KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt

Author :  Rufaida Umar Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   22 / 38

63K to 66K   out of 113.5K words

Ciki-ciki ya yi musu sallama sai dai
ba wanda ya yi yunkurin amsawa, wannan ya fi komai
ƙular da shi. Wato don ubansu har sannan ba su ɗauke su
wata tsiya ba. Ya yi kwafa ya karasa ciki. Ba laifi ya samu
tarba daga Amarya sosai, ganin haka ya ƙi shiga ɓangaren
Hajja Fatuma ya shantake har dai ta sanarmishi da
shigowar Kawun daga kasuwa. Tsam ya miƙe ya nufi
sashinsa. Yana zaune saman kujera ya shiga da sallama.
Dubansa ya yi yana mai amsawa sai dai ganin ko waye ya
karasa amsawar ciki-ciki. Hussein ya taɓe baki don dama
ya shirya ganin fiye da hakan.
"Barka da yamma." Ya gaida shi a ladabce.
"Kai, me ya kawo ka gidana?"
Kallonsa ya yi kyam.
"Zumunci."
Kawu ya ji wutar tsanar Hussein ta ƙara ruruwa a ƙoƙon
ransa, shekaru kusan bakwai rabon da ya tako gidansa,
Alhassan kan shigo koda ba ya so.
"Na lura ba ka da kunya! To ko Aminu ubanka bai isa ba
balle kai! Ni na fi ƙarfin tsagerancinku! Illar auren bare
kenan...
"Ubana Aminu ya rasu, gidan da ya je ba wani da zai
dawwama a duniya bai je ba. Gidan biyu ne, wuta da
aljan. Don Allah Kawu ka yimin dukkan zagi, banda
ambatar iyayena."
Miƙewa Kawu ya yi ma matukar fusata. Jikinsa har rawa
ya ke yana kumfar baki.
"Ni ka ke faɗawa baƙar magana?! Ni? Na maka kama da
sa'an Uwarka?!"
Hussein caraf ya mike a fusace, bai san sadda ya soma
ɗaga murya a magana ba.
"Kawu! Tsanar ta isa haka! Haba! Wadannan mutanen da
ka ke zagi babu ranar da ba sa yi mana nasiha akan mu bi
ku mu yi biyayya! Mene laifinsu ma zuwa a bare?! Waye
bare? Ina ku ka samo wannan al'adar marar tushe?!
Wallahi wallahi! Ina girmamaka ne domin Dada, darajar su
ka ke ci nake ragamaka a dukkan wulakanci da cin kashin
da ka ke yi! Amma... (Ya nuna shi da yatsa) Daga yau na
zubar da girman a idona na take shi! (Ya yi amfani da
ƙafarsa wurin murje ƙafet ɗin ɗakin) Daga kai har zuri'arka
duk wanda ya ƙara gangancin cin zarafin iyayenmu sai na
nunamaku cikakken ɗan halak ne Hussein! Mu zuba da
ku!"
Yana kaiwa nan ya juya yayinda kalaman Kawu ke shiga
kunnuwansa.
"Ni ka ke gayawa magana haka? Lallai zan nunamaka
ƙarshenka!!"
Wannan kalaman tsaf sun shiga kunnensa sai dai ko
kaɗan bai ji ko ɗar ba, bai tsaya sallama da kowa ba ya
kama hanyar fita. A zaure suka hadu da daya cikin
samarin gidan ɗa ga Hajja Fatuma, Bashir. Fiito ya soma
yi yana waƙe wanda hakan ya ƙular da Hussein ya kuwa
haɗa kansa da bango ya bishi da lafiyayyen mari.
"Ubanka ma ya yi kaɗan balle kai!"
Daga haka ya fice ya bar shi da ihu da kururuwa.
Ranar dai gidan abokin Baba Naziru ya kwana washegari
da sassafe ya juya gida Adamawa. Kwanansu uku, ya yi
mamakin yanda Kawu bai kira Dada ya sanarmata ba,
shima ya haɗiye bai faɗa ba. Har hutunsa ya ƙare bai ji
wani bayani ba don haka da dariyar mugunta ya bar ƙasar.
Ya dai gane a baya ma Kawunnasu wuri ya samu!
***
Daga AlHassan har Hussein, kowanne ya na iyakar kokari
wajen yin karatu yanda ya dace. Basu da wani buri face su
fito first class ko don su farantawa uwa da uban da suka
rikesu tamkar su suka haifesu rai.
Hussein saurayi ne mai daure fuska da tsauri a wasu
lokutan, zai yi wuya ka ga dariyar Hussein. Ya killace
kansa ya kasa yin abokai sai abokinsa daya haifaffen garin
Saudiyya kuma mazaunin can, Rasheed. Sun shaƙu sosai
da Rasheed wanda ya kasance ruwa biyu. Mahaifiyarsa
irin Takarunnan ne dake zuwa daga ƙasashe daban-daban,
sai dai ita din ƴar Katsina ce a Nijeriya. Mahaifinsa kuwa
haifaffen garin Makkah ne a Saudiyya. Zama ne ya haɗasu
har aka kai ga yin aure, Allah Yasa Rasheed ta hanyar aure
suka haifeshi.
Wasu ƴanmata basu a gaban Hussein, akwai da yawa da
suka yi suka gaji bai ko kallesu ba. Don ya wulakanta duk
macen da ta tunkareshi ba kunya ta nuna tana sonsa, ba
komai ne a wurinsa ba lokacin. Hakan yasa wasu da yawa
suke komawa tsanarsa shi kuwa ya dau hakan wai harara
a duhu don bai ɗaukesu da wata ƙima ba.
Ɓangaren karatu, kusan yana daga cikin ƙwarin ajinsu
wadanda za'a iya kira da gifted. Allah Ya ba shi fasaha da
saurin daukar karatu hakanan Rasheed.
Da taimakon Allah lokacin yayesu daga makaranta ya yi.
Murna a wurinsu ba'a magana idan ka cire Rasheed da
Hussein wadanda basu kaunar rabuwarsu. Sun tabbata sai
ziyara ce za ta ƙara haɗa fuskokinsu, kafin ma a ziyarci
junan zai iya daukar lokaci.
***
Hajiya Zeenatu Bashir wacce ta kasance marainiya, ta
tashi a hannun kakarta mai son abin duniya. Sanadin
hakan ne ta hadata da wata Agent mai safarar yara zuwa
Saudiyya aikatau da Bara. Ta yi wannan aikin na shekaru
goma kafin a karshe kanta ya waye ta samu ta tara kudi
sosai ta dawo gida Nijeriya. Haifaffiyar garin Katsina ce,
sai dai kasuwancinta da kuma rasuwar Kakarta a
shekarun baya, ya maidota Kano da zama. Ta zama mace
mai zaman kanta, sun haɗu da Ƙawarta Hajiya Batool
wacce itama ta ke kasuwanci, a jirgi sadda za ta dawo
daga Saudiyya. Nan suka ƙulla aminta sosai, don haka
koda ta dawo Kano sai suka hada jari suka ci gaba da
harkallar kasuwanci. Tana da zaurawa da dama waɗanda
ta k rage dare da su,wannan a wajenta bakomai ba ne, a
irin wannan harkar ne ta san da zaman Aliyu Dikko wanda
a baya sun zuba lokacinsu tare duk kuwa da tazarar
shekaru biyu da ta ba shi.
Haduwarta da wani ƙusa a gwamnati yasa jarinta daɗa
faɗaɗuwa, ta soma fita sarin kaya Dubai tana kawowa
katon shagon da ta buɗe a nan Sabon gari, kuma takan
taɓa siyasa musamman wurin kamfen.
A wani zuwan karshe da ta yi ne a wani shagon kayan
kwalam ta haɗu da wata ƙawarta da suka hadu a aikin
Hajji, Hajiya Basira ƴar asalin garin Katsina da aure ya kai
ta Saudiyya.
Da mamaki ta kira sunanta, Hajiya Basira na ganinta suka
cafke suna dariya. Kowannensu bakinsa cike da hira,
karshe dai tare suka fito zuwa masaukin Hajiya Basirar.
Anan ne ta ke jin cewa ɗanta Rasheed ne ya kammala
karatu ta zo bikin yayeshi.
"Ke dai Hajiya Zeenatu kin ƙi yin aure kin zauna kina cin
karenki ba babbaka, nima fa nayi irin rayuwarnan a baya
kafin Allah Ya tseratar da ni, kin fi kowa sanin yanda
rayuwa irin haka ke ƙarewa."
Wani fari da murmushi Hajiya Zeenatu ta yi.
"Me kike ci na baka zuba ne? Tunda na tara abinda na
tara dagaske yanzun nima aure zan yi. Kwantar da
hankalinki."
Suka yi dariya gami da cafkewa.
"Yauwa, yanzu naji batu."
Da wannan suka shiga hirarsu kafin a karshe Hajiya
Zeenatu ta yi mata sallama da alƙawarin goben za ta zo
su je taron yaye ɗanta a makaranta.
***
Washegari kuwa ta cika alƙawari, a gidan Rasheed da
Hussein suka kwana sai dai da sassafe suka koma cikin
makaranta.
Hajiya Zeenatu suka ɗunguma zuwa makarantar. Wuri ya
cika ya batse, dalibai sun sha kyau sun gaji. Baba Naziru
ne kaɗai ya zo wa Hussein, hakan ma ya mishi dadi sosai.
"Yauwa ga ɗannaki." Muryar Hajiya Basira ya katse Hajiya
Zeenatu daga kan wayarta, tunda ta ɗora idanu akan wani
matashi da bai fi shekaru ashirin da biyar ba, mai cikar
kamala da zati ta ji kamar an shanyemata jinin jikinta. So
da kauna da sha'awa wanda ya fi komai rinjaye, ya tafi
kacokan kan HUSSEIN. Tafe suke tare da Rasheed yana
murmushinnan mai kashe zuƙatan ƴan mata.
Har suka ƙaraso suka ɗan russuna suka gaishesu, Hajiya
Zeenatu ba ta iya amsawa ba. Kallo ɗaya Hussein ya yi
mata bai ƙara ba tuni kuma ya ɗan daure fuska, kallo ne
irin wanda ya san ƴanmata da ke bibiyarsa na yi gareshi,
wannan ma kusan ya fi nasu muni a wajensa don kallo ne
har da na haram.
"Ana gaisheki." Sai a nan ne Zeenatu ta dawo hayyacinta
ta amsa gami da taya musu murna. Hussein dai rarraba
idanu ya ke, can ya hango Babansa, da sassarfa ya karasa
ya rungumeshi. Shima Baba Naziru shi yake nema, suna
murmushi suka saki juna ya mishi fatan alheri.
Har suka bar wurin Hajiya Zeenatu tunanin Hussein ta ke
yi, so da kaunarsa take ji na ratsata. Ba ta yi ƙasa a
gwuiwa ba ta nemi lambarsa wurin Rasheed. Ta kuma
nuna ta na son ganinsa. Rasheed bai kawo komai ba ya
gayyaci Hussein gidansu, haka ya bar Baba Naziru a Hotel
ya zo.
Suka kebe da Hajiya Zeenatu
"Lafiya Mama?" Abinda ya soma cewa kenan da ya soki
Hajiya Zeenatu a ƙahon zuci. Murmushi ta yi da yin fari
cikin jan sa.
"Lafiya dai dan samari, oh, Hussein na Hassan."
Ya ɗan daure fuska.
"Sauri nake yi."
Ta gyara zama.
"Ka yi hakuri na sa an kiraka na kashemaka dukkan uzuri
ko? Ba komai bane Hussein, wallahi sonka nake tun ganin
da .."
Dariya da ya shiga yi ne ya dakatar da ita kafin ya gimtse.
Kallon raini ya watsamata ya mike tsaye
"Dube ki don Allah! A haihuwar kauye wallahi kin haifen
amma hakan bai sa kin ji kunyar ki kalleni ki ce wai kina
sona ba! Ƴanmata ma basu isheni kallo ba ballantana
kuma ke ƙatuwar da an girma ba'a san an girma ba. Don
Allah ki kama girmanki , zai fi miki akan wannan budurwar
zuciyar."
Daga nan kama hanya zai fita. Muryarta ya tsaida shi.
"Za ka yi dana sanin wadannan kalaman da ka furta gareni
Hussein."
Ya juyo yana murmushi ya dubeta don dagaske abin dariya
ya bashi musamman na ganin hasashensa ya zama
gaskiya, girgiza kai ya yi.
"Naji daga bakin ƴanmata bila adadin. Ki yi duk abinda
kika yi niyya, ni din dai har abada na fi karfinki."
Daga haka ya banko labule ya fice ya bar Hajiya Zeenatu
na cika da batsewa.
"Alwashi na ci! Wallahi wallahi Hussein sai na aureka, sai
na juyaka kamar waina a tanda."
Ta furta a fili.
Bata rabu da Rasheed ba sai da ta yi mishi dabarar da ta
karbi har address din Hussein na Adamawa kamar yanda
ya fadamasa.
Da wannan ta koma Kano cike da shaukin Hussein da
bege.
***
Ƴan biyun Dada suka dawo Adamawa da sakamako mai
kyau, kowa a dangi murna yake. A sannan aka yi bikin ƴan
matan Dada su uku, aka bar ta daga ita sai Auta Hafsat
wacce a sannan take ajin farko a Sakandire.
Da shekara daya suka kammala bautar ƙasa aka shiga
neman aiki, a sannan ne alaƙa ta soyayya ta ƙullu tsakani
Alhassan da Kausar. Shi kuwa Hussein ya rantse ba zai
auri kowa a dangi ba don auren dangi ba ya burgeshi
musamman kasancewar a sanadinsa aka tsani iyayensa.
"Duk da haka ka fito da matar aure. Ba zamu zubamaka
idanu ba." Abinda kakansu kuma mahaifin Baba Naziru ya
ce kenan. Taɓe baki Hussein ya yi.
"Ga matarka nan Hajiya Zahida mai naira, nikam ta isheni."
Aka sa dariya. Hajiya Zahida ta gyada kai.
"Eh na isheka, amma ina bukatar abokiyar zama."
Miƙewa ya yi.
"Bari naje, ina da aiki dagaske." Ya fadi da harshen
fulatanci.
***
MAFARIN KOMAI...
Yammacin Laraba ce a garin Adamawa, fitowarsa kenan
daga katafaren shagon Ikhlas, hannunsa rike da leda ya
siyo Ice-cream.
Tana tsaye jikin motarta, tun fitowarsa daga gida ta ke
biye da shi, koda shigarsa shagon, ta ja kwallin da Gora ya
bata, da tabbacin duk inda ta yi ido hudu da Hussein,
komai zai kasance yanda ta so.
Da wannan ta yanke tunaninta ta ƙarasa inda yake.
"Hussein." Fuska a daure ya ɗago ya dubi mai maganar,
ido cikin ido suka kalli juna. Wannan ɓacin ran da ya
tasomasa da wannan daure fuskar, sai ya nemesu ya rasa,
wata soyayya ce ke shigarsa da kauna. Kansa ya yi wani
nauyi, ga mamakinsa, murmushi ya shiga yi mata.
"Nasan ba ka gane ni ba, Hajiya Zeenatu ce da ku ka haɗu
a Dubai."
Maimakon baƙar magana sai ya yi ƴar dariya da lumshe
ido.
"Na ganeki mana, Zeenatu ai kyanki kadai ma ba zai sa na
manceki ba."
Wani dadi da farin ciki ya kusan zautar da Hajiya Zeenatu.
Gora da Hajiya Batool ta shiga sanyawa albarka. Sanadin
Hajiya Batool ta san Gora, yau gashinan ya ba ta abinda
bata taba tsammanin zuwansa da sauƙi ba.
***
Tun daga wannan ranar magana da tunanin Hussein ya
koma kan Hajiya Zeenatu, kamar yanda ta kwaɓeshi da
faɗar alaƙarsu a gida, haka ya bi. Idan bai ji muryarta ba
har hawaye yake fitarwa ya bazama hotel din da ta sauka.
Hussein ya sauya a gidan, Dada ta zaunar da shi ta mishi
tambayar duniya ya nunamata ba komai. Hakanan Hassan
ya kasa gane kan ɗan uwansa.
Haduwar Hajiya Zeenatu da Hussein na karshe ta fashe da
kuka ta nunamasa idan har yana sonta ya amince ya
biyota su wuce Kano a dauramusu aure don kuwa ta
tabbatar ba wanda zai amince da aurensu a danginsa
tunda ta girmeshi. Hussein ya ji maganar babbarakwai,
hankalinsa ya tashi. Yana so ya ce mata a'a amma abin
ya faskara, ganin bai ce komai ba ta ƙulla gaba da shi ta
ce ya rabu da ita har abada ba ta sonsa. Kowa ya kama
gabansa.
Ta fadi hakan ne don ta san ba mai yiwuwa bane, tuni ta
juyamasa ƙwaƙwalwa ta hanyar zubamishi siddbaru a
abinci da abin sha. Wani irin soyayyarta ke addabarsa da
wani irin tsoro.
Sai dai batun ya bar ƴan uwansa dominta ne ya ji kamar
ya mishi nauyi. Da wannan suka rabu ta koma Kano kamar
yanda Hajiya Batool ta bata shawara, sun riga sun san zai
biyo bayanta don aikin da aka yi mishi mai karfi ne. Layu
ne aka sanya a gaban gawar mace. Hakanan an kwaƙule
idanun jariri sabon haihuwa an haɗa da maganin.
***
Kwanaki uku ya biyo baya Hussein ya rame ba walwala.
Wannan ya tashi hankalin kowa. Aka haɗa meeting aka
zaunar da shi don jin bayani.
"Aure nake so a yimin. Na samu matar aure amma ta
girmeni don za ta yi shekaru arba'in. Wallahi ita nake so,
don Allah kar ku hanani aurenta."
Ran kowa ya ɓaci, nan Baba Naziru ya rantse ya kara ba
zai aureta ba. Kowa kuma ya goyawa hakan baya ba tare
da sanin abinda hakan zai haifar ba. Ga mamakin kowa
Hussein ya mike a fusace.
"Eh dama ai kun fi son Hassan! Shi da ya kawo wacce ya
ke so wane ne ya hanashi? Sai don zan auri bare? To ai
nima uwata bare ce a cikinku don haka ba wanda ya isa
hanani auren wacce nake so!"
Daga nan ya fice daga dakin ya bar kowa baki a sake.
Dada kuka ta sanya saboda kunyar da Hussein ya bata.
A karshe Baba Naziru ya fusata ya ce da kansa zai
zaɓamasa matar aure.
***
Washegari cikin dare Hussein ya shirya kayansa da
takardunsa masu muhimmanci, ya kalli Hassan dake
bacci na ƴan dakiku. Kirjinsa na faduwa hakan bai sa ya
sauya ƙudurinsa ba. Hannu ya kai ga wani hotonsu da
suka yi a tsaye da ƙananun kaya, asalin hoton a waya
suka yi amma saboda kyansa suka wankeshi suka sanya a
frame. Ya dauka ya cusa a jakarsa. Ji yake kamar muryar
Hajiya Zeenatu na amsa kuwwa a kunnensa. Gani yake
idan har ya kara kwana bai je inda take ba haukacewa zai
yi. Daga wannan tunanin ya sa ƙafa ya bar gidan. Maigadi
na can yana sharar bacci ya fice gaba daya.
Wannan tafiyar da Hussein ya yi, shi ne tafiyar da bai ƙara
takowa gidansu ba har wannan lokacin.
***
Koda ya isa Kano ya nemi Hajiya Zeenatu, ji ta yi kamar ta
zuba ruwa a ƙasa ta sha. Da kanta ta daukoshi daga tasha
zuwa gidanta.
"Nasan dama ba za ka iya rayuwa babu ni ba."
Da jajayen idanunsa ya dubeta ya bi ta da murmushin
yaƙe.
Ta mike zuwa dakinta ta faɗa bandaki, zirr ta yi ta wanke
jikinta da ruwan magani kafin ta dawo ta shirya ta
rambaɗa kwalli. Wani gari ta ɗebo a hannunta ta dawo
falon.
Yana kallonta har ta zauna, a hankali ta bude tafin hannun
ta huramasa a fuska. Tun yana ganinta daidai har ya yi
luuum ya soma lumshe ido.
Wani magana ta shiga yi mishi a dodon kunne yana
nanatawa.
"Ni kadai ce a wajenka, ni kadai ce a zuciyarka, ba ka da
dangin da ya wuce ni. Ba ka da kowa a duniya sai ni."
Ya nanata, tun yana yi har a hankali ya kwanta kamar mai
bacci. Wani mahaukacin dariya ta sanya.
***
Malami har gida ta kirawo ya daura aurenta da Hussein.
Rabon goro da aka yi a makwafta ne ya sa suka san ta yi
aure. Daga wannan lokacin Hussein ya zama mallakin
Hajiya Zeenatu ita kadai, jallin jal!
Ya samu aiki a wani babban kamfani ta hanyarta, tun yana
matsayin ma'aikacin har a karshe saboda jajircewa da
amanarsa da kuma sanin makamar aiki, ya zama Manajan
kamfanin.
Hajiya Zeenatu likkafa ta ci gaba, ta gina shaguna da
dama, auren Hussein sai ya zama kamar wani buɗi a
kasuwancinta. Ta dinga samun albarka a ciki kamar me.
Har ya kasance ta bude shagon siyar da gwala-gwalai a
sabon gari, tana kuma da na abayoyi, takalma da jaka a
sabon gari. Suka hadu ita da mijinta suka bude katafaren
shagon kayan maƙulashe mai suna A&Z Snacks and
more.
***
CI GABAN LABARI...
KARFEN KAFA Chapter 65
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323


By Rufaida Umar


ADAMAWA
Hafsat ce tsaye a farfajiyar gidan suna hira da Tahir,
murmushi sosai ne saman fuskarta, ko ba'a faɗa ba
duniyar ta mata daɗi. Tahir kuwa jin komai yake yi kamar
a mafarki, dama an ce mai hakuri kan dafa dutse har ya
sha romonsa, yanzun gashinan ya gani. A hankali
soyayyarsa ta kama zuciyar Hafsat.
"Dariya na ba ki?" Ya fadi yana murmushin shima. Hafsat
ba ta kai ga ba shi amsa ba, suka ji hon. Nan da nan ta
rude, ta san AlHassan ne don ya kira Dada ya sanarmata
cewar yana hanya, ba wanda zai zo gidan da darennan
idan ba shi b, hakan yasa ta dubeshi.
"Mu yi magana ta waya. Bari na shiga ciki."
Ba ta bari ya kai ga amsawa ba ta yi gaba da sauri. Tahir
ya shafi ƙeya yana murmushi. Daidai sadda motar
AlHassan ta faka, ya nufi wurin. Sai dai ya tsaya cak yana
kallon wanda ya soma fitowa daga mazaunin gefe. Kamar
AlHassan kamar ba shi ba, kafin ya kai ga tantancewa sai
ga AlHassan ya buɗe murfin ƙofar ya fito
Wani tsalle da Tahir ya yi ya rungume Hussein yana ihun
murna sai da ya ba AlHassan mamaki, sai kuma ya yi
dariya. Duk wanda ya zauna da Dada ko na minti talatin
ne, sai ya san yanda take kewar Hussein. Balle kuma Tahir
wanda dama shi a baya ya san Hussein din, duk da ba su
wani saba ba. Sanadin zamansa a garin kuma a gidan
yasa shi damuwa da damuwar Dadan har yakan taya ta
addu'a.
Suka dunguma ciki zuwa falon, Hussein jikinsa har rawa
yake, burinsa kawai ya sanya Dadarsu a ido.
Tana falon zaune, a gefenta Fatima ce ke cin Popcorn duk
ta ɓata hannunta da madara. Hafsat kuwa ɗaki ta shige
gudun kar AlHassan ya gan ta. Sallamarsa ta yi yanayi da
ta AlHassan, hakan yasa Fatima wurgi da ledar Popcorn a
guje ta nufeshi idanunsa akan Dada, ya durkusa ya ɗaga
ta cak kafin ya rungumeta. Dada tsam ta miƙe jiki na rawa
tana mai ƙuramasa idanu, a hankali idanunta suka ciko da
kwalla. Nan da nan ta shiga zubar da hawaye, ta kalli
AlHassan ta dubeshi, da sauri ya ajiye Fatima wacce ta yi
turus tana kallon wanda ya ɗaga ta alhalin ga babanta a
baya ya shigo. Da sassarfa ya isa ga Dada ya rungumeta
kawai sai hawaye masu ɗumi suka zubomishi.
"Dadata." Dada ta lumshe idanu ta bude, shakka babu ba
mafarki ta ke

22 / 38