FITINAR DUNIYA HAUSA NOVELS PART 1 BY SHATAN MARUBUTA.pdf

Author :  Abubakar Salisu Shatan Marubuta Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   1 / 6

1 to 3K   out of 15.7K words

Fitinar Duniya

Shatan Marubuta

BABI NA DAYA



Mugun tsaanin mafarkin da take yi a kowane dare ne yake dada tayar mata da b civarta kuwa
take ta faman bugwa saurarawa kamar yadda numfashi yake fita ta kin bunbu

Bayan haka kuwa sai tsananin mugun bakin kishin da yake cikin ranta makil, kishin yana dada
cin ran nata kamar yadda wuta ke kona suduga, da kuma maguwar zigar kawarta da take
kokarin kamawa na zuwa gun boka yai musu gagarumin asiri na hana mijinta Alhaji Abubakar
yai mata kishiya, abokiyar zama kamar yadda addinin musulunci ya sharadantawa da namiji
aurun mata hudu idan yana da wadatar yi, sannan kuma zai yi adalci a tsakanin auran na sa,
idan kuma ba zai yi adalcin ba, to masalaha ya hakura ya zauna da dayar tasa da Allah ya hore
masa ita

Mugun mafarkin nata da take yawaita yi ne ya sa hankalin nata ya ki kwanciya, shi ne ta sa wa
mafarkin da take yi din mugun mafarki. Saboda mafarkin nata maimaituwa yake yi guda daya
ba ya canzawa, yau shi ne gobe ma shi din ne. Saboda tana yin mafarkin ne a kan ya auro
mata kishiya limarya budurwar yarinya
kyakkyawa faru soll Mai zubin itin kamanni na Larabawa, gashin amaryar har gadon baya,
amarya mai alkunya, mai ladabi da biyayya, kamar da gaske, amma

A cikin mafarkin nata da ta yi ne da mijin nata Alhaji Abubakar, ya auro mata kishiya, sai ta fara
ganin canji a rayuwarta, wulakanci kuwa habu irin wanda ba ta gani a wajen Alhajin ta, da
rashin mutunci, yana bantararta da raki, ba da ma ya bari ta yi masa Korafi. Amarya kuwa yar
lele da hannu biyu yake tarairayar abar sa, da zarar ta bukaci abu nan da nan yake yanke
hukunci ya bi umarninta, da gaggawa yana himmatuwa.

Ita kuwa uwar gida sarautar mata, Hajiya Nafisa sai kawai ta zuba musu idanuwanta na mujiya,
ba ta cewa eh, sannan kuma ba ta cewa a'a. Saboda sun mayar da ita saniyar ware a cikin
shanu. Domin kuwa amarya da angonta Alhaji Abubakar kansu a hade yake, sun hade mata kai
sun zama tsintsiya madaurinki daya, amarya tai mata raki Alhaji kuwa saj masifa da yi mata gori
kamar wanda amarya ta mai asiri ta mallake shi, da ta yi umarni cikawa, tana yi masa hani
denawa.

Yan da gobe ta fi karfin wasa, ta yaro kyau, take ba ta yin karko, abin da babba ya hango wane
yaro ya hango, ko da kuwa zai hau (DALA da GORAN DUTSE). Saboda abin da yake faruwa a
gidan Albaji Abubakar bai tsaya kan Hajiya Nafisa uwar gidan tasa ba, abin har a kan 'ya'yanta.
Kama su amarya take yi tai musu dukan kawo wuku a gabanta, da ta bude baki za ta yi magana

sai Alhaji Abubakar ya zaburar mata da fada yana zare mata idanuwa. "Dan tsabagen rashin
mutunci irin naki watakan ba za ma ta hukunta sit ba ko, so kike yi su raina mata wayo har ta
kai suna zaginta? To wallahi bara na sahar da ke, duk abin da amarya ta yiwa 'ya'yan nan babu
ruwan ki, ki rabu da ita, ke kuma amarya kar ki saurara musu.
"To Alhaji babban angona". Ta amsa masa cikin shagwabar amarci da marairaicewar murya mai
kashe zuciya irin ta masoya na gaskiya, kamar wani tsohon wuju-wujin mahaukaci haka Alhaji
Abubakar ya bazami doguwar malin-malin dinsa ya fada dakin amarya yaoa yin huci mai
tsanani kamar wani tsohon maye.
Shigarsa dakin ke da wuya sai amarya 'yar masu gari cin dan wake da tsinko, ta harari Hajiya
Nafisa ta kare mata kallon raini sama da kasa. Ita kuwa Hajiya idan zuciyarta ta kai dubu yau
ranta ya gama facewa, yarinya kamar wannan da thi kannai da ita za ta yi mata kallon hadarin
kaji.
Hajiya Nafisa ta daka mata tsawa, "Ke yarinya ko mahaifiyarki ba ta isa ta yi min irin wannan
kallon ba ballantana ke, butulin amarya mai shigewa miji kin fi uwar gida matsayi a wajan miji.
To wallahi bari ki ji (this is the last warning), wannan shi ne gargadi da zan yi miki na karshe, kar
ki sake dukar min 'ya'yana su Halifa da kuma yi min kallon banza".
"Idan na sake yi miki kallon banza me za ki yi min? Sannan kuma idan na daki su Halifa ine zai
faru?"
bankali Keyarinya yar gidan marasa tarbiya, bismilla fan halak ya fasa dake su ga su nan a
gabana, ki ga jafa'in da zai faru a gidan nan da tsananin tashin

Kalin Hajiya Nafisa ta gama rufe bakinta amarya ta fusata cikin tsananin fushi ta janyo 'yarta
Momi ta wanka mata mari, ji kake fasss! Marin ya sauke a fuskar kumatunta, Momi yarinya 'yar
shekara biyu da rabi da haihuwa a duniya, saboda rashin imani amarya ta yi mata wannan
mugun marin. Momi ta hantsalia Easa saboda karfin marin ta fashe da kuka matsananci.
Hajiya Nafisa saboda fusatar da ta yi ba ta san lokacin da ta daga hannunta ba ta wankawa
amarya wani bahagon mari dauuu! Amarya ta ji fuskarta ta dade idanuwanta suka fara ganin
taurari na wahala, 'yan yatsun Hajiya sukai shati a kan kumatun amarya

Tafdijan! Tashin hankali ba a sa masa rana katsam yake zuwa, sannan ya ruda zuciya: Amarya
tana jin saukar marin Hajiya Nafisa a fuskarta tai ihun mahaukaciya ta kama Hajiya da kokawa,
Hajiya ta ce Karfa mai na ci ban baki ba, kar ta tsaya karamar yarinya ta ba ta kunya ta dokata
da kasa.
Haka suka cukuikuye juna suna yin fada irin nasu na mata. Kukan kurar da amarya ta yi na
mahaukaciya ya sa Alhaji Abubakar ya san babu zaman lafiya a cikin gidan nashi tsakanin
amaryar sa da uwar gida Hajiya Nafisa

Da gudu ya fito waje daga dakin amarya ya ga

me yake faruwa ne? Ai kuwa yana lekowa daga dakin ya ga abin, mamaki, Hajiya Nafisa ta
daga amaryarsa sama ta raba ta da časa tana shirin danfarawa, amma kafin ya budi baki yai
fürucin da zai hanata yin hakan, tuni Hajiya Nafisa ta bai wa mai uwa kunya, haka ta danfara
masa amarya a kasa, ta turmushe tana naushin ta da hannu.
Lokacin Albaji Abubakar ya kurma salati, de sauri ya karaso ya raba su, suka mike suna yin
haki saboda gajiyar da suka yi, suna jan numfashi sama-sama Haka suka tsaya kikam kamar
wasu gumaka, kowacce ta hau kan dokin zuciya, ba su ki su ei gaba da fafatawar tasu ba,
kowacce ta yiwa kugunta damara da daurin dan kwali suna mayarwa da junansu munanan
kalamai na Satanci.

Alhaji Abubakar ya shiga tsakaninsu yang yi musu fada, "Me ya hada ku fada ne? Ba kwa ji ina
tambayar ku kun yi min shiru?"

Kowacce ta tsuke bakin ta ba su ce da shi kala ba. A lokacin da ya kalli Amarya ya ce, "Amarya
me kika yi mata kuka kama yin fada kamar kaji?"

Amarya tana jin ya yi mata wannan tambayar sai ta fashe da kukan munafurci da ya kashewa
Alhaji Abubakar zuciya, cikin kisisina ta langabar da murya ta ce, "Wallahi Alhaji ba zan iya
zaman aure da kai ba ina ganin rashin mutuaci na uwar gida, dan ina matsayin kishiya ta dinga
gallaza min".
"Don Allah ki yi hakuri, ki kwantar da hankalin ki zan dauki mataki, atana ki sanar dani abin dan
miki na yi miki maganin ta

Sharri kayan kwalba in ji masu iya magana, nan take amarya ta kirkiro mummunan sharrin ta ta
jefi Hajiya Nafisa da shi, ta ce, "Alhaji cewa ta yi sai ta kashe ni da raina ta ra ca bar duniya, ita
ce ajalin

rayuwata! ta ce?" "Janalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Sai ta kashe ki

Amarya ta girgiza kai alamar na'am. Saboda kunar zuciya da bakin ciki na takaici kwalla ta
zubowa Hajiya Nafisa ta cikin idanuwanta tana yin shasshekar kuka tana cewa, "Alhaji abin da
Armarya ta fada ba gaskiya bane kazafi ta yi maka a kan ta mari Momi ne".

Amma ina kamar wanda Amarya ta yiwa asiri, sai ya ki ya amince, yai kememe ya na kafarsa ya
dinga naushinta a gaban Amarya, yanabalida ita yana kai mata duka da hannaye, tana kokagie
karewa dan gudun ka da ya illata mata kyakkyawar fuskarta.

In dai duka ne na rashin mutunci yau Hajiya Nafisa ta ji jiki, baiwar Allah haka Alhaji Abubakar
ya dinga ribdar ta kamar ya kama jaki mai gardama. (MUGUWAR AMARYA) mai bakar zuciya,
farin cikin Alhaji yana dukan Hajiya sai ran Amarya ya faranta, kamar Alhaji ya biya mata kudin
kujerar kasa mai tsarki, tana murmushin mugunta zuciyarta fal keta da kin Hajiya Nafisa.

Ko da Hajiya ta ga dukan Alhaji ba mai karewa bane ba, sai tai maza ta mike ta shige dakinta
da gudu ta

tada tana yin kuka mai tsuma zuciyar mitummai ta zauna akan makekiyar kujerar ta sai matsar
wala take vi da takaici, tunani da bakin ciki ya inaney zuciyarta, Allah ne kadai ya san abin da
yako dama rayuwarta

Tuna cikin rusa kukanta sai Halifa yaro mai way ya shigu cikin dakin na ta, yana rike da huinun
Ma tana yin kukan marin da Amarya ta yi mata dazu S kuwa Halifa kukansa la yake yi na ganin
irin dukan mahajfinsa ya lakadawa mahaifiyarsa ne a gal idanuwansa, shi no abin yake kona
masa ruhin raciy har ta kai ba zai iya jurewa ba kakan nasa yu hayyana fili Karara.
Halifa suna shigowa cikin dakin ya zauna a ku kujerar da mahaifiyarsa Hajiya Nafisa take zaune
a ka ita kuwa Momi sai ta fada kan cinyoyinta ta ci gaba da yin kukan ta babu kakkautawa. Yaro
ke nan, du mahaifiyar tats ta yi lallashin ta: Da da uwa sai dai Allah mahalieci mai raba tsakanin
soyayyar rankatakaf!
Fa tsayar da kukal rata dole ta sa hannu tana sharewa Momi &walia tana rarrashin ta, "Yi shiru
Momi kin ji ki dai na yin kuka, hakuri za ki yi marin da ta yi miki Allah zai saka miki da gaggawa".

Momi ta yi shiru ta dai na kuka, Hajiya Nafisa ta mike daga kan kujerar da take zaune ta je
gaban sil dinsu ta budo ta fara jidar kayan sawa tans shirya su cikin wata karamar akwatu ta
hannu, ta gama shirya n tsaf ta rufe sif din, ta dawo wajen su Halifa, "Momi

"Aunty ina za mu?" Halifa ne ya tambaye ta "Na or maka ta so mu tafi ko sai na sanar da kai

tafi za kai min tsirfar tsiya? inda za mu tafi Jikin Halila ya yi sanyi, bai kara tanka mata ba, ta

kama hannun Momi, Halifa yana biye da ita a baya suka fito daga cikin dakin, ta jawo kofar
dakin garam! Ta rafe da karfi, sannan te sa kwado ta datse kofar dakin nata

Kamar wani tsobon wuju-wujin mahaukaci yana jin karar rufe kola ya fito daga cikin dakin
Amarya a razane, sai Amarya ta biyo bayansa, a tare suka fito su biyun. Nan fa su kai arba da
Hajiya Nafisa da 'ya'yanta a tsaye kikam za su yiwa gidan balaguro, ran Alhaji Abubakar idan ya
kai dubu ya baci, a razane ya daka mata tsawa, "Ina za ki je haka riki-riki kika rarumi kaya a
akwati?"

Tambayar da ya yi mata ke nan, ba ta kuma ce mai ga inda za ta je ba, abin da kawai take yi shi
ne zubar da kwalla tana matsar hawaye mai dumi a idanuwanta, gami da zufa suna ketowa ta
jikinta tamkar wata mai zazzabi

A karo na biyu Alhaji Abubakar ya kuma maimaita mata tambayarsa da yai mata, ta kalle shi
"Ka bani hanya na wuce na fice ma daga gida".

Furucin da ta yi masa ke nan, sai ya ji kamar ta soka masa allura a zuciyarse, ya zaro mata
idanuwansa ya nuna ta da dan yatsan hannunsa ya ce, "Wallahi Hajiya zan mari fuskarki idan
ba ki sanar dani inda zai
"Saidai kuwa ka mare ni tun da uwata jaka ta haifa ma duniva, amma bazan sanar da kai ba sai
dai ka kashe ni a gidan nan tun da haka kake so".

"Innalillahi

warinna

ilaihi raju Subahanallahit! Hajtya yanzu ni kike gayawa baka da bakin ki? Lallai na varda duniya
ta zo karshe, kuma ba ki da mutunci, zuciyarki ta mutu da rashin tarbiya idanuwanki sun
kyankyashe kwarkwatar su, zan kuma y maganin ki

Ya zo nan a jawabinsa Hajiya ta kara fashewa da kuka, "Ka bani hanya na wuce na fita daga
gidan ka, gida mai kucin takuru, nice uwar gida an mayar dani moriyar ganga

Alhaji Abubakar ya sha gabanta da gaggaw "Karya kike yi babu inda za ki, idan kuma kina da
kari sai ki ture ni ki wuce mu gani, sannan zan kara tabbatarwa da kaina ba ki da kunya ke
fitasararriya ce"

Amarya kuwa ba ta da ta cewa, kallo ne kawai na ta, domin ta san cewa ran Hajiya ya gana
baci, komai zai iya faruwa idan har ta kuskura ta sa baki Hajiya za ta kuma yi mata kuli-kulin
kubura ta kuna doka ta da kasa, dalilin da ya są ke nan ta tsuko bakin ta ba don kuwa tana so
ba. Amma tana da bakaken maganganun da za ta fadawa Hajiya na batanci.
Zuciyar Hajiya ta narke da bacin rai na fusatuwa, sai kuma zuciyar tata ta sake kawata mata
cowa ko mene ne yau sai dai ya faru a gidan, amma sai ta fita ko me zai

biyo baya, Na ce da kai ka matsa ka bani hanya na wuce"

Ta gaya masa cikin nuna isa da gadara, ama duk da haka zubar da kwalla take yi ba
kakkautawa kamar wadda Allah subhanahu wata'ala ya halicce ta da baiwar-kuka.

Alhaji Abubakar ya ga da gaske take yi tana fada masa bakaken maganganu na Satanci kamar
wata raai tabin bakuken aljanu a kanta na mahaukata

Ganinta a cikin irin wannan kamannin ne ya sa jikinsa ya yi la'asar, saboda ya san yadda ta
dauki fi haka sai dai kawai gyaran Allah a kan lamarin uwar gidansa, ya san cewa matukar
matar tasa ta fusata ba ya iya shawo kan abar sa, sai dai matukar ita ce ta so hakan ma'ana dai
ta huce a kan dokinta na zuciya da ta hau mai wuyar sauka.
Ya dube ta ya ce, "Hajiya ta ke nan, dan Allah ki sanar dani in da za ki tafi haka, me kuma ya sa
din za ki rafi?"

Ko da ta fuskanci ya yi mata magana mai sanyaya zuciya sai ta ji hankalinta ya kwanta, dole ce
ta sa ba dan tana so ba ta sanar da shi cikin wata irin muryar sarewa mai kashe jiki da raunana
zuciya, da tsumar da kwanciyar hankali irin na kalaman masoya..

Ta ce, "Alhaji gidan iyayena zan tafi da 'ya'yana yanzun nan, kuma ka fi kowa sanin dan me ya
sa zan tafi da wannan munafukar Amaryar mai bakar zuciya?"

Ta nuna Amarya da dan yatsan hannunta

Amarya da ma kwantan bouna ta yi, Kiris take jin Hajiya Nafisa ta yi mata tari, "Ke malama ki
bar núna ni da hanmi, ni ma kin sani kanwar ja co, haka ma gautan, ba na barin wargi kowa ya
nuns min yatie sallari cizaina karya shi

Amarya ta tafa hannayenta ta rike kugu, tans tsammanin jiran tashin haokali daga wajcu Hajiya
Nafisa, sa'a daya kawai ta samu Hajiya Nafisa ba a warginta take yi ba; yanzu da Alhaji tako
bruguwa, shiya sa ma ko tsayawa ba ta yi sauraran sakarur banzar ba mai wauta

Ganin hakan ne ya sa ran Amarya ya baci, taji zuciyarta kamar ta fito ta fashe sakamakon cewa
Hajiya ba ta tanka mata ba. "Wai dan Allah Alhaji mai kake jirs ne da wannan matar haka, tun
da ta co gidan iyayents za ta tafi kawai ka ba ta hanta ta wuce, ko na sanu na hota na wataya ni
da kai mu bararraje a gidan, hankalin mu a kwance mu sha iskar duniya"
Alhaji Abubakar ya so ya shirya da uwar gidansa su sasanta tsakaninsu, amma da ya ji umarnin
Amarya sa tana sa shi abu nan take yake aiwatar wa kanmar wanda ta yi wa asiri, irin mugun
asirin nan mai tasirin raba miji da mata ana zaman lafiya, asiri mai haukata matan aure, ma sa a
manta uwa da uba da sauran dangi, da 'yan uwa da kuma garin da mutum yake ya manta
komai.

Asirin zuwa makabarta da daddare, asirin gidan fururuwa, asirin tsohuwar rijiya, asirin tukubar
mai tsire, asirin yi wa mahaukata mata lalata ayi zina da su (fyade),

asiri na hankaka mugun asiri ke nan mai taliyar da rayuwar mata har abada, ba za a sake
tunawa de wanda a kai wa asirin ba, ko mace ko namiji. Sai kuma asirin bishiyar Raya.
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Subahanallahi! Wannan asirin Allah ya yi mana tsari da shi,
wallahi mummunan asiri ne, Allah ya kysuta, ya kiyaye mu da FITINAR DUNIYA
Asiri da sassan jikin mutum bil adama ko tsafi, asirin binne jakuna da mtuum da ransa a kama
sa a binne da ransa yana yin ihu saboda rushin imani irin na mitane masu nikata wannan
mummunar ta'asar saboda rashin mutunci da imani.

Haka dai asirirrika suke da dama bila adadin, Alhaji Abubakar ya kalli Hajiya Nafisa ya ce, "Na
yarıla zan baki hanya ki wuce, amma ba zan barki ki tali da su Halifa ba a nan za ki bar min su,
ki kama hanya ki fice min duga gida" ab

Ta ji kamar ya tsira mata allura, cikin tsananin firgici ta kalle shi, "A gaskiya Alhaji ba zan bar
maka su ba, saboda

1 / 6