Author : Rufaida Umar Category : Top Hausa Novels 2025
ma ya ba ta. Ya
yi ƴar dariya ya gyara zama sosai ya fuskanci talabijin ya
matso gareta sosai. Daga yanayin nutsuwarsa ta fahimci
ko me yake shirin cewa mai ma'ana ne.
KARFEN KAFA Chapter 73
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323
By Rufaida Umar
"A rayuwata, kar ki yi mamakin cewa ban taɓa soyayya ba.
Ban yi ba tun ma kafin zuwan Zeenat, balle a bayanta."
Ta dubeshi, dama idanunsa na kanta, sai ya yi murmushi
ya riƙo hannunta ya damƙe cikin nasa yana murzawa a
hankali kafin ya ɗora.
"Sadda Allah Ya soma haɗa ni da ke, mun haɗu ne lokacin
bana cikin nutsuwata sakamakon ɓacin ran wata
hatsaniya da muka yi da Zeenat, ban ji komai a kanki ba
sai sadda na ƙara cin karo da ke a ma'aikatar Revenue da
muka je tax payment. A hankali a hankali haɗuwarmu kan
zo akai - akai, tun bana daukarki da wani muhimmanci har
ban san yanda aka yi na soma kula da lamuranki ba. Na
soma jinki kamar wata ƴar uwata. Ba ki ƙara burgeni ba
sai haɗuwarmu a A&Z da kika nunawa duniya da ma
Zeenat, akwai soyayya tsakaninmu. Duk a matan da suke
bibiyata da sunan so, babu wacce ta taɓa rainawa Zeenat
hankali kamar ke."
Suka yi murmushin tuna ranar kafin ya ɗora.
"Tun daga wannan ranar na ji ina son kusancinnamu ya fi
haka, na dinga hasashen da ace gaskiya ne muna
soyayyar ya kenan? Wane yunƙuri Zeenat za ta yi? Duk fa
da cewar a sannan ina ɗan shakkarta, hakan bai hana ni
tunaninki ba. Dangantakarku da Hisham ya ƙara ƙarfin
shaƙuwarmu. Da tafiya ta yi tafiya, na fahimci ba wai
kawai burgeni kike ba, kaunarki nake dagaske. Akwai
ranar da na ji Zeenat na waya da Chairman tana
kyakyata dariyar mugunta. Maganarki suke yi akan ya ci
gaba da yin duk yanda zai yi ya aureki, za ta ba shi kyauta
ta musamman idan hakan ta kasance. A lokacin har
jaddada masa ta dinga yi kan ya yi amfani da masu gidan
rana, sai kuma ga Hisham ya zo min da batun aurenki da
Chairman. Bayan tsananin kishin da naji yana neman
zautar da ni, sai na dinga ayyanawa a zuciyata ashe
dagaske ƙarfin dukiya na saurin rinjayar zuƙata. Ban yi
zaton kina daga cikin kwaɗayayyun mata ba, sai gashinan
lokaci guda kin ban mamaki. Daga lokacin kuma tunanina
ya sauya a kanki."
Ramlat jin haka ta bude baki za ta yi magana ya yi saurin
dakatar da ita ta hanyar ɗora yatsansa ba bakin. Murya a
tausashe ya ce.
"Yi shiru please, labari ne fa nake ba ki, ki bari na kai
ƙarshe."
Ta gyaɗa kai sai dai tuni idanunta sun cicciko, ta kasa
kunne tana sauraronsa.
"Baki ba zai iya misalta maki ɗumbin damuwar da zancen
aurenki da mutuminnan ya jefa ni ba. Na rasa walwalata,
ke kaɗai nake ganin za ki mayemin gurbin ƴan uwana da
ban san su ba, ina da su ko bani da su, ba zan tuna ba.
Sai gashinan lokaci guda wani can zai rushemin hakan. A
sannan har kwanciya nayi a asibiti, aka tabbatar da cewa
damuwa ce. Na rage tunani. Bayan na farfaɗo na kasa
samun sukuni da walwala, ban yi ƙasa a gwuiwa ba sai da
na nemi gidan Baba Dakta, naje a matsayin manemin
aurenki."
Da mamaki ta tsuramasa idanu baki a sake, hawayen da ta
ke dannewa tun ɗazun suka zubo. Ya yi murmushi gami da
sa yatsa ya sharemata.
"Kar ki yi mamakin ta yanda aka yi na san Baba Dakta. A
hirarrakin da mukan yi da Hisham, yakan sanyamin shi a
ciki don ya cemin ma a wurinsa ya soma neman auren
Aisha kafin ya sada shi da Kawunnanku. Yanda na
fahimta, banda ma makwafci kuma amini ga mahaifinku,
kun daukeshi tamkar mahaifin. Kuna girmamashi sosai
kamar yanda ya ke kula da ku. Sau ɗaya na taɓa yiwa
Hisham rakiya gidansa, a wata ziyarar gaisuwar Juma'a da
ya yi. Yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa nake ganin
girman Hisham, mutum ne mai son sada zumunci
musamman ranakun juma'a, wataran yakan ɗauke ni muje
tare, wataran kuwa shi da matarsa suke zuwa. Wasu
lokutan kuma uzuri kan hana ni zuwa. Ko Hisham bai san
na je gidan Baba Dakta ba, ya sa aka kai ni falon saukar
baƙi, daga bisani ya fito muka gaisa. Na yi mamaki sosai
da ya shaida ni alhalin sau ɗaya muka ga juna. Bayan mun
gaisa sai na rasa ta inda zan fara, karshe ya dube ni da
kyau ya ce na saki jiki da shi, na daukeshi kamar Uba, kar
nayi shakkar komai na fadamasa meke tafe da ni. Wannan
yasa nan take na ji kaunar mutumin nan. Zuciyata ta samu
nutsuwa na fayyacemasa cewa na zo neman iznin aurenki
ne. Ya gama saurarona, a karshe har ya yimin tambayar ko
dama muna soyayya da sauransu. Duka na ba shi labarin
gaskiyar yanayin alaƙata da ke. A karshe ya yimin yar
nasiha game da hakuri da kuma fawwalawa Ubangiji
komai, ya sanarmin cewa an riga da an yi maki miji don
magana yanzu ma ta je ga Kawunnanki kuma sun karɓi
mijinnaki da hannu bibbiyu. Ya bani hakuri ya kuma ce na
ci gaba da addu'a duk abinda Allah Ya yi na sa a raina shi
ne mafi alheri. Ba haka na so ba, amma na ji sauƙi daga
radadin da naji akan batun an miki miji da farko saboda
Baba Dakta mutum ne wanda ya iya kalamai masu nutsar
da zuciya da kwakwalwa. Anan ne na nemi alfarma a
wajensa kan yanda muka yi maganar ya zama tsakanin ni
da shi. Murmushi ya yi ya nunamin kar na sami damuwa."
Ramlat kallon Hussein kawai ta ke yi, so da kaunarsa na
ƙara samun matsuguni a kwakwalwarta da ma dukkan
wasu sassa na jikinta. Shima idanun ya ƙuramata na
sakanni kafin a hankali ya sauke ajiyar zuciya ya ɗan
murza hannunta ya ɗora.
"Ramlat, na ci wuya a ƴan tsakaninnan, daga lokacin da
na gane ina matuƙar sonki har zuwa sadda ake rikice-
rikicen aurenki da Chairman. Ban ƙara samun walwalwa
ba. Komai kika ga ina yi maki wala da farin ciki ko
akasinsa, kawai yi nake. Idan na yi tunanin zan rasa ki sai
na ji hatta da ke din ma haushinki nake ji. Babban dalilin
da ya hana na kasa faɗamaki a lokacin, ban gama
haƙiƙancewa kina sona din ba ne ko kuwa kawai tausayina
kike. Sannan ni mutum ne mai burin duk matar da nake
so, na nunamata son a aikace. Ya fi armashi akan mu
tsaya muna ta maida martanin kalamai ta waya da zahiri.
Ke yanzu abin ma bai fi burgeki ba?"
Ta sunkuyar da kai tana murmushi. Ya ɗora zancen.
"Kinsan wani abu? Nayi mamaki iyaka da na ji labarin ke
ce silar haɗuwata da ɗan uwana, mamaki bai ƙara kashe
ni ba sai da na ji labarin a sanadiyyata aka harbe ki. Sosai
abin fa ya taɓa ni ya dakarmin zuciya. Wannan ne yasa na
ƙara ƙullatar Zeenat. A lokacin kuma na kara ji a jikina
babu wani abu da zan iya sakamaki duk wata sadaukarwa
da ki ka yi gareni face na maidaki karshen ikona kuma
mallakina. A bakin Hisham na soma jin labarin duk wani
faɗi tashi da ki ka yi kafin aurenki da Hilal, har ma bayan
aurenki da Aliyu. Kinsan me? Sai na tsinci kaina da wani
mugun farin ciki, tausayi da ma soyayyarki a zuciyata,
amma ban nunawa Hisham ba asalima haushi na dinga ba
shi har ya yi fushi ni kuwa na haye mota na wuce na yi
maki siyayya na dawo. Bana duba Ramlat, amma a
lokacin haka kawai na dinga ji a raina da yardar Allah za ki
zama mallakina. Musamman da Hisham ya ba ni tabbacin
ba kya son Chairman kuma su Hajiya ma ba sonsa su ke
yi ba. Abin dai daga Kawunnanki ne. Wannan ne ya sanya
ni cikin annashuwa. Kinga wancan aurennaki, ke ki ka yi
kiɗa da rawarki, wannan karon kuwa tunda har yan uwanki
ma ba sa ta Chairman, to fa abun zai zo da sauki. Na ci
gaba da addu'a da miƙawa Ubangiji kukana har zuwa
lokacin da na ji labarin fasa aurenki da Chairman. Sai
kuma ga wanj Baban Hanif na neman yimin shigar sauri.
Sai dai ban sha wahala da shi ba saboda takanas Baba
Dakta ya neme ni ta waya lokacin muna Adamawa ya ce
idan har dagaske nake to shi kam hankalinsa ya fi
nutsuwa da ni, bai kuma tunkareni ba sai da ya ji ta bakin
Hajiyarmu. Bai fadamin dalilin da yasa aka bar maganar
Baban Hanif ba, ya dai bani damar na turo magabatana
tunda har kin bar masa wuƙa da nama, to shi kuma ya
zaɓamaki ni a matsayin mijin aure. Na ji dadin lamarin
sosai. Anan ne muka yi shawara da iyayena, ba ɓata
lokaci muka taho Kano tare da ɗan uwana da Kawu
Adamu. Aka shige gaba aka yi duk abinda ya dace. Kin ji
dukkan abinda ya faru."
Ta gyada kai tana murmushi, ya saki hannunta ya miƙe,
kayan kallo ya shiga kashewa kafin ta ga ya soma rage
fitilun falon bayan ya tabbatar kofar falon a rufe ta ke gam!
Ganin haka sai ta mike ta tayashi da rufe kofar fita na
kicin da kuma kashe fitilun da rufe kofar kicin din gaba
ɗaya. Koda ta juyo sai suka ci karo, ya yi saurin riƙota.
Goshinsu haɗe wuri guda kowannensu na maida
numfashi, za ta zame ya yi saurin riƙeta da kyau. A hankali
kuma ya ja baya.
"Ban gama ba ki labari ba, ki yi shirin kwanciya ki zo, ina
jiranki."
Daga haka ya yi gaba tana kallo ya buɗe ƙofar ɗakinsa ya
shiga. Ta sauke ajiyar zuciya, ba ta daina murmushi ba
kamar yanda ba ta gaji da jin wannan daddaɗan labarin da
ya ke ba ta ba. Ta tuna Kawu Bello da ya ce dama
Hussein din ya taɓa neman aurenta wurin Baba Dakta bai
samu ba sai a wannan karon. Da wannan tunanin cike da
wata iriyar kasala ta ƙarasa ɗakinta. Sai da ta ƙara wanka
don ƙamshin da ta ji Hussein yana yi sai ta ke ji kamar ita
banda wari ba abinda ke fita daga jikinta. Loko da saƙo
duka sai da ta bi ta wanke kafin kuma ta fito ta goge jiki ta
shiga mulka turaruka masu kamshi kala-kala. A ƙarshe ta
fiddo wata doguwar riga mai hawa farare ƙal ta sanya, ta
ɗora hula da ya rufemata gashinta. Duban kanta ta ke yi a
madubi, rigar ta ciki da kaɗan ta wuce gwuiwarta sai top
din da ta ketare zuwa ƙaurinta. Girgiza kai ta yi, a haka ma
kwarjini Hussein ke mata ina ga kuma ta isa gabansa a
haka? Da saurinta ta karasa wardrobe ta fiddo zani. Ido ta
fiddo waje kirjinta ya harba jin hannuwansa zagaye a
ƙugunta.
"Kin yi kyau, shi ne ki ke kokarin rufemin abinda Allah Ya
halarta min gani?"
Ta lumshe idanu, kunya sosai ta ke ji, ta kasa kataɓus.
Juyo da ita ya yi suka fuskanci juna. Har lokacin ta kasa
buɗe idanun. Kallon fuskarta kawai ya ke yi yana jin sanyi
a zuciyarsa. A ƙasan ransa banda hamdala babu abinda
ya ke yiwa Ubangijinsa. Jin shirun ya yi yawa ne ta bude
idanunta ta dubeshi. Ganin idanunsa har sannan a kanta
suke sai ta yi azamar ja baya ta cire jikinta daga nashi.
"Ki yi alwala." Ya juya ya koma ɗakinsa, ta sauke ajiyar
zuciya. Hussein zai kasheta da kala-kalan soyayyarsa.
Jikinta ya yi sanyi da ta tuna ba ta da sallah, daga yanayin
Hussein ba sauki. Sai kawai ta ji ya ba ta tausayi. Ta kashe
fitilu ta rufe kofar, tana tafe tana tuna aurenta da Aliyu,
ranar da aka kawota sam ba ta da walwala ko misƙala
zarra, wannan karon kam Allah kadai Yasan yanda ta ke jin
zuciyarta musamman idan ta tuna yan uwanta da ma
abokan arziki duk suna son aurenta da Hussein. Wannan
ma abin ta ƙara godewa Allah ne. Fatanta Allah Ya basu
zaman lafiya da iyali nagari.
Yana saman darduma, ga dukkan alamu sallah ya idar, ba
ta shiga dakin ba tun da aka kawo ta sai lokacin. Sosai ya
burgeta. Dardumar da ta ga ya shimfida sai ma ya ba ta
dariya ta danne. Ganin ta koma gefen gado ta zauna ya
sanya bayan kammala addu'arsa ya dubeta.
"Sallah fa?"
Ta kalleshi ta sunkuyar da kai, daga yanayinta ya gane
cewa ba maganarsa. Don haka ya mike kawai ya yi
nafilarsa ya yi addua, tare suka shafa ya miƙe.
"Taho mu kwanta na ƙarasa ba ki labari."
Yana fadin hakan ne yana nufar makunnin fitilun dakin,
kashesu ya yi gami da kai hannu ya kunna na gefen gadon.
Hasken ba yawa, kwanciya ya wuce zai yi kai tsaye.
"Ɗan tsaya." Ta dakatar da shi, ya ja ya tsaya kawai yana
kallonta. Abin rufar ta ja ta kakkaɓe gadon ta gyara zaman
filon kafin ta dube shi da murmushi.
"Bismillah."
Ya kwanta itama ta kwanta, fitilar ya kashe. Ɗakin ya yi
shiru na wani lokaci, numfashinsu na gauraya wuri guda
kowanne na shaƙar daddaɗan ƙamshin jikin ɗan uwansa.
Ya kai hannu ya zame hular kanta, yana shafa kitsonta, ta
lumshe idanu. Ya soma magana.
"Heart, kin yi zaton ba sonki nake ba, kamar ma dai kawai
zan aureki ne. Ba ki san cewa Hussein ya soma sonki tun
kan ki soma sonsa ba."
Duk da cewa babu haske sai da ta zaro ido. Kunya ta
sanya ta runtse idanunta. Dama ya san tana sonsa?
Shi kuwa jin ta yi shiru sai ya kai hannu saman fuskarta,
murmushi ya yi mai sauti.
"Kar fa ki yi mamaki, na sani. Sai dai ba karamin
nishaɗantuwa na dinga yi idan naga kin yi narai-narai kina
son yin kuka duk a tunaninki na bana sonki. Sai Hisham
wanda yake sanya ni nishaɗi idan ya sauya fuska yana
tayaki yaƙi. Kuma yasan sarai ina sonki amma na
nunamasa nifa a'a."
Hannunta ya kai saman kirjinsa. Ta nutsu tana jin yanda
ya ke bugu da ƙarfi.
"Kamar yanda kike jin zuciyata na bugawa a kowane
daƙiƙa, wallahi Ramlat haka nake jin sonki a kowane
dakika. Kwakwalwata ba ta taɓa samun hutu daga
tunaninki ba, kar ki ƙara ji a ranki cewa zaman doya da
manja zamu yi. Kar ki ƙara sanya wa a ranki wannan
bawan Allahn ba ya sonki. Kinji?"
"Uhm." Ta faɗi a hankali, hakan yasa shi janyota ba shiri
ya shiga aikamata saƙonnin da suka birkita tunaninta har
ta shagala itama wurin maida martani. Nan fa ta ruɗa
Hussein, ita kuwa shawarwarin yayyunta da su Amrah ke
yawo a kwakwalwarta.
_*"Kar ki wasa da kowacce dama, kar fa ki manta Hussein
bai san soyayya ba sai a kanki. Don haka ki saki jikinki ki
rike mijinki da hannu bibbiyu." *_
Ta tuno kalaman Maman Twins.
***
WASHEGARI....
Tana jin sadda ya maida kanta saman filo madadin a
farko da yake a saman kirjinsa, ya gyaramata ya ƙara rufe
ta da tattausan bargon sannan ya miƙe. Murmushi ta yi ta
buɗe idanu, banɗaki ya buɗe ya shiga, nan ya fahimci
Asuba ce. Ta kai hannu a hankali ta shafi makwancinsa,
so da kaunarsa marar adadi na kara ninkuwa a zuciya da
gangar jikinta. Idan ta tuna manyan kalamai da kuma
yanayin ruɗewar da ya yi duk a kanta, Hussein kuka na
hawaye ne kawai bai mata ba, ya yi wani furucin da dole
ya ba ta tausayi a sannan wato inama a kanta ya soma
aure. Jin motsin fitowarsa bai sa ta rufe idanunta ba
saboda fitilun ɗakin a kashe suke. Ganin yana laluben
makunni yasa ta saurin rufe idon. Kimtsawa ya yi ya fice
masallaci a gaggauce don ya so ya makara.
Tana jin fitarsa ta kunne bedside lamp ta mike zaune
rungume da bargo, murmushi take kamar wata sabuwar
kamu, ta gaji da murmusawar ta koma ta kwanta bayan ta
kashe fitilar. Har Hussein ya dawo ya hau gadon ya
jawota jiki, idanunta ƙirr. A hankali kuma wani sabon
daddaɗan bacci ya soma fisgarta.
Ita ta riga shi farkawa wuraren karfe bakwai da rabi na
safe, miƙewa ta yi ta nufi dakinta. Kai tsaye brush ta soma
sannan ta faɗa wanka tana ji kamar an mata albishir da
gidan Aljanna. Ba ta da wani sauran buri mai yawa a
yanzu face na ta kyautatawa mijinta hakanan da addu'ar
Allah Ya rayamata yaranta, Ya ja kwanan Hajiyarta mai
sonta.
Koda ta fito shiryawa ta yi cikin doguwar rigar atamfar da
ta matse daga sama, ƙasan kuwa ya buɗe amma ba sosai
ba. Ta yi kyau musamman ma kwalliyar da ta yiwa
fuskarta. Sai da ta shafa turare a gaggauce kafin ta fito da
zummar shiga kicin. Sai dai ƙarar wayarta ya katse
hanzarinta, ganin sunan Hafsat ta ɗaga. Suka gaisa.
"Dama kira nayi na ji ko kun tashi. Ganinan zan kawomaku
abin kari."
"Toh Hafsat, sai kin karaso."
Daga haka ta ajiye wayar, ba jimawa aka kwankwasa
ƙofar. Buɗewa kawai ta yi don ta san Hafsat ce. Suka yiwa
juna murmushi. Ta karaso ta ajiye kayan hannunta saman
tebur. Duk yanda ta so akan ta tsaya su yi ƴar hira amma
ina ta ƙi.
"Rufamin asiri Adda Amal, zan dawo anjima dai in sha
Allahu. Ban shiryawa faɗan Hamma Hussein ba."
Dariya ma ta ba Ramlat, suka yi sallama ta tafi. Ciki ta
koma don ta ga ko ya farka. Tsaye ta iske shi daga shi sai
gajeran wando sai kuwa tawul yana faman goge sumar
kansa. Sunkuyar da kai ta yi gami da kokarin fita. Caraf ya
damƙo hannunta.
"Dodo na zama?"
Ta girgiza kai tana murmushi ba tare data juyo ba. Dawo
da ita baya ya yi, ta kasa kallonsa. Karshe ta wayance da
gaidashi. Maimakon ya amsa sai ya sumbaci kuncinta.
"Kin yi kyau sosai."
"Na gode." Ta furta a hankali.
"Tunda ba za'a taya ni ba, a zauna a jira na kammala."
Ba musu ta karasa gefen gadon ta zauna, ganin ya
juyamata baya yana kallon madubi yasa ta ɗago kai tana
ƙarewa mijinta kallo da irin baiwa da ni'imar da Allah Ya
mishi na kyawun sura. A fakaice yana kallonta, dariya ma
ta dinga ba shi, satar kallon na mene alhalin shi ɗin nata
ne halak malak? Har ya kammala da gaban madubin ya
juyo bai bar murmushi ba, ganin ya juyo kuwa ta yi saurin
kauda kai. Ƙananun kaya ya fiddo ya sanya. Ya koma
gaban madubin ya fesa turare, a ranta ayyanawa take son
ƙamshi irin na Hussein ko mace sai haka.
Kafin ma ya tunkarota ta mike, suka dubi juna kowanne da
abinda ya ke saƙawa a ransa. Ta sunkuyar da kai.
"Barka da Asuba, fatan ka tashi lafiya?"
Ya kama hannunta ya jawota ya sa a jikinsa sosai.
"Lafiya na tashi, ina fatan kema haka?"
Suka kwashi ƴan sakanni kafin ya hau yi mata raɗa a
kunne, kunya ta sa ta tureshi tana murmushi.
"Mene hakan wai?" Ta faɗi kamar za ta yi kuka. Ya taɓe
baki.
"Gulma ce bana so."
Hararar wasa ta mishi ta juya da sauri ya kuwa bi bayanta
yana fadin.
"Ni kike wa wannan kallon?"
Ganin dai kokarin cafketa ya ke yasa ta juyo tana dariya.
"Don Allah ka yi hakuri, na tuba."
Ya shafi sumar kansa kawai ya yi gaba zuwa tsakiyar
falon.
"Nan za ki kawomin mu ci, bana son can."
Ta amsa da toh kafin ta yi gaba yana binta da kallo kamar
za ta gudu ta bar shi. Sai da suka kammala karyawa tsaf
sannan ya bata umarnin saka mayafi su je gaida Dada.
Ɗakinta ta koma, dama ba nisa mayafin ya yi ba, ta gyara
zamansa sosai ta zura flatshoe. Koda suka kama hanya,
hannunta ya lalubo ya kama ya murza har sai da ta
lumshe ido ba ta yarda ta kalleshi ba. Ɗan matsowa ya yi
har kafaɗunsu na gogan juna.
"Wai ni bakin tsiwar naki mutuwa ya yi? Ko na lalubo
amsar a daren jiya?"
Ta tsaya cak ta shiga kokarin zame hannunta