ABU ZAID HAUSA NOVELS COMPLETE BY SASAAL.doc

Author :  Nafisa Aliyu Salsal Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   14 / 43

39K to 42K   out of 126.7K words

bar wannan maganar ina Papi?"
Ba don Siya ta gamsu da zancen Mahaifiyartata ba ta ce "yana wajen Daddyn shi"
da muryar nishaWin da kullum takeji idan ta tuna ta haWa jini da irin su Muhammad ta ce "maza tafi wajen su zamuyi waya da safe kuma kar na ?arajin maganar Ibrahim a bakinki".

A Sangaren Zainab
Abu Zaid yana fita ta fashe da kuka Safeera na lallashinta.

Bayan tagayawa Safeera wacece Waya Matar da suka gani a inda suka je. Safeera ta ce;
"Amma Mommy maiyasa kike damuwa haka bayan duk abinda ta yi?,kina so Uncle ya?ara sonta bayan bata so shi a lokacin da ya samu matsala ba? ba ma wannan ba she is now a someone's wife Mommy, Uncle bai dace da ita ba, ba Mace irinta yake bu?ata a cikin rayuwarshi ba,daWi fa kawai ta sani Mommy rayuwa kuma za?i ne da maWaci,kuma da ta ganku ya kamata ta nuna tagane ku, ko da bazaku saurareta ba idan har dagaske ta yi nadama ta kuma yarda tayimishi ba dai-dai ba amma fa ba ta nuna alamar komai ba sai kallonshi da tajeyi, sannan ki Sata hawayenki don kawai kin ganta,ko ni ce Uncle fushi zanyi dake gaskiya"

Kallon mamaki Zainab takeyiwa ?iyarta ta da ta fita hangen nesa.
cikin sanyin da Muryarta ya yi ta ce;
"tausayi Abu Zaid yake bani gara ni ina ganinku a matsayin ?a?ana amma shi fa bashi da kowa sai ni, nasan ganinta a matsayin matar wani bazai barshi ya runtsa ba Safeera nasan yanda yake Sonta kamar ranshi" juya ido Safeera tayi kafin ta ce "Mommy ke kike ganin haka,duk zu?a-zu?an turawan dake ?asar nan ya kasa son wata kawai dai bai nuna miki bane,Mommy wallahi zan so naga Matarta da Uncle zai aura, idan Allah yaso sai ya ba shi Marainiya irinsa su taru su rungumi maraicin su" murmushi da ajiyar zuciya Zainab ta saki kafin tace;"Allah Ya amsa bakin ki Safeera"..

Abu Zaid
Har hai kai Masaukin su Zayad ransa baiyi sanyi ba. Da ga shi sai Zayad sukayi Dinner kafin su tattauna muhi??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????mmin hirar daya shafi sana'ar su. Da zasuyi sallama Zayad ya nemi iso don zuwa duba jikin Zainab kafin su wuce gobe. Bazai iya musamai ba don haka kai tsaye ya amince mai tare da nuna farin cikinsa.

Siya tafi minti biyar tanayiwa Muhammad magana bai kulata ba,har sai da ta samishi kuka sannan ya waiwayo kanta cikin zafi da haushin irin kallon da ya kamata tanabin Abu Zaid da shi ya ce
"kin raina kyawuna da kuWina right? Kinga wanda ya fi komai kin manna mishi idonki kamar zaki cinyeshi Safiyya dama Zayad ya sha faWamin a mabambantan lokuta kuWi da alfarmar mu kike so kawai, amma na ?aryata shi yanzu ga shi nagani da idona"

kafin Siya ta samu damar yin magana ya fice daga Wakin. Tsabar fargaba da tsoro hannunta har karkarwa yakeyi wajen share hawayen fuskarta tana lalubo wayarta. Maiyake shirin faruwa da ita???...

Abu Zaid bayan ya komo gida
Bai nemi su Zainab ba ya wuce Sashensa, kanshi ya fara tsefewa yana kallon fuskarshi ta cikin ?aton mudubi da akayiwa luxury Bedroom Winsa ?awa da shi.
Ya rasa ina zaisa ransa ya ji daWi da ?arfi yake tsefe lallausar gashin da tsadaddun mayukan wanki kai da na shafawa yasa yayi laushin daya haWe da na asalin halittar gashin,ba don ya saba tsefewa da kanshi ba sai don rage raWaWin dayake ji.
Maiyasa take kallonshi,saboda ya zama Abu Zaid Win da take son gani,a kanta ya fara so kuma a kanta ya tsani so, wallahi ko da duniya za su taru wajen mayar da soyayyarta cikin zuciyarshi da salon birgiya mabambanta bazai taSa maiduwaba sai idan har Ubangijin daya cire masa ne zai maida mishi, ganin fuskarta yafi komai Satamai rai, saboda fuskarta ya tuna mishi girman butulcinta, da tuna irin Soyayyar da ya yi mata, ashe daWine yasa ta take son shi, da tsanani ya ratso sai ya zama abin kyankyami. Yana jin ana ?wan?wasa ?ofa amma ko kallon ?ofar baiyi ba.
Har ya shiga wanka ya fito duk daWewar da yayi Zainab na bakin ?ofa tana magiyar ya buWe mata. Har ya shirya cikin Pyjamas ma su tsananin taushi Zainab ba ta daina buga ?ofar ba, girar shi Waya ya Wage yana kallon ?ofar,ba don ta ba shi tausayi ba sai don ta daina damunshi da bugun ?ofar ya samu barci ya buWe muryasa da asalin sautin da yakewa kowa magana ya ce;
"Karki ?ara buga ?ofar nan kina damuna"

Kuka mai ?arfi Zainab ta fashe da shi don tafara kokwanton anya wannan Abu Zaid Win da ta sanine mai tsananin rauni da tausayi batare da ta daina kukan ba ta ce;
"tun kafin mu zo gareka nake kokwanton anya kaine,amma ganinka a karon farko ya gogemin wacce zargin,sai dai yanzu taurin zuciyarka da tsaurinka ya sa na cigaba da kokwanton anya kai ne? Abu Zaid Wan uwana mai tausayine bayason ganin kowa cikin ?unci da damuwa,ya na ha?ura da abubuwa dayawa don wa su su ji daWi,amma kai ba haka kake ba,fushinka a kusa yake sannan tausayinka ?alilan ne,ban da haka tayaya zan kai wajen hour huWu ina kwankwasa ?ofarka ka?i buWemin"
Ta ?arasa faWa ta na cigaba da buga ?ofar dayace kar ta ?ara bugawa. Jajayen Idanuwanshi ya zubawa ?ofar yana sakin murmushin gefen bakin dayake nufin abubuwa da yawa. wallahi banda ta zo a Wiya Mace da yau sai ta bar masa gida a darennan saboda tuna mishi halayyarsa na baya da suke ma su sau?i da dadin sha'ani da kuma na yanzu da suke ma su tsauri da wuyar fahimta yasa ya?arajin tsanar kowa, a kallon da yake kowa yanzu, duk wanda zai raSeka yana raSarka ne don kanada wani amfani a wajensa ko da kaWan ne,amma idan baka da amfani kai da banza duk Waya kuke,fahimtar Abu Zaid kenan.

Kwanciyarsa yayi batare da ya ?ara tanka mata ba don matsawar ya fita wallahi sai ya sauke mata marin da zai cire mata kokwanton komai a ranta tace kai tsaye ma ba shi ba ne. Wani irin bugun dake amsa dukka girman sashen takeyi amma kamar an shuka dusa Abu Zaid bai buWe ba kuma bai ?ara tanka ma ta ba.

Da?yar Safeera tasa ?arfi wajen janye Zainab zuwa Waki. Kamar wacce kanta ya kunce haka ta fara haWa mu su kayan su. Kallon mamaki da anya depression bai mayar mata da Uwa mahaukaciya ba Safeera takeyi mata cikin surutanta take ta maimaita "wallahi wannan ba Abu Zaid ba ne shi da ko fushi kayi yayita damuwa kenan,ko sau nawa zaka cuceshi ko gayamishi magana mara daWi baya damuwa,haba ai da sake tayaya dama Abu Zaid zai zama mai kuWi kuma shahararre irin haka" baki Safeera ta saki tana kallonta don ita bata ga wani abun fushi ba.

Zainab tana cikin wannan surutan wayarta yafara ringing da mamaki dukkan su suke kallon wayan kira ne ta What'sApp kuma Number Mommyn Siyaa ne don Zainab bazata taSa manta Numbern ba saboda abinda tayi mata,kamar bazata Waga ba sai dai ganin a irin lokacin da ta kira yasa ta Wauka ko wani abunne ya faru,duk Safeera tana kallonta.
Da muryar alhini bayan sun gaisa sama-sama Mommyn Siyaa tace"ashe Abu Zaid ya bayyana Zainab ina tayaku murna"kuka Zainab dake jiran ?iris ta fashe da shi kamar ?aramar yarinya ta ce;
"wallahi ba Abu Zaid ba ne dama tun kafin mu zo nagayawa Safeera amma ta?i fuskantata yanzu ga shi.." sai kuma tayi shiru saboda tuna da wacce take magana, murmushi Mommyn Siyaa da barci ya ?auracewa idanuwanta ta saki daWi na mamaye ruhinta dama tasan wallahi ba Abu Zaid ba ne,cikin son ?ara dulmiyar da Zainab cikin tsananin duhu ta ce;
"Ni ma sai da na faWi haka Abu Zaid fa yana Kano yana aiki a Companyn robobi,wallahi Karki biyewa shirmen Safeera ku tatt.." da wani irin zafin nama Safeera tayi jifa da wayan tana fashewa da matsanancin kuka haWe da faWin
"Mommy yaushe zaki fahimci rayuwa ki dinga banbance ma?iyi da masoyi ..
' BY NAFISAT SASAAL

22
Safeera
"Mommy yaushe zaki fahimci rayuwa ki dinga banbance ma?iyi da masoyi wallahi wannan Matar ?arya takeyi,saboda me zaki yarda da zancenta,idan ba Wan uwanki ba ne maiyasa zai karSe mu har ya bayyanawa duniya mu,ya ya akayi yasan abinda ke da Wan uwanki ne kawai kuka sani,Matar da ta watsar da ke lokacin da kika rasa kowa,kuma ba ta ?ara nemanki ba har sai da kika samu inda Wan uwanki yake sannan kuma ta kira tace miki ba shi ba ne ki yarda da ita,Mommy dole halayyar Uncle su sauya saboda irin rayuwar da yayi a baya zuwan mu na kwana biyu kacal bazai canza sababbun halayyarsa ba,kuma ire-iren ma su Halayyar Siyaa da Mommynta ne suka mayar da shi haka,dole yarda,so da tausayi su bar zuciyarshi,ba lokaci Waya zai dawo yanda kuke a baya ba saboda zai ji tsoron ?ara yarda da wani duk girman kusancin su"
Safeera rufe bakinta ta yi bayan ta ?arasa,ta na ganin kamar maganganunta sunyi girman da baidace tagayawa Mahaifiyarta su kai tsaye ba, cikin sanyi muryar ta ?aracewa"I'm sorry Mom" Kai Zainab ta girgiza tana buWe mata hannayenta alamun ta zo gareta. Dasauri ta shige suna sakin kuka tare. Da?yar Zainab ta samu barcin wahala mai cike da tunani kala-kala ya Wauketa.

&washe gari Bayan sunyi sallar Asubahi Sarawon barci ya?ara Wauke Zainab,Safeera tana zaune tana kallonta dama kuma haka take so.
A hankali ta bar Wakin zuwa na su Al-hussain ?annenta. Su na dawowa daga Masjid tana shigowa,rige-rigen gaisheta suka farayi ta amsa ta na tambayar su ina Uncle"ya na Masjid..." bata tsaya jin sauran bayanin su ba ta nufi sashen shi.
A hankali ta murWa handle Win ?ofar da ta ke kyautata zaton a buWe yake, ajiyar zuciya mai ?arfi ta sauke saboda wani irin ?amshi mai daWi da ke fita a ?aton Parlon da ranar ta taSa shigarshi. Waje ta samu ta zauna batare da shakkar komai ba a ranta. Har gari ya yi haske sosai bai shigo ba,ita ma kuma bata ba wa idanuwanta damar da barci zai yi galabar kulle su ba,?amshin da ke ?ara shiga ?ofofin madaidaicin hancinta ne yasa ta ?ara gyara zamanta don ta haddace ?amshinsa ne.
MurWa handle Win ?ofar da bayyanarshi gaba Waya ne yasa Safeera ?ara gyara zamanta a karo na biyu. Daa babu tsoronshi a ranta sai dai kallon Waurarriyar Fuskarshi da babu alamun sau?in kai a tare da shi yasa tsoro ya mamaye zuciyarta.cikin sanyi da karayar da zuciyarta ya yi ta ce;
"Assalamu alaikum Uncle" ta ?arasa faWa ta na mi?amai hannunta da ke rawa. Girarsa shi ya tattare ya na rage girman idanunshi a kanta kamar mai jin barci. Da takun da ke ?ara sanya tsoronshi da shakkarshi a ranta ya ?araso kusa da ita,tanajin ya zauna a gefenta da fashe da kuka jikinta da hannunta na rawa. Kallon mamaki yake mata yana ?ara tattare girarshi saboda ciwon kan rashin isasshen barcin da bai samu ba. Da Muryar da ke bayyana tsananin kamewarshi da zafin kanshi ya ce;
"Safeera menene yasa ki ka fito da Asubahi jirana,kin ganni kuma kina kuka,menene matsalan" ya ?arasa faWa yana yana kama hannun da ta mi?o mai. Da rawar muryar daya sirka da tsoron ta ya ya akayi yasan tun Asubahi ta ke jiran shi ta ce;
"Mommyna ta na ta kuka batayi barci ba,kuma ni ma yanzu tsoro kake bani" ba bu murmushi ko Wigon mamaki a kan fuskarshi ya ce;
"saboda ?afata kike tsorona Safeera?" Dasauri ta Wago kanta anata ganin saboda me don ya na da ?afa Waya zai ba ta tsoro, mayar da kanta ?asa ta yi don bazata iya ?ara wa su da?i?un ta na kallon Lion face Winsa ba, Siyaa ce ta faWo mata a rai, a take kuma ta gano ina tambayar tashi ta ydosa. Girgiza kanta ta yi tana kallon dogayen yatsun hannunshi ma su kyawun gani a ido,
"menene ya samu Mommynki takasa barci?" Abu Zaid ya tambaya.

Kamar wacce take kan gaSa dama kuma abinda ya kawota kenan saboda ya kira Mommyn Siyaa ta daina kiran Mamanta.

Bayan ya gama sauraronta tsaf ya kalleta da kyau cikin hausarshi da ke matu?ar burge Safeera ya ce; "Safeera ki daina jin tsorona ki Waukeni kamar Mahaifinki I'm here for you okay,, sannan ki bawa Mommynki ha?uri ta daina damuwa,kar halayyata da sauyin fuskata ya dame ku yanayina ne a haka"
Wago kanta ta yi tana kallon fuskarshi da still ba bu murmushi a kai,da sauri ta kulle idonta ta na dariya,?aramin murmushin da bai bayyana sosai ba ne ya ?wacewa kyawawan laSSansa. yana ?o?arin mi?ewa ta ?ara cewa;
"dan Allah Uncle kai ma kasan kana da kyau sosai?" Mamaki tambayarta ya ba shi, girgiza kai ya yi yana mi?ewa tsaye
"Safeera ki je ki kwanta anjima za mu ?arasa hirar mu, ki faWawa Ummi, Zayad zai zo duba jikinta" ya ?arasa faWa yana tafiya.

bayansa ta bi da kallo,ta lura dariya da yawan surutu ya Waukewa rayuwarsa,ita kuma Mommynta ta saba da waccan rayuwar da suke yi na raha.


A Sangaren Ummee da Sulaiman

"Ina tambayarki kinyi shiru Ummee" cikin sanyin murya da kukan da ta sha ta ce"Yaaya Mammy ta tafi ta barni" da wani irin karaya da ya bayyana a muryar Sulaiman ya ce
"Subhanallahi maiyasa Maryam zatayimin haka maiyasa,Nima ban san maiyasa na ke mata haka ba amma ai na bata ha?uri" Ummee ba ta tsaya jin ?arashen sabbatun dayake yi ba ta bar wajen don yin Sallah magriba.

Gabaki Waya sai rayuwar Ummee ya koma wani iri,ba ta samun kulawa ba bu abokin hirar da za ta tattauna sirrinta da shi,don ba sa shiri da Zahra kullum a faWa suke ita kuma ba ?awa ne da ita ba. Hudayya tayi tunanin Ummee za ta zamema mata abar juyawa ta sau?i amma sai ta ga lamarin ba mai yiwuwa ba ne,don har lokacin a sashen Maryam take kwana ita kaWai.
Ba don ran Hudayya ya so ba sai don bata da zaSi ta ha?ura su ka koma Ikeja da su Zahra da Ummee.
Sabon Gidan Sulaiman na Ikeja ya yi kyau ba kaWan ba Unguwar ya fi wanda su ka baro tsari gine-gine ma su kyau. Farin cikin da Hudayya ta ga Ummee na yi wanda rabon da taga ta yi irinshi tun kafin barin Maryam gidan ne ya Warsa mata wani mugun ?ullin a ranta ?arin abin haushin da ya gusar da farin cikinta shi ne part Win da Sulaiman ya ware da sunan Maryam kuma komai iri Waya ya zuba mu su.
Bayan ta gama sa?e-sa?e kai tsaye ta kira Inna tare da bata shawarar mai zai hana ta dawo gidan da zama tunda a ?auyen ma babu abinda take yi.

Innar Zara'u Matar Mahaifin Sulaiman Guda mai ?arfi ta saki farin ciki na mamaye ranta,don ta daWe tanason dawowa gidan Sulaiman ragowar ?a?anta su ka hanata, tunda ba shi ya bu?aci hakan da kanshi ba. Bayan sun gama waya idanu Hudayya ta runtse ba wai don tanason zuwanta tayi haka ba, sai don tasan Sangaren Maryam ne kawai inda Innar Zara'u zata samu wajen zama, kuma itace ta isa ta hana Ummee zaman lafiya har ta gaji ta tattara ta koma ?auye gaban danginta.

Sulaiman Bayan ya gama sauraron hujjojin Hudayya da bayananta marasa tushe balle makama kai ya dafe a karon farko zafinsa ya fito ?arara tun bayan biye-biyen da takeyi a kanshi da kaushin murya ya ce "ba wa Innar Zara'u shawarar ta dawo nan bazai hanani dawo da Maryam ba Hudayya,ina da kuWin siyamata wani gidan,amma kawai dan na tabbatar da adalci ne yasa na haWaku,kuma Indai Innar Zara'u ce ga ki ga ita,kar na ji wani ?orafi da ga baya don ke kika gayyatota da kanki" yana gama faWa ya tashi yabar Wakin kamar iska.
Da yammaci a kan idon Hudayya babban motar Companyn da suka kawo furnitures Win su suka zo su ka kwashe komai tas ba'a bar ko tsinke na sashen Maryam ba sai kayan Wakin Ummee. Kasa barci ta yi itama sai a lokacin take ganin wawtarta Matar da tana ?auye ma Mijin su bai tsira ba,balle a ce yanzu tana ganin komai a kan idanuwanta.

&bayan kwana biyu da yammaci Innar Zara'u tayiwa gidan Sulaiman dirar bazata don babu wanda ya kawo zuwanta a lokacin. A Sangaren Maryam ta sauka sai dai babu komai a ciki sai kayan gadon Wakin Ummee,kuma Sulaiman ya tafi Kaduna a safiyar ranar saboda bai san da zuwanta ba, Zahra ce kaWai ta sani kuma itama sai da ta ja kunnenta a kan karta gayawa kowa. Maimakon ta tafi Wakin ?arta dake Sangaren Hudayya sai ta yi zamanta a Wakin Ummee. Wani irin kallon ?yashi da hassada takebin Ummee da shi Hudayya dake zaune a gefenta na tayata, cikin hayaniya da rashin son zaman lafiya Innar Zara'u ta cewa Ummee
"ke kam ?ar mallam(Mahaifiyarta) ba ta baki tarbiyya ba,don Allah Huda tayani ganin wa ni uban gashi a kan ?arnan kamar wata tsohuwar mahaukaciya kuma a haka gani takeyi ita kyan gani ne da ita har da ?in Waura kallabi,maza ta shi fitsararriya ki nemo kallabi ki ?unshe wannan abun takaicin na daina ganinshi" ta ?arasa faWa da tsantsar tsanar da ta yiwa gashin Mahaifiyarta saboda a kanshi Mijin su yake mata gori kafin ta samu nasarar korar mahaifiyar su daga gidan.

Ran Hudayya fari tas har wani murmushi take saki. Cikin son ?ara dasawa Innar Zara'u tsanar Ummee Hudayya ta ce "ai Ummee rashin kunya ma haka ya ganta ya ?yale,yanzu idan bakiyi magana ba gado Waya zata kwanta dake, babu mai gayamata ta Wauka banda haka saunawa ina yimata faWan Waura Wankwali,daga ni har Yayanta duk ta raina mu " murmushi Innar Zara'u ta saki kafin ta ce"wane ita aini ?ar Mallam ma haka ta ganni ta ?yale"
hawayen da ya zubowa Ummee ta share ta na rakuSewa a ?asan gefen kujerar da Zahra take kai tana chating da samarinta...

A Sangaren su Safeera

A zaune ta samu Mahaifiyarta da alamun ma ta jima da farkawa. Da yanayin damuwar da take ciki har lokacin ta ce "Safeera ina kika je haka inata jiranki har Wakin su Al-hussain na je bakyanan" da

14 / 43