ABU ZAID HAUSA NOVELS COMPLETE BY SASAAL.doc

Author :  Nafisa Aliyu Salsal Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   6 / 43

15K to 18K   out of 126.7K words

yafe miki ba,kin raba zumuncin waWannan ?an uwa biyun da suka rayu cikin so da ?auna bayan ?asa ya lulluSe idanuwansu,ko da nayafe miki bazan taSa kallonki ko mu'amalantarki a fuskar da kikeso ba, bazan kuma daina nanata miki girman Butulcinki ya daWe da kurmantar da ni ba Hudayya,zaman lafiyarki shi ne ki nisanta kanki da ni,dama ai a haka kikeson ganina,if not bazaki zaSi yimin sharri mafi muni a idon duniya ba" ya faWa yana barin living room Win saboda girman tsanarta dayake ji a cikin zuciyar shi.

Bai sauya daga ?in kulata ba,sai abinda ya?ara gaba da muni,bayacin duk wani abu daya fito daga hannunta,baya kallon TV kullum idan ya dawo daga wajen aiki yana Waki sai zuwa Masjid ke fito da shi,baya dariya da kowa,sai dai Murmushin ya?en da idan ya kamashi dole,motar da Taufiq ya siya mishi ma bayason hawa kullum yana compound Win gidan a lulluSe,ya gwammace ya hau Taxi ko express.

Acikin wata biyu Abu Zaid yayi wani irin rama kamar ba shi ba,kamannin Siyaa yafara barin fuskarshi.

Kamar yanda ya al?awarta Private University da bata taSa zatan zai affording ba ya kaita,sai jikinta yayi sanyi. Wani irin kyakkyawar zuciya gareshi mai tsananin rauni da tausayi? Sai takejin inama bata wannan hanyar ta biyo ba wajen mallakar shi a matsayin Miji.

Kullum zai bata transport amma bazai yimata magana ba.

SIYAA da magiya da ro?o takecin abinci shima Wan kaWan kamar abinci yaro ?arami. Magana kaWan kuka,daga Mommynta har Mijinta duk sai abu yafara damunsu. Gaba Waya slim face Win ta yakoma duk ?ashi. A baya ita ma'abociyar kallo da danne-danne a wayane amma a wannan lokacin duk ta daina yi.kashe su tayi gaba Waya.

Shawarar tafara fita da ita wajajen sha?atawa Ziyaada suka yanke da Mijinta.

?akyar ta shirya cikin ?ananun kayan da suka haska farin fatarta. Duk da zuzutata da Mommynta takeyi batayi dariya ba kamar yanda takeyi a baya.

Gurine da Manyan ma su kuWin kasashe mabanbanta da celebrities suke zuwa hutawa.

Tun shigowar Dogayen Matansa da samun irin tsahon su a cikin miliyoyi kaWan ne hankalin mutane da Wan dama ya koma kan su ana yimusu video mussamman ga waWanda suka san su,gashi ne akan kowannensu mai yawan da sukayi parking Winshi. Paul Maher da Zayad Maher.

Wa su na kiran Paul wasu na kiran Zayad dalilin dayaja hankalin Siyaa kenan harta waiwayo kan su.....ABU ZAID

11

BY SASAAL

A kaikace take kallo da tantace halittar tsayin su,abu ne mai wahala kasamu ma su irin wannan tsayin a cikin mutane mafi akasari tafi sanin Basketballers da shi.Tunda ta Wago Paul yake kallonta rashin damuwarta da su balle har ta Wauki hoton su kamar yanda ragowar sukeyi ne ya ja ra'ayinshi duk da ?aramin Camera da ke gefenta,"who is she?" ya tambayi kanshi yanajin feelings na daban a kanta.Bata ?ara kallon su ba ta cigaba da sipping drinks Win dake hannunta duk da bawani daWi yake mata ba.Har suka zauna hankalinshi yana kanta saSanin Zayad mai zafin kan da ko kallon mutane bayayi balle ya tantance su wanene suke Waukar su da waWan basa Waukar su.

A hankali ya furta"love at first sight"yana shafa tarin sumar kanshi.

Saitin kunnen Mommynta dake zaune a gefenta ta ce"I'm tired Mommy ina bu?atar hutu"kama hannunta tayi alamun ta mi?e don batason wani abu dazai Sata walwawalar da take ciki.

Paul na ganin sun mi?e shima yami?e. A bakin Mota ya samu Mommy tana ?o?arin shiga bayan Siyaa ta shiga ta zauna,dukka guards Win shi na bayanshi har lokacin wa su basu daina Waukarshi a hoto ba.Da British accent Win daya kama mishi harshe dakyau yace"Excuse me Mam".Da wani irin farin ciki Mommyn Siyaa ta karSeshi bakinta kamar zai ?ara faWi saboda dariya duk da ?o?arin kame kanta da takeyi.

Card ya mi?a mata batare da dogon magana ba ya juya saboda yawan mutane da suka fara zagaye su,suna Waukar su hotuna.

Fuskarshi ya shafa yanajin nutsuwa na shigarshi,har ya zauna murmushi bai Waukewa fuskarshi ba. Kallon Mummynta da ta shigo da farinciki takeyi kafin a hankali ta furta"Who is he?" Da wani irin ?warin gwiwa mai surke da farin cikin da take ciki tace"Siyaa=?3? the greatest Basketballer Brother yabani Card dinshi, can you imagine,Allah Yasa yace sonki yakeyi Siyaa da nafi kowa farin ciki in dai zai musulunta".kamar saukar hammer haka taji saukar zancen Mahaifiyarta ta,bata ?ara magana ko tankawa surutan Mommyn na ta ba, a ranta take mitar ba ma shi kanshi Basketballer ba a'a his Brother shine take wannan murna,anya Mommynta tasan girman Soyayyar Abu Zaid a ranta kuwa?.Saboda ta kame kanta da mutuncin ?arta yasa bata kirashi a ranar ba sai after two days.Paul bai huta da bawa Zayad mai zafin kan tsiya labarin Siyaa ba har sai da yabawa zancenta muhimmanci, ga shi har lokacin Mommyn Siyaa bata kira ba. Da mamaki Zayad yake kallon Paul da ko zancen budurwa bayaso sai dai idan sha'awarshi ta dameshi ya nemi na rage zafi,kuma asanin dayayi mishi ba mutum ne mai son Musulunci ba don dalilin bin addinin Mahaifiyarsu kenan duk da bata raye.may be tunda ya haukace a kan Soyayyar musulma ya musulunta. Da?yar yayi controlling kanshi lokacin da Mommyn Siyaa takira, batare dogon magana ba ya ro?i alfarmar zuwa gidanta idan ba damuwa.

Dinner mai rai da lafiya Mommyn Siyaa suka shirya ita da Maigidanta. ?amshin shi kaWai ya isa ya shaida maka how wealthy he is. Bata bu?aci fitowar Siyaa ba don batason ta kunya ta su a agaban shahararren ba?on na su.

>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?

Ba ta daina gwada sa'ar ta ba,nayin ado da kwalliya da tsaftace ko ina kullum, amma babu alamun zatayi nasara sai komai dayake ?ara dawowa baya. Da sallama ta shigo a gajiye with surprise take kallon shi bayan ya amsa sallamarta don ba lokacin dawowar daga aiki bane. Cikin Wari-Wari ta zauna a gefenshi saitin ?afarshi daya Wan mi?e cikin salo da yanga tace"Barka da yamma Yayaa" batayi tunanin samun amsarshi ba as usual amma sai taji ya amsa mata batare da ya kalli gefenta ba. Da ?warin gwiwar amsa matan dayayi tace"Yayaa wani abu na damunka ne"tana kai hannunta kan ?afafuwanshi dake kusa da ita. Da zafin muryar da bata sanshi da shi ba ya ce"Get your filthy hands off me" dasauri tacire hannunta tana mi?ewa zuwa Bedroom Winta cikin sanyin jiki,bayanta yabi da kallo ?walla na cika idanuwanshi,maiyasa ta zaSi yimishi irin wannan budulcin bayan halaccin dayayi mata? Idanuwansa ya runtse ciwon da ya fara ji a babban Wan yatsar kafarsa kwanaki biyu da suka wuce na ?aruwa.
A Sangaren Hudayya Bata sake fitowa ba har sai da ya tafi Masallaci sallar Magriba.



A Sangaren Siya;
DaWi ne yasa Mummynta rungume Mijinta bayan gama tattaunawarsu da Paul ya bar gidan.

Ta na jin farin cikin abinda Paul ya zo mu su da shi a cikin zuciyarta, domin yayi al?awarin musulunta kamar yanda suka bu?ata kafin su bashi auren Siya.

A hankali ta nemi waje ta zauna saboda sanyin da jikinta yayi lokaci Waya, ba lallai Siyaa tabasu haWin kai ba domin har lokacin akwai raWaWin rabuwarsu da Abu Zaid a cikin ranta. ?akin ta nufa da Addu'ar Allah Ya sa ta amince acikin ranta.

A zaune ta sameta tana sana'ar da ta saba na tunanin.

Da wani irin tsoro da mamaki take kallon fuskar Mommynta bayan ta gama koro mata bayanin Paul ?anin shahararren mai buga wasan ?wallon kwando Zayad yace yana sonta kuma a shirye yake ya aureta idan ta amince.
Mommyn siya da sigar lallashin da tasan dole jikin Siyaa yayi sanyi ta ce;
"Siyaama kina bu?atar abokin rayuwa ko don lafiyarki,nasan Abu Zaid shima zaiyi farin ciki idan ya ji kinyi aure kin kwantar da hankalin ki,kuma zaki samu lada mai girma na zama sanadiyyar musuluntar Paul,bazan takura miki ba,amma idan kikayimin biyayya zanji daWi , na kuma ?ara sa miki Albarka da fatan rayuwar farin ciki mai Worewa".

Zugum?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? tayi tana jiran amsar Siya tare da addu'ar Allah Ya sa ta amince da Paul suyi Biki na alfarma.

Siya kuka mai raWaWi dake ?ara tabbatar mata da ta rabu da Abu Zaid ta fashe da shi hannayenta na rawa ta kamo na Mahaifiyarta tana cewa
"na amince Mommy,na amince" kuka sukasa dukkansu kafin su rungume juna.
A zuciyar Mommyn Siya ba laifi ta Wan ji datasani da tausayin cutar Abu Zaid da tayi a cikin zuciyarta.
itama Siyaa tausayin Abu Zaid ne ya?ara tsarga mata, tanajin kamar bai dace tayi aure ta haihu bayan Mahaifiyarta ta nakasa tasa rayuwa ba.

Zayad Wan uwan Paul da Mahaifinsu ba?aramin farin cikin karSa Musuluncinsa sukayi ba, ko da Siyaa bata amincewa aurensa ba, iyakacin musuluntarsa wani babban nasara ne a wajen su. Babu inda labarin musuluntar Paul daya koma Muhammad bai zaga ba, a cikin ?asar har ma da wajen ?asar.

Har shuWewar wata biyu Paul da ya koma Muhammad baya samun sakin fuskar Siyaa duk da haka bai da muba balle yaji raguwar sonta a cikin zuciyarsa burinsa kawai su yi aure.
Yasan da labarin Abu Zaid a bakin Mommynta don bata Soyemasa ba gudun faruwar matsala a gaba. Kyaututtuka masu nauyin kuWin dake ?ara ruWar da Mommyn Siyaa Muhammad da Zayad suke aikowa Siyaa da shi wa su lokutan kuma Muhammad yakawo da kanshi.

Muhammad bashi da ciwon kai da kowa nasa kan maganar auren su Siya, domin rayuwar ?anci da zaSin kai sukeyi balle kuma yasamu amincewar Mahaifinsa da ?an uwansa.


Siya har lokacin bata son auren haka Dangin su rabi da kwata duk basaso amma banda Kakarta, Mahaifiyarta da kuma Yayan Mahaifiyarta Alhaji Sunusi.

Mommyn Siya har su Aunty da Zainab ta kira kan su lallashi Siya tun da taga a gidansu ta taso wata?ila ta ji nasu lallashin ta fara sakarwa Muhammad fuska.

Da lallashin Aunty, Zainab, Kakar Siya ta ?auyen Tofa da Mijin Mahaifiyarta Siya ta amincewa aurenta da Muhammad.


Siya Bata wani ji alfahari ko jinta ta musamman dan zata auri Muhammad ?an uwan Zayad da duniya take damawa da shi ba, tunaninta da zuciyarta gaba Waya na wajen ?an uwanta Abu Zaid.

Babu wani masoyin Ziyaada da Siya da bai ta yasu murnar mallakar Muhammad a matsayin Siriki ba, don kowa shaharar ?an uwansa da dukiyar su suke kallo bawai asalinshi da tushenshi ko addininshi ba.

A Sangaren Abu Zaid
Ya daina samun barci saboda ciwon Wan yatsar da ya tisasa a gaba. Wajen aiki ma a daddafe yake zuwa ya dawo.


A Sangaren Siya
Duk nacin da akayi mata ?iri-?iri ta nuna ita bazata yi taron komai ba akanki kanta, idan su zasu yi ita bata hana ba.
Domin nuna isa a Lagos Gidan Yayanta Mommyn Siya ta shirya bikin bugawa a jarida, saboda irin kuWin da Muhammad yake sakar mu su.

Lokacin da komai na bikin Siya ya kammala aka Waura aure, Siyaa tayi kuka irin wanda batasan iyakarsa ba, Zainab tana tayata saboda kishin da take taya Wan uwanta da har lokacin basu san a duniyar da yake ba. Daga Siya sai Mommynta da Matar yayan Mahaifiyarta Alhaji Sunusi suka tafi Coventry kaita gidan Muhammad..
A ranar da aka tafi da Siya Coventry Aunty da Zainab suka bar Lagos, lokacin Safeera babbar ?ar Zainab ta na da shekaru bakwai da Woriya a duniya, ?annenta Maza ma duk sunyi wayo.


Muhammad Bayan an kawo masa Siya gidanshi
Bai ga alamun zata karSi soyayyarsa ta daWin rai ba, wannan dalilin yasa daren tarewarta ya sa mata ?waya a lemo.


& Siya bayan ta farka washe gari taga abinda Muhammad ya yi mata tsanarsa da danasanin aurensa ne suka mamayeta.
Duk yadda Muhammad yake tarairayarta da lallashinta ta?i ta daina kuka balle ta saurareshi.

A kwanakin da suka biyo baya ta fara gane matsawar zata zauna da Muhammad waje Waya to fa dole sai ta so shi wata rana.
Muhammad kyakkyawane irin asalin kyan da ya haWe da hutu, ga kulawa kamar zai lasheta ga sau?in kai.
Haka ?an Uwansa Zayad, shima yana ?o?arin nuna kulawarsa akanta, haka Mahaifinsu shima kamar zai goyata saboda so, dukkan su kulawarsu akanta na musamman ne.
A Sangaren Mommynta da su Aunty har da Kakarta kusan kullum suma sai sun kirata. Sun ji lafiyarta.

Watan Siyaa biyu a gidan Muhammad ta tabbatar shigar ciki a jikinta.

Kayanta ta haWa a Soye, bayan sun yi sallama da Muhammad ya fita office, ta nufi Airport ko gidan Mahaifiyarta bata biya ba.

Cikin sa'a ta samu jirgi, da sa'ar rashin nemanta da kowa bai yi ba tabar ?asar.
Bata tsaya a Lagos ba kai tsaye gidan Kakarta na ?auyen Tofa ta nufa, domin ta ro?eta su haWakai su zubar da cikin ita bazata haihu da Muhammad ba.

A Sangaren Abu Zaid;

Wajen masu sayar kayan marmari ya sauka lokacin da yake dawowa daga wajen aiki, tun safe ya kasa cin komai saboda zazzaSin daya Wauke masa appetite. Kafin ya mi?awa mai kayan marmari canjin da ya rage masa ya hango ?anin Mahaifiyar Siyaa yana ?o?arin tarar Taxi daga Wan nesa da tsallaken titin da yake.
Da ?arfi Abu Zaid ya ?wala kiran sunansa "Saleem!" Yana barin wajen mai kayan marmarin zuwa inda Saleem Win yake tsaye

Saleem a Wan firgice ya kai dubansa inda ya ji ankira sunansa, kallon mamaki yake bin Abu Zaid da ke ?o?arin tsallakowa titi dashi, don har ga Allah bai ganeshi ba domin wannan wani Abu Zaid Win ne daban ba wanda ya sani ba..
Sai da ya matso kusa da shi sosai sannan Saleem ya Wan ganeshi amma duk da haka yakasa yarda da gaske shine.
Tambayar da ya fara zuwa bakin Abu Zaid bayan ya ?araso kusa da Saleem sun gaisa shi ne;
"Saleem ina Siyaa ta ha?ura tayi aure ko?".
Saleem, Raunin da ya hango a idon Abu Zaid da yanda Abu Zaid Win yakoma kamar mai matsalar kai yasa yace
"a'a yanzu haka tana gida ta?i yarda ta zauna a can".
"Subhanallah ku lallasheta ku bata ha?uri kaji, bari na siyamata kayan daWi ka kai mata, amma karka gayamata ka ganni kaji" Abu Zaid ya faWa yana komawa wajen mai saida kayan Marmarin daya baro.
Wani irin abu mai Waci Saleem ya haWiye tare da ?wallar daya taho mai, a hankali ya furta
"Allah Karka jarabbaceni da son abinda bazan samu ba".

Dukka kuWin jikin Abu Zaid ya tattara ya siyi fresh fruits ma su kyau a ido sannan dasauri ya ?ara nufowa gurin Saleem. Daga sama har ?asa Saleem yake kallon Abu Zaid kafin ya ?araso.
"wai dagaske Abu Zaid ne wannan? Ya tambayi kansa, Ya tsinewa Hudayya a cikin zuciyarsa babu adadi.
Numfashi Abu Zaid yake saukewa yana ?o?arin shanye raWaWin da Wan yatsarsa yake mai, bayan ya ?araso kusa da Saleem a hankali ya furta "ga shi ka kai mata amma kayimin al?awarin bazaka gayamata ka ganni ba ".
kai kwai Saleem ya Wagamai alamun ya ji saboda idan yayi magana kuka ne zai biyo baya.
Abu Zaid yana tsaye har Saleem ya hau Taxi yabar wajen. Bayan Taxin ya bi da kallo, kafin ya Wauke ?wallarsa yana kife tafukan hannayensa a kan fuskarsa, kuka mai sanyi ya fashe da shi har da sheshe?a.

Ya daWe a tsaye yana kuka kafin ya fara tafiya domin Ba shi da kuWin siyan wani kayan marmarin kuma ba shi da na Mota, tsakanin wajen da gidan su akwai Wan tazara. Dole haka yafara takawa da ?afa yana hutawa idan raWaWi ?an yatsar ya ishe sa, a haka ya?arasa gida a gajiye ....
'

By Nafisa Sasaal

12

A parlor yasamu Hudayya tana kallon tv harda kyalkyala dariya. Bai ce mata komai ba bayan sallamar da ya yi.


Dariyarta ce ta Wauke lokaci Waya.
cikin sanyin hali da na muryar da take ?o?arin nuna tanada shi tun bayan barowar su Zaria ta amsa sallamarsa kafin ta Wora da;
"sannu da zuwa Yayaa"

kai kawai Abu Zaid ya Waga mata ya wuce Wakinsa.
Bayansa tabi da kallo, sai take ganin kamar akwai abinda yake damunsa yake Soyewa, koma dai menene a hankali zata sani, kallonta ta tacigaba dayi ranta fari fes tana kyalkyala dariya.


Abu Zaid bayan ya isa da?insa; numfashi mai Wumi ya sauke lokacin da ya fito daga wanka, raWaWin abu biyu na haWemai labarin Siyaa na gari Waya da shi da kuma ciwon Wan yatsarsa da yakeji a duk sassan jikinsa.
Kullum sai dare ya raba idan Allah Ya taimakesa yake iya barci, amma daren ranar sai yafi na kowani dare muni saboda tunani da ciwon da ya addabesa.



&Hudayya washe gari da wuri ta bar gidan zuwa Makaranta batare sun haWu da Abu Zaid ba.

Bata da ?awa sai Mutum Waya mai suna Maryam kuma itama ba sa hirar personal issues a tsakaninsu, sai hirar karatu da hirar daba'a rasa ba,ranar dai kasa jurewa tayi ta gutsurowa Maryam labarin iyakar inda zata wanke kanta batare taga aibunta ba,

bayan Maryam ta gama sauraran labarin Hudayya baki ta ri?e kafin ta kwashe da dariya. Ta Wan Wauki da?i?u ta na yi sannan ta tsagaita, tana cewa;

"hmm Hudayya baki iya neman soyayyar ?a Namiji ba,ai da hirar Siya zaki dinga jansa ko da yanuna bayaso, idan zaki iya ma kice masa zakije har wajen kakarta ki tambayeta ko Siya tananan lafiya tunda kin ce can wajen zuwanta ne, wallahi ina gayamiki dole yafara sakar miki fuska."

Hudayya da tantama tace
"Dagaske Maryam kina ganin hakan zai janyomin hankalinsa kuwa",

Da ?arfin Gwiwa Maryam ta ce;
"?warai kuwa da kanki zaki bani labari" ta ?arasa faWa tana juya idanuwanta.

Hudayya gaba Waya sai ta matsu ta koma.

Su na tashi bata tsaya surutan da ta saba ba ta nufi Gida.

Lokacin da ta isa gida, a parlor ta samu Abu Zaid yana kwance kan doguwar kujera kamar ma bai fita aiki ba, da tsoron abinda yake ranta ta gaisheshi, bata jira amsawarshi ba tayi gyaran murya da addu'ar Allah yasa ya karSi zancenta. Sannan ta ce;

"Yaaya inason zuwa Tofa wajen Kakar Siya na ji ya ya lafiyar Siyaa, don Allah kabani addireshin gidan".

Abu Zaid mi?ewa ya yi ya zaune da mamaki kwance a saman fuskarsa.

Da a waya yayi magana da Saleem jiya da sai yace laSewa Hudayya tayi ta ji tattaunawarsu.

murmushin da bata taSa samu daga garesa ba yasakar mata, don kamar tasan hanyar da zai ?ara samun wani labari akan Siyaa yake nema da sanyin Muryar daya haWe da ciwon dayake ji yace
"yaushe zakije Hudayya"

cikin zumuWi Hudayya tace;

"ko gobe

6 / 43