse

Haseena da ta hade rai ta dafa kugu tace
kai subhanallah Kuna jinmaganan karyan nan kamar ba ku da 'ya'ya. dan Allah Ku bar zancen gulman nan ya huta, Yaran nan fa kananane suna ribibin shirin gama makaranta dama kuma ai kowanne irin taro yanada tsautsayinsa nide Ban yarda da sharrin da ake yadawa ba snn bazan amince asauke sharrin banza akan y'ay'ana ba yawwa.


"To ai shiyasa mukazo
nan muna tambayarki dan inba rami toh me yakawo rami wai naga polisawa ne sunzo miki question har gida da sassafe...

sunakan fetsawa mrs haseena habaici da baqar magana sai ganan motar javeed yay parking ata gaban su kadan, magana suke amma hanklinsu sosai ya koma kan motar duk inda kaga abu me masifar aji da tsada dole ne ka kalla

Cikin wannan yanay suka komar da kallonsu kan motar Javeed Mufasa da ta tsaya a gefen layin gidan mrs haseena hasken fitilarsa ya kashe duk sai aka yi shiru nan take


Da wata irin kasala Nur Firdaus ta farka daga baccin daya kwasheta koda ta bude ido mamakine ya cikata na yadda akay javeed yasan kofar gidansu..

tana daga kai da niyyar masa magana caraf sai ta hango taron mutanen dake a kofar gate dinsu koda taga mrs haseena atsaye da su maman saeid atake taji ta birkice gabaki daya zuciyanta ya hau buga kirjinta na dukan tara tara, ahnkli tasunkuyar dakai kamar mara lfya data kalli time a wayarta kawai sai idonta yafara fidda sabbin ruwan hawayen tausayin kanta dan ta riga tasan me zai biyo baya.

Javeed ya gama kare masu mrs haseena kallo yaga suma nan din suke satar kallo
duk da

42 / 52