Chapter 50 Reading NUR FIRDAUS BOOK 1 HAUSA NOVELS BY SURAYYAHMS.txt Arewa Novels

NUR FIRDAUS BOOK 1 HAUSA NOVELS BY SURAYYAHMS.txt

Author :  SURAYYAHMS Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   50 / 52

147K to 150K   out of 155.6K words

Didi ta kama hanyarta ta bar Abuja.

sosai tafiyar Didi babu sallama yay ma Mrs haseena zafi arnta bana kadan ba, kenan ita kadai zata aurar da layla babu wani dangi na jini sai kawayen siyasa, she was so frustrated dan waliyan laylan ma da kyar tay convincing din wani abokin mijinta ka harhada mutane jiya aka karbi aure kuma tun daga nan basu sake dawowa ba.

dakyar tazo ta iya danne komi ta watsar snn ta cigaba da hidimarta abunta.

ranar da didi ta wuce yolan layla bata wani daddara ba haka ta sace kayan sawar nur kankararru taje bridal photo shoots dasu,

da kyar Adnan yaje wajen ahakan ma wai saida mum dinsa tay kamar zatay hauka koda yaje wajen yana ta babbasarwa layla taga ruwan walaqnci awajen dan adnan yaqi sam ayi wani style da zaisa ta matso kusa dashi amma ko ajikinta ana gamawa da wann da dare can suka dawo gida da wani uban rawan jiki tazo ta samu nur ta fito daga wanka kenan dan is almost 10pm na dare
tana zuwa kuwa ta fara nunawa Nur hotonan biki, abinka da rai da jini, dataga nur ta dauke kai bata kalla ba kuma bata kulata ba sai kawai ta hade rai ta fita kai kararta wajen mrs hasina, tana zuwa ta samu mrs hasinan nakan waya ana mata batun za'a kawo lefen laylan washe gari Duk hanklinta ya tashi dan bata da wani isashen kudi ahannunta da zata tarbesu yadda ya kamata dan karamin walima sukeyi anasu al'adar bakaramin kashe kudi akeyi ba wajen bada tukuici da sauransu.

ganin Hanklin mrs hasina a hargitse yake sai kawai ta koma dakin ta samu nur harta kwanta, kawai sai ta fara habaice habaice, tana cewa wai ai baqinciki ake mata akan aurenta daga karshe dei nur earpiece ta saka ajikin system dinsu na dakin tana jin karatun qur' ani har tay bacci.

washe gari sassafe Mrs haseena ta fita neman kudin tarban baki dukansu sun farka basu ganta agidan ba.

bangaren ussy kuwa tin jiya dayaje asibiti ya gudanar da bincike ya kira sanata farida awaya yace mata bai samu matsala wajen likita ba tace sam bata yarda ba, garin bincike yaji labari cewa Dr surayya ta amshi jinin nur taje asibitin datake aiki tana gudanar da gwaje gwaje akai

atake Sanata farida ta bashi oder akan ya nemi Dr surayya cikin daren nan ya kwace duk wani abunda ta samu sann ya gama da ita. koda yaje asibitin da dr surayya take aiki ya samu bata shigo ba tukuna mei aikin lab ya biyasa kudi nan yace masa aijiyan tana wajen meeting ne amma da safene zata shigo.

haka ussy ya zauna a asibitin har safiya yay disguising kansa as a patient, around 9:30 am na safiya sai ga doc surayyan ta taho sanye da hijab da gilashinta dake mata mugun kyau. kai tsaye tawuce cikin lab din da key inda ta boye results da duk wani sakamakon gwajin
nur dan bata yadda da kowa ba tana kuwa daukowa tawuce dashi offishinta duk bata san ussy yana kallon duk wani motsinta ba.

she is a gyneocologist dan haka bata bukatar wani ya fassara mata sakamakon test din,

tana sakawa a yar computerta ya fara nuna mata complte blood scan result for nur firdaus harouna

sample din jininta na farko yanuna yana dauke da high dose of human chorionic gonadrotropin mixed with progestrone injection.

shi HCG wani nauin hormone ne da jikin ya mace yake producing dinsa naturally idan ciki ya shigeta, snn duk wanda aka masa allurar HCG in high amount atake jikinsa zai fara wasu reacting kamar na me cikin gaske koda bai sadu da namiji na.alluran yana iya tricking bodyn mace into thinking cewa akwai embryo a mahaifarta koda kuwa babu komi. barema da aka mixer shi da progestrone wanda shikuma babban aikinsa shine ya saka symptoms na ciki kamar amai, su kumburin nono kasala da daukewar jinin al'ada sabida shi asali dama pregnancy supporting hormone ne. ana maka high dose na wnn allurar zai atake fara reacting within d first 24hrs,

sann bayan kwana biyu kuma zaka fara jin alamar shiga ciki early prenancy signs and symptoms haka zaiy ta worsening musmn inyakai 1-2 weeks and can even produce a false positive test result
in akaje gwaji.


Bazai kuma fasa nuna wa mace tana da ciki ba harse karfin alluran ya ragu sosai ajikinta nan ne in akaje akay gwaji za'a ga negative snn ahankli sai sign nd symptoms duk zasu washe. the main amfaninsa shine asaka mace taji kamar eh tana da ciki for a while dan a kawo wani rudani ko hatsaniya.

Dr surayya was soo shocked and excited at the same time sai kabbara takeyi tana gode ma Allah dan tsabar murna tama kasa rufe baki face sai dataga result na biyu na dayan jinin nur firdaus data dauka shekaranjiya aikuwa taga yanuna pregancy negative da alaman ruwan Alluran ya fara ficewa ajininta.

Da karfi tace masha Allah, Alhamdullahi ya Allah nan ta mike tsaye tace zama bai kamani ba masha Allah..cikin lumshe ido da budewa tace Allah mungode maka da ka cire yarinyar nan a wann fitinar..

wayarta ta dauka ta dinga shekawa mrs hasina kira dan ji take bazata iya ma jira takai musu result din ba, saidai mrs hasina na can acikin rubibin shirya shiryen tarban yan kawo lefen layla bata ma ji ringing din wayar ba.

ganin ta mata 6 miss call bata dauka ba kawai sai ta dauki files din da misalin karfe goma da rabi ta kama hanya zataje gidan mrs haseenan dashi aikuwa tana ficewa ussy ya dinga binta abaya, ya kira sanata ya gaggaya mata cewa ai yaga Dr surayyar da file tana haba haba ta fice da alaman gidan mrs haseena zataje..

atake ta bashi wani sabuwar oder nan ta turo wasu suka fara binsu, Dr surayya tana tuki akan hanya bata hankara ba kawai tag an wani yanka an shigo gabanta kafin tay control taga wata baqar motar tayo kanta da gudu ta mugun tsorata ta fara salati babu imani suka gwarata da kwalbet saida suka tabbata ta fadi ciki.

motar ce tay tumbul ta fadi da gefe take ta suma kafin mutane masu wucewa su tsaya dubata nan ussy yay sauri yazo ya cakka mata wani allura snn ya mika hannu ya dauke file din ya cusa a rigarsa sai kuma ya fara ihu yana cewa jamaa ataimaka ataimaka

duk masu wucewa sukayo wajen acikin rubibi ussy ya bace abunsa, ahanya ya kira mutuminsa na lab yace masa ya dauke laptop din Dr surayya sann ya share history na sakamakon gwajin

haka aka dauki Dr surayya aka kaita asibiti emergency direct bawani rauni taji ba amma atake ta shiga comma.

bayan sun cimma wann lami lafiya sukabar abuja da file din dan sanata ta riga ta bada aiki an bazama ana neman mata inda sadaat ya shiga.


Wajajen bayan azahar hasina ta dawo gidan a mugun gajiye batako duba wayarta ba bare taji meke faruwa ta shigo kenan ko zama batay ba saiga kirar hajiya mairam, dan ringing tone na daban tasaka mata dan haka kirar nashiga ta dauka jikinta na bari tafara gaisheta cikin girmawawa.

maganan kawo kayan lefe tay mata lkcin layla na gefenta tanajin yadda ake ma haseena lisafe lisafe abunda zata tanada

bayan haka kawai sai tasako maganan zubda cikin nur, cikin sassauto da murya mrs Haseena tace ranki shi dade likita ne yace mudan dakata cikin yay kwari sai acire in ba haka yarinyana zata iya rasa ranta. wani irin tsawa Hajy mairam ta daka mata tace kika ce mene? tun hseena bata gama budan baki ba..

hajya tafara masifa ke hasina ba haka mukay dake ba karki sake ki rainamin hankli wato dankinga an daura auren dana da yarki shine zaki maidani abun wasarki ko..to wallh bakaramin aikina bane insaka adnan ya maida yarki bazaura yau din nan.
atake mrs haseena tafara bata haquri

..cikin masifa da balbalin balai tace ni bandamu da wani case dinku da likita ba just find a way and abort it kafin ya zame mana cikas a hidimar bikin nan..haseena was shocked data ga kamar kawai de hajy mairam bata damu da nur tay rai ko kar tay ba. ahaka har suka katse wayar bata sake cewa komi ba sai toh

ganin ta sauke nannauyar ajiyan zuciya cikin matsanancin damuwa yasaka layla ta matso kusa da ita tafara bata baki da dadadan kalamai masu kwantar da hankali

ahaka ahaka ta shigo da maganan nur, tace mummy kinata neman kudi yaa nur fa tana da Dollars dayawa ajakrta wallh tun ranar nagani ta boyesu da wasu perfumes da wasu set na kaya masu tsada kuma king ai na roketa taki ta bani...gashi kinata shan wahalar neman kudi amma ya nur tana dasu taki tako taimaka mana hmmm

Baki bude haseena take kallon laylah da mamakin jin wann maganan layla kikace nur tanada ajiyayyun dollars? layla tace wallh tana dasu suna nan acikin box dinta da mukaje kd dashi in karyane kice mata ta kawo box din nan wajen aduba.

ahrgitse hasina ta mike zata je saiga kira ya shigo wayarta tana daukawa aka gaya mata cewa ai ga abunda ya same doc surayya harma ana zaton hala bazata yi rai ba tana sauke wayar sai kuma taga 6 miss call dinta bada jimawa ba, nan take mrs hasina taji ta mugun rudewa kawai saita rarumi jakarta ta kama hanya zasuje asibitin. sunfito kenan adede coridorn ta wajn kitchen suka hadu da noor firdaus ganin yadda suka fito yasata tambaye layla meke faruwa laylan ne tagaya mata ai dr surayya ne tay mmnan hatsari.

atake ta aje plate din itama ta bisu suka je asibitin koda suka ga yanayin Dr surayya rai a hannun Allah kusan kowannensu sai da jikinta yay mugun sanyi.

Kuka nur takeyi da tunanin hala itace silar dagawa matar nan hankali hartaje tasaka kanta a hatsari

aikuwa haseena tana fara tambaye tambaye aka gaggaya mata cewa ai test dr surry take running wa jinin nur firdaus, ta fita kenan da file din result din zataje gidansu shine aka kawota wai tay hatsari.

mrs hasina tasha mamakin jin hakan sai kuma ta jajanta sosai
agefe ta kira me lab ta dinga masa question akan test din shikuma bai boye mata yace ai tana reconfirming ne akan cikin nur firdaus amma dake ita daya tay abubuwnta shima besan outcome din ba gashi ance file din ma yabata a rububin hatsari. godiya kawai ta masa at around 3:0 pm suka bar asibitin
dukansu uku duk ta kullace abubuwa aranta game da nur

aikuwa isarsu gida kenan ko wani hutawa basuyi ba kawayenta sukazo sukaje mata masu kawo lefe na hanyar zuwa agurguje haseina tay wanka tun bata gama cancara adon bama sai ga mutane hilimi guda a motoci na alfarma sunzo, gabaki daya bata shirya ba gidan ma saida kawayenta sukazo suka dan saka mai turaren wuta suka kimtsa, babu komi face chops da drinks na alfarma da suka sisssiya, bayan haka duk abunda ala gindaya bata samu daman shiryashi ba

gashi manyan mata masu ajine suka rako kayan akwatunan lefen layla masu shegen tsada sunkai set 34 komi yaji dake harkan show off da pubclity ne komi da akeyi awajen ana daukawa for media sake. sai sum sum Mrs haseena take da abun kunya da suka isheta sabida komi anyishine na nuna iyawa da wani irin almubazarnci itakuma
harga Allah Capactyn ta bai kusa kai nan ba.

kyaun fuska da wayewar haseena shine kawai ya dan ceceta ayau dan duk yadda tay packaging
abun yakiyi sosai taji kunya awasu abubuwan musmm wajen maida tukuici dan milliyan goma akasa akasar akwati

few anties na adnan saida suka dinga ma haseena habaici masu ciwo acikin raha wann kawo akwatin layla bazata taba manta shi ba cos she actually feel insulted amma dai haka ta daure tana yake har aka gama aka watse bayan magrib.

kawayenta ne suka tayata tattara komi aka shiryasu a daki, wasu sun kasa haquri saida suka gaggya mata magana akan cewa dolene fa ta nemi kudin da zaty barazana wa mutanen na inba haka ba layla ta shiga uku da gori gashi dama auren hadi ne ba daukarta da daraja zasuyi ba.

magnganu dayawa suka taru sukama zuciyar haseena yawa gashi tana alhinin babban kawarta dr surayya dake asibiti rai a hannun Allah wanda duk tana alaqanta faruwar hakan ne da lefin nur firdaus aciki.


Daren yau gabaki daya dakyar Mrs haseena tay bacci, takaici da baqin ciki yabi ya cikata badan komi ba saidan abubuwan da suka faru worst ma shine nawajen karban lefe, sake sake ta dingayi aranta akan nur firdaus tasan dolene kawai gobe ta dau kwakwaran mataki dan gabaki daya takeji tagaji da ukubar da Nur firdaus take jawo mata a rayuwarta gabaki daya.

layla kuwa kusan kwana tay tana ta creating anynmous acct tana tura video na lefenta wa media pages kamarsu arewa blogs big big nigerian celebrity wedding an co, da captions kala kala #Aurensoyayya #LayAd20## lefen yar gata. laylanAdnan.

wani irin tsantsan farinciki takeji yadda ake yaba kyaunsu ana ta anticipating din event dinta a coment sections tana kallo just few bad comnts na wasu yan schl da suke cewa ta auri sauryin yayarta amma duk wnn be dameta ba. bata runtsa ba sai wajen karfe biyu na dare lkcin nur ta jima da yin baccinta acan gefe atakure.

washe gari sassafe Nur ta farka tay sallah haka ta dinga tashin laylan tanajinta amma taki motsawa harta dauki qur'aninta ta fita waje domin karatu.

nur tana ficewa da kamar minti biyar layla ta diro akan gadon ko sallan batay ba tasaka sleepers dinta ta wuce dakin mrs haseena kome suka kulla oho..

nur tana tsaka da karanta suratul yousuf
da muryanta me dadi sai ga nan layla tazo ta tsaya mata akai babu ko yar sallama bare gaisuwa tace
..."mummy tana kirarki tace kizo yanxu karki bata mata lokaci. nur tadago kai da mugun mamaki tanata kallon layla da already har juya tana tafiyarta abunta. karamin ajiyan zuciyane ya kufce mata batay kasa agwiwa ba ta rufe qur'anin gently ta kamo hanya cikin gida

ahnkli take tahowa dan tanajin jiri jiri ga wani dan banzan yunwa dataji ya fara damun cikinta duk de batajin dadin yanayinta.

tana shigowa ta same su a kofar dakinsu suna tsaye a wajen doguwar corridor da zakabi kaje kitchen mrs Haseena ta mugun harde ranta har tana girgiza kafa tana huci.

Nur tana zuwa ta rusuna kasa cikin ladabi tace ina kwana mummy...wani irin mugun kallo mrs hasina tamata a tsawace tace rike gaisuwarki babban munafuka muguwa
..nur wallh kin yi asara. ta inda take shiga batanan take fita ba, tace ma nur ai tsabar baqin ciki da kishin layla datakeyi yasaka ta tursasa Dr surayya akan aje asake mata gwajin ciki dan kawai ta wargaza auren layla da adnan ita kuma ace she is innocent


yau babu kalar zagin da hasina bata mata akan haka ba, she call Nur desparete evil and toxic, me kwadayin abun duniya tace wai nur batason cigaban yar uwarta layla sam sam.

Nur harta budi baki zata fara kare kanta
kenan sai ta tuna Mrs haseena bazata ma saurareta ba kawai sai tay shiru tana kuka ahankli.

kafin tagama hadiye zafin zagi da zargin da hasina take mata akan hatsarin Dr surayya kawai sai taji Haseena ta shigo da maganan karuwanci.

tafara cewa nur ai ta jima da sanin cewa suna zuwa yawon iskanci da adnan shiyasa suka kasa rabuwa da juna haryaje yana cusawa iyayensa baqin ciki akanta, ta kafa hujja da gulman da layla tagaya mata akan taji sunacewa zasuje su huta awani waje. snn tace ai agabanta ma wani me mota ranar yazo ya ajiyeta da asubah tafito a motar ko dankwali babushi akanta kuma agaban nebors yoo ina take zuwa inba yawon karuwancin dare ba?

tanata masifa kawai tasako maganan su abayarta data saka a Kd, dana kudin da nur take kashewa har dana komi ma, ta dinga zazzagawa nur firdaus din zagi yau din ta kirata da sunan karuwa awajen yafi sau akirga...tace ai fyaden da aka mata ma kamuwar Allah ne hakama cikin Allah ne ya tozarta dan mutane susan wacece ita.

duk dai nur batace mata uffan ba saida layla ta shiga dakin ta fara kwaso jakunan ta tana kawowa gaban mrs Haseena,..

ana budewa kuwa suka fara cicciro expensive gifts da hajy bilki da hjya saadatu suka bata
jeweries, da set na veil me takalmi da clutch dinsa akwali da turarruka masu tsada da qamshi na meduguri aikuwa sai ga tumin bunch bunch na Dollars har guda bakwai da wrapper na 1k me dauke da 200 thousand naira dan nur bata wani kashe kudinta duka ba.

ganin wayannan kayan yasaka hasina ta fasa ihu ta jawo nur tsakiya tafara kai mata duka kota ina tana gullin cikinta tana takata

wallhi baki isa ki kasheni ba saidai ke ki mutu munafuka kawai
algunguma kawai yau Allah ya toni asirinki.

saida tama nur dukan da bata taba mata ba, kafin nan ta kyaleta awajen suka kwashe dukka kudin da kayan sann suka wuce dashi dakin mrs Haseena suka barta akasa tana murkususu tanata kuka tanata kiran babanta cikinta ya fara murdawa jini ya fara bin kafarta sosai numfashinta harya zo ya dauke

saida layla ta fito sann taganta ahaka taje ta gaya ma mrs hasina tazo takira likita anan anguwansu aka kai nur wani private asibiti
anan ne aka mata gwaji likita yace ai shi bega wani ciki bama

Wani dadi mrs haseena taji da tunanin ai dukan data mata ne yasaka shegen cikin ya fita..

she was not even remoseful at all suka dawo gida nur batajin
karfin jikinta takwanta a daki ita dayanta maganganun mrs haseena na tozarci da muzantawa haka ya dinga dawo mata tay kuka bana kadan ba.

yaudai babu kalar tunanin da batay ba,

Mrs haseena tuni duniya ta zame mata sabuwa dan duk kudin na zasu isheta har ma su fiddata akunya inta juyasu zuwa naira, ga wann shegun jeweries da bridal veil da shoe da clutch komi ya zama musu deidei yau din nan sun samo abunda zai fiddasu a kunya saidai harynxu mrs hasina bata dena jin matsanancin mamakin inda nur ta samu wann uban kudin hartake ajesu a jakarta batare da saninta agidan ba..

Da yamma suka shirya tsaf suka bar gidan ita da layla, mrs hasina takai result ma hajy

50 / 52