ABU ZAID HAUSA NOVELS COMPLETE BY SASAAL.doc

Author :  Nafisa Aliyu Salsal Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   10 / 43

27K to 30K   out of 126.7K words

muka haWu"

Da mamaki kwance a muryoyinsu Mommynta da Alhaji Sunusi suka haWa baki wajen faWin

"Basketball kuma? Hassada kikeyi da Waukakarsa"
Da sauri Siya tace "a'a"

Cikin barazana Mummynta tace
"Siyaa kiyi mana bayani menene dalilinki kafin nayimiki abinda bazaki ji daWi".

Da kame-kamen da tasan bayaninta bazai yimusu daWi ba tace

"natsani wasan ne saboda shine dalilin fara shan sigarin Abu Zaid, amma kallon da yakemin ne yasa na ?ara tsanarsa kuma ko na gayawa Muhammad ba zai yarda da ni ba"

kamar ta faWi mugun abu haka Alhaji Sunusi ya yamutse fuska ransa fal tsanar ?alhatu da zuri'arsa.

numfashi Mummynta ta sauke haWe da ?ura mata ido alamun ta cigaba suna jinta

"Abu Zaid yanason Basketball, amma Daddy ya hanashi bayan ya gama wahala yakai matakin ?asa,yace Business yake so yayi ba aikin wahala da tsalle-tsalle ba"

Siya ta ?arasa faWa komai daya faru a waccen lokacin na dawo mata.

Cikin Wacin zuciya da kuma tsanar Abu Zaid da Mummynta takeji a ranta tace;

"amma Siyaama kanki ya samu matsala, kawai saboda wannan dalilin sai yasa ki tsani Zayad kinsan waye Zayad kuwa? sau nawa kikeso na ja miki kunne a kan Ibrahim? Tayaya ?alhatu zai barshi ya zama ?an wasan ?wallon kwando tunda burin mallakar dukiyar da ba nasa ba ne a ranshi,
Yayaa ina ganin magannan ba anan ya dace muyisa ba ina bu?atar ganin Nenne"
Ta ?arasa faWa tana kallon Alhaji Sunusi.

Kai Alhaji Sunusi ya Waga mata don yagane so takeyi su je Tofa a gogewa Siyaa tunanin Abu Zaid.

A daren ranar Alhaji Sunusi ya kira Muhammad ya naimi alfarmar tafiya da Siyaa.
Muhammad bai cee a'a ba fatan dawowa lafiya yayi musu.


A can Legos wajen Taron buWe sabon Ma'aikar Nazeer.

Taro ya shirya na gani na faWan daya tara wayayyun mutanen da mafi akasarinsu Abokanan Kasuwancinsa ne, da yawan su sun san Abu Zaid saboda kasuwanci ya taSa haWasu, wasun su sunyi farin cikin rashin hallattar Abu Zaid, saboda yawancin su damfararsa sukayi suka Soyewa ganinshi.

Nazeer ya Wan rame saboda damuwar Sacewar Abu Zaid, rashin Abu Zaid a cikin rayuwarsa wani giSi ne da bashi da abin maye gurbinsq da shi. Abu Zaid bai taSa cutarsa ko cin amanarsa ba, amma sai gashi shi yazama Waya daga cikin waWan da sukayi silar rugujewar rayuwarsa, yasan da bai bada shedar da gaske Abu Zaid yana neman Hudayya ba da Mahaifinsa bazai amince da zancen Hudayya da na Yan'uwanta ba.

Bayan angama taro kafin Mutane su watse Nazeer ya nemi alfarmar ayiwa Abu Zaid Abokinsa kuma Dan uwansa addu'a Allah Ya bayyanashi Ya kuma kareshi a duk inda yake.

Dukka waWanda suka sanshi idan aka cire Taufiq sai a lokacin suka san Abu Zaid Sata yayi ba ?in zuwa taron ya yi ba, a take sai jikin su s'yayi sanyi.

Taufiq Wani irin gumi mai tahowa tun daga cikin gashin Kaa har ?irjinsa sane yake tsatsafomai.
Da wani irin sauri ya bi bayan Nazeer dake ?o?arin shiga Mota. Da rawar murya yace "Nazeer ina bu?atar magana yin dakai yanzu Please"
Nazeer fasa shiga Motan yayi ya bi bayan Taufiq suka nemi waje suka zauna.

Bayan sun zauna Taufiq ya ro?i Nazeer ya sanar da shi yaya akayi Abu Zaid ya bar gida, Sata ya yi kome?
Nazeer ?wallarsa ya sharce yana jin kamar idan ya bawa Taufiq labari zai Wan samu sau?i a cikin ransa, don haka ya gyara zama ya fara ba shi labari.

Kuka da ba kasafai Namiji mai jin daWin duniya yake iya yiba Taufiq yakeyi bayan ya ji labarin taimakon da Abu Zaid yayiwa Hudayya. Nazeer na tayashi.

kenan da baiji asalin labarin ba haka zata rabashi da ?ar Aljanar Matarsa? cikin tunanin irin sakayya da yayiwa Abu Zaid yace;
"shekaru biyu da Woriya da suka wuce Abu Zaid ya zo tare da Hudayya, Hudayya tayimin ?arya mai girma Nazeer saboda bansan komai akan Ahalin Ibrahim ba, Ibrahim ya rasa ?afa Waya amma duk da haka banji tausayinshi ba na koresa daga aiki, yanzu haka bansan ina yake rayuwa ba, ko yana Gidan da na kakamai ko ya tafi wani wajen bansani ba"

kamar hoto haka Nazeer yake kallon Taufiq na tsahon wasu mintoci, kafin ya mi?e batare da ya ce mai komai ba yabar wajen,shi bai ga ma amfanin labarin Taufiq Win ba tunda ya fitar ya kori Abu Zaid daga rayuwarsa to manene ya rage?. Har Motar Nazeer ya bar wajen Taufiq na zaune bai motsa ba saboda takaici.
Sha'awar Hudayya da yake ji kamar ba zai daina ba Abaya duk sai ya bi ruwa nan take.

Bayajin sakin Hudayya kaWai zai wadatar da shi wajen hukuntata dole sai ya yi mata wani abinda sha'awar ?arya ko cutar wani zau fice daga a ranta.

A San??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????garen Abu Zaid

Drivern dayake jan Baturen ne ya dakatar da securities Win dake ?o?arin janye Abu Zaid daga bakin Ma'aikatar.

Baturen da shekarunsa zasu bawa arba'in baya ne ya sauko, da turancinsa da basa fahimta da kyau yace su taimaki Abu Zaid ya mi?e su daina jansa.
Rawan da jikin Abu Zai yakeyine yasa ya kasa tsayuwa da kyau, Mota Baturen yace a shigo da shi don yana tsoron shiga Ma'aikatar da shi don bai san wanene shi ba. Kallo irin na ?urilla Bature John yake yiwa Abu Zaid kafin ya tambayesa yanajin turanci?

Abu Zaid amsa ya bashi da turancin dayasa Mr John ?ara kallon cikin Idanuwansa da har lokacin rauni ne lulluSe cikin su da kyau.

Murmushi Mr John ya yi kafin ya ce;

"ina da muhimmin abinda zanyi yanzu amma zan haWaka da driver ya kaika gidan ku idan iyayenka sun amince nayi al?awarin taimakon ka, ina ne garin ku?"

kai Abu Zaid ya dafe sunan ?auyen su Siyaa da address Win gidan su ne kawai ya rage a kanshi don haka kai tsaye yace "Tofa".

Mr John yasa ansiyawa Abu Zaid abincin da ya tsakuri kaWan saboda bakinsa da ya jima bai wanke ba, sannan suka Wauki hanyar Tofa shi da Driver.

A washe garin ranar da su Siyaa suka sauka Tofa Motar Mallam Sa'adu Driver da ya Wauki Abu Zaid yayi parking a dai-dai ba?in bishiyoyin dake ?ofar gidan.

A mota Mallam Sa'adu yabar Abu Zaid shi kuma ya sauko ya matsa kusa Yaro ya tura ayi masa sallama da mutanen gidan.

Jin sallama yaro kuma yace Abu Zaid aka kawo yasa suka yo waje dukkan su Nanne,Alhaji Sunusi,Siyaa da Mommynta.

Da ?warin gwiwa Abu Zaid ya Woraga sandarsa ya sauko ganin sun fito gaba Waya har da Siyaamar shi.

Sai dai irin kallon da kowannen su yake binsa da shi ne yasa jikinshi yayi sanyi, Siyaarshi ta ?ara zama ?ar gayun matashiyar budurwa duk da yaji ance tayi aure.
cikin rawar murya bayan ya Wogaro sandarsa ya matso kusa da su yace "Siyaa"

Siya daga yadda ya kira sunanta tasan dagaske Abu Zaid ne,sai dai har cikin ranta ?ya?yami da mamakin rasa ?afarsa Waya takeyi da kuma irin ramar dayayi. Jiki a sanyaye ta?ara matsowa kusa da shi,cikin Wari-Wari da ?ya?yamin dake kwance asaman Fuskarta ta ce;
"Yayaa kai ne ka koma haka maiyasameka ka koma haka? ina Daddy mai yasamu ?afarka Waya ya guntule?"

Abu Zaid bai bata amsa ba sai Kukan da ya fashe da shi don baiyi tunani akwai yanayin da zai shiga ya hango ?yamarsa a idanuwan Siyaa ba,
Da sanyi Muryarsa dake rawa yace "Siyaa bakiyi farin cikin ganina ba ko saboda banzo a yanda kike so na ba a baya?"

Siya dasauri ta toshe hanci tana komawa baya haWe da zare iduwanta, gefe ta matsa takwara amai,saboda Wan warin ranar dake tashi a jikinshi da kuma bakinshi dake Wan bugawa.
Hakan da Siyaa tayi ba?aramin faranta ran Mummynta da na Alhaji Sunusi yayi ba, saSanin Drivern daya kawoshi da Nenne dake tsaye suna kallon ikon Allah.

Abu Zaid kansa ya sunkuyar ?asa hawayensa na Wiga a cikin ?asa.
Daa labari a ka bashi da ya ?aryata, har wani irin wari yake yi da Siyaa zata toshe hancinta tana amai? Dama kenan a baya kyansa, tsaftarsa da gayunsa takeso? to manene ya ragemai kuma? Tasa ta riga ta?are.

Cikin isa da rashin tunanin mai gobe zata haifar Mummynta ta matso Wan nesa da shi alamun kar itama taji warin dayake yi sannan ta ce
"Ibrahim zuwa yanzu ya kamata ka nemi gobenka don ?ata tafi ?arfinka kai da annamimin Ubanka, kasan wa take aure? Hamsha?i mai arzi?in Win da baya zalama da sanya ido akan na wa su, ka ri?e maganganuna ko Allah zai taimakeka ka zabura ka nemi gobenka domin na lura ?wa?walwarka da ta Ubanka ya jima da toshewa, karka ?ara neman Siyaa domin Siya tafi ?arfinka,mai zatayi dakai Gurgu,mai warin baki da na jik.."

Marin da Nenne ta saukewa Mommyn Siya ne ya hanata ?arasa abinda tayi niyyar faWa, Da faWa sosai Nenne ta ce;.

"Ya isheki haka Ziyaada wani irin zuciya gareku fisabilillahi ?alhatu Mahaifinsa, ne amma da ya samu mai taimakonsa kai tsaye saboda soyayyar ?arki ya taho garinku, Yaro duk ya rame ya lalace ga ?afa Waya a gutsure amma ku kasa tausayamisa, itama waccen munafukar har da Aman gulma ashe son da kike ikirarin kina yimai na ?arya ne, ma za wata rana naji kina kiran sunansa sai na fasa bakinki sha-sha-shai kawai. Kuma wallahi duk wanda ya ?aracin zarafin Yaron nan bada yawuna ba idan bazaku taimakesa ba ku barshi mana haka yaji da abinda yake damunsa"

Mallam Sa'adu Driver bai taSa ganin rashin tausayi irin wanda sukayiwa Abu Zaid ba,ba su bashi wajen zama ba,ba su ba shi ruwan sha ba balle abinci,ba su tambayi dalilin da yasa ya zama haka ba don daga shigarsu kasan ma su wadatar rayuwa ne,?arshe suka tozartashi duk da tsananin taimakon dayake bu?ata a lokacin.

Har lokacin Abu Zaid bai Wago ba sai yakejin jikinsa kamar ba nasa ba, yanajin takun su har na Siyaa suka koma cikin gida sai Nenne kawai ta tsaye, bata Soyewa Mallam Sa'adu dalilin barin Abu Zaid gida ba.

Sai dai sun gano ainihin gaskiya abinda ya faru a ?uraren lokaci, domin ita kanta batasan ina Mahaifin Abu Zaid yake ba kuma tana kyautata zaton baya Zaria, amma su matsawa Abu Zaid da tambaya wata?ila ya tuno ya gaya musu. Ba tare da ?yan?yami ba Nenne ta kamo hannayen Abu Zaid da suke a yamushe cikin rawar murya kuka ta ce;
"karka Wauki nakasar ka amatsayin kasawarka Ibrahim kayi gwagwarmaya kuma ka ro?i Allah wata rana komai zai zama labari"
kai kawai ya Waga mata saboda tsoron magana ma yakeyi. Har su Abu Zaid suka shiga Mota Nanne bata tafi ba har sai da suka Sacewa ganinta.

Da haka Abu Zaid yabar ?auyen Tofa Soyayya da tausayin mutanen duniya na barin ranshi.

Bayan su Abu Zaid sun dawo, Tafinta aka nemo yake sauraren Mallam Sa'adu ya kuma fassarawa Mr John abinda ya faWa.

Ran Mr John ba ?aramin Saci yayi ba cikin Wacin zuciya ya tambayi Abu Zaid ina Mahaifinsa yake? kansa Abu Zaid ya dafe haWe da girgizarwa kamar wanda a ka tambaya mugun abu. Dakatar da shi Ne John yayi saboda gudun matsala.
Masau?i mai kyau Mr John ya kai Abu Zaid.

Da dare yayi bayan Abu Zaid yayi wanka anyi misa aski yayi brush, likita Mr John ya kira ya duba masa shi, saboda zazzaSin da ya rufe shi, Allura likita ya yiwa Abu Zaid haWe da basa magani. Bayan wani lokaci barci mai daWin daya jima baiyi ya Waukesa.

&washe gari bayan Abu Zaid ya karya Me John ya tura a kirawo masa shi.

A ladabbace Abu Zaid ya gaishe shi, Mr John ya amsa yanajin Soyayyarsa a ranshi takaitaccen labarin shi ya so ji.

Iyakacin abinda Abu Zaid ya iya tunawa ya bashi labari.

Kai Mr John ya jinjina kafin ya tambayesa maiyake burin zama a rayuwa tunda da ?uruciyarsa.
Murmushin tuna marafin shanye-shayensa ya yi kafin Allah ya tsayarmai iya kan sigari, sannan yacewa Mr John burinsa na baya shine ya zama Basketball player, har mata?in ?asa yakai amma daga baya mahaifinsa ya hana.
Shi yanzu ba shi da wani buri daya tunda ya rasa ?afa Waya waccen burin nasa ya ?arasa rushewa gabaki Waya, sai dai ya zama Wan kasuwa idan zai taimakamai da jari.

Kai Mr John ya girgiza sannan ya fara magana da salon ?arawa Abu Zaid ?warin gwiwa.

"Rasa ?afarka Waya bashi ke nufin mafarkin ya rushe ba Ibrahim, kasawa ranka da zuciyarka zaka buga kuma zakayi nasara, idan har da gaske kanada ?warewa ni nayi maka al?awarin cika maka burinka wanene yayi maka horo?"
Nan ma Abu Zaid kansa ya dafe na tsahon lokaci Mr John ya na kallonsa kamar ya fizgo maganar daga bakinsa.
Da kame-kame Abu Zaid ya ambaci sunansa da lambar wayar da.

A Sangaren Hudayya

Mganin Matan manyan kuWin da aka kawo mata tun Waga Gwarzo kafin dawowar Taufiq ta Wurawa cikinta, cikin shiga mai jan hankali tayi ado tana jiran isowar Taufiq.

Da Taufiq ya dawo gidan Uwargidansa ya fara biyawa kamar mahaukaci haka ya Wauki Matarsa da Wansa zuwa shopping mall siyayya na fitar hayyaci ya yi mu su bini-bini sai ya sumbaci goshin Matarsa yana ?an?ame hannunta, ita dai batayi mamaki ba don Allah ta ro?a Kuma babu abinda ya gagare Sa.
Bayan sun dawo gida, shiryawa ya yi ya wuce gidan Abu Zaid.

Bai samu Abu Zaid ba daya tambayi mutanen Gidan sai aka sanar da shi ai ya jima da barin gidan tuntuni.
Taufiq bai sha wahalar samun Unguwar da Abu Zaid yakoma ba ta hanyar dillalin daya nema mai gidan. Nan ma bai sameshi ba daya tambaya sai aka sanar da shi labarin sana'ar dayayi ?an unguwa suka karyashi a lokaci kaWan da cin bashi, ?arshe ya koma Bara a bakin kamfanonuwa su dai ba su san ina ya tafi ba don kwanansa uku bai dawo ba kuma sunje bakin Companyn da ya saba zuwa ance bai zo ba.

Zafin da zuciyar Taufiq ya Wauka ne ya sa kai tsaye ya wuce Gwarzo, yasa aka kama su Baba Ilu gaba Wayansu, ?auye kaf sai dariya ake mu su.

&washe gari Hudayya tanajin an ?wan?wasa ?ofa ta taso ta?ara zazzago da wuyan shara-sharan rigan jikinta haWe shagwaSe fuskarta. Ta riga ta kitsa makircin da zatayiwa Matarsa don tasan tun a jiyan ya dawo ya wuce wajenta, Da salo ta buWe ?ofar....
' BY NAFISAT ALIYU SASAAL

17

A can Tofa wajensu Siya.
Da Sacin rai Nenne ta shigo gidan. A sitting room ta same su amma banda Siyaa da ta wuce Waki,cikin faWa da takaicin abinda suka aikata tace,
"yanzu kai abinda ka goyi bayan Ziyaada tayi dai-dai ne a wajenka? kun san me gobe za ta haifar"
da salon son su kwantar mata da hankali Alhaji Sunusi yace;
"zuwan Yaron nan zai iya kashe auren Siyaama don hure ma ta kunne zai yi,gara yaje can ya ?arat.." bai samun damar ?arasawa ba saboda masifan da Nenne ta rufe su da shi,da tafiyarta mara sauri ta faWa Wakin da Siyaa take ta fara janyota da iya ?arfinta tana faWin

" fita ku bar mun gida tunda ba uban wani ne ya ginamun ba kuma babu gadon uban kowa a ciki marasa kirki kawai"

da murya kuka Siyaa tace

" Nenne mana ki fahimceni wallahi Yaaya wari yakeyi sosai sannan ki ganshi fa da ?afa Waya wallahi tsoro ma ya bani amma ai ban ce na daina son shi ba kawai dai wani irin wari yake yi da ban taSa ji ba"

daina janta Nenne tayi ta tsaya kallon fuskarta da wani irin kallon ashe haka kike? Cikin fushin dayafi na baya Nenne tace;

"ashe baki da imani bansaniba Safiyyah,fita ki bar min gida kije ki samu Mijinki mai ?amshi da rashin warin baki,wallahi naa kuma ganin wannan sili-silin ?afafuwan naki sai na sa anyi miki dukkan tsiya a garin nan"

Duk magiya da ro?on Nenne da sukayi bata saurare su ba sai da tabbatar sun bar gidan sannan hankalinta ya kwanta bayan ta kafawa Ziyaada sharaWin ko ta koma ta nemo Abu Zaid ko taje su warware asirin da suka yimai idan ba haka ba wallahi ko bayan ranta bata yafe mata ba.

Bayan sun bar gidan ajiyar zuciya Mommyn Siyaa ta sauke bata da bu?atar naiman taimakon da Siyaa zata manta da Abu Zaid iyakacin abinda Siyaa ta yi masa ya isheta amsar ta daina sona. Kuma da ta nemosa kamar yadda Nenne ta kafa mata sharaWi ya dawo cikin su gara ta bada ko million nawa ne a warware asirin da suka yimai yaje can ya ?arata. Jirgin Lagos suka bi zuwa gidan Alhaji Sunusi.


A Sangaren Hudayya

Cikin Shanye sakayayyun idanuwata ta take kallon Taufiq haWe da cije ?asar leSenta.

fuskar Taufiq sam babu wani walwala balle ya nuna zumuWin ganinta. Cikin hayaniyar zafin da ya taho da shi yace "bani hanya Mallama" gabanta ne ya faWi zuciyarta na bugawa kamar zai fito,Taufiq bai taSa yi mata tsawa irin haka ba maiyake shirin faruwa? Bayanshi ta bi zuwa Wakin daya shiga tana ?ara zazzago da wuyar rigarta. A tsaye ta sameshi yana zarya a ?akin da sabon belt Win wandonsa a hannunshi. Gabanta na ci gaba da faWuwa ta tsaya daga bakin ?ofa har lokacin mamakin sauyinsa bai gama sakinta ba.

" mai zai yi da belt kuma?. Ta tambayi kanta Kafin da gama sa?a da warwara ya fincikota da zafin namanshi yafara lafta ma ta belt Win da iya ?arfinsa.

Tunda uwarta ta haifeta ba'a taSa yimata irin wannan dukan da ya yi mata ba.
Da ?arfi Taufiq yake faWin;
"Ni zaki yaudara ki cuceni wacece ke? nayi miki kama da sakarai da zakiyi wasa da hankalinsa? wallahi yau saikinyi da kin sanin aurena" Sai da yaga bata motsi da kyau sannan ya ?yaleta ya faWa washroom yana nurfarfashi. Tana gani ya shiga washroom ta mi?e da Wan ?arfin daya rage mata, ta Wauki wayarta ta bar gidan gaba Waya kafin ya rabata da ranta.

Gidan Abu Zaid marainin wayonta ta nufa tasan raunin zuciyarsa bazai barsa ya?i karSarta ba. Amma sai ta tarar wani ne a Wakin ba Abu Zaid ba, da taimakon ma?otan shi ta samu gidan dillalin da ya raka Taufiq waccen gidan. Nan ma sun sanar da ita har lokacin Abu Zaid bai dawo ba,kuka ta fashe da shi tana tunanin mafita shawarar tafiya Gwarzo ta yanke sai

10 / 43