Author : Rufaida Umar Category : Top Hausa Novels 2025
ta ga wata sura marar
kyan kallo don kamar babu ɗigon imani cikinsa. Ya ƙaraso,
yanzun ne tunanin Ramlat ya ba ta cewar tarko ne aka yi
mata kuma ya faɗa. Da wani irin sauri ta ja gefe ta
yunkura za ta gudu, tuni Gwaska ya damƙe ta tana kokarin
ihu ya rufemata baki.
"Ki kashe ta! Me kike jira?!" Ya yi maganar a tsawance
ganin Halima ta kasa sarrafa bindigar kamar yanda ya
koyamata. Ta runtse idanu ta harba ba tare da saiti ba.
Wata ƙara Gwaska ya saki sakamakon samunshi da ta yi a
cinya. Ramlat ganin hakan ta ture shi za ta gudu, Halima
ta damƙota.
"Ki kashe ta nace!" Gwaska ya fadi iyakar karfinsa yana
dafe da cinyarsa. Jin haka AlHassan ya fito daga
maɓoyarsa sai dai kafin ya karasa tuni Halima ta ƙara
sakin bindigar wanda cikin sa'a ta samu Ramlat a kafaɗa.
"You are under arrest!"
Muryar mutum suka ji. Gaba daya suka juya, fitilun
motocin da ke shigowa gurin ya haskewa Halima fuskar
AlHassan. Ta zaro ido ta cikin mask din fuskarta. Hussein
ne?! Hajiya dama karya ta yi da ta ce ta saka shi bacci?
Ganin haka ta yunkura za ta gudu sai dai da wani irin zafin
nama na ɗaya daga cikin ƴan sandan, ya cafketa tana
kiran wayyo Allah. Ramlat dake zube anan tana gani
dishi-dishi hannunta na dafe da kafaɗarta da Gwaska ya
samu. Ba shiri ta zube a ƙasa. Wani irin sunguma da
AlHassan ya yi mata a gigice yana ambaton sunanta,
amma ko motsi.
"Kai ta mota mu je asibiti!" Hisham daga bayansa ya faɗi
a gaggauce. Kafin ka ce me, sun isa mota tuni rigar
AlHassan ta ɓaci da jini. Hisham ya bada umarnin tafiya
da su Gwaska da nufin zai je station din daga baya. Suka
tafi da ɗan sanda saboda ba da shaida.
Munir wanda ya taho, suka yi waya ya ke sanarmasa halin
da ake ciki, hankali a tashe ya juya kan abin hawa ya nufi
asibitin da Hisham ya kwatantamasa.
Kafin su je ya riga su isa, don haka suna zuwa ya tarbesu.
Shi ya karɓi Ramlat ya ƙarasa ciki da ita. Sai dai aka
kammala dukkan wani sa hannu aka hau ceton rai da
gaggawa.
Munir ya kira gida ya faɗawa Zulaihat wacce ke faman
kiransa a waya. Jin abinda ya faru daga ita har Hajiya
suka kasa zama gidan suka nufo asibitin.
"Laifina ne, meyasa na bar ta ta je ita kaɗai ban maramata
baya ba?"
"Ka daina faɗin haka Hassan, rai da ajali duk a hannun
Ubangijin al'arshi su ke, kaddararmu ce haka. Mu yi fatan
samun saukinta." Hajiya ta faɗi tana mai sharce hawayen
saman kuncinta.
AlHassan hankalinsa sam bai kwanta ba, ga tsananin son
ganin Hussein da ya ke yi. Yanzun da ya san inda yake sai
ya ke jin kewarsa ta ƙaru. Fitowar Likita ne yasa suka
dubeshi.
"Alhamdulillah an cire harsashin, ba dai ta farfaɗo ba.
Amma muna sa ran komai zai zo da sauƙi. Dafin bai shiga
jikinta sosai ba."
"Alhamdulillah." Suka furta kusan a tare. Hajiya ta dubi
Zulaihat bayan sun gama addu'a da godiya ga Allah.
"Uwani maza ki wuce Muniru ya sauke ki gida, dare ya yi.
Ni zan tsaya anan da ita."
"Aa Hajiya, ba za'a yi haka ba. Su Ummi da aka bari a gida
fa?" Cewar Zulaihat.
"Ina ce Ladidi na nan? Zan ƙarasa na nemi alfarma ta
kwana yau dai ɗaya. Daga nan zan haɗaku a waya idan da
abinda ki ke buƙata sai na dawo na kawomaki. " Faɗin
Munir yana mai ƙarashewa da mayar da akalar zancen ga
Hajiya.
Suka yi na'am, Hajiya ta ƙara duban AlHassan.
"Hassan sai hakuri ka ji? A kara godewa Allah tunda a
baya ma ba'a san inda yake ba. Yanzun kuma da Allah Ya
nuna in sha Allahu komai zai zo karshe. Kar wannan ya
dameka. Ya kamata ka wuce gida duk ka ɓata jikinka da
jini."
AlHassan ya jinjina kai yana gyara zaman gilashinsa, suka
yi sallama aka tafi aka bar Hajiya ita kaɗai ta na jiran
likitoci su kammala su ba ta umarnin shiga.
A harabar asibitin bayan tafiyar Munir da Zulaihat, Hisham
ya dubi AlHassan.
"Dama nayi mamakin ta yanda za'a ce wani abin zai sami
Hussein. Ba wai ba za ya taɓa faruwa ba ne, sam aa, sai
dai idan har zargina ya tabbata da hannun Hajiya Zeenatu
a abinda ya faru ga Ramlat to ba zai taɓa zamtowa an
riski Hussein a wurin ba. A irin son da Zeenatu ke yiwa
Hussein ba za ta bari a haɗa baki a cutar da shi ko ya ya
ba."
"Kai ma kana da labarin Hussein kenan?"
AlHassan ya tambaye shi da gaggawa. Ya gyaɗa kai yana
duban agogo.
"Ina da labarin komai, na taƙaice maka Hussein aminina
ne, bani da aboki sama da shi a faɗin duniya. Sai dai
kuma ya dace ko me zamu yi kada ya wuce gobe, idan ba
haka ba za mu rasa damar mu."
"Me kake nufi?"
Tiryan-tiryan Hisham ya ba shi labarin duk abinda ya sani
dangane da Hussein. Ya ɗora da faɗin.
"Babu damar a yiwa Hussein zancen ƴan uwansa, ba ya
so. Da zarar ka tambaye shi game da asalinsa, kansa zai
ɗau zafi ya sauya gaba ɗaya. Ransa kuma idan ya yi dubu
toh zai ɓaci. A ranar idan mutum bai yi dagaske ba
girmansa zai iya faɗuwa a idanun Hussein."
"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Mace ce? Ita ta rabamu
da Hussein? "
"Hum, sai addu'a." Hisham ya furta, a ƙasan ransa yana
jimamin yanda AlHassan zai ji idan ya gane da sa hannun
Kawunsa ciki. Hakan yasa bai faɗamasa ba har sai
gaskiya ta yi halinta.
"Ya za'a yi na gan shi yanzu? Bana so su kai ga barin
ƙasar."
"Kada ka damu, a gobe da safe in sha Allah zan haɗaka
da ɗan uwanka. Za ku ga juna."
Murmushi AlHassan ya yi mai haɗe da dariyar farin ciki,
kasa hakuri ya yi sai da ya rungume Hisham yana murna.
"Na gode, Na gode sosai. Allah Ya bar zumunci."
Hisham ya yi dariya gami da dukan kafaɗarsa.
"Ameen. Kar ka samu damuwa. Ka kara godewa Allah,
sannan Ramlat. Ba karamin namijin ƙoƙari ta yi akan ɗan
uwanka ba."
Murmushi sosai AlHassan ya yi tare da fatan Allah Ya ba
ta lafiya.
Hisham ya amsa kafin su yi sallama, shi ya nufi gida,
Hisham kuwa ya zarce Police Station don jin abinda ake
ciki.
***
_*LAMIƊO CRESCENT*_
Safa da marwa ta ke faman yi a tsakar falon, ta ɗauki
waya ya fi a ƙirga. Kiran Halima ta ke jira kamar yanda
suka yi alƙawari.Ta kira Hajiya Batool ya fi sau goma don
ta ji ko sun yi waya amma shiru ka ke ji, Malam ya ci
shirwa. Ta kara kai idanunta kan wayoyin Hussein da ke
ajiye saman kujera. Baƙin kishin Ramlat ya ƙara ƙarfi a
zuciyarta. Ta gwada amfani da yatsarsa ta buɗe wayar,
hakanan ta gwada shiga lambobin Ramlat, HEART da ta
gani a rubuce ya sanha ta saki ƙarar da har sai da John
suka fito daga kicin zuwa falo. Ta dakamusu tsawar da
dole suka koma.
Hajiya Zeenatu ta sauke ajiyar zuciya tana jin wani
malolon abu ya tokaremata maƙoshi. Awanni biyu kenan
da ta ba Hussein lemo ya sha wanda ya yi sanadiyyar
baccinsa, a wannan lokacin ba abinda ta ke burin ji sai
saƙon mutuwar Ramlat. Wayarta ta yi ƙara da wani irin
zumuɗi ta duba. Tsaki ta ja ganin lambar Kawu Modibbo,
sai da ta kalli ƙafar benen ta tabbatar babu mai saukowa
sannan ta amsa a fusace.
"Ina jinka."
"Ya ake ciki?"
Ta safe goshi gami da runtse ido cikin soma gundira da
tunani.
"Ni kaina na gaji da tambayar kaina. Abinda ya fi shi ne
zan nemi Halima har gidansu na bincika."
"Ga dukkan alamu lamura sun ɓaci."
"Ina tsoron hakan ta kasance."
Ba ta jira cewar Kawu ba ta kashe kiran.
"Zeenat."
Da wani irin ruɗewa ta juyo tana dubansa, yana dafe da
goshi a hankali kuma ya shiga saukowa daga
matattakalar. Ta yi kokarin saita kanta ta karasa gareshi
da murmushin yaƙe.
"Sannu, ka sha bacci."
Hussein ya gifta ya karasa ya zauna saman kujera kansa
na ci gaba da sarawa.
"Me ki ka ban na sha?"
Ya tambaya ba tafe da ya kalleta ba. Ta zauna gefensa.
"Ba ka samun bacci yanda ya kamata, ga gargadin likita
da ya ce ka dinga samun hutu, shiyasa na sanyamaka
maganin bacci a lemu na kashe wayoyinka."
Ya dubeta da idanunsa da har sannan ba ya jin baccin ya
sakeshi.
"Haba Zeenat, shi ne dalilin sanyamin maganin bacci?
Meyasa haka? Wane irin hutu ne ba na samu? Cuta ba ta
Allah ba ce?"
"Hakane, to ka yi hakuri." Ya mike rai a ɓace ya ɗauki
wayoyinsa ya haye sama. Ta bishi da kallon munafuki
karon farko a rayuwarta.
"Ka ci darajar son da nake maka Husseini, da yau sai ka
gane shayi ruwa ne."
Ta furta a hankali yanda ta san ba zai ji ba. Har hango
hotonsa da Ramlat ta ke yi a kwayar idanunta. Takaicinta,
meyasa ba ta nemi kwararrun ƴan daba sun aiwatar mata
da komai ba? Meyasa sai Halima?
Ta ja tsaki tana sharce gumin da fargabar ko Hussein ya ji
wayar da ta yi ya haifarmata.
***
"Ita kuma wace ce wannan?" Hisham ya tambaya yana
karewa Halima da ke faman sharɓar kuka a bayan cell
kallo.
"Sharrin shaiɗan ne wallahi, don Allah don Annabi s.a.w ku
yafemin wallahi nayi alƙawari ba zan ƙara ba. Nima san..."
_*"Halima, ki tabbata koda wasa aka samu matsala, kar
bakinki ya yi kuskuren ambaton sunan ɗaya daga cikinmu.
Ki ce kawai dai kina kishin Ramlatun za ta auri Chairman
dinku ne. Ki ka kuskura ki ka yi gangancin tonamana asiri,
ki sani rayuwarki ce za ta ƙare a doron ƙasa saboda za mu
bar ki ki rayu kuma ki mutu a gidan yari ba tare da mun
ɗauki matakin fiddoki ba. Idan kuwa ki ka bar komai a
cikinki ki ka faɗi yanda na ce, toh shakka babu ina mai
tabbatarmaki ko kwana uku ba za ki yi a hannun ƴan sanda
ba za mu sanya a fiddo ki kuma ki bar garin. Idan kunne ya
ji....jiki ya tsira." *_
"Kin yi shiru? Me ki ke son ki ce?!"
Tana kuka sosai ta dubi Sajan da ke mata tsawa, a
gefensa Hisham ke tsaye yana jiran ji daga bakinta.
Girgiza kai ta yi.
"Nima sharrin shaidan ne."
"Ƙarya ki ke! Ba haka ki ka so ki ce ba!Ki fito ki faɗi wanda
ya sanya ki!"
Cewar Hisham a ruɗe. Ya ja, itama ta ja. Gwaska tuni an
yi asibiti da shi.
Dole haka Hisham ya hakura ya bar case hannunsu
sannan ya wuce gida, lokacin sha biyu ta wuce.
***
WASHEGARI...
Da sassafe Hajiya Zeenat ta shirya. Motsinta ne ya tashi
Hussein dake bacci. Ya dube ta sadda ta ke kokarin
ficewa daga ɗakin.
"Lafiya? Ina zuwa haka da sassafe?"
A firgice ta juyo tana dubansa,ta wayance da yaƙe.
"Am..am..dama Hajiya Batool ta kirani ba lafiya har an kai
ta asibiti ma. Shi ne zan je dubiya." Ya gyada kai kawai ya
juya ya kara jan bargo, ta sauke ajiyar zuciya ta fice. Ta
bar Hussein da tunanin irin nasu auren, wannan wane irin
aure ne da mace ke da ikon fita ba tare da iznin miji ba?
Anya kuwa hakan zai haifarmusu da ɗa mai ido?
Ya sauke ajiyar zuciya gami da lumshe idanu cikin tunanin
laifinsa ne tunda tun farko haka su ke yi. Bai kuma san ya
hakan ta faru ba.
Wayarsa ce ta yi ƙara, sunan Hisham ya gani yana
murmushi ya ɗaga.
"Kira da safiyar Allah, bashin me na ci?"
"Haba Malam, ina ka shiga ne wai? Jiya na kira duka
wayoyinka amma a kashe, lafiya dai ko?"
Hussein ya lumshe ido ya ja guntun tsaki tuno da shirmen
Zeenatu.
"Share kawai, lafiya lau ne. Ya aka yi?"
"Ba ka da labarin an kai wa Ramlatu hari?"
Wani irin miƙewa Hussein ya yi gaba ɗayansa har santsin
bargon na ƙoƙarin kifar da shi ƙas.
"What?"
Labarin komai Hisham ya ba shi.
"Tana wane asibitin?"
Ya sanarmasa.
"Yanzu zan zo."
Daga nan ya katse kiran bai jira komai ba.
***
MISALIN ƘARFE TAKWAS NA SAFE...
Hawaye ta ke fitarwa yayinda ta ke tariyo komai a
kwanyarta. A yanzun da Hajja ke salati da tambayar wa zai
aikatamata hakan? Itama a sannan kwakwalwarta ta shiga
aikin tunani. Kasancewar ta juyamusu baya ya sa ba
wanda ya lura da tashinta. Cikin dare dai ta farka sannan
ta ƙara komawa bacci.
"Abin dai da ɗaure kai." Hajiya ta furta tana ƙara riƙe
carbin hannunta da ta ke ja.
"Nifa ina zargin matar Hussein wallahi. Tunda..."
"Yi shiru kawai Rafee'ah, zato dai zunubi. Irin haka ne sai
ki ga ana zaton wuta a maƙera sai aka same ta a
masaƙa."
Rafee'ah ta yi shiru amma dai kam zuciyarta cike take da
zarginta. Kwankwasa ƙofar da aka yi ne suka bada iznin
shigowa. Hisham ne da AlHassan, suka karasa aka gaisa.
"Kada dai ace har yanzu ba ta farfaɗo ba?" Cewar
Hisham.
"Aa, ta farfaɗo cikin dare, har na taimaka ta ɗan zagaya.
Sannan ta yi salla da Asuba ma. Baccin ne dai ya ƙara
kwasarta."
Ramlat da ke jin bayanin Hajiya sai ta runtse idanu, wani
radadi kafaɗarta ke mata, sai dai idan har za ta iya jure
wannan adalilin Hussein, idan har zaa iya yaudararta a
kafamata tarko a kansa, toh ba karamin so ta ke yi mishi
ba. Ta ƙara aminta da hakan.
"Au dama idanunki biyu?" Cewar Rafee'ah wacce ta
zagayo domin gyaramata ɗankwalin kanta da ya zame.
Ta dube ta, ganin tana hawaye ta sa hannu ta shiga
sharemata.
"Haba Ramlat, meye kuma na kukan tunda Allah Ya riga
da ya tsare? Yi shiru don Allah. Ko za ki tashi zaune?"
Ta gyada kai. Da taimakon Rafee'ah ta miƙe zaune ta
jingina da filo. Ta gaida Hajja da su Alhassan.
Wayar Hisham ta yi ƙara ya duba, shi kansa AlHassan
tunda ya ji batun zuwan ɗan uwansa ya rasa sukuni.
Burinsa kawai ya gan shi don ya tabbatar da komai.
Aikuwa shi ɗin ne.
"Kana waje? Ok gani nan zuwa."
Yanda Hisham ya miƙe hakanan shima AlHassan ya mara
mishi baya. Rike hannunsa ya yi.
"Ka yi hakuri, nan zai shigo, ka jira ya karaso ciki ka
ganshi."
Ramlat da kirjinta ya tsananta bugu ta dubi Hisham a
hargitse. Nan da nan wasu hawayen suka kwaranyo. Baki
na rawa ta ce.
"Hussein..Hussein ne?"
Hisham ya dubeta.
"Shi ne, ku kwantar da hankalinku yanzu zan kawo shi."
AlHassan a dole ya dakata sai dai ya kasa tsayuwa wuri
guda, safa da marwa ya shiga yi yana kallon ƙofa. Koda
aka tura ƙofar aka shigo. Hisham din ne a gaba, a
bayansa kuma Hussein. Kamar wani gunki haka AlHassan
ya ja burki yana kallonsa ƙurr.
"Hussein...?" Ya furta, furucin da ya ja hankalin Hussein
dake sanye da Maroon shadda da hula, ya dubeshi.
KARFEN KAFA Chapter 60
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323
By Rufaida Umar
Kallonsa yake yi sosai kirjinsa na bugawa da sauri. Ramlat
ta runtse idanu tana mai addu'ar komai ya tafi daidai.
Da wani irin sassarfa AlHassan ya tako ya rungume
Hussein kawai sai ya soma kuka.
"Hussein." Ya ƙara kiran sunansa karo na biyu, Hussein ya
yi ɗif sai hawaye da ke zuba saman fuskarsa. Ji ya yi
kamar ana saramasa guduma a tsakiyar kansa, a hankali
ya soma ganin dishi-dishi, lokaci guda idanunsa suka juye
yayinda baƙin kwayar idanun ta ɓace ɓat. Hisham da ke
tsaye a baya shi ya lura da sauri ya karasa ya rike Hussein.
Jikinsa wani irin kakkarwa ya ke yi.
"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!"
Cewa Hisham yana rike hannun Hussein, jin haka
AlHassan ya ɗago wanda saura kiris Hussein din ya zube
don kuwa da jikinsa ya samu madafa.
"Riƙe shi sosai." Cewar Hisham, suka taimaka suka fitar
da shi sai wurin likita. Ramlat tuni ta miƙe tsaye. Su kansu
su Hajiya sun rude. Ganin tana kokarin ficewa yasa
Rafee'ah riƙo ta.
"Ina za ki je? Ba ki ganin halin da ki ke ciki? Idan kin je
lafiya za ki ba shi?"
Ta girgiza kai tana hawaye, ta bude baki sai dai ta rasa me
za ta ce don haka ta koma ta zauna. Hajiya ce ya fidda
waya don ta kira Malam ta sanarmasa halin da ake ciki.
Nan take ya ce maza ta aiko a karɓi ruwan da ya haɗa da
ganyen magarya ya yi addu'o'in karyewar sihiri. Ba shiri ta
yiwa direbanta waya ta ce ya biya Yakasai ya karɓo mata
saƙo.
***
Duk iyakar awon da likitocin su ka yi ba su gano komai
game da ciwon Hussein ba. Don haka koda suka samu ya
bar jijjigar, idanun suka dawo daidai sai Likitan da ya karɓi
Hussein ya fito wurin su AlHassan. Suka tarbe shi da
gaggawa.
"Ku yi hakuri.."
"Mutuwa ya yi?" Faɗin AlHassan a gigice, girgiza kai
Likitan ya yi yana mai riƙe hannunsa.
"Ko kusa ba haka ba ne, asalima yanzu mun samu komai
ya daidaita. Sai dai hakikanin gaskiya ba za mu ce ga
abinda ya jawomasa hakan ba, yanzu dai halin da ake ciki,
dole zamu yi mishi tests don mu gano ainahin inda
matsalar take."
Suka jinjina kai.
"Ba damuwa Dakta. Allah Ya ba shi lafiya." Cewar Hisham
da hankalinsa ya ɗan kwanta.
Bayan wucewar Dakta ya dafa kafaɗar AlHassan wanda ya
cire hular kansa tsabar gumin da fargaba ta haifarmasa.
"Kada ka damu ɗan uwa, na fadamaka dama duk sadda
maganar dangi ko ƴan uwa ta haɗa mu da Hussein ya kan
shiga wani irin hali, ina kuma ga yau ya yi ido huɗu da
ɗan uwansa?"
"Hakane, sai nake ganin kamar ba na asibiti ba ne."
AlHassan ya faɗi bayan kai karshen nazarinsa.
"Hisham, ya jikinnasa?"
Suka juya, Rafee'ah ce. Ta karaso suka yi mata bayani.
"Allah Ya ba shi lafiya. Kada ku damu, Hajiya ta aika a
karɓo ruwan ganyen magarya mai addu'o'in karya sihiri,
da yardar Allah komai zai daidaita."
AlHassan ya sauke ajiyar zuciya yana ɗan murmushin jin
dadi da wani irin kaunar zuri'ar da ke kara mamaye
zuciyarsa.
"Na gode kwarai, Allah Ya sakamaku da alheri. Allah Ya
bar zumunci."
Ta yi dariya kadan.
"Ameen. Ai yiwa kai ne. Bari na koma, dama Hajiya ce ta
ce na sanarmaku sannan na gano halin da yake ciki don
marar lafiyarmu ta tashi hankalinta sai kuka ta ke yi."
Murmushi AlHassan ya yi yana mai hasashen wani abu da
tun a jiya ya yi zaman dirshan a kwakwalwarsa.
***
TA FARU TA ƘARE...
"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Halimar aka kama?!"
Hajiya Zeenatu ta faɗi tana tsaye a bakin ƙofar gidan
Kakar Halima wacce ke rike da ita. Ƙanin Halima uwa
daya uba ɗaya wanda daga ita sai shi, su uku iyayensu
suka haifa kafin rasuwarsu, dayayar Halima, Halima sai
Yusufa. Kakarsu ta karɓi riƙo. Yusufan ya share hawaye
yana duban Hajiya Zeenatu.
"Wallahi ranki ya daɗe, ɗazu aka yi mana waya, naje har
ofishin ƴan sandan na sami Aunty Halima, wai dumu-
dumu aka kama ta da bindiga za ta yi kisa. Wannan abu
ne da ko a mafarki ba mu zaci faruwarsa ba. Su biyu aka
kama, shi ɗayan ko Gwaska ko wa? Yana asibiti. Yanzu
Kaka na kwance ba lafiya tun da ta ji halin da ake ciki."
Hajiya Zeenatu wacce ta yi mutuwar tsaye, ta yi sauri ta
dawo hayyacinta. Baki na rawa ta ce.
"Ta..ta..faɗi wadanda suka sanya ta?"
Kallon da Yusufa ya yi mata na nazari sai da ya sa ta sakin
ƙaramar tusa mai haɗe da fitsari ba shiri. Ya girgiza kai.
"Abin kunya ne ace saboda ɗa namiji za ta aikata hakan.
Kishi ne kawai don uban gidansu na aiki zai auri abokiyar
aikinta Ramlat. Haka ta sanarmin."
Ya karashe da wani irin jin kunya. Ajiyar zuciya Hajiya
Zeenatu ta sauke ta juya za ta shige mota.
"Amm..Hajiya, na ce sai dai ban sanki ba. Kema wurin
aikinta ki ke ne?"
Ta juyo.
"Eh, tare muke aiki." Tana kaiwa nan ta juya da sauri ta
faɗa mota, ta ja. Kiyayewar Ubangiji ce kawai ta isar da ita
gidan Hajiya Batool. Itama nan ta iske ta su na dambe da
surukarta. Dakyar ta raba su. Ɗan Hajiya Batool ba