KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt

Author :  Rufaida Umar Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   26 / 38

75K to 78K   out of 113.5K words

ni, kuma shigowar ta
gaggawa ce shiyasa ban samu na karaso ba. Amma ayi
hakuri don Allah."
Kawu Modibbo ya yi shiru, can kuma ya ce.
"Wane uzuri ne haka?"
Har Kawu Adamu zai ba shi bayani sai ya tuna roƙon
alfarmar da Hussein ya yi mishi akan cewar ba ya son
Kawun ya san da batun aurensa. Bai faɗamasa dalili ba ko
ba komai dai ya sani Kawun bai kaunarsu, amma shi
kuma ya ce ba komai zai mishi wannan alfarmar.
"Daurin auren wani ɗan abokina ne ya kawo ni."
Kawu Modibbo ya ji sai dai bai yarda ba, maimakon ma ya
ci gaba da sauraronsa kawai sai ya yanke wayar. Shiru ya
yi yana tunani, ɓacin ransa na ƙara ninkuwa. Yanzun ya
lura yan uwansa da wadanda ma suka tsani Amina da
Aminu a baya da kuma wadanda dama ke sonsu, duk sun
hada kai, shi aka ware. Wani bakin ciki ya ji a ransa,
karshen satinnan zai tattara ya je Adamawar tunda akwai
bikin yar gidan ƴar uwarsu, Gwaggo Karime. Tunda gaba
daya za'a hadu, zai kara zaman meeting da yan dakinsu
ya ji dalilin wannan sabon sauyin.
***
Bakwai da mintuna, Ramlat ta hada lafiyayyen friedrice da
gashin kifi wanda a gefensa ta soya dankali ta saka sai
sauce. Ta yi zoɓon da ya ji kayan kamshi ta sanya a firij.
Sosai ta saki jikinta musamman wayar da suka yi da
Amrah ta kara ba ta shawarar yanda za ta tafiyar da
Hussein har ya fahimci shayi ruwa ne.
"Sannunki, sai a je a kimtsa jiki. Allah Ya yi albarka."
Ta juya bayan ta dora komai saman tebur, ta dubi Hajiya
da ke fitowa daga ɗaki. Murmushi ta yi kawai ta kauda
kanta. Ita kadai ta san me ta ke kissimawa a zuciyarta.
Kwafa ta yi don gani ta ke komai ma za ta iya kawai don
Hussein ya fahimci ya ƙuntata mata.
Maimakon kimtsawar, sai ta zube saman gado, wayarta ta
jawo. Missedcalls har uku duk daga Baban Hanif. Kafin ta
gama shanye mamakinta sai wani kiran ya kara shigowa.
Ta ɗaga da sallama, ya amsa.
"Allah Ya huci zuciyarki Maman Affan, ina ta kira an ƙi a
saurare ni ballantana kuma a yimin uzuri."
Ta mike zaune.
"Ka yi hakuri, ba haka bane. Ba na kusa. Ina wuni ya gida?"
"Lafiya kalau. Babu damuwa, na yi."
Shiru ya ɗan biyo baya kafin ya ɗora maganar.
"Na so maganar da zan maki ya kasance gani ga ki,
amma ba na tunanin yanzu ina da wannan ikon na zuwa
kofar gidanku. Da farko ina mai ba ki hakuri bisa dukkan
wani abu da ya faru a dalilin aurenmu. Na yarda haka
Ubangiji Ya tsaramana. A gaskiya Ramlatu, tun fara
zancen aurena da ke, iyayena suka dakatar da ni bayan
bincikensu yasa sun binciko tarihinki. Sun kuma gane
cewar aurenki biyu ba kamar yanda ki ka fadamin cewa
aure daya ki ka taɓa yi ba. Duk da labarin aurenki na farko
da aka ban, hakan bai sa na gwuiwata ta sare ba. Na ci
gaba da zuwa wurinki, idan ba ki manta ba, kin sha
tambayata meke damuna, na ce maki ba komai. Wallahi
wannan shi ne dalili."
Ya ɗan tsahirta, itama ba ta ce komai ba don dama ta san
hakan kan iya faruwa, sai dai ba ta zaci za ta ji zafin abin
har haka ba.
"Kina ji na?"
Ya tambaya, ta amsa da Uhm. Sannan ya ɗora.
"A takaice dai, wancan dalilin shi ne yasa iyayena suka ce
sam ba da yawunsu ba muddin na aureki. Ina kokarin
shawo kansu ne sai ga kira daga Kawunki (Baba Dakta),
ya yimin maganar turo magabata, na ba shi bayanin halin
da ake ciki. A karshe ya nuna ya kamata na hakura tunda
har iyaye ba su so. Koda an yi ba dadinsa za'a ji ba.
Amma wallahi Ramlat ina sonki. Ba yanda..."
"Karka damu, komai ai nufin Allah ne. Allah Bai kaddara
zan zama iyalinka ba. Mu bar shi a haka. Allah Yasa ya
zamemana alheri."
Ajiyar zuciya ya saki har tana jin hucinsa kafin ya amsa da
amin. Daga nan suka yi sallama tare da yiwa juna fatan
alheri.
Ta kurawa wayar idanu cike da tunani, kenan wai wannan
abu da ta kusan aikatawa har ake fasa aurenta dominsa,
da ace ta aikata yaya kenan? Nan da nan ta ji kwalla ta
cicciko a idanunta. Da yanzun tana cikin yanayi irin wanda
Halima ta tsinci kanta, da yanzu ita an ma kashe ta.
Tausayin Hilal da ya fadomata a rai ta ji, rabonsa da Kano
yanzun wata kusan biyu kenan. Tun sadda ya zo ya yi
musu sallama akan ya samu sauyin wurin aiki zuwa Benue
ba su ƙara jinsa ba sai jefi-jefi idan ya samu hawa online a
whatsapp sukan gaisa.
"Uncle oyoyo!" Muryar Ansar da Affan ta ji daga falon,
wannan ya nunamata cewa Hussein sun shigo din kenan.
Ta mike ta shinshina jikinta, gaba daya kamshin girki ta ke
yi, dolenta dama ta yi wankan ko ba don shi ba don haka
sai ta rage kaya ta ja zanin wankanta ta fada bandakin.
Bayan ta fito ta shirya tsaf cikin doguwar rigarta na
material, ba ta shafa komai a fuskarta ba, shimfida
darduma ta yi ta zura hijabi ta hau sallar isha'i. Hajiya ta
shigo har sau biyu tana magana. Na farko ta shigo tana
wanka, na biyun kuwa yanzun tana sallah. Koda ta idar a
gaggauce ta ninke dardumar ta fita. Ba ta son Hajiyar ta
ƙara dawowa a karo na uku ta san rai ne zai ɓaci. Ba tare
da ta cire hijabin ba ta fita.
Su biyu ne da shiga iri ɗaya, shadda ce ruwan blue, hatta
da karamin aikin da aka yi musu iri guda ne. Hular kansu
ma hakan ta ke, sun yi kyau har sun gaji. Su biyun ne
kadai a falon, Hussein na zaune a ƙasa yayinda AlHassan
ke saman kujera yana danna waya su Ummi zagaye da shi.
Sallamarta ya sanya shi ɗago kai ya dubeta. Ta wani ɗaure
fuska babu wani zumudi balle har ta kalleshi. Sai kawai shi
din ya ci gaba da kallonta ƙasa-ƙasa yana kokari ya ga sun
hada idanu. So ya ke ya karanci idanun ko zai gane
manufar sauyawar fuskarta. Ta karaso gami da zama a
hannun kujera ta gaishesu.
"Ranki ya dade Mrs Hussein, girman kujerarki ne ai. Idan
laifi muka yi a yafemana, irin wannan shan ƙamshi, fitowar
sai an ga dama?"
Kalaman AlHassan suka sa ta murmusawa, tana jin
nauyinsa hakanan kawai.
"Ba haka bane, sallah na tsaya yi ne."
"To dafatan an samu a addu'a? Allah Ya amsa."
"Amin. Ina zuwa."
Daga haka ta mike ta nufi kicin, sarai ta na kallon Hussein
ta gefen idanu, kallonta yake sosai, ta yi mamaki kwarai
ganin ba ya daga cikin ɗabi'unsa.
Kayan abincin ta hada komai a tebur har ruwa da lemu ta
ajiye kafin ta dawo falon ta yi musu iso zuwa saman
teburin.
"Nikam da dai za ki sa a ƙasa ya fi min dadi. Kai fa?"
AlHassan ya fadi gami da duban Hussein. Ya gyada kai
alamar hakan ma ya yi. Ta amsa da toh sannan ta koma
kicin ta dauko katuwar ledar abinci wacce da wuya su yi
amfani da ita idan ba azumi ne ya taho ba. Yanzun kam
gashinan a kusa-kusa. Falon ta dawo ta matsar da
centertable sannan ta shimfida. Bisa kuskure idanunta ya
kai kansa, ta kauda kai lokaci guda tana kara hade fuska.
Juyawa ta yi bayan ta ba Ummi umarnin bin bayanta.
Marasa nauyin ta dinga ba ta ta kawo falon, ita kuma ta ji
da masu nauyin. Komai ta jera, tuni AlHassan ya sauko,
tana ji yana jan Hussein da hira amma yana amsawa
tamkar ba ya so, a karshe sai shima ya kama girmansa ya
watsar da shi ya maida hirar ga Ramlatu don tuni ta kora
yaran ɗaki da kallo kawai. Sun san halinta, muddin aka yi
baƙi zasu ci abinci to fa basu isa su zauna ba musamman
ma tunda sun ci.
"Wai nikam Ramlat a ina kika koyi girki haka? Kamshin
kadai ya mamaye hancina har yawuna ya tsinke tun kafin
na kai baki."
Ba ta san sadda ta yi dariya har fararen haƙoranta na
fitowa ba.
"Wurin Hajiyata mana. Amma dai ka bari ka ci kafin ka
yanke hukunci."
Ta karashe gami da turamasa plate din da ta shaƙe da
shinkafa ta kuma ɗoramasa kifin a gefe, ga zoɓo har turiri
yake a kofi.
AlHassan ya jinjina.
"Gaskiya ne. Amma ko a ido ai an san mai dadi."
Ba ta ce komai ba banda murmushin, ta ja plate ta shiga
zuba wa Gogannata wanda ya hau danna waya amma
kacokan hankalin a kan hirarsu yake, shi kansa ƙamshin
abincin dukan kofofin hancinsa yake yi, ya haɗiyi miyau ya
fi a ƙirga. Ƙamshin zoɓon da ya ji citta da abarba da su
flavour, yana kara kwaɗaitamasa son sha.
"Bismillah."
Ta fadi da wani salon kashe murya kamar ba ita ba. Ya
ɗago kai ya dube ta. Hankalinta na ga zoɓon da take
tsiyayawa a kofi ammafa kirjinta wani bugu yake don ta
san idanunsa a kanta su ke kamar yanda jikinta ya ba ta.
"Na gode."
Ya fadi a ciki-ciki, ta ajiyemishi zoɓon, ta mike ta bar
falon. Koda ta kai ƙofa, ta dan saci kallonsa, har sannan
ita ya ke bi da ido duk kuwa da cewar ya kafa kofin zoɓon
a baka. Mamaki ya sa ta saurin kauda ki ta shige daki.
Wani dadi ranta ya yi tana jin kamar ta zuba ruwa a ƙasa
ta sha. Wato dai haka Hussein ke ji idan ya na mata
wannan shan ƙamshin. Ta yi dariya ita ɗaya a ɗaki kafin ta
kife saman gadon cikin annashuwa. Sai da aka kwashe
mintuna talatin sannan Ummi ta shigo kiranta. Ta maida
hijabin ta fito, sun kammala har ma Hajiya ta fito, kayan
kuwa ta tabbatar Ladidi ce ta kwashe tunda ba ta kai ga
tafiya ba.
Hussein ya miƙe ya fita tare da Ansar, zuwa can sai ga
Ansar din ya dawo.
"Mami, ki zo inji Uncle."
Ta dan saci kallon Hajiya da AlHassan, hira suke abinsu
kamar uwa da ɗa, ganin ba su damu da kallonta ba yasa
ta miƙewa ta shiga daki. Sai da ta ɓata mintuna fiye da
biyar ba don kuma wani abun ta ke shafawa ko gyarawa
ba, can kuma ta fito ta fice.
Yana tsaye a jikin motarsa ya harde kafafu hakanan
hannunsa a harɗe a kirji. Tun tahowarta ya ke kallonta. So
da kaunarta na ratsa dukkan wani ɓangare na zuciy da
gangar jikinsa sai dai shafe mintocin da ta yi ba ta fito ba
ya yi masifar sosa ransa. Don haka koda ta tsaya sai
shima ya ja baki ya yi shiru. Ramlat ta soma gajiya da
tsayuwar don haka ta dubeshi babu fara'ar a zo a gani.
"Shikenan ina iya tafiya?"
Kallon da ya watsamata yasa ta kallon gefe guda.
"Idan har ba ki daukeni a bakin komai ba, kina iya tafiyar."
Shiru ya biyo baya, jin ba ta ce komai ba sai ya sauke
ajiyar zuciya.
"Akwai abinda na yi maki? Ko kuwa duk baƙin cikin na
rabaki da masoyinki karo na biyu ne?"
"Komai nufin Allah ne. Haka ya tsaramin a rayuwa. Na
kuma karɓa da hannu bibbiyu."
"Hakane, sai dai kina nufin ba da son ranki ba?"
Yanda ya yi maganar da wani irin sanyi, yasa ta yin
murmushi kadan.
"Kamar yanda kaima ba da son ranka ba, haka nima yake
a wurina. Ina ganin dai mun yi anko."
"Yaushe kika fara duba? Me kike nufi da mun yi anko?"
Daga muryarsa ta gane ɓacin ransa, ta kara gyara tsayuwa
gami da ɗan dubansa.
"Daga ni har kai, mun yarda da kaddara mai kyau da
marar kyau saboda mu din musulmai ne. Kamar yanda na
ji batun aurenmu da kai daga sama, haka Allah Ya bani
ikon karɓar lamarin matsayin kaddarata kuma mai kyau.
Ko ba komai na shaida kana da ɗabi'u masu kyau daidai
gwargwado. Hakanan iyayena da suka haɗa ni da kai, na
tabbatar ba za su cutar da ni ba har abada. Bana so na
ƙara yin gangancin saɓa umarninsu."
Tana kaiwa nan ta sunkuyar da kai don ba ta kaunar kallon
da yake jifanta da shi da ta kasa ganewa.
"Ba wannan na tambayeki ba. Tambayar da na maki,
kenan ba...Shikenan dai. Hakan ma is good."
Ya fasa nanata tambayar, sai ya share. Can kuma ya kara
magana.
"Ku mata kun fi kaunar wadanda za su tsaya su na
furtamaku kalaman so a baki alhalin idan aka yi auren ba
lallai su iya tafiyar da lamuranku yanda ake so ba. Ina da
tabbacin har da wannan a bahagon tunaninki."
"Me ya kawo batun so? Ai bana jin akwai shi a
tsakaninmu. Ba ka san cewa ko ba aure ana yin so ba?"
Ya ji zafin kalamanta don haka shima ya shirya ramuwa.
"Shiyasa ki ka kasa hakuri da auren da babu so?"
Ta dubeshi, wani murmushi ya ke ganin ya ci galaba ta
fusata. Ta kasa haɗiye maganar da ke cinta, ta maida
mishi martani nan take.
"Yanzu ai gashinan zan yi. Ko ba komai a rayuwa ana
koyon darasi, da auren so da wanda ma babu soyayyar,
duk darasi ne a gareni. Na kuma gani. Idan a baya na yi
na soyayyar, yanzu na hakura zan jarraba wanda babu
soyayyar na ji yanda ake ji. Ko itama tana dauwama ko
aa."
Tana kaiwa nan ta soma tafiya da zummar barin wurin, ya
riƙo hannunta ta dawo baya. Ta juya da sauri gami da
kokarin janyewa amma ina karfin ba ɗaya ba.
"Ka cikani tunda dai ka riga ka san cewa haramun ne."
Idanunsa tuni sun kaɗa. Shi Ramlat ke nufi da ba ta so ko
me?
"Idan wasa ki ke yi, bai miki kyau ba. Ina miki rantsuwa da
Allah, ko yankar naman jikin Hussein za ki dinga yi kullum
kina gasawa tsabar ƙiyayya, sai kin zauna da ni muddin
aka ɗaura aurenmu. Idan kika ga kin fita daga gidana, to
ki sa a ranki, ƙasa ce za ta zama makwancinki a ranar.
Babu fitar yaji ko kuma saki. Kar ki shigo gidana da
makami, zan miki tanadin kala-kala sai wanda kika zaɓa.
Zan iya mutuwa, amma har abada kar ki ji a ranki za ki
shigo gidana kuma na rabu da ke. Har abada Ramlat."
Ta dubeshi da idanunta da suka cicciko, ba karamin fusata
ya yi da zantukanta ba. Jikinta ya yi sanyi, ya saki
hannunta ya faɗa motar gami da rufewa da karfi. Ta ci
gaba da tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta bar
harabar wurin zuwa ciki.
KARFEN KAFA Chapter 69
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323


By Rufaida Umar


Kiciɓus ta yi da Alhassan dake fitowa, ta yi saurin sunne
kai kamar mai jin kunya. Shi kuwa a fisge da suka hada
ido ya gane kamar ranta a ɓace yake.
"Har ka fito?"
Ta furta cikin dakiya, ya dan yi dariya.
"Na fito Amarsu, zan wuce. Gobe dai zan koma Adamawa
sai ranar daurin aure in sha Allah."
"Allah Ya tsare hanya. A gaidamin su Aunty Kausar da
Fatima."
"Zasu ji in sha Allahu."
Daga nan suka yi sallama ta shige ciki shi kuma ya nufi
wurin motar yana ta tunani. Koda ya shiga, ya dubi
Hussein da ya ɗago kai daga saman sitiyari.
"Lafiya? Na ganka wani iri kamar yanda itama Ramlatun
na lura da damuwa a fuskarta. Meyafaru?"
"Nothing."
Ya amsa a gajarce sadda ya tayar da motar suka bar
harabar gidan. AlHassan bai kara magana ba banda baki
da ya taɓe. Sai da suka yi nisa ne kafin ya ji ya kamata ya
ce wani abu ko da shawara ce sanin halin mutumin.
"Idan mutum yana son mace, kwantar da kai ya ke yi ya
nemi soyayyarta. Mace ba ta son gadara ko taƙama,
mace kulawa ta ke so da kuma a nunamata soyayya a fili
kuma a gaban kowa. Ban san me ya haɗaku da Ramlatu
ba, amma na kalli abin a mahangar ba ka taɓa soyayya ba,
asalima matan ke binka a baya kana yanƙwana su. Idan
har ka ce ta wannan hanyar za ka siye zuciyar Ramlatu,
abun zai ba ka wuya daga kai har ita. Kar ka yi wasa da
damarka."
Hussein tun soma maganar ɗan uwansa, bai katse shi ba,
kamar yanda kunnuwansa ba su bar sauraronsa ba. Sai da
ya kai karshe ne ya ɗan yamutse fuska.
"Su matan ba za su iya hakuri da kowace kulawa ta biyo
bayan aure ba? Dole burinsu tun su na waje a nunamusu?"
Abin ya ba AlHassan dariya.
"Ka taɓa ganin inda aka yi cinikin biri a sama? Ko kuwa su
matan kana tunanin sun san gaibu da nan take za su
karanci halayyar mutane irinku? Su ba wannan a gabansu,
su dai su gani a ƙas. Kuma dama ai amfanin taɗin kenan,
a fahimci juna a kuma ga ko za'a iya zama a jure halayyar
juna. Na tabbatarmaka idan ka ci gaba da tafiya a wannan
shan ƙamshin naka da rashin maida hankali, za ka sha
wuya a hannun Ramlatu bayan aurenku."
Murmushi Hussein ya yi don shi mamaki ma maganar ya
ba shi.
"Wai zan sha wuya hannun Ramlat? Anya? Don Allah na yi
kama da mazan da za su sha wuya hannun mace?"
Murmushin shima AlHassan ya yi gami da gyara zaman
gilashinsa.
"Da sauranka ɗan uwa. Bari na kyaleka, gani ya kori ji.
Nidai idan ta fara gasa maka aya a hannu, kar na ganka a
ƙofar gidana."
Suka yi yar dariya a tare. Shi Hussein dariya yake don
ganin hakan yake kamar wani almara ko tatsuniya. Bai ce
Ramlatun ba ta da kyau ko tsarin da namiji zai rikito a
kanta ba, tunda shi shaida ne, ganinsa da ita tun farko ya
ji kawai ta burgeshi kafin ya tantance abinda ya ke ji
taƙamaiman a kanta, sai dai ya na da ja akan cewa akwai
macen da za ta iya juyashi ba tare da asiri ba kamar dai
Hajiya Zeenatu a baya. Amma zai jira ya ga irin juyawar ta
Ramlatu. Kulawar ba zai nuna ba kamar yanda dan
uwansa ya buƙata har sai bayan aurensu.
***
Tana tuƙi a hanyarta na zuwa Ofis bayan ta sauke yara a
makaranta, tana tunanin zantukan Hajiyarta.
_*"Magidannaki fa ya bukaci ki bar aiki hakanan tunda can
Adamawa za ki zauna. Ko ba don haka ba dama na
fadamaki duk radda kika tashi aure idan mijin da za ki aura
bai amince ba, to za ki bar aiki." *_
Sauke ajiyar zuciya ta yi. Kenan dai rabuwarta da yaranta
ya zo, wani kewarsu ta ji ya kamata. Dama tasan aiki ko
ba dade ko ba jima za ta bar shi kamar yanda suka yi da
Hajiya a farko. Hon da aka cikamata kunne da shi yasa ta
kara nutsuwa a tuƙinta, ganin ma ba wani tare hanya ta yi
ba sai abin ya yi mata zafi, ta cikin gilashi ta ke duban
motar, sam ba ta ganeta ba. Don haka ta yi gefe ta ba mai
motar hanya. Ido suka hada ya yi mata murmushi ita kuwa
dubansa ta shiga yi baki a sake sai kuma ta dara.
"Hilal?" Ta furta a bayyane, a hankali ta ga ya ja gefe ya yi
parking, itama dolenta ta tsaya don su gaisa. Ba ta kai ga
fitowa ba ya rigata isa wajenta.
"Ranki ya daɗe."
"Yaya Hilal? Saukar yaushe a garin?"
Ya yi ƴar dariya.
"Ko kwanaki uku ban yi ba da zuwa, shima daurin auren
abokina ne ya kawoni, amma nan da jibi zan koma in sha
Allah."
Ta yi murmushi.
"Allah Ya nunamana. Ya Fa'iza da Ɗiyarmu?"
"Suna nan kalau. Ai nake gidan Sis Bilki jiya, na ji kuma
abin alheri. Allah Ya sanya albarka. Yasa zamu gani."
Ba ta yi mamakin yanda aka yi Bilkisun ta sani ba, tana da
tabbacin daga bakin Mijinta ne. Amma faɗawa Hilal sai ta
gani kamar da biyu ne. Cike da jin nauyinsa ta amsa.
"Amin. Ina godiya. Wato dai da ace ba mu haɗu

26 / 38