KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt

Author :  Rufaida Umar Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   34 / 38

99K to 102K   out of 113.5K words

fada ta ƙara, bai ɗauki halin
mahaifinsa ba balle na mamansa, Hamma AlHassan ma
haka. Hamma Hussein bai zauna da shi sosai ba da na
tabbatar zai gamsu da kyawawan ɗabi'un Taheer. Adda
Amal sanadin aurena da Taheer zai iya sanyawa su shirya.
Babban damuwata Hamma Hussein ya kwace wayata,
Rasheeda ta kirani ta wayar Dada tana kuka ta shaidamin
yana asibiti kwance ba lafiya."
Hafsat na kaiwa nan ta mike zaune, ita Ramlat kallonta
kawai ta ke tana fidda hawayen tuna baya, itama dama
haka ta kafe? Amma ba za ta taɓa bari Hafsat ta yi irin
nata ba.
"Adda Amal kimin alfarma ki ban wayarki, sau daya kawai
zan kirashi, daga haka ba zan kara ba. Wallahi kawai
gaisawa zamu yi na kuma roƙeshi mu ci gaba da addu'a.
Har abada ba na fatan na bijirewa iyayena da yan uwana."
Ramlat ta yi jim, tana tunanin anya kuwa idan ta yi hakan
ba matsala? Sai dai kuma irin magiya da nacin Hafsat ya
sa ta miƙamata wayarta. Kasa fita ta yi daga dakin ta jira
har Hafsat ta kammala wayar, Ramlat banda kallon ƙofa
ba abinda ta ke yi. Tsoronta kar Dada ta faɗo ɗakin don ta
san abu ne mai matsanancin wahala Hussein ko AlHassan
su shigo ɗakin.
Da murmushi ta dubi Ramlat.
"Adda Amal."
Sai ta rungumeta don farin ciki can kuma ta saketa.
"Cemin ya yi za su zo nan da kwanaki kalilan har Babansa,
zai zo neman gafarar Dada da su Hamma."
Sosai itama Ramlat ta ji dadin hakan. Ta rike hannunta.
"Toh kinga ni, don Allah ki saki ranki, kinga Dada kin jefa
ta a damuwa. Ta ce ko ganin idon baƙuwarku ba kya yi, ba
ki san ki danne zuciyarki da abinda ke cikinta ba. Jefa
iyaye cikin damuwa masifa ce a garemu. Kuma ina mai ba
ki shawara ki dage da nemawa kanki zaɓin Allah, ki rabu
da biyewa son zuciya wurin dagewa akan zaɓinki."
Hafsat wacce tuni ranta ya yi fari sumul ta gyada kai.
"In sha Allah Addata. Ina godiya sosai. Sai dai Adda ba ki
ban labarin da ki ka ce."
Ramlat ta murmusa.
"Kar ki damu, ai ana tare."
"Da'iman kuwa da yardar Allah." Fadin Hafsat, suka dara
kafin Ramlat ta fice ita kuwa bandaki ta shiga ta wanke
fuskarta. Ramlat na sallama da Dada sai ga Hafsat din,
sosai ta yi mamakin walwalarta, ta karasa ta fda jikin
Dadar tana neman gafararta cike da shagwaɓa. Murmushi
Dada kawai ta yi gami da jinjinawa Ramlatun. Ta tabbatar
aikinta ne.
***
A ɓangarenta kuwa, ganin fitilu a kashe ya ba ta mamaki
matuƙa, ita dai ta san ba ta kashe ba. Haka ta ci gaba da
tafiya a hankali har ta kai ga makunnin, kafin ta kunna ya
riga ta. Ta juyo ta dubeshi, kafin ta kai duba ga cikin falon.
Baki da hanci kawai ta saki tana dubansa ta kuma maida
duba ga abinda idanunta ke gani.
KARFEN KAFA Chapter 76
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323


By Rufaida Umar


Wani ƙaton enlargement ne na ɗaya cikin hotunanta da ya
ke da su, ta karkace kai tana murmushi har fararen
haƙoranta sun fito, sai wani ƙaton kwali da ba za ta iya
cewa ga abinda ke ciki ba sai kuwa akwatuna jere reras
har guda sha biyu. Ta kai dubansa gareshi, murmushi ya
ke sakarmata sosai. A hankali ya matso ya kama
hannunta suka karasa cikin falon. Wani ƙaramin kati mai
adon heart da fulawoyi ne ya soma daukar hankalinta don
haka ta sa hannu ta ɗauka ta bude.
_*From the moment I first laid eyes on you, I knew you
were a perfect match for me. I love everything about you
Heart. *_
Ta juyo ta dubeshi, yana tsaye kawai hannuwansa cikin
aljihun wando yana zubamata murmushi. Da ido ya mata
nuni akan ta ci gaba da buɗewa. Ba musu ta kai durkusa
ta kai hannu ta bude wani karamin gida na zobe, ai kuwa
zoben ne mai matukar sheƙi, ya fi mata kama da na
azurfa. Ya yi masifar burgeta, idanunta ya ƙara kaiwa
saman wani kwalin karami da aka ɗaure bakinsa da igiya
mai ƙyalli, ta bude, ganin mukullin mota kawai sai ta ɗago
ta dubeshi, idanunta nan da nan suka cicciko da kwalla.
Ta ajiye kafin ya taimaka mata da bude akwatinan, kaya
ne maƙil, kowanne da set dinsa. Yanda dai ku ka san lefe
irin na budurwar yarinya don wannan ma ya fi na budurwar
kyau da tsari. Ko iyaka haka aka tsaya a na budurwa sai
sam barka. Laces, atamfofi, mayafai, shadda, yadika,
abayoyi da dukkan sauran kayayyakin shafa da sarƙoƙi ba
abinda ba'a haɗa ba. Wannan ya bata tabbacin ba yau ya
soma haɗawar ba. Bayan sun mayar da komai ta dubeshi,
tuni hawayen da ta ke dannewa sun zubo. Ya kai hannu da
sauri ya ɗaukemata su. Ba ta bar kallonsa ba ta soma
magana.
"Allah Ya saka da dumbin alheri, na.."
Ya kai yatsa saman lebbanta.
"Shii...Ba kalar godiyarnan nake so, buƙatar fin haka nake.
Kar ki manta kuma haƙƙi ne na maki sutura da ma duk
abinda bai fi ƙarfina ba wanda zai farantamaki. Kin
cancanci fiye da haka."
Ya ƙarashe gami da ɗagamata gira. Kunyar ta nema ta
rasa, kawai sai ta juyo gaba ɗaya ta rungumeshi har
bayansa na jingina da kujerar. Ya kuwa ba ta kyakkyawan
mazauni a kirjinsa, kafin kuma kiɗa ya sauya salo.
***
KANO..
Wutar da ta tashi a wani gida dake unguwar ya sa mutane
duk suka fito, cikin dare ne da misalin karfe biyu da
mintoci. Banda salati da kokarin kashewa ba abinda ake
yi. Da yawa suna aikin kashe ta amma fadi suke don kawa
kar wutar ta haɗa da nsu gidajen ne amma banda haka
dama sun gaji da Maigidan, bokancin da ya ke yi musu a
unguwa yana tare matasa abin ya ɓaci.
Gora kuwa yana daga ciki banda ihu da neman agaji ba
abinda ya ke yi, ya rasa ta inda aka yi wuta ta soma cin
gidansa, babban abinda ya ƙara haukata shi neman jakar
kudadensa da ya yi ya rasa, ga yaronsa ba ya nan. Wannan
ya ɗan ankarar da shi cewa cin amanarsa ya yi. Nan fa ya
haukace, tun akwai hanyar ficewa har ya zamana ya rasa
ta inda zai bi ya tserar da rayuwarsa daga halaka. Haka
dai kafin mutane su yi nasarar tsayar da wutarnan, Gora
rai ya yi hali.
A ɓangaren yaronsa kuwa har da shi cikin masu kokarin
kashe wuta kamar gaske, har ya tafi sai ya yi tunanin
gwara ya tsaya ya tabbatar da mutuwar Gora kafin ya
gudu, idan kuwa har aka yi rashin sa'a ya tsira, to ya
tabbatar duk inda ya shiga a duniya ba zai tsira daga
ta'addancin Gora ba. Ganin an fito da Gora a mace ya
sanya ya ji wani sanyi a ruhinsa, ajiyar zuciya ya sauke
kafin ya hau mashin dinsa ya wuce can filin makaranta
inda abokinsa Jabir da suke kira da Jabson ke jiransa su
wuce. Yana zuwa suka cafke su na dariya. Nan ya ba shi
labarin komai, ya dubeshi da kyau.
"Jakar fa?"
Jabson ya yi wani malalacin murmushi gami da mishi nuni
da aji. Ya bubbuga kafadarsa suka dara kafin ya shige
gaba zuwa ajin, sai dai shigar ya yi daidai da sokamishi
wuƙa a baya ta ɓullo ta ciki, Jabson ne. Sai da ya tabbatar
ya kashe shi har lahira sannan ya ɗauki jakar ya
tsallakeshi. Mashin dinsa ya haye ya bar wurin a miliyan.
Shi da garin Kano kuma sai nan da wasu shekaru.
Misalin ƙarfe sha biyu na rana, labarin ƙonewar Gora da
tsintar gawar yaronsa ɗan aikensa Salmanu, ya karaɗe
unguwar. Ko'ina maganarsu ake yi, ga Jabir abokin
Salmanun da aka nema sama ko ƙasa aka rasa. Dama
almajirai ne, wannan yasa aka shiga tunanin ko sace Jabir
din aka yi bayan kashe Salmanu. Daidai sadda ake
wannan hargitsin, motar Hajiya Zeenatu ta tsaya. Tun
kafin su fito cikinsu ya ɗuri ruwa ganin yanda gidan Gora
ya zama kango lokaci guda.
"Ke Zeenatu, anya gidan ne?"
Hajiya Zeenatu ta kasa amsawa Hajiya Batool, kokari ta yi
kawai ta yi parking suka fito, yaran almajirai na ciki su na
ta ɗage-ɗage ko za su yi tsintuwa. Daga ƙasan bishiya
wasu samari suka hangosu. Ɗayan ya ce.
"Waɗannan su ne na goma sha takwas kenan, wannan
mutumin fa yana wankar mata, yanzu haka ma wani
mugun aikin su ka zo ya musu."
Wani ya mike.
"Bari mu je mu ji, idan ma shi suka zo nema mu ba su
labari ko Allah zai sa su tsorata da lamarin rayuwa su
shiryu."
Ganin haka sauran ma suka mara mishi baya don ba za'a
yi babu su ba.
"Hajiya wurin Gora ku ka zo?"
Hajiya Batool da Zeenatu wadanda sun rasa ta ina za su
soma, su ka dubi saurayin kusa a tare suka amsa da eh.
"Ayya, ai a daren jiya gobara ta cinye gidansa tas babu
abinda ya tsira. Shima ya mutu ɗazunnan aka dawo daga
binne abinda aka tsinta na gangar jikinsa. Shima dai
yaronsa Salmanu an tsinci gawarsa a filin makarantar
Firamare an kashe shi."
Hajiya Zeenatu sai da numfashinta ya bar motsi na wani
lokaci kadan, ta kasa magana sai kawai ta ɗora hannu a
kai ta fashe da kuka. Jiki na rawa Hajiya Batool ta ce.
"Shikenan Gora ya mutu dai ku ke nufi?"
Suka bisu da kallo kamar taɓaɓɓu, kusan ma duk kalar
ruɗewar da sauran matan da suka zo suka yi, bai kai na
wadannan Hajiyoyin ba. Mai magana ɗazu ya matso.
"Eh ya mutu. Duk wani mugun aiki da ya ke shukawa ya
kare. Ya koma gidan gaskiya inda zai girbi abinda ya shuka
din. Kuma ya kamata ku ji tsoron Allah ku tuba daga
tafarkin shaidan tun kan lokacinku ya ƙure. Idan har ba so
ku ke yi kuma ku zama tarihi ba, ku tafi a wofi."
Hajiya Batool ba ta ce uffan ba balle Hajiya Zeenatu da ke
faman kuka, ashariya kawai ta ke narkawa Gora kamar ta
mance da cewar ya mutu. Har dai dakyar Hajiya Batool ta
maidata mazaunin kusa da direba ita kuma ta tuƙa motar
suka bar layin, yara duk an cika ana binsu da kallo.
Haka suk isa gidan Hajiya Batool hankali a matukar
tashe. Ita kanta Batool din dakiya kawai ta fi Zeenatu,
amma ba ta ga laifinta ba don kuwa ta fi ta zazzage bakin
aljihu a wannan harkar. Nutsuwa ta gagaresu, Hajiya
Zeenatu kawai zama ta yi kamar kayan wanki a saman
kujera tana ci gaba da surfa ruwan bala'i ga Gora da ya
jima a gushewa.
"Yanzu shikenan Hussein da Ramlatu haka zan zuba ido
ku cigaba da cin amanata?! Shikenan wai hakan na nufin
sun yi nasara?! Wallahi ko zan yi yawo tsirara sai na ga
bayan Ramlatu da Uwarsa! Sai Hussein ya dawo karkashin
ikona. Ba zan dauki wannan dumbin asarar ba! Batool
nemomana Maryama a waya! Zuwa Nijar ya kama mu, ya
zama dole mu kara gwada aikin Bokansu. Buzaye ne!Za
mu yi nasara, za mu yi nasara."
Ta na maganar kamar wacce ta samu taɓin kwakwalwa.
Itama Batool ta gane zuwannasu Nijar din kawai shi zai
zame musu mafita don haka ba musu ta zaro waya ta
dannawa Maryama kira lokaci guda kuma tana sharce
gumi. Magana sosai suka yi, ba ta ɓoyemata duka
asarorin da ya hau kansu ba. Maryama ta jajanta musu
sosai karshe ta ce musu za ta yi musu booking na layin
ganin Boka Buzu, kawai dai da zarar sun saka ranar zuwa
su fadamata.
"Gobe ma zamu taso jibi mu iso."
Hajiya Batool ta katse ta da gaggawa, ƴar dariya Maryama
ta yi kafin ta amsa da toh hadi da musu fatan zuwa lafiya.
Washegari kuwa da sassafe suka kama hanyar Nijar,
direba ne ya kaisu. Yardaddan direban Hajiya Batool,
Audu. Wannan karon ma sun tattara maƙudan kudade don
ita Hajiya Zeenatu ba ta bi ta kan Manajanta ba, ta nemi
manyan gwala-gwalanta har biyar ta shiha kasuwa ta siyar.
Itama dai Hajiya Batool sai da ta haɗa da siyar da kadara,
kowaccensu ta taho cike da burin samun abinda aka je
nema. Idanunsu ya rufe, gani suke yi tamkar ga su ga
burinsu har ya cika tsabar imanin da suka yi da abinda zai
kai su.
Wuraren karfe sha biyun rana da mintoci suka iso
Damagaran, anan suka kwana washegari da sassafe suka
kama hanyar Niamey. Sun sha tafiya sosai kafin su isa
Niamey, kai tsaye suka kira Maryama a waya. Da
kwatance da tambaya suka iso katafaren gidanta wanda
ya sha kayan alatu. Ta musu kyakkyawar tarba, ba kamar
wancan lokacin ba, wannan karon gidanta ne na kanta ba
na Maigidanta ba. Tun bayan rasuwar Mijinta ta siya gida
inda ta ke harkar safarar yara zuwa Ƙasar faransa da ma
wasu ƙasashen yawon bariki. A yanzun da su ke zaune a
falon suna cin abinci bayan sun yi wanka, ba tare da
kowaccensu ta damu da kallon gabas ba, ƴan mata ne ke
safa da marwa cikin shiga mai ƙayatar da masu iri
halinsu na bin maza. Babu wacce ba ta fito ta gaida baƙin
Madame dinsu ba, a karshe Hajiya Zeenatu ta kora ruwan
sanyin da aka ajiyemusu ta dubi Maryama.
"Kin tabbatar dai goben babu fashi a zuwanmu wurinsa
ko?"
Wani murmushi Maryama ta yi ta dauki tuffa ta gutsira.
"Haba Hajjaju, zan maki ƙarya ne?"
Ganin haka Hajiya Zeenatu ta saki fuska.
"Ba haka nake nufi ba, kin dai ji komai ai daga bakin
Batool, banda haka nan da kike ganina duk sadda zan
runtse idanu ba abinda nake haskowa sai Mijina tare da
waccan karamar karuwar. Gani nake duk kwana daya
tamkar shekara ce."
"Ki sa ranki a inuwa, za ki sha mamakin yanda komai zai
lalace. Mijinki ya dawo kamar kwai a hannunki sai yanda
ki ka yi da shi."
Dariya suka yi har da cafkewa, nan da nan zuciyoyinsu
suka ɗan waske sai dai ko ya ya suka tuna asarar da ta
hau kansu na miliyoyi sai sun tsinewa Gora. Basu ma
batun nemar masa gafara.
Kamar yanda Hajja Maryama ta fadi, hakan ce ta kasance.
Washegari bisa jagorancin yaronta sai dai ba wancan na
farkon da ya taɓa yi musu rakiya ba, suka rankaya gidan
Bokansu Buzu. Koda suka tsaya babu layi sosai, kamar
wani layin asibiti haka aka basu kati karami mai dauke da
numero (number). Wannan dai ba ɗayan bane, wani sabon
Boka ne gagarumi da Maryama ta tabbatar musu cewa
aikinsa wane wancan! Daga yanda ma ake yi a wurin ba
ka ganin kalar talauci a wurin ka san harka ce ta manya
don kowacce ta sha shadda mai dandasheshan kyau sai
kuwa daidaiku masu leshi. Su da suka yi shigar atamfa ma
sai suka raina tasu kwalliyar. Ba don komai ba sai don ba
su zo da tsadaddun ba na gani a faɗa. Hankalinsu na kan
aikinsu.
Sai da layi ya iso kansu suka yi zumbur suka miƙe, ganin
su na kokarin shiga tare mai tsaron wurin ya dakatar da
su. Cikin Hausarsa da ba ta fita sosai ya dakatar da su.
"Ba'a shiga mutum biyu komai kusanci."
Jin haka suka dubi juna jin abin banbarakwai wai namiji da
suna Hajara. Ba su taɓa zuwa an musu iyaka da shiga
wurin Boka tare ba, karshe dai ganin mutumin na
harararsu ya sa Hajiya Batool ta ja baya.
"Soma shiga bari na yi jira."
Hajiya Zeenatu ta shige ita kuma ta koma ta zauna.
Kwarjini iyakar kwarjini mai bada tsoro shi ta gani a fuskar
wanda aka kira da Gamsheƙa, fuskarsa babu ɗigon
walwalwa. Tana zama babu tambaya ya nemi sanin
sunanta kawai kafin ya soma motsa wasu irin ƙaho da
duwatsu da ke cikin wani ƙaton abu kamar tire kamar
kuma ba shi ba. Sai da ya gama ya dubeta ya shiga kora
jawabi.
"Mijinki da kika yiwa asiri mai suna Husseini, ya dawo
hayyacinsa ya sake ki, ya kuma auri wacce a duniya kika
tsana, kuma burinki bai wuce na ganin kin hallakata ba.
Sai dai kuma ki sani, tuni kin makara don soyayyarsu babu
karfin shaiɗancin da zai iya hallakata. Amma ina mai
tabbatarmaki juya tunaninsa abu ne mai sauki idan kin
aikata duk abinda za mu sanya ki babu musu."
Hajiya Zeenatu wacce idanunta ya rufe nan da nan ta hau
gyada kai tamkar ƙadangaruwa.
"Wallahi a shirye nake, ko menene zan aikata idan har
burina zai samu cika."
Ya jinjina kai da yin murmushi mai kama da na mai jin
kashi.
"Shikenan, a yanzu za sadu da ke ta gaba da kuma baya,
daga karshe zan ɗebi abinda ya fita daga jikinki na najasa
na haɗamaki wani ƙullin magani wanda za ki tabbatar kin
yi yanda ki ka yi, kin fesa a fuskarsa. Sai kuma wani tulu
da zan ba ki wanda ke dauke da zucciyar mutum soke da
allurai, shi ne mafi hatsari cikin ayyukan da zan maki. Kar
ki kusa ki bari ya fashe, muddin ya fashe ki sani komai zai
iya faruwa da ke, wannan hukuncin ya rage ga aljanun da
suka satomin zucciyar. Don haka kin yarda kin amince za
ki iya?"
Hajiya Zeenatu wacce tun sadda ya yi batun saduwa ta
baya ta yi turus, kirjinta ya shiga dukan tara-tara, abu ne
da ba ta taɓa aikatawa ba, bar ta dai da aikata zina shima
a baya ne kafin shigowar jarumi kuma namijin duniya
Hussein rayuwarta. Daga shi babu waki namiji da ta ƙara
yiwa kallon abin marmari.
'Ki tuna fa, wannan namijin kike kwaɗayin maidoshi
rayuwarki yanzu Zeenat, kada ki yi sake. Wannan ce kadai
mafita.'
Wani ɓangare na zuciyarta ta mata tuni, nan da nan ta
dubi Gamsheƙa da har ya soma gundira da shirunta.
"Na amince. Zan kiyaye dukkan sharuɗa."
Ya miƙe tsaye ya ba ta umarnin ta biyoshi. Daga haka ya
nufi uwar ɗaga bayan sakin labulen window, hakan ya sa
Maitsaron ya fahimci shugabannasa ya shiga aiki. Wannan
yasa bai yi gigin lekawa ba.
Sun kwashe kusan fiye da awa ana abu ɗaya don
Gamsheƙa dai ya samu ya da yake so, a karshe ya fito ya
bar Hajiya Zeenatu da ɗibar abinda ya umarceta a kwalba
sannan ta mike ta fada bandaki ta dauraye jiki ta fito.
Koda ta dawo ta iskeshi har sannan ba walwala kamar ba
shi ne ya gama kukan mage ba.
Gani ta yi ya haɗamata komai ya miƙamata sannan aka yi
bayanin kudade ta biyashi da kudin Ƙasar don tun a
Damagaran suka yi chanji.
Koda ta fito mai tsaron ya ba Hajiya Batool damar shiga,
ita kuma ya ce ta fice don baa kara zama idan an fito,
hakan laifi ne babba. A gaggauce ta fita, yaron Maryama
zai karbi tulun hannunta dake cikin kwali ta yi saurin
dakatar da shi ta ce ya bar shi. Don ji ta ke idan har ba ita
ce ta riƙe ba to fa komai zai iya faruwa. Duk fargaba ta
cika zuciyarta.
Tana nan zaune a motar har kusan shudewar awa guda
kafin Hajiya Batool ta karaso, ita har da hawayenta ma
don ita kadai ta san me ta ke ji a bayanta tun abinda ya
gudana tsakaninta da Gamsheƙa. Hajiya Zeenatu ta kalleta
kawai don ta san duk kanwar ja ce. Ita ba tulu sai wani
kwalba a cikin kwali, ba su ba junansu labari ba
sakamakon ba su daya ne a motar ba, haka suka kama
hanyar gidan Maryama kowannensu da abinda ya ke
saƙawa. Kamar yanda kowanne ke tunanin bala'in da zai
sameshi idan har suka yi gangancin ɓata aikinsu.
***
ADAMAWA
Kwanakin da suka biyo baya, banda soyayya ba abinda
Hussein da Ramlat ke gurza, gaba dayansu sun sauya sun
kara wani fresh da kyau. Hafsat ba ta bar aron wayar
Ramlat a faƙaice ba tana gaisawa da Tahir. Ita dai Ramlat
a tsorace take da hakan sai dai ganin Hussein bai taɓa
kamata da laifin ba yasa ta ɗan ji nutsuwa kaɗan.
Ranar da ta cika sati ɗaya cif a garin Adamawa, tana
zaune a falonta, dawowarta kenan daga sashin Dada.
Hussein ya shigo fuskarsa kaɗai ka kalla za ka san yana
cike da tsantsar farin

34 / 38