FASIKI NE COMPLETE HAUSA NOVELS BY ZAHRA MUHAMMAD SURBAJO.doc

Author :  Zahra Surbajo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   4 / 9

9K to 12K   out of 26.2K words

taita ?ara mata ?warin guiwa,suka cigaba da hirarsu.

"diamond tunda yanzu laulayi yayi sau?i,next week inada bikin ?awata,a kd kuma tare zamu tafi dan bazan iya barinki intafiba,kwana huWu zamuyi"cewar jiddah tana kallonta.

Murmushi zahra tayi tace"kd fa jiddah ni bantaSa zuwabafa,wai nufinki bikin fateema hassan zaayi?"

"wlh ita da sisterta duka zaay bikinsu,dan tuni ma nace anko biyu zaa ajiye mana,zamu tura majourment"

"to Allah ya kaimu amman driving ke zakiyi badaniba"ta faWi tana murmushi.

"dama ya zaay???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?i inbarki da driving"cewar jeeddah tana dariya.

**********


A can gidansu mj ko biki suke shiryawa nagani na faWa,sabida bikine na manya,shiyasa amare,har sun fara tarbar ba?i.

shima mj da fareeda gidan suka koma dan gudanar da hidimar bikin.

gida ya fara cika,dan tuni makusantansu sun fara hallara.

Jiddah da zahra ma sun kamo hanya,dan halartar bikin,sede zahra time to time tana jin gabnta na faWuwa,sede tana yawan karanto duk adduar data zo bakinta.

sun iso kaduna lafiya,fateema ta tarbesu sosai tayi murna da ganinsu.

bayan sunci abinci sunyi wanka sun hutane,suka nufi falon gidan dan su gaisa da iyayen amarya.

zaune suke mj da daddy,da mummy suna mgnr kuWin da zaa warewa bikin,su fateema suka shigo dasu zahra dansu gaisa.

bakinsu Wauke da sallama suka shiga,Wagowar da mj yayi da kansa,idanunsu ya sar?e ana juna,

Arazane,ya mi?e tsaye,jikinshi na Sari,agigice zahra ta Wam?o jiddah tana ?araji take faWin,"jiddah ga ba?in karan nan daya min fyaWen nan,ki fitar dani kar ya maimaita mn"ta faWi tana ?o?arin fita sabida razanar datayi.

Mj da sauri yayo gunsu,sede firgicin da tayi,ganin ya tunkarosune yasa kawai numfashinta ya Wauke.ta yanke jiki ta faWi,jidda a hargitse takalli inda zahran ta nuna mata,ganin mj yasa ta dam?o wiyanshi tana kuka tana duka,"mugu azzalumi,mazinaci,ka cutar damu wlh bazamu taSa yafe maka."sune kalaman dake fitowa bakinta.

Kowa dake gurin sun shiga ruWani,shiko mj ?o?arin ?wace kanshi yake dan ya isa kan zahra yabata taimakon gaggawa dan ya hangi jini na bin ?afafunta.

ganin jidda bazata barshi bane yasa ya wanketa da mari,yace,cikin ?araji"bakida hankaline ko bakiga halin datake ciki bane,koma menene,rayuwarta first"

Da sauri jidda ta waiga gun zahra,ganinta yashe a?asane yasa ta ?wallah ihu sukai kanta atare.

mj ya rigata isa kanta,be Sata lokaciba yasa hannu ya sunkuceta,ya fice,da gudu,jiddah da fateema suka mara masa baya.

mota yasata sannan,suka shiga suka rungumeta,yajasu zuwa asibitin da yake ayki.

?akin taimakon gaggawa yasa aka kaita sannan ya shiga dan bata taimakon daya dace.

yayi mmkn samun ciki ajikinta,tunaninshi ko tayi aurene,dan haka besa komai aranshiba,yayi duk meyiwuwa wajan ganin komai ya dawo normal.

Allurar bacci yayi mata,sannan aka fito da ita,daga Wakin zuwa Wakin bedrest.

sai a lokacin yasamu natsuwa,koda ya fito samu yayi su daddy suma sun iso asibitin hankalinsu atashe,office Winshi yamusu jagoranci,kasancewar akwai falon karSar ba?i.

Daddyne ya dubeshi yace"majeed,inasnon sanin gaskiya gameda yaran nan,dama kasansune,wacce ala?ace tsakaninku?"yakai mgnr yana kallonshi.

Hawayene najin kunyar abinda ya aykata sukafara biyo idanunshi,cikin kuka,ya fayyacewa daddy abinda ya faru,be Soyeba,ya ?ara da cewa"wlh daddy na tuba,tuban danayine yasa nakawo fareeda lokacin da kowa beyi zatoba kuyafemin"ya faWi cikin kuka.

"wlh bazamu yafe makaba,ka cutar damu,sanadin abinda kai mata cikine ajikinta,kuma mahaifinta ya koreta,kuma cikin baze zububa"cewar jiddah cikin matsanancin kuka.

gaba Waya gurin ya kaure da salati,mj bakinshi har harWewa yake yace"Nufinki cikin jikinta nawane?"

"Da to na uban waye,ay wlh se kotu ta rabamu"cewar jiddah gamida mi?ewa agurin,ta nufi Wakin da zahra take.

wayarta ta ciro ta kira number mamy ayko bugu Waya ta Wauka,kwashe komai daya faru tayi ta faWawa mamyn.

ayko mamy kashe wayar tayi ta kira number yayan zahran wanda yakasance,lauyer ne me suna hameed.

"Hameed matsiyacin dayayiwa ?anwarku fyaWe gashican sun ganshi a kd"ta kwashe komai daya faru ta faWa masa.

ya fusata matu?a,dan har neman hydar yaje abuja dan ya faWa mishi wnda yaba key Win gidanshi besameshiba,dan tun barinshi asibitin yabr estate Win.

wayar number wani babban Wansanda dake police headquater dake kd yayi yamasa bayani,ayko mota aka shirya da jamian tsaro suka tafi dan kamoshi..


********

bayan fitar jiddah,daddyne,yace cikin fushi"kaban kunya majeed,kuma kasani,wlh ko iyayenta basu haWaka da hukumaba ni sai na kaika,dan ko ?ata akaiwa hakan bazan ha?uraba"


mamyce tyi hanzrin tarar numfashinsa da cewa
"haba alhaji,taya zakace haka tsakani da Allah Wan namijin ?waya Waya,zaka kaimin gun hukumomi,a bari asasanta mana,waya sanima ko..."mj ya katseta da cewa.

"duk abinda akace nayine momy,ba ?arya aciki,tun lokacin na rasa natsuwata,ni kaina zan kai kaina ga hukumomin,dan fuskantar hukuncin laifin dana aykata"ya faWi cikin kuka.


"to in banda sakarci irin naki,har danki yayi wannan abun wa yar wasu ki tsaya surutun banza"

shigowar yansanda office dinne yasa suka mimmike,kowa na kallon kowa.

Nunashi jiddah tayi tace"gashi can"

ayko kanshi ?ansandan sukayi,ba tare da musun komai ba ya Waga hannunshi,suka kamsashi.

daddy beyi yun?urin komaiba,se mummy dake ta kuka,haka aka fice dashi,

tuni gurin ya cika da mutane ?an kallo kowa nason sanin laifin me doctor mj yy aka kamashi,amman ba amsa har aka tafi dashi.

jiddah komawa tayi Wakin da zahra take tana sauke ajiyar zuciya,dan tasan zaa ?watowa ?awarta hakkinta.

Shiko mj direct office Win commissioner ?an sanda akayi dashi,inda shi kanshi yayi mmkn ganin doctor mj agurinsa a matsayin me laifi.

Duk wani bincike daya kamata shi aka shigayi.

acan ko asibiti jiddah gidansu mj tace ta ?waso kayansu tasaka a motarsu,fatima ba irin ha?urin da bata ba jiddah ba amma sam ta?i sauraronta.

asibiti ta koma inda ko tai saa zahra ta farka,da sauri ta ?arasa jikinta, ta rungumeta,kuka zahra ta saki me tsuma zuciya.

"calm down diamond,be cuceki a banza ba dan yanzu haka yana hannun jamian tsaro,ze fuskanci hukunci"cewar jiddah tana rarrashinta.

Dasauri zahra ta Wago ta dubi jiddar tace"bestie hukuma kuma,?"

"eh mana hukuma,koko tunaninki ido zamu sa masa yaci banza,no se ya biya wlh"cewar jidda cikin fushi.

"Amma jiddah hakan zani gurin hukumomin kowa ya gama ganeni a mazaunin wacce akawa fyaWe?"

"karki damu zaki sa face mask ko nikab,amman ba makawa,kuma yanzuma ki tashi mu tafi daga asibitin nan,dan nan din gurin aykinsane"cewar jiddah tana janyota a hankali.

Ba musu zahra ta sauko a hankali,jiddh ta kamata suka nufi mota,tasata aciki sannan ta shiga taja suk fice a asibitin.

hotel ta kama musu na gani na faWa,bayan sun shiga Wakin ta haWawa zahra ruwan wanka me zafi tayi dan taji daWin jikinta.

koda zahra ta shiga wankan tsayawa tayi tana kallon cikinta daya Wanyi tudu kaWan a mararta,shafashi tayi wasu hawaye masu zafi suka zubo mata na tausayinsu.

da?yar ta rarrashi kanta tayi wankan ta fito,

*********

"Daddy lokaci yayi da zaka nunawa diamond gata,amatsayinka na mahaifinta,mun faWa maka countless time,cewa her case is rape,amman baka gamsuba,to yanzu gashi gaskiya tayi halinta wanda yay mata ta ganeshi kuma yanzu haka yana hannun jamian tsaro a kaduna"cewar hameed,yayan diamond,sanda yasamu mahaifinsu da maganar.

Gyara zama maina yayi sannan ya cire glass Win dake fuskarsa,yace a tausashe"hameed ina ?aunar diamond Wita she is my preciours diamond,amman mamynku ta kasa controlling zuciyart game da son da ita take mata,tabarta tayi abinda takeso,wlh ina ba?inciki buWe ido inga diamond da cikin nan ajikinta,"ya faWi hawaye na biyo idonshi.

"komai ?addarane daddy,Allah ya zana hakan zata faru,so be kamata muyi fushi ba,addua da neman mafita agurin Allah shine"cewar hameed cikin taushin murya.

"Hakane hameed,yanzu me kakeso inyi acikin case Win?"

"na farkode diamond ta dawo gida dan acan abj din ba aykin take zuwaba.na biyu,kayi mgn da gomna ayi mgn da shugaban kasa,ayi me yiwuwa adawo da case Win nan yola,zamu fi samun sau?in gudanar da komai"

Daddy bashi da sauran tacewa hakanne yasa ya amince da abinda hameed Win ya bu?ata,dan ya gama kashe mishi jiki da ayoyin Allah.

********


Mj duk wata tambaya da zaa masa amsawa yake,da yayi kawai,shiyasa koda lauyanshi yaje yasameshi a cell,beji daWin sakin bakin da mj Win yayiba.

"Haba ranka ya daWe,meyasa zakai ta zuba irin haka,bakasan nan nigeria bace,tsab zamu juya mgnr"cewa barister nasir.

Wagowa mj yayi ya dubeshi,da murmushi afuskarsa yace"Barrister yau koda ace Waurin rai da rai aka yankemin wlh bana danasani,dama danasani na Wayane in mutu da hakkinta to ina farin cikin sake haWuwa da ita akaro na biyu,abun daWin har cikina take Wauke dashi nasir"

"Abun daWifa kace mj,are you out of ur sence?"cewar nasir cikin kallon mmk.

"Yes,nasir, ina farincikin haWa zuria da ita"

"Bata hanyar aurenba?"cewar nasir cike da mmk

Sata rai mj yayi,sannan yace"Wa nane,kowa da yadda Allah ya tsara zuwansa duniya da yadda ze mutu,shi tashi a hakan tazo,look nasir banason ganinka a kotu koda ankaini pls kabarni amin hukunci daidai laifina"Yana kaiwa nan ya juya cikin cell din yabarshi tsaye agurin.

Bashi da zaSin daya wuce shima ya wuce Win.

******

kamar yadda hameed ya bu?ata hakan akayi,akazo da mota,aka Wauki mj cikin dare aka wuce dashi yola,ko kaWan mj be damuba,dan shi hakan daWi yake masa.

koda iyayenshi suka samu labarin an tafi dashi yola,hankalinsu ya tashi ba ma kamar mummy,kuka take iya ?arfinta.

"haba alhaji,me yaron nan ya maka da ka cire hannunka akanshi,kana kallo suna shirin salwantar maka da rayuwar Wan guda Waya magajin da Allah ya baka,meyasa kai shuru?"ta daWi cikin matsanancin kuka.

sosai maganar ta shigeshi,dan son da yakewa mj shi kanshi besan adadinsa ba.

"ki kwantar da hankalinki,zanje yola gobe,zan nemi ganawa da mahaifan yarinyar,suyi masa sassauci,inda wata diyyama dasuke bu?ata,duk zanyi,amma bazanyi amfani da kuWi ko ?arfi wajan tseratar da majeed daga hukunciba,sabida ya cutar dasu da yawa."cewar daddy cikin sigar rarrashi.

"To Allah yasa su masa afuwar amman wlh inajin tsoron hukuncin"cewar mummy cikin kuka.

Sun jima yana rarrashinta,sannan tayi shuru,.

*******

Bayyana irin farincikin zahra da mamynta sukayi lokacin da maina yabata damar shiga gidanshi abune dabaze misaltuba,haka itama jidda taji daWin hakan koba komai zata samu natsuwa.

Ranar da zahra ta isa gidan nasu kuwa guri guda suka kwana da mamy,koya ta motsa mamy sannu take mata.

sosai tausayin iyayen nata ya cika zuciyarta,dan tafi kowa sanin son da suke mta.

"mamyn yara,kisa diamond ta shirya kuje anti natal,aduba lafiyarsu,tunda kinga yadda taita fama da rashin lfy"cewar maina lokacin da zahra taje gaishesu.

Fashewa zahra tayi da kuka,ta kama ?afafun sa tana faWin"kagafarceni daddy,na tuba"

hannu yasa ya Wagota ya rungumeta akaron farko tun faruwar lamarin"karkiyi kuka my diamond,?addararmuce tazo a haka,kuma na miki al?awarin hukunta koma waye,wanda yay miki hakan inaso ki cire damuwa,aranki don Allah"ya ?arasa hawaye na biyo idonshi.

shuru zahra tayi wata natsuwa na sake shigarta,tabbsa babanta masoyintane.


***********


Kamar yadda mahaifin mj yaywa mummy al?awari hakance ta faru,ya iso yola lfy,inda besha wahala ba,wajan ganin mj.

sosai mj yaji daWin ganin mahaifin nasa,bayan sun gaisane daddy yace"matarka jiya jin abinda ya faru tayi yaji zuwa gidansu,so banbi ta kanta ba tukunna,inaso ne yanzu in gana da mahaifin yarinyar nan,muji in akwai wata masalaha."

"daddy banaso a tursasu ko ay musu magiya,nafiso ko zasu yafemin suyi hakan dan rajin kansu badan an tirsasasu ba"cewar mj cikin rashin walwala.

"To bari inje office Winsu su haWani dashi"cewar daddy gamida mi?ewa ya nufi office Win.

Shigarshi tayi daidai da shigowar maina,ayko idanunsu ya sarke ana juna.

"Alhaji hassan"cewar maina

"Maina namu"cewar daddy cike da faraa suka rungumi juna kowa na mamakin ganin kowa.

Gefe suka koma nanfa hira ta tsinke kusan zan iya cewa sun mance da aynihin abinda yakaisu gurin.

Maina da daddy de,kusan aminan junane,a wani Sangaren ma daddy uban gida yake ga maina dan sosai ya taimaka masa da dukiyarsa alokacin shi be kai hakaba,shekarun baya lokacin duka suna ayki a lagos,bayan barowarsu can Winne yazamana zumuncin sede awaya,kowa na wa?ar ze ziyarci Wan uwansa amman yanayin ayki ya hana hakan,

wannan kenan.

Bayan sun Wanyi shurune maina yace"me kuma ya kawoka yola,baka faWamin na Waukoka a airport ba"?

Damuwace ta bayyana afuskar daddy sannan yace"Wankane majeed wlh yaje ya Waukomin mgn,ya Waukowa kansa,yaje abuja,yayiwa wata yarinya fyaWe,yanzu haka harda ciki take dashi to iyayen yarinyar nazo insamu inga ko Allah zesa asasanta"

Tunda ya fara maganar,maina bece komaiba,har ya gama,sannan,ya Wago ya dubeshi,yace"Alhaji,ita yarinyar da yaywa fyaWen itama ?arkace,domin autar ?atace zahra"

Arazane daddy ya Wago ya dubeshi yace bakinsa na harWewa "nufinka dama zahrace,yaywa hakan,ayko yazama wajibi ahukuntashi!"

"wallahi inde ni na haifi zahra wannan mgn ta mutu,har abada,yaje kawai yayta istigifari,yanzuma zan janye case Win muje gida"

"Maina yarinyarfa tana da hakki acikin yafe masa ko akasin hakan,baka ganin afara jin ta bakinta"cewar daddy cikin damuwa.

"Mu muka haifesu basu suka haifemuba,"cewar maina yana kaiwa nan ya isa gaban shugaban gurin.

Ayko cikin ?an?anin lokaci aka rufe case Win,akafito da mj,wanda jin ansalameshi yasa yacika da mamaki.

Bayanin komai aka masa har ransa beso hakanba so yayi ita abarta ta yafe da kanta,amman shi beso hakanba.

Duk yadda sukaso susashi ya shiga gidan na maina kasawa yayi sabida yanajin kunyar idon mahaifiyarta,dan yasan ko kowa ze yafe banda ita.

Lokacin da mamy taga daddy tayi mmkn ganinsa,gaisuwar girma da mutunci tai masa,sabida tasan wayeshi agurin mijinta.

bayanin komai maina yay mata,har zuciyarta bataso yafiyarba,amman bata da ja.

"ina neman alfarma agurinku,wannan abu na gidane,kuma Sarna de tariga data afku,in har munaso wannan yafiya ta tabbata ta har abada to in zahra ta haihu ataimaka abawa majeed auranta,don Allah,dan gujewa gori da tashin hankali a wani gidan saSanin nasan"cewar daddy atausashe.

Kusan mamy tafi kowa farinciki da hukuncin,dan ita dama tsoronta,waye zezo ya aureta bayan yasan har shege tayi.

Murmushi maina yayi dan har zuciyarshi shawarar tai masa yace"Alhaji duka ?a?ankane kuma ?ar?ashin ikonka suke,dan haka wlh komai kaga yadace ka zartar zamu bi"

Daddy yaji daWin karamcin da suka nuna masa,dan haka sawa yayi aka kira mishi zahra.

cike da girmamawa taje ta du?a ta gaisheshi,inda ya amsa cike da tausayinta.

"nine mahaifin yaron daya keta mutuncinki zahra,ki gafarceshi don Allah,ina neman afuwarki bisa laifin da yay miki"yana kaiwa nan ya du?a akan guiwowinsa ya haWa hanayensa guri guda,

da sauri jikinta har rawa yake ta mi?e tsaye tana kaWa kai,tabar gurin da gudu,tana kuka ta shige Wakinta, ta rufe kanta,watakan adakeka ahanaka kuka.

"Karka damu Alhaji komai ya wuce zamu rarrasheta,"cewar mamy.

Daddy jiki asanyaye ya koma yazauna,maina ne ya dubeshi yace"Alhaji nacema komai ya wuce,yarade namune,kuma muke da iko da su,kuma bamu haifi ?a?an dasuka fi ?arfinmu ba da yardar Allah so ka cire damuwa."

"to maina Allah yasa alkhairi muka haWa"cewar daddy yana murmushi.

"Amin ya Allah"suka amsa.

Sai dare daddy yabar gidan,zuwa hotel shida mj,bayan sun natsane,daddy ya dubi mj,yace.

"Majeed,nida mahaifin yarinyar nan,mun yanke hukuncin haWaku aure bayan ta haihu"

Arazane ya Wago kanshi ya dubi daddyn yace bakinsa na rawa"dad kuma ta amince zata aurenin?"

"no bata aminceba,kaima kuma ba amincewarka muke nemaba,umarni ne"

hawayene kebin idanunsa yace"dad ay auranta agareni,rahamace da kuma samun damar gyara kuskurena,zan rayu cikin ba?in cikine in akace,bata yafemin ba"

daddy yaji daWin kalaman na mj,rungumoshi yayi jikinshi yace yana Wan dukan bayansa"majeed inaso kazama jarimi,domin ya?ine zaka fara na soyayya,kazama lover boy,majeed,free ur mind,kasa aranka kai bame laifi bane,da hakane zuciyarka zata buga wasan daya dace my son i wish u all d best"cewar daddy yana dariya.

Mj cusa kanshi yayi jikin daddy Win yana dariyar dake nuna alamun yaji kunya.

*******

"mammy nayi mmkn jin wai kema kin amince da batun aurena da wancan laanannan Allah,haba...."bige mata bakin da mammy tayine yasa tayi shuru.

"Kidinga gyara kalamanki nanda watanni shida mijinkine shidin,kuma nasan kinsan ba na zagin mahaifinku bare kice aguna kika gani"cewar mamy cikin faWa.

"are you seriours mamy?"cewar zahra cike da mamaki.

Hawayene ya zubowa mamyn tace"zahra inbe aurekiba wa kikeso ya aureki,ya Sataki,yayi tarnishing image Winki,ya shafa black color a background Winki,zahra ribarki shine komai da yay miki back to sender,kinga zaki rayu as a queen agidanki,zaki samu darajar data dace dake diamond,abinda zaki haifa yana da ?enci agidan ubansa don Allah zahra karki watsa mana ?asa a ido"

"Duk wannan bayanin naki mamy,zeyi aykine in azuciyata inada raayin aureko?"cewar zahra

"Zahra aure ay dolene,koda baki da raayinsa"cewar mamy.

"Wlh mamy bazan taSa sonshiba,kuma duk wata biyayya ta aure wlh bazan masaba,no matter what mamy"tana kaiwa nan ta ruga da gudu Wakinta tana kuka.

mamy bata damu da kalaman na zahra ba,shiyasa ta mi?e tabar gurin.

*****

"haba daddy don Allah taya na shigar da case kawai se inji wai ka janye case Win,kuma nazo jin baasi kana faWamin wai zahra shi zata aura haba daddy,diamond batayi lalacewar da zaa haWata dashiba,sabida kowa yasani shiWin FASI?INE!!!"

"look hameed mune muka haifeku baku kuka haifemuba,secondly mafitarmu muka nema kuma mun samu,kuma what ever he is before,now he is ur inlaw ka kiyaye hakan"cewar maina cikin yanayin dake nuna no play.

Hameed be sake cewa komaiba,yayi masa sallama yabar gurin ransa na masa zafi,dan itama mamy dayaje gunta tana goyon bayan aurenne.


********


"Kamal taya zan iya fuskantar ta,wlh ni tsoroma take bani,ka ajiye batun wasa"cewar mj cikin yanayin damuwa.

"Mj wlh innine kai bazan baro yolaba sena fara kai kaina gareta,amman katashi kawani biyo dady,ay baa haka tabarmar kunya kawai zaka naWe da hauka mutumina"cewar kamal yana dariya.

Gyara zama mj yayi sannan yace"matsalar kamal ba garinmu dayaba,love distance akwai wahala,taya zan fara?"

"well,hakane maganarka,to amma abu na farko da zamuyi shine muje yola mu fara bada ha?uri,maana mukai kanmu,bayan munje sekuma muzo mu nemi transfer from kd to yola,shikenan mun zama fulani muma kaga in muka samu muka Waukota semu sake dawowa nan"cewar kamal yana dariya.

"are you seriours kamal zaka bini yola?"cewar mj cikin tsananin mamaki.

"Ofcourse abokina,ya?in ka nawane,so we are together in this insha Allah"kamal ya bashi amsa.

Rungumeshi mj yayi yana masa godiya.

*******

"Ni aganina zahra kiyi ha?uri kiyiwa iyayenki biyayya kiso abinda sukeso,shine mafita,sabida ?in bin umarnin daddyne yakaiki ga wannan ?addarar,amman wlh maganarsu har raina ina goyon bayanta inde gaskiya kikeso in faWa miki"cewar jiddah lokacin dataje gidansu dan itama yanzu bata aykin ta ajiye tukunna.

Gyara zama zahra tayi tace"jiddah biyayya ay tazamarmin wajibi,zan aureshi,amman abinda nakeso ki gane seya zaSi kabari akan ya zauna dani"

"in kuma kika samu yafiki sanin hanya,se labarin ya sauya"cewar jidda tana dariya.

Duka zahra takaimata tana faWin "ayni hanyoyina suna da yawa,saninsu se Allah"

**********

Yau su mj suka shigo garin yola dan zuwa suba zahra da iyayenta ha?uri.

Hannu biyu aka tarbesu,mamy tasa akai musu sha tara ta arzi?i..

bayan sun gaisane mj yasa ?afafunsa a?asa yace hwaye na biyo idonshi "mamy ke uwace,kuma nasan zafi da raWaWin da kikeji aduk sanda kika ga halin da zahra take ciki,wlh mamy ?addarace,ban taSa yiwa kowa fyaWeba se ita,may be ta haka ?addara ta shiryo aure tsakanina da zahra,wlh mamy na miki al?awarin kulawa da zahra sama da rayuwata,raina fansane ga farincikinta mamy,zan zamo bawa agareta wanda baya bu?atar ?enci,kuyi ha?uri ku yafemin"ya faWi cikin matsanancin kuka.

ita kanta mamy kukan take,maina ma seda ya share ?walla,yayinda itako uwar gayyar taja wani dogon tsaki ta mi?e tabar gurin,bayanta yabi da kallo.

"An yafema tuntuni kaji yarona,Allah ya kyauta gaba,ita kuma waccan drama doll Win karma ka damu da abinda take."cewar mamy tana murmushi.

"Allah ya baku zaman lfy,my son,sede inaso kasake jajircewa kai namijine"cewar

4 / 9