FASIKI NE COMPLETE HAUSA NOVELS BY ZAHRA MUHAMMAD SURBAJO.doc

Author :  Zahra Surbajo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   5 / 9

12K to 15K   out of 26.2K words

maina yana dariya.

Ba mj ba hatta kamar yaji daWin tarbar da akai musu.



Shiyasa suna komawa kaduna suka fara neman transfer,dan tafiya ya?in soyayya.


"kafin ka tafi yakamata kaje gidan su fareeda kadawo da ita,dan kaga ta jima agidansu"cewar mummy cikin kulawa.

"Mummy kibarta nasanta sarai wlh zata dawo,muna zaune zakiji ta dawo ni ba korarta nayiba jin labarin zahra yasa ta gujeni,mummy,laifin daze gogu shi ake zuwa bada ha?uri,wanda ko baze goguba,ko maganarsa baayi,kinga zahra jinina ce,banida maraba da itaa"cewar mj yana dariya.

"To ayni zani,dan bikin su fatima duk da komai baa cikin natsuwa akayiba,mamanta tazomin Allah sanya alkhairi"

"to sekin dawo"ya faWi yana dariya.


Anyi approving transfer Winsu dan haka parking sukayi shida kamal to yola.

wani abun daWin maina da kanshi ya basu BQ Win gidansa su zauna kamin su kammala aranging.

wannan abu yafi komai yiwa mj daWi bada wasaba.

*********

BAYAN WATA BIYU


Cikin zahra yanzu watansa bakwai,tana samun kulawar data dace,agurin iyayenta da ?an uwanta,

kullum tsanar mj ?aruwa take aranta musamman yanzu dayazo ya tare musu a gida,ji take kamar ta hayo ?an daba su kashe mata shi ta huta.


Yau da ?yar take iya tashi,dan gaba Waya jikinta nauyi yake mata,saukowa tayi a gadon,ta nufi toilet tayi wanka sannan taWanli daWi,amman da ciwo koina keyi.

kamar kullum takan Wan fita motsa jiki sabida kumburin da ?afafunta keyi,ayko fitowarta kenan sukai kaciSus,akaro na farko tun bayan dawowarsu gidan.

da sauri ta juya zata koma cikin gidan,cikin tafiyar masu ciki hannu a kan kwankwso,ayko shima hannun ya Wora yashiga kwaikwayon ta yana tura ciki gaba.

daddy da mamy dake tsaye bakin window sosai abun ya basu dariya,ganin be denaba harseda ta shige falo sannan ya koma yana dariyar cimma nasara.dan dama beso ta fitane,dan yanzu ?irarta tamafi da fitowa shi kuma baze jureganin wani na kalle masa ita ba.

Yau ?an uwan maina suka kawo masa ziyarar bazata,ga zahra tirtsi tirtsi da ciki a gaba,kunya ce ta kamasu duka kowa nagidan,dan basu san me zasuce ba,gashi harda mahaifiyar maina akazo,da sauran yayye da ?annenshi.

"wai maina zahrau aure aka mata baka sanar damu ba?"cewar kawu bello,yaya ga maina.

?an soshe soshe duka suka fara,anrasa jarumin daze fara basu amsa dan falon kowa sauraron amsar yake.

Shigowar mj falon besa sun san ya shigoba sabida tashin hankalin da suke ciki.tsayawa yayi yana karantar abinda ya faru da yasa kowa natsuwa haka.

"maina ko baka ji bane nace aure kayiwa zahra batare daka sanar damuba"cewar goggoji mahaifiyar maina.

Da sauri mj ya ?arasa tsakiyar falon cikin ?warin guiwa,ya isa gaban zahra wacce takeji dama ?asa ta tsage ta shige,ga wasu siraran hawaye,dake biyo idonta.

Hannu yasa ya kamo kafaWunta ya mi?ar da ita tsaye yana faWin"oya taso mu tafi asibitin madam motar tazama ready,kuma saura muje kici gaba da kukan allurar,"dubansa yakai gun maina yace"daddy don Allah ka dinga mata faWa,bata bin dokar likita,kuma kagade lalurar datasa aka mana aure,dan lfyrtane,amman batajin mgn sam,wai ita haushin ?in yin taron bikintane har yau bata huceba,nace ta kwantar da hankalinta inta sauka lfy daddy ze haWa mana big wedding"ya faWi yana ja mata hanci.itako mamakin kalaman nasane yasa motsi kirki takasa yi,sema sinne kai da tayi a ?irjinshi.

Kallonshi yakai gun goggoji,da sauri ya du?a yace yana sosa ?eya"don Allah kuyi h?r ban lura kuna nanba,barkanku da warhaka,da fatan kunzo lfy"

faraace ta bayyana akan fuskokinsu,suka amsa gaisuwar cikin sakin fuska,sabida sun fahimci shine mijin zahran.

Daddy ko tsananin mmk da mj ya bashi seda hawaye ya taru a idonshi,lalle zahra tayi dacen miji da baze bari ta kunyataba,gashi da ya rasa abun cewa amman cikin hikima yasa masa mgn abaki,cewa bata da lfy ne yasa aka Wauramata aure,kai lalle yaronnan wonderfull ne.

"maza majeed ku tafi asibitin pls kayi driving da kulawa"cewa maina cikin faraa.

Ba musu zahra tabishi,yana ri?e da hannunta zuwa mota,dan zatonta wasan ze ?arene a iya motar.

bayan fitarsune maina yafara mgn."kuyi ha?uri nauyi naji yasa nakasa zuwa sanar muku,duba da cewa yanayin ayki kuna gombe,zahra lalurar ciwon mara ta haWu da ita,inda watannin baya har asibiti ta kwanta,?arin jini da oxygen ba wanda batai going through ba,shine yasa likitoci suka bamu 48 hours amata aure,dan matsalar nada ala?a da hakan,shiyasa na bari seta haihu in zaayi taron sena sanar muku"ya faWi yana ware ido,dan betaSa ?arya datakai girma da farashin wacce yayi yanzuba.

Sosai suka fahimceshi sukai mata fatan samun lfy,da kuma fatan sauka lfy.

wannan kenan.


"Stop the car"cewar Zahra batare data kalli gefen da yake ba.

"What's wrong?"ya faWi ba tare daya tsaya Winba.

"jakin inane kai,nace ka tsaida mota,ko bakajine?"ta faWi a fusace

Dariya yayi me ?ayatarwa,sannan yay ?asa da muryarsa,bakinshi setin kunnenta,yace".that's the way it works in the real world of jakuna madam"ya faWi yana cije laSSansa.

"wlh idan baka tsaida motarnanba sena nuna maka you are dealing with an agent for a terrorist organization,"ta faWi cikin kakkausar murya.

"fantabulus"ya faWi yana dariya

"i'm too wiped to argue with you,"she warned

Dariya yake me rai da lafiya,danshi yanayin nata ya masa,

"Rack out with me pls"ya faWi cikin tsokana.

"in banda kai Win dabbane taya zaka yarda ka haWa hanya dani,koda yake banyi mamaki ba,laanannen Allah ze iya yin abinda yafi hakama"

maganar ta bugeshi,amman seya shanye yace yana murmushi,"naji koma meye ki faWi,nide bazan tsaya ba se naje na duba lafiyar babyna dake cikinki,secondly ga wasu ?ansanda can agabanmu in da bu?atar neman taimakon atsaidani"ya faWi yana shafa gemunsa.

"i'm not going to scream for help,if that's what you're asking.this is between me and you,da kaina zanyi maganinka,wlh karamin dan iskane kai"ta faWi kamar zata sha?eshi dan ba?in ciki.

"that's the way i see it too."ya faWi gamida maida hankalinsa kan tu?in.

kifa kanta tayi akan cinyarta ta fashe da kuka dake nuna zallar ba?in cikin da take ciki.

"ki tashi zaune kin dannemin baby,inba hakaba wlh zansa hannu in Wagoki"ya faWi muryarsa ba wasa.

cike da mamaki ta Wago kanta akaro na farko datakai dubanta inda yake,murya can ?asa tace "what father of the year attitudes is this?"

"do as i said or else"ya faWi yana murmushi.

"or else what!?"ta faWi hawaye na biyo idonta,gamida mi?ewa zaunen tana ci gaba da kukanta.

kukan jinshi yake har ransa amman be nunaba dan akwai bu?atar ya nuna jarumtarsa.

har suka iso asibitin da suke ayki shida kamal bata dena kukaba.

fita yayi ya zagayo ya buWe mata,?ofa,yace"fito in kuma bazaki iyaba in Waukoki"be gama rufe bakiba ta sa ?afafunta waje ta fito.dan ta tsani ko hijabinta ya ri?e.

direct office Winsa yakaita,sannan yay mata umarni data hau,gadon dake office Win na duba marasa lafiya.

harara ta watsa masa tace"Allah ya isa tsakanina dakai wlh bazan taSa yafe maka ba har abada"

"ki adana kalamanki har zuwa ranar da zanzo neman yafiyar,amman yanzu bashi bane akan layiba,oya zo ki hau gado ko inzo in hawo dake"ya faWi cikin tsare gida.

Fahimtar da tayi yin abinda yace Winne zesa suyi saurin barin gurin yasa taje ta hau ta kwanta.

"Waga rigarki"ya faWi cikin dakewa.

tashi tayi zaune tace,"kasan zan Waga rigar meyasa baka faWamin kan mutaho ba,bayan yanzu doguwar rigace ajikina,taya zan Waga kaga cinyoyina"ta faWi hawaye na bin idonta.

"oh wai cinyoyin that i don't see before?"ya faWi yana kallonta cikin ido kallon da ba wata bace dazata iya jureshi,matu?ar gabanta lafiyarshi lau.

?asa tayi da kanta tace bakinta na harWewa"Allah ya isa"ta koma ta kwanta ta janye rigar.

Daga ita se farin pant,daya kwanta ajikinta me taushi da burgewa,se hips Winta daya baje gefe da gefe,fararen cinyoyinta abun burgewa.

Mi?ewa tsaye yayi,yasa hannayensa akan fatar cikinta,ay kamar jira abinda ke cikinta ya fara wani irin motsi,hawayene kebin idanun mj,hannunshi yasa ?asan mararta sannan yasa kunnenshi ajikin jikin cikin yace a tausashe"babankane ya taSaka,Wana ina fatan haWuwa dakai cikin aminci"ya faWi yana shafa cikin.

hannunshi ta bige tace cikin faWa,"kai zaka haifi namiji,ba niba,me mugun fata,to ni mace zan haifa"

murmushi yayi yaci gaba da auna cikin batare dayace mata komaiba,dan ya tabbatar da komai lafiya.

Basu baro asibitinba seda ya kammala duba marasa lafiyar dake jiran zuwanshi,ayko masifade agun zahra da zagi da tsinuwa ba wabda beshaba na ajiyeta a asibiti da yayi,uwa uba kiran abinda ke cikinta da Wa namiji da yayi.


shiyasa suna tsayawa ta fice a motar tashige Sangarensu.

gyara parking yayi sannan shima ya shige Sangarensu da kamal.

a kwance yasamu kamal yana latsa waya,duka ya kai masa yace"guy how per?

"Baka da kirki zaka fita amman ko kanemi rakiyata ka barni zaune agida kamar mace"cewar kamal yana harararsa.

Zama yayi gefenshi ya cire rigar jikinshi,yace yana sauke ajiyar zuciya"bro tafiyarce ba shiri da madam fa muka fita"ya faWi yana dariya.

"da gaske ko wasa mj?""cewar kamal fuskarsa Wauke da yanayi na mmk.

"wlh,asibiti na kaita,amman fa a hanya ba kalar balain da baai fatan faruwarsa akaina ba,kai ?arshema de cemin tayi am dealing with an agent for a terrorist organization."ya ?arasa maganar yana dariya.

dariyar shima kamal yake yace"wlh na ?osa inga kalar zaman auren da zakuyi kaida zahra,abin ze bada citta time Win da take cin ubanka""

gaba Waya dariya suka sa,kamin mj yace"kamal ina ?aunar yarinyrnan da dukkan zuciyata,wlh Allah kamal domin farin cikin zahra zan iya bada rayuwata,"

"ta cancanci fiye da hakama mj,nide shawarata gareka shine kayi ha?uri sabida soyayyace ta Sangare Waya to akwai alots of problems,dan haka kayi h?r ka kauda kai ze wuce".cewar kamal

"Insha Allahu zanyi ha?uri kamal da komai daze zo daga gareta."

"Allah ya baka iko abokina"

"amin"

***********


Bayan watanni biyu.


Zahra yau tun safe takejin bayanta na mata ciwo kaWan kaWan,gashi gidan yau sun WaWe antafi gaida goggoji bata da lfy ankawota asibiti anan yolar daga can gombe.

Sanin da tayi weekend ne su mj basa fitane yasa ta?i fitowa tai zamanta a falo dan ta tsani,haWuwar da sukeyi Win.

suko mj da kamal zaune suke,suna yin ludo a waya,a harabar gidan,batare da tunanin komaiba,amman shi mj dama tunda watan haihuwar yatsaya baya iya koda baccine isasshe,fatanshi kawai yaji ta haihu lfy.

Zahra tun tana Waukar abun na wasa ne harde ta fahimci yau de ranace ta faWan ?arshe,gashi a falon ?asa take wayarta nacan sama,bare ta kira wani.

rarrafowa tayi tanaso tazo ta buWe ?ofar amman ina ta kasa,tana kwance agurin tana kuka kamar daga sama take jiyo sautin muryar mj,suna hira.

Runtse ido tayi tana dukan ?asa,na takaicin neman taimakonsa da zatayi,dan tasan dole seta nemaWin.

wata murWawa mararta tayi,batasan sanda ta ?wallah ?ara me Wauke da sunan mj acikiba,inda tace"majeed kataimakeni zan mutu!!!!"da dukkan ?arfinta.

zumbur suka mi?e da gudu suka nufi falon sede kamal har ze shiga se kuma yafasa yabar mj Win,shiko mj da gudu ya shiga falon inda ya smeta kwance ta ri?e mara tana yarfe hannu.

ay tana ganinshi da dukkan ?arfinta ta ri?eshi,guiwowinta na ?asa duk ta ji?e da gumi da?yar take iya cewa"ka rabani da ciwon nan zan mutu,wayyo Allah na bayana"tayi mgnr hawaye na biyo idanunta.

Shima hawayen yake,na tausayinta,yn?urin Waukarta yayi da niyyar tafiya asibiti,kawai,yaji ?an Wa,ayko da sauri ya kwantar da ita akan tiles Win ya wara mata cinya,dan masifa harda pant ajikinta,hannu yasa ya ccire pant Win,yana mata sannu,"sorry baby,daure kinji Allah yay miki albarka,kiyi nishi da zaran kinji shi,kinji ko zaki haihu lfy"sune kalaman dake fitowa abakin mj,

ayko nanfa,ta rirri?eshi tana neman taimakon Allah,shima haka,ayko nishin ta fara,da sauri ya kwantar da ita,ya je ta gabanta,yana ri?e mata ?afa,ayko sega babyn gaba Wayansa ya faWo a tafin hannun ubansa se chala kuka yake,dake bada tabbacin lafiyayyene.

mj rikicewa yyi,da ganin Wan a hannunsa kawai seya fashe da kuka ya rungumeshi ,yana sumbatarshi,zahra dake kwance kallonsu kawai take abun na Waure mata kai,rigar jikinshi yacire ya rufawa babyn sannan ya je kusa da ita,ya zuge rigarta,ya sa babyn a ?irjinta dake ta faman tsala ihu..

hannunta har rawa yake ta rungumeshi ajikin nata,mi?ewa yayi yace"ki kula da kanku bari,in Wauko firstsaid,pls"ya faWi lokacin daya fice da sauri jikinshi duk jinin haihuwar.

da sauri kamal ya nufeshi,fuskar mj ce ta bashi tabbacin an haihu lafiya,

"kamal zahra ta haihu,ta haifamin baby boy,alhmdllh inacikin farinciki"ya faWi yana daga kamal

"na tayaka murna,mj,Allah ya raya ya bata lfyme Worewa"cewar kamal yana dariya.

First aid Win daya tanada domin haihuwar tata ya Wauko sannan ya koma ya samu,tana nan kwancen,cibiya ya yanke,sannnan ya mata allura,hannu ya mi?a ya karSi babyn,sannan ya mi?a mata hannu da nufin Wagota,se ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ga mamy da gudunta,ta shigo dan tuni kamal ya shaida mata ta haihun.

Da sauri mj ya waiga dan ganin waye,se yaga mamy,mi?ewa yayi yana sosai kai yana mata sannu da zuwa.

gun zahra ta nufa wacce ke zaune ta rungumeta tana faWin"kiyi ha?uri diamond Wita bansaniba da bazan fitaba,edd Winki be gama cika bane yasa"

rungume mamyn tayi itama tana kuka tace"ay danace zan biku ?i kukayi,kinjawomin se wannan ba?in karanne ya taimakanil"ta ?arasa maganar tana kuka.

mj ko ajikinshi yace yana murmushi"ay Allah ya kawo komai cikin sauki mamy,"ya faWi gamida mi?awa mamyn jinjirin yafice ransa fess ya nufi Sangarensu.

wanka ya farayi ya sauya kaya sannan ya kira wayar daddynshi ya shaida masa anyi haihuwar.

daddy yaji daWin jin cewa ta haihu lafiya,fatan alkhairi yayi sannan sukayi sallama.

mi?ewa yayi ya shiga toilet ya Wauro alwala yazo yafa nafila,bayan ya idar da sallah ne ya Waga hannunsa sama ya fara addua kamar haka.

"ya Allah natuba kayafemin laifukana nida mahaifiyar wannan yaro,ya Allah wannan aure inda alkhairi acikinsa na ro?eka daka tausasa zuciyar zahra ta soni mu zauna lfy,Duk wani abu daze kawo tashin hankali ko damuwa Allah ka kaudar mana dashi,wannnan jinjiri kuma Allah ka rayashi kai masa albarka,kasa yazamo abin alfahari ga addinin musulunci ameen"sannan ya shafa.

Kamal ne ya shigo ya zauna kusa dashi yace"to angon ?arni ay zama be ganmu ba tashi zakayi mu tafi mu siyo kayan baby tunda dama ba abinda muka siya."

murmushi yayi ya dubi kamal Win yace,"kamal inason Wana da dukkan zuciyata,bandamu da hanyar dayazo duniyaba,what i know kawai jininashi,amman confirm zahra bata sona inaji kamar inyi step back"

"step back to where?kana da hankali kuwa mj,taya zaka fara rauni tun yanzu,ay bazaka duba ?iyayyarba,kawai son da kake mata zaka duba,ze baka ?warin guiwa,kuma wlh ko ita tasha ?arya tace bata sonka,kawai laifinka ya danne son,kuma asannu ze wuce,pls be a man don Allah"cewar kamal cikin sigar rarrashi.

"To kamal naji kuma zanyi ?o?arin ci gaba da rakawa"

"yauwa ko kaifa"cewar kamal yana dariya.

"Mu jira ?awarta tazo jiddahn nan semu fita tare ta tayamu Wauko abinda ya dace kar muje mu Wauko shirme"cewar mj lokacun daya mi?e daga kan abun sallah.

*********

mamy ko bayan fitar mj,aykin gyara zahra da baby tashiga yi,inda cikin ?an?anin lokaci,bame cewa haihuwa akayi,mai jego ta fito fess da ita haka babyn shima me kama da babanshi anshiryashi cikin fararen kayan sanyi,daya ?ara fito da ?yan nashi.

Maina yayi murna lokacin da mamy ta mi?a masa babyn,sun karSeshi matsayin ?addara shiyasa suke mantar da kansu ta hanyar dayazo.

"akira mahaifinshi yay masa huWuba,"cewar maina yana sumbatar yaron.

"To Alhaji wannan aykinkane ay"cewar mamy tana dariya.

Mi?a musu yaron yayi sannan ya fice zuwa Sangaren nasu mj.

sallama yayi dasu,ayko da hanzari suka fito,suka dur?usa agabanshi,murmushi yayi yace"ku mi?e iyayen Wa,kuma yanzu ay kun girma tunda kun zama iyaye"

sunkuyar dakai sukayi,suna murmushi,mainane yaci gaba da cewa"majeed kaje kayiwa yaro huWuba,kasa mishi sunan da kakejin ya maka,naji ?o?arin da kayi Allah ya ?ara mana kusanci,kaita ha?uri kaji ba wani abu da beda iyaka se ikon Allah"

"insha Allahu dady zaa sameni me ha?urin"cewar mj kanshi a?asa.

?arar buWe get ne yasa suka waiga su duka jiddace,fuskarta Wauke da faraa wacce ko baa faWaba kasan tasamu labarin haihuwar.

?arasowa tayi gurinsu ta du?a ta gaida daddy sannan ta gaidasu mj gamida yi musu barka,ta shige cikin gidan.

kamal ko dama betaSa ganinta ba se ranar,shiyasa gaba Waya hankalinshi yatafi gurinta yama mance da maina suke tare.

barin gurin maina yayi,duka mj yakaiwa kamal yace"kai kallon ya isa haka mana karkasa ?ar mutane ta faWi"ya faWi yana dariya.

"mj who is she pls?"cewar kamal cikin za?uwa.

"zahra's best friend jiddah"ya bashi amsa.

Murmushi kamal yayi,yace"Allah ysasa rabonace amma batu na gaskiya nifa nayi mata"

"hhhhh watakan har ma ka aureta,to duk zalamarka wlh seka jira,abun layine,se anfara dani tukunna.

Suna dariya suka rankaya cikin falon yiwa yaro huWuba.

a falo suka sami mamy gaisheta sukayi,ta amsa cikin sakin fuska,tace"ku ?arasa ciki jiddah tazo suna cikin Waki"

umarninta suka bi suka nufi Wakin bakinsu Wauke da sallama,suka shiga.

zaune take,ta rungume babyn yanashan nono,jiddahce ta amsa sallamar,yayinda ita uwar gayyar tai kicin kicin da fuska,

da?yar ta amsa gaisuwar kamal,dan shima haushi yake bata.

"Majeed kunde yimana wayo babynmu da abbanshi yake kama"cewar jidda cikin faraa,

Murmushi mj yayi yace,"?arfinjini aka fiku,jiddah,dashi da sauran ?annenshi da zata haifomin duk ni zasu biyo"

"uwar waye zata haifa maka wasu ?a?an,?lalle Wan iskane kai na gidi"cewar zahra cikin zafin rai.

Daga jiddah har kamal,maganar batai musu daWiba,shiyasa jiddah tace"meye haka zahra kikeyi,taya zaki dinga ce masa Wan iska,agabanshi,why zahra?"

"ba Wan iskan bane,koko ?arya akai masa,tsabar iskancinshi nefa yajanyo zuwan wannan yaron duniya,ta dattin zina,wlh ka cuceshi,koshi nasan baze yafe maka ba"ta faWi hawaye na biyo idonta.

maganar tawa mj zafi matu?a gaya,amma seya cije yace"banida haufi zahra Wana zesoni,sabida ni na karSeshi da dukkan soyayyata,bankuma taSa shaawar kallonshi amatsayin Wan daba aurene ya baniba,da uwarshi batai kamanceceniya da mutanan banza ba ubansa bazeyi silarsa zuwa duniyaba,inaso ki ri?e wannan har iya ?arshen rayuwarmu,"yana kaiwa nan ya matsa kusa da ita yasa hannu ya Wauki babyn acinyata,da sauri,takai hannu da niyyar amsa amma be bataba yasashi akafaWa,ya juya ze fita,da sauri tace"ina kuma zaka fitarmin dashi?"

be kulataba yasa kai yayi wucewarsa tare da kamal,zata bishi jidda ta ru?ota tana faWin"ina zaki ?aramar mara kunya,wlh zahra inkikakai bawan Allahnan bango ya gujeki kin kaWe,kowane yake lalata mace ya aureta,ke kinsamu shine kike masa irin wannan wula?ancin,kifa tuna ciki akace kinyi hydar ya gujeki,shida kike so Win,to ?addara auranki yayi yaji fanko,ze cigaba da zama dakene,wlh kiyiwa kanki faWa"cewar jiddah cikin matsanancin fushi.

"Amman fa kinaji har goriyamin shi meyasa baki mishi faWanba dalailul khairaty,seni marainiyar wayonki"cewar zahra cikin fushi.

"ke kika fara masa kuma ya rama,meye to"cewar jiddah gamida mi?ewa ta fice aWakin taje falo gun mamy,tasameta ita kaWai.

faWa mata abinda ya faru tayi,ayko mamy taji rashin daWin abinda tai masa ba,"jiddah tunda haka ta zaSa musa mata ido,ayshi majeed Win yafita koma metaketa?ama dashi,kisa musu ido"

ayko jidda na zaune kiran mj is iskota dan haka mi?ewa tayi ta fita jin dalilin kiran

a tsaye tasameshi shida kamal sunata kallon babyn da mj yaywa huWuba da Muhammad.

"don Allah majeed kayi ha?uri da abinda diamond tayi,bata kyautaba"cewar jiddah lokacin data ?arasa kusa dasu.

murmushi yayi yace"bakiji da wanne suna kika kirataba,diamond fa,jiddah,to ay baa samunsa tasau?i dama,karki damu"

Murmushi tayi tace"wlh mj zaman auranku,seya sa nishaWi azukatan duk wani masoyinku dan irin zaman a littattafan

5 / 9