Author : Rufaida Umar Category : Top Hausa Novels 2025
ya nan
ya yi tafiya Dubai, shi ne surikar ta zo gidan kwana.
"Haba Hajiya, me ya yi maki zafi za ki tsaya dambe da
suruka? Ke kuma don ba ki da kunya wannan ba uwar
mijinki ba ce?"
Fareeda wacce ke tsaye tana huci ta narkawa Hajiya
Zeenatu uwar harara kafin ta saki dariya gami da tafa
hannu.
"Ahayye! Ai fa da yake daga ke har ita jirgi ɗaya ya kwaso
ku dole ne ki ga laifina! Tsoffin banza da ba su riƙe
girmansu ba ai ba zan ji kunyar taka su son rai ba. Kin
tauye hakkin yaro kin danne kina zaune da shi! Ko an
fadamaki bani da labarin mijinki? Kina kai min uwar miji
yawon bin bokaye don mijina ya ƙara aure ko? To wallahi
karyar ku domin tun kan a haifi uwar mai sabulu balbela
ke da farin kai. Don haka idan ku na son na lulluɓe dukkan
sirrikanku to ku tabbatar an fasa batun auren Mijina da
kowace shegiyar kucaka. Idan kunne ya ji..." Ta ƙarashe da
rike kunne kafin ta wuce tana dariya ta bar su baki galala.
Bayan shigewarta ɗaki Batool ta yi gaba ta haye sama,
Hajiya Zeenatu ta bi ta a baya. Su na shiga ɗaki suka sa
mukulli.
"Batool akwai matsala!"
Hajiya Batool da ta zauna rike da ƙugu tana ambaton
wash sakamakon cizon da ta sha a wurin Fareeda. Ta
amsa wa Hajiya Zeenatu kamar za ta yi kuka.
"Matsala nima cikinsa kika tarar da ni Zeenatu. Kamar
Gora yaudararmu ya ke yi yana cin dukiya a ɓagas. Ni na
rasa kan wadannan lamuran."
Hajiya Zeenatu ta yarfar da jaka da mayafi, da sauri ta
faɗa banɗaki. Can kuma ta fito ta zauna tana sharce gumi.
Ta kora dukkan bayani ga Hajiya Batool gaba dayanta a
rude.
"Ya zan yi ne Batool? Ga Visa ta yi wuya an ce mu kara
hakuri zuwa sati na sama, ga wannan lamari na neman
kwaɓemin? Ba mu ga ta zama ba Batool, ta inda aka hau
dai ta nan ake sauka idan ba haka ba mai afkuwa za ta
afku. Ba ni da tabbacin Halima ba za ta tonamana asiri ba.
Ban san iyakar lokacin da za ta riƙe sirrinmu matsayin sirri
ba. Wannan fa barazana ce garemu. Tashi za ki yi mu
kama ƙafa muje mu ga Gora tun kafin komai ya lalace."
Hajiya Batool ta share hawayen takaici, yau ita suruka ke
dambe da ita, ta rantse sai ta ga bayanta tunda dama ba
ta haifarmata ko ƴartsana ba sai afkin ci da kasayarwa.
"Muje. Bari na lallaɓa."
Ta miƙe dakyar ta dauki gyalenta. Suka fice. Fareeda na
leƙensu ta window ta yi dariya ta saki labule. A fili ta ce.
"Munafukan banza, da alama an tafi yawon abinda aka
saba. Zama daram ni Fareeda!"
Ta furta tana mai zama kan gado tana dariya.
***
Tunda Hajiya Zeenatu ta sanarmasa da batun kama
Halima ya gaza samun nutsuwa. Don haka ya kira Dada a
waya karon farko. Hakan ba karamin mamaki ya ba ta ba
don har sai da ta ce.
"Yaya lafiya dai ko?"
"Ah lafiya kalau mana Amina, ba damar na kira ki kenan
sai idan babu ita? Mtsw. Ina yaran nan kuwa? Hassan?
Yana gari?"
Dada ta amsa a sanyaye.
"Aa, ya shigo nan Kano wani uzuri na ma'aikatarsu, bai
ƙaraso nan ba?"
Wani zufa ya karyowa Kawu a goshi, ya samu wuri ya
zauna ɗabas! Sai ya ɓige da faɗan borin kunya.
"Ina na isa dama ya zo wurina? Ai ban isa ba! Kin koyawa
yara tsanata da tsanar iyalina. Sai ki yi idan hakan zai
haifarmaki da ɗa mai ido! Mu din dai mu ne nasu."
Daga haka ya katse wayar bai saurari ban haƙurin Dada
ba. Miƙewa tsaye ya yi yana sunturi, ba zai yiwu ba. Babu
abinda zai ruguza dukkan sirrinsa. Idan ya tabbata lamarin
Hussein ne ya kawo AlHassan garin Kano kamar yanda
Bokansa ya buga ƙasa ya bincikamasa, toh shakka babu
komai ya rushe. Tonuwar asirinsa kamar jin kunyarsa ne a
cikin dangi, ya san duk tsanar da sauran yan uwansa suka
yiwa jinin Aminu da Amina (Dada), bai kai tsanar da ya
yiwa HUSSEIN ba.
Ya dau waya ya dannawa Hajiya Zeenatu kira, haka ya yi
ta ringing ba'a ɗaga ba, wannan yasa shi kasa zama ya
fice daga gidan don ƙara tuntuɓar Bokansa karo na ba
adadi.
***
Ya mike zaune dakyar daga saman gadon da yake
kwance. A hankali ya dafe kai yana salati.
"Sannu Hussein, ka tashi?" Ya dubi mai maganar da sauri,
shi dai wanda ya gani a ɗazun ne mai kama da shi. Ɗan
uwansa da ya daina sanyawa a idanu shekara da shekaru.
Ƙuri ya yi mishi da idanu, daidai nan Hisham ya miƙamasa
kofin ruwan tofi.
"Shanye duka please." Ba musu ya karɓa ya shanye tas.
Kamar yanda jini ke zagaye a cikin jiki, haka ya dinga jin
ruwan na zaga dukkan wata gaɓɓa ta jikinsa, a hankali
hawayen da suka sauya kalar kwayoyin idanunsa suka
samu damar kwaranyowa saman kuncinsa. AlHassan ya
taso ya zauna a gefe gami da sanya hannu cikin nasa.
"Hussein, ka gane ni?"
Gyada kai kawai yake yi bakin na rawa amma kalmar A ta
kasa fita daga bakinsa. Kawai sai ya ɗora hannunsa haɗe
da na AlHassan saman goshi ya shiga kuka kamar ransa
zai fita. Hisham a hankali ya juya ya fita daga ɗakin yana
share kwallar dake kokarin zubowa a kokarinsa na katse
ta yana mai hamdala ga Mahaliccin Sammai da kuma
Ƙassai.
"Na gane ka. AlHassan Aminu Gidado."
Hussein ya furta da kakkarwar murya, jin haka AlHassan
ya ƙara jan sa a jiki shima yana kukan. Zai so ace Dada na
zaune a dakinnan, matar da idanunta ba su taɓa kafewa
da zubar hawayen rashin Hussein ba. Kullum kiranta,
amanar Allah ne su din a hannunta, koyaushe ɗorawa
kanta laifin ɓatan Hussein ta ke yi.
"Ina Daa...da, Baba Naziru.?"
Hussein ya tambaya, AlHassan ya ɗago fuskarsa da wani
irin murmushi mai haɗe da dariya-dariya.
"Dada tana nan, tana nan kullum cikin kuka da addu'ar
Allah Ya nunamata kai. Babban burinta ta samu wani ko
wata da zai kawomata kai koda labarin mutuwarka ne, ita
dai ta san cewa ka mutu cikin musulunci kuma an maka
kyakkyawan sutura. Da yawa ya faru bayan gushewarka
Hussein, abubuda da dama sun faru garemu da baki bai
isa ya buɗamaka su ba."
Hussein ya jinjina kai yana jan hanci.
"Eh, da yawa ya faru. Irin yawan da ban taɓa kawo wa
kaina a rayuwa ba. Ban sani ba ko ni na jazawa kaina ko
kuwa dai.."
Rufemasa baki AlHassan ya yi yana girgiza kai.
"Kar ka ce komai ɗan uwana, ka yi shiru mu ƙara godewa
Allah da ganin wannan ranar da muka kwashe shekaru
muna jira. Haɗuwa da Ramlatu alheri ne garemu baki
ɗaya. Ina zan manta da ita da zuri'arta?"
Hussein ya ci gaba da dubansa da idanunsa da suka kaɗa.
A idanun AlHassan ya gano karin bayani ɗan uwannasa ke
nema. Murmushi ya yi.
"Mai hali ba ya fasa halinsa, ashe ba ka sauya ba?"
Suka yi dariya gami da ƙara rungume hannun juna gam!
Kamar ance ga wani abu zai ƙara raba su. Tirya -tiryan ya
ba shi labari tun daga haɗuwarsa da Ramlat har zuwa
yanzu da aka harbe ta sanadinsa. Hussein ya yi shiru, ya
rasa me zai ce. Ya kuma rasa wane yanayi ya ke ciki,
tunani sosai ke neman shigarsa don haka ya gaggauta
yanke tunanin.
"Mu je na ganta don Allah."
Ba musu suka mike, ya zura takalmansa, bini-bini za su
kalli juna shi da ɗan uwansa su yi murmushi, haka suka
jera idanun jama'a a kansu don ba karamin burge su suka
yi ba musamman masu juna biyu, nan suka fara addu'ar su
ma Allah Ya basu ƴan biyu masu bala'in kama irinsu, su
gan su sun girma haka tare.
***
Gora ya duba, ya ƙara buga ƙasa ya duba, ya ɗago kai ya
kalli Hajiya Zeenatu da Hajiya Batool da ke zaune gabansa
cike da wani fargaba da tsoro.
"Lafiya dai?" Zeenatu ta nemi sani.
Ya girgiza kai ya ƙara maida hankali ya yi buge-buge da
rubuce-rubucensa. Can ya ɗago ya dubesu yana sharce
gumi.
"Bana jin akwai sauran duhu da yanzu haske bai
mamayeshi ba a rayuwar mijinki. Yanzu haka maganar da
nake maki yana tare da ɗan uwansa. Gaskiyar magana
babu sauran asiri a jikin yaronnan. Da alama akwai wanda
ya tsayamasa." (Allah Ya raba mu da aikin jahilci da jahilai.
Ya kiyayemana imaninmu. Ameen).
"Na shiga uku na lalace ni Zeenatu!" Ta dora hannu a kai
ta kurma ihu da kuka.
"Na fadamaki ai! Duk ranar da ya yi tozali da abokin
haihuwarsa aikinki ya rushe. Ko kin manta wannan
gargadin? Toh bari ki ji, akwai wani babban bala'i da ke
tunkaroki daga ke har Batulu, ina mai gargaɗinku akan ku
gaggauta barin garinnan kafin komai ya ida lalacewa.
Wallahi kun ji na rantsemaku, taku ta kare domim ruwa ya
ƙarewa ɗan kada!"
Gora ya na kaiwa nan ya mike ya gyara zaman malun-
malun hadi da ɓantalar goro ya hau tauna. Da wani irin
tsalle Hajiya Zeenatu ta miƙe ta shaƙe wuyansa ya hau
kakari.
"Karya ka ke wallahi! Karya ka ke! Nawa na kashe?! Har
kabari na tona! Hatta da jariri nayi amfani da shi duk akan
Husseini! Karya kake ka ce duka wannan aikin ya tashi a
banza Gora! Dole ne ka nemomin mafita idan kuwa ba
haka ba wallahi sai na kashe ka!"
Gora wanda ya ji shaƙa dakyar ya iya ɓanɓare hannun
Hajiya Zeenatu daga wuyansa. Bai yi wata-wata ba ya
kwaɗamata lafiyayyen mari da rawar hannu ya hau nunata
da yatsa.
"Ni ki ke kokarin kashewa? Yau sakamakon da za ki yimin
kenan? Shegiya ƴar zina! To ki sani kin taɓowa kanki
tsuliyar dodo, yanzu kika soma ganin bala'i da masifa!
Babu ke ba jin dadi a rayuwa wallahi. Ni na miki wannan
alƙawarin."
Jin haka ta ƙara daka tsalle ta shaƙe wuyansa ta hau bori,
ga hawaye caɓe-caɓe ga zani na neman kuncewa sanadin
jijjigar da ta ke yi. Tana faman ikrarin ko mutuwa ta yi
kaɗan ta raba ta da Hussein. Hajiya Batool ta yi iyakar
yinta amma ta kasa kwatar Gora don haka ta bazama
rumfar da matan aure da karuwai har ma da ƴanmatan ke
bin layin ganin Gora, ta nemi ɗoki. Nan da nan suka
bazama aka shigo dakyar suka kwaci Gora wanda tuni ya
galabaita har ya suma. Ruwa aka watsamasa ya farfaɗo.
Idanun na kyarma ya shiga nuna Hajiya Zeenatu.
"Za ki yi dana sanin wannan yunƙuri da ki ka yi na kashe ni
Zeenatu. Sai na nunamaki waye ni! Na fi karfin
wulakancinki!"
"Hoo! Shege tsinanne wanda ba ya kallon gabas! Ni
Zeenatu baƙar ashana ce! Ka san tarihina ka kuma san
asalina! Babu uwar da ban gani ba don haka ka shirya! Sai
na ga bayanka da karyar bokancinka. Ba wanda ya isa ya
raba ni da Hussein! Wallahi sai na kashe ko waye!!"
Da haka Hajiya Batool ta janye ta suka bar wurin zuwa
mota. Hankali a tashe Hajiya Batool ke tuƙi, Allah Ya
taimakesu gilashin mai duhu ne sosai ba'a ganin haukar
da Hajiya Zeenatu ke yi. Ita Hajiya Batool ma ta fi ta
kwanciyar hankali. Ita dai Hajiya Zeenatu kira ta ke sai ta
kashe AlHassan da ma Ramlatu idan hakan ne kadai
hanyar da za ta rayu da Husseininta!
***
Tana zaune daga ita sai Rafee'ah da Amrah, Hunainah da
Zulaihat sai Muniru. Hajiya ta wuce gida wanka da ɗan
runtsawa. Hira suke yi amma ita kam tana zaune ko
abincin da aka zubamata ta kasa ci, hankalinta na kan
Hussein. Kwankwasa ƙofar da aka yi ce ta sa da sauri ta
dubi ƙofar. Amrah ce ta mike tana gyara lulluɓi ta buɗe.
Basu damar shigowa ta yi baki sake tana ƙara kallon
tagwayen masu tsananin kama. Bambancin kaya da
gilashin AlHassan ne kawai ya raba su. Hisham ke
bayansu.
Idanun Ramlat ya kasa ɗaukewa a kansu, ta kuma kasa
tsaida hawayen farin ciki. Kawai sai ta shiga murmushi ga
hawaye na zuba.
KARFEN KAFA Chapter 61
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323
By Rufaida Umar
Gaisawa suka yi da Munir yana ƙara taya su murnar
daidaituwa.
"Allah Ya kara kiyayewa, Ya yi sakayya" Cewar Munir. Da
murmushi ƴan biyun suka amsa da amin. A hankali ya kai
duba ga Ramlat, ganin haka ta yi saurin sunkuyar da
kanta. Ya maida idanunsa ga ƴan ɗakin, kafin waninsu ya
kai ga cewa wani abu, an ƙwanƙwasa ƙofar. Hisham
wanda ya fi kusa da ƙofar ya buɗe. Chairman Aliyu Dikko
ne tsaye daga bayan masu kula da lafiyarsa biyu, yana
aikin gyara zaman malun-malun dinsa.
"Assalamu alaikum. Don Allah nan ne ɗakin da aka
kwantar da Ramlatu Khalid?" Faɗin ɗaya cikin security din
da suke tare. Hisham ya dubesu, yanzun ya gane ko
wane. Kofar gaba daya ya buɗe. Suka dubeshi, Ramlat nan
da nan ta haɗe fuska gami da gyara zaman mayafin da ya
ɗan rufe jikinta. Hussein ya harɗe hannu a kirji yana
kallonsa kamar yanda shima Chairman ya yi musu ƙuri da
idanu. Ya kalli AlHassan kuma ya kalli Hussein ɗin wanda
bambancin sutura da kuma gilashi kadai ya sa ba zai iya
rantsuwar mutum guda ba ne. Ya daure ya dake yana mai
miƙa hannu a yi musabaha, Munir da AlHassan duk suka
miƙa banda Hussein wanda ya kauda kai, fuska a ɗaure ya
dubi ɗan uwansa.
"Muje ko?"
Yana kaiwa nan ya fice daga ɗakin, ganin haka da yawa
cikinsu ma suka fita, ya yi saura daga Ramlat sai
Chairman. Ya zauna saman kujera gami da ba ƴan
rakiyarsa umarnin tsayawa daga waje.
"Sannu Baby, ashe kuma harbinki aka yi? Su waye
wadannan?"
Tun Baby da ya kira ta da shi, ta ji gabanta ya yanke ya yi
wani irin faɗuwa, ba wanda ya faɗomata a rai sai Aliyunta.
Ta yi mishi addu'a a ƙasan ranta kafin ta ƙara yin ƙasa da
kanta, har dai ya kammala ɓaɓatunsa ya mike ba ta ce
mishi uffan ba sai da ta ga ajiye bandir na ƴa dubu har
biyu a gefenta.
"Bana so, ka ɗauke abinka."
Ta furta a kausashe. Ya yi murmushi.
"Haba Baby..."
"Kar ka ƙara kirana da wannan sunan!"
Ya jinjina kai.
"Na ji, lokacinki ne yanzu, ki yimin duk abinda ki ka yi
niyya. Nan ba da jimawa ba za ki koma ƙarƙashin ikona."
Ta ja guntun tsaki, ya gyara zamam rigarsa ya fice. Ba
jimawa da fitarsa su Amrah suka dawo ɗakin.
"Yau naga ikon Allah, wannan shi ne ƙarfin hali wai
ɓarawo da sallama. Mutumin nan ba zai gaji ya kyaleki
ba?"
Faɗin Rafee'ah tana ɗaga kuɗaɗen da Chairman ya ajiye.
Kafin Amrahbta ce wani abu aka ƙara ƙwankwasa, da
sauri Rafee'ah ta ajiye kuɗin. Ɗaya daga cikin abokan
tafiyar Chairman ne, manyan ledoji ne har uku ya shigo da
su. Ya ajiye.
"Ranki ya daɗe, Alhaji ya ce a miƙo. Allah Ya ƙara lafiya."
Har zai juya Ramlat ta dakatar da shi.
"Maida."
Ya yi murmushi.
"Ki yi hakuri Ranki Ya Daɗe, ban isa na ketare umarninsa
ba. A dai yi hakuri a karɓa."
Daga haka ya kama ƙofa. Za ta ƙara magana Amrah ta
girgizamata kai, dole ta haɗiye gami da yin ƙwafa.
"Ki rabu da shi, ba laifinsa ba ne tunda dai shi ɗan aike ne.
Allah Ya kyauta. Amma dai babu alamar mutuminnan zai
saduda."
Amrah ta fadi bayan ya fice.
"Wai nikam Aunties, anya Hussein ba ya son Antinmu?
Kun ga yanda fuskarsa ta sauya da ganin Chairman?"
Hunainah ta furta tana duban dariya ƙasa-ƙasa na zolaya.
"Ke Hunainah! Kin riga ni a fili amma nikam na rigaki a
zuci. Ni wani kallo ma na gani kamar a duniyar romeo da
juliet wallahi."
Abinda Rafee'ah ta ce ta basu dariya sosai idan ka cire
Ramlat wacce ta san ba haka tsakaninta da Hussein,
asalima ita ke kiɗa da rawarta. A fakaice ta share kwallar
da ta cika idanunta. Shigowar Munir ya sa suka bar
maganar, hakan ya fi komai yi mata dadi. Anan ya ke
sanarmusu Hussein sun wuce tare da AlHassan da
Hisham daga can za su biya wurin police station.
"Af, nikam Yaya su waye suka yi wannan aika-aikar? Sun
yi magana?"
Ya taɓe baki jin tambayar Rafee'ah.
"Eh toh, su na ta dai walagigi da hankulan jama'a, amma
ko mene idan an shiga kotu gaskiya za ta yi halinta. Mace
ce, sunanta Halima. Ta dai yi ikrarin kishin Ramlatun ne
yasa ta aikata hakan. Ganin za ta auri Chairman. Wannan
shi ne rashin sani wanda ya fi dare duhu. Idan ma da
gaske take, toh ta yi a banza."
"Ya sunanta?" Ramlat ta tambaya a hanzarce. Ya ɗan yi
shiru don shi kam ya mance ma da sunan.
"Nan fa ɗaya, na mance."
"Halima?"
Ta tambaya gabanta na faɗuwa.
"Yes! Sunan kenan. Amma ya aka yi ki ka sani?"
Girgiza kai ta yi, ta ba su labarin takun saƙar da suke yi
tun zuwanta ma'aikatar Revenue kafin ta bar shi.
"Amma ba na tunanin ta san akwai wata alaƙa tsakanina
da Hussein."
"Ki kwantar da hankalinki ke dai, ko ma mene yanzu kam
ai zai fito fili tunda an cafke ta."
Ramlat ta girgiza kai karo na biyu tana duban Yaya Munir.
"Hakane, amma ban taɓa zaton tsanar da Halima ta yimin
ya yi ƙarfin da ko bindiga aka ba ta za ta kasheni ba, na yi
mamaki matuƙa."
"ƊAN ADAM aka ce maki, mai wuyar gane hali. Allah Ya
kyauta." Cewar Amrah. Suka amsa da Amin. Ita dai
Ramlat har sannan mamaki bai sake ta ba, ta ƙara jin
tsanar auren Chairman.
***
Chairman Aliyu Dikko, wanda ganin mijin Hajiya Zeenat da
wani photocopy dinsa ya ɗaurewa kwanya, ya kasa haƙuri
sai da ya fiddo waya ya dannamata kira. Har ya katse ba
ta ɗaga ba sai a karo na biyu sannan ta ɗaga.
***
Lokacin tana gida ta hargitse tana jiran shigowar Hussein
don su bar garin zuwa wata Jahar kafin lamura su kwaɓe.
Ga dai tana ta kiransa ya ƙi ɗagawa. Lokacin ne kuma
kiran Chairman ya shigo, kamar ba za ta ɗaga ba a farko,
sai dai ta ɗaga.
"Nikam Zeenat, mijinki Hassan da Husseini ne?"
Ta saki rigar Hussein da ta ke shirin sanya wa a akwati.
Gaskiyar Gora kenan da yace su na tare?
"Lafiya? Kin yi shiru?"
"A ina ka gan su?"
Daga amsar ya fahimci ruɗewarta. Kai tsaye ya ce.
"A asibiti na je duba Amaryata Ramlatu, kinsan harbinta
aka yi. Shi ne na tadda su a ɗakin. Sai wani hararata yake
yi kamar na kashemasa wani. Na yarda da zarginki, son
yarinyarnan yake kuma kwalalensa."
Tusa Hajiya Zeenatu ta saki wanda ya tahomata da guntun
kashi. Ta sharce gumi ta hau safa da marwa.
"Yanzu a can ka baro su? Wane asibitin?"
"Zan miki ƙarya ne? Nawa za ki ban idan na miki ƙaryar?
Idan kina son ganewa idanunki ki taka ki je."
Ya sanarmata asibitin, ba ta jira komai ba ta katse wayar.
Banɗaki ta shiga ta sauke nauyin cikinta, ta kimtsa jiki
sannan ta fito. Sun rabu da Hajiya Batool akan zasu haɗu
su je wani ƙauye domin a yi musu aiki maikyau. Sai dai ba
ta jin za ta jure wanzuwar Ramlat a doron ƙasa, za ta sa a
karo na biyu a kashemata ita. Duk abinda zai faru sai dai
ya faru.
Ta fice daga gidan gaba ɗaya.
***
Chairman da tun bayan kammala wayarsu da Zeenatu ya
yi shiru yana tunani.
"Ina maka rantsuwa da Allah zan sa a kashe Ramlatu idan
ni ban kashe ta da hannuna ba muddin ta yi kuskuren shiga
rayuwata da mijina."
" Dakata!" Ya ba direba umarni, ganin haka direban ya ja ya
yi parking a gefe.
Chairman ya fidda waya ya ƙara kiran Hajiya Zeenatu,
yana ta ringing ba ta ɗaga ba. Haka ya yi ta dialing shiru,
don haka ya yi saurin cewa direban ya mishi magana da
daya daga cikin abokan tafiyarsa. Da sauri direban ya fita
zuwa ɗayar motarya kira.
"Sir."
Chairman ya dube shi.
"Ku juya ku koma asibitinnan, ku tabbatar kun kula da
marar lafiyarnan. Ina zuwa."
Ya hau lalube cikin hotunansa har ya fiddo hoton Hajiya
Zeenatu a wajen wani taron biki da suka