Namiji Kudan Zuma Book by Hassana Abdul'aziz Yakasai .txt

Author :  Hassana Abdulaziz Yakasai Category :  A Books

Chapter   1 / 7

1 to 3K   out of 19.4K words

NA MIJI K'UDAN ZUMA


By maman Islam


☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION


Page 1


"Assalamualaikum maman Khalid yaudai gani a kar ki ciny...............d'if maganar ya d'auke sakamakon ido hud'u da sukayi da SAMAD dan haka tayi kicin kicin da rai yayin da taji aranta kamar ta juya ta koma sai dai ta san idan ta koma anty DEENAH bazata tab'a jin dad'i ba tunda sun riga sunyi da ita yau zata zo, sannan kuma tana yawan yi mata korafin rashin zuwan ta wanda hakan yana da nasaba da yadda tayi masifar tsanar Samad d'in.


"Oyoyo mommy" yaron anty Deenah da fito yanzun wajen daddynsa ya kwala ihun murnan ganinta, saurin durkushe wa tayi ganin yayo kanta da d'an gudun sa ai kuwa yana zuwa ya fad'a jikinta ta rungume shi tsam tsam ajikinta tana mai jin dad'in ganinsa.


Itama cikin murnan ganinsa tace "oyoyo my boy ina Momma?"
Bai bata amsa ba yace "mommy ina tweets tin da titace a kawo min ya?"
Ya tambaye ta cikin tsatstsamar hausar da bata gama kama bakin sa ba.


Murmushi tayi ta d'an ja kumatunsa tace "kai my boy mai yasa baka mantuwa ne?"
Ta fad'a tana d'ebo alwan a cikin Jakarta ta mik'a masa karb'a yayi da murnan sa na gode my mom ya fad'a yana barin wajen da gudu yayin da tashi da kallo har ya haye jikin daddyn sa wanda tun shigowar SUHANA yake binta da wani mugun kallo suna had'a ido itama ta galla masa harara karab sai a idon Deenah wacce ta fito yanzun.


"A a SUHANA bana son iskanci meye haka wai Daddy sa'anki ne da kikayi masa irin wannn rainin?"


Itama sak'on hararan ta aika mata kafin ta saki wani mugun tsaki ta mik'e da sauri ta juya.


"SUHANA SUHANA SUHANA" Deenah ta bita da sauri tana kira harda d'an gudun ta, "SUHANA dan Allah karki tafi" Deenah ta fad'a da da d'an sanyi jiki, cak SUHANA ta tsaya tana goge hawayen da ya zubo mata amma bata juyo ba.


"Haba SUHANA me yasa kike haka ne duk kin bi kin canja hali sam raina Babba ba halin ki bane me yasa yanzun kika canja haka da yawa?"


Kuka ta fashe dashi tace "to anty me na masa da zai rik'a hantarana yana min kallon tsana da hararana?"


"Ba hararan ki yake ba SUHANA abinda mutane suke zargin ki dashi shine shima yake tunanin hakan sam baya jin dad'in yadda mutane suke ya mud'id'i dake akan abinda ba haka bane"


Kafeta tayi da ido tana kallonta yayin da wasu irin hawaye masu mugun zafi ya zuba mata tace "anty kema ZARGINA KIKE?"


girgiza kai Deenah tayi tace "ko kad'an bana zarginki 'yar uwata tunda nike dake ban tab'a ganin wani abun assha atare da ke ba dan haka ban tab'a zargin ki ba SUHANA' amma kinsan cewa dole zargi ya hau kanki abisa abubuwan da kike aikatawa"


"Ai kema kinsan dole ce tasani hakan bani da yadda zanyi ina samawa kaina nutsuwa ne amma wallahi bana aikata wani mugun abu"


"Na sani SUHANA amma dan Allah ki rik'a taka tsantsan da rayuwa saboda kinsan yanzu kiwon mutum ake"


"Naji kuma zan kiyaye ta fad'a tare da shafar fuskar ta tace"ni zan wuce anty"


"Au bazaki shiga ba?"
"Eh"
"Me yasa?"
"Saboda na tsani SAMAD kuma bana son ganin sa"


Murmushi Deenah tayi tace "SUHANA kenan kedai wallahi rigiman ki yawa ne dashi"
Itama murmushin tayi ta sumbaci hannun yayar tata tace "good by my ant"
Ita ma hannunta ta d'aga mata jikinta a sanyaye aranta tanaiwa kanwar tata fatan samun sassauci abisa matsalar ta.


Sanda ta koma d'akin tuni SUHAIL yayi bacci ajikin daddyn sa wanda yai kicin kicin da rai.


Yadda ya had'e rannan tasan saboda ganin SUHANA ne dan haka ta d'an saki murmushi ta k'arasa ta shige jikinsa tana kafe shi da kallon ta mai sanya masa nutsuwa da gusar da duk wani fushin sa, a sanyaye yace "ki hanata zuwa gidannan bana son ganin ta"


Kallon da tai masa shi da kansa sai da yaga rashin da cewar maganan sa,ko ba komai SUHANA yar uwarta ce kuma JININTA bai kamata ya rik'a nuna mata tsana karara haka a gaban taba.


"Wa fa akan wa kake magana?" ne ta tambaye sa fuskar ta d'auke da wani murmushi mai CIWO, rungumeta yayi ya kasa ce mata komi domin tunda wuri ya gano kuskuren shi.


"Dan Allah ka sassauta mata ka daina nuna mata baka sonta saboda idan BABU NI ITACE ZATA MAYE MAKA GURBI NA"


"Allah ya sauwake min" ya fad'a tare da hankad'e ta daga jikinsa tayi wani irin baya zata fad'a kan tsohon cikin dake jikinta, cikin wani irin zafin nama ya fisgota ta dawo jikinsa kafeshi tayi da wani irin kallo kafin ta fusge jikinta ta tashi ta barshi anan.


Ya k'ure ta Kennan?
Ya ayyana hakan a ranshi take ya durk'ushe anan tareda dafe kansa cikin takaici sam Deenah bata ganewa batasan wacece SUHANA ba, batasan tantirancin SUHANA ba shiyasa har take iya fushi dashi dashi akanta tunda yake bai tab'a ganin mara mutuncin yarinyar sama da SUHANA ba bai tab'a jin tsanar mutum kamar SUHANA ba a rayuwar sa ya jima sosai a wajen yana saka da warwara.


Niko ina fitowa daga gidan anty Deenah nasawa raina cewa nida gidanta har abadan saboda bana k'aunar ganin samad ko kad'an a rayuwata, ta fad'a tana hararan gidan kamar gidanne yayi mata laifin.


Kanta tsaye gidan su Sameer ta nufa yana ganinta ya tare ta cikin farin ciki ya rungumeta tsam a jikinsa yana sakin wata ajiyar zuciya "SUHANA jiya kin barni cikin tashin hankali da damuwa dan Allah SUHANA ki taimaka ki AURENI wallahi zanyi miki duk abinda kike so"


K'wace jikinta tayi daga nasa tare da galla masa wata katuwar harara tace "amma baka da hankali Sam, sau nawa zan fad'a maka cewa babu aure a tsakanin mu wannan ya zama na farko da k'arahen da zaka kumayi min zancen wani aure idan ba hakaba to wallahi saina yanke duk wata alak'a dake TSAKANINMU kaji na fad'a maka" ta k'arasa tana kuma galla masa wata hararan da tafi ta karko tare da sakin wani mugun tsaki ta zari mayafinta da jakkar ta da ya yasar mata anan gefe ta gaba ta barshi dafe dakai.


Allah ya sani yana k'aunar yarinyar sai dai yarasa dalilin dayasa koda wasa bata k'aunar yayi mata batun aure baisan dalilin ta nayin hakan ba ko kuma shine bata k'auna?


MAMAN ISLAM CE


Yawan comment yawan typing insha Allah






NA MIJI K'UDAN ZUMA


BY


MAMAN ISLAM
BISMLLAHI RAHAMANIR RAHIM


☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION☀️


😘
Page 2


Ita ko SUHANA tana fita a gidan wayar ta yayi k'ara, tayi saurin d'auko wa a Jakarta tana dubawa taga hajiya cemahaifiyar ta sai da gabanta ya fad'i, sai kawai taki d'agawa ta maida wayar Jakarta ta bayan ta sakata a silent.


"SUHA SUHA" ta tsinci muryarsa daga bayanta yana kiranta da sunan da ya saba kiranta da shi sai da ta daidaita nutsuwar ta kafin ta juyo fuskar ta a d'inke babu alamun wasa a cikinta, sam baya fushi da halinta hakanan Allah ya jarabta masa wata fitanannen SONTA sai da ita kuma sai jan sa take ak'asa iya son ranta sai yayi sa'ar gaske sannan zata kalleshi har ta tanka masa.


"Hajjaju na daga ina haka?" hararan sa tayi tace "daga inda ka aike ni malam ban guri na wuce"


"Allah ya huci zuciyar sarauniyar kyawawan matan duniya" bata san sanda wani murmushi ya k'wace mata ba sai dai bata yi ba ta barshi a zuciyar ta.


"Haba kyakykyawata masoyiya ta bugun zuciya ta abar alfahari na tunda nake ban tab'a ganin matar da yanayi na yake sauyawa ba idan na ganta saike kece wadda idan ban ganki ba nake kasancewa cikin damuwa da tunani kuce farin ciki na dan Allah SUHANA ina rok'an alfarma ki taimaka ki tsaida ni amatsayin mijin ki, zaki farin ciki zaki alfahari da kasancewana mijinki abin Alfa"""""" dakata malam dan Allah"


Ta fad'a cikin d'acin rai da wani mugun bak'in ciki,haka sauran ma suke fad'a mata haka suke riritata su tattala ta su nunawa duniya babu kamarta su rik'a ambatar itace duniyar su, saidai kuma da zaran ta shiga gidan ta zama nama ta zama wata irin baiwa mara gata da 'yanci ita ko ME ZATACE DA MAZA???????


Jin hawaye na shirin sauko mata yasa tayi saurin juyawa Khalil baya, bata so yaga raunin ta tayi alwashin babu wani D'A NAMIJI da zai k'ara ganin raunin ta bare ya mai da ita garaigaransa takawa tafara yi cikin takun ta mai tafiya da imanin duk wani na mijin dake tak'ama da isashiyar lafiya.


Kafeta da ido Khalil yayi yana K'are mata kallo yayin da zuciyar sa yake wani mugun bugu damuwar sa fargabar sa tashin hankalin sa SUHANA tace bata sonsa bazata aure shi ba wannan ranan ya tabbatar saidai ya tsinci kansa agadon asbiti dan ya tabbatar da cewa zuciyar sane zai buga kowa ma ya huta.


Yana ci gaba da kallon ta da mamakin ta har ta b'ace wa ganinsa, wata irin ajiyar zuciya ya sauke ya d'aga hannunsa sama "Allah ka mallaka min wannan baiwar taka badan ni ko halina ba badan na'isaba dan fiyayyen halitta sallallahu alaihi wassalam.


Hakanan taji kalaman Khalil sun b'ata mata rai wai me yasa MAZA suke haka ne me yasa suke da son kansu tana mamakin yadda na yaudara da son zuciya yake tasiri a zuciyar mata, tana tausayin duk wata yarinya da take rawan kai akan wani d'a NAMIJI wanda basu san cewa duk d'aya suke ba duk kurane da fatar akuya


"Uku fa uku, uku" ta fad'a tana k'ara maimaitawa tare da d'aga 'yan yatsun ta guda ukun, sai kuma wasu irin zafafan hawaye suka zubo mata "Allah ka dubani Allah ka zama gatana Allah kazama gatana Allah kazama gatana haka ta rik'a maimaitawa cikin wani irin fitinannen kuka, kasa zuwa inda zata tayi kawai ta nufi gida duk da kasancewar bata so komawa gidan a wannan lokacin ba saboda gudun abinda zata tarar a gidan.


Tana shiga babban falon ta ci karo da hajiya wacce take zaune a kujeran dake kallon k'ofar shigowa, ido hud'u sukayi da hajiya wacce ta kafe SUHANA da ido wadda har lokacin idanunta basu daina tsiyayar da ruwan hawayen ba, wani irin mugun fad'uwa gabanta yayi ganin irin kallon tsanar da mahaifiyarta take mata wanda yake haddasawa rayuwar ta bak'in ciki da tashin hankali wanda yasa sam take jin zuciyar ta babu dad'i har taji gwanda ta bar gidan ko zata samu sassauci abisa halin da take kasan cewa a ciki, duk kuwa da kasancewar halin ZARGIN da take kasancewa a idon iyayen nata sum sum tayi zata wuce, wata uwar tsawa da Yaya maleek ya buga mata batasan sanda ta tsinci kanta a gabansa tana hawaye ba " daga gidan uban wa kike?"


Ya tambaye ta cikin d'aga murya, cikin inda inda tace "gid an anty Deenah


"K'arya kike munafukan banza daga dai yawon iskancin da kika fi kwarewa akai kike"


MAMAN ISLAM CE




*NAMIJI K'UDAN ZUMA*


Page 3


Ita ko SUHANA wani mugun kallo ta watsawa Yaya maleek tace "nasan abokin ka kake tayawa k'ina bazaka tab'a burge ni ba sai ka taya shi kun had'u kun hak'a rami kun binne ni da raina.


"Ni kike fad'awa magana SUHANA?"
"Eh Yaya da abinda zakayi ne?"


"Kindai ci darajan hajiya da wallahi sai na taka kanki anan wajen" wani mugun kallo ta watsa masa ta wuce d'akin ta tana ci gaba da matsar hawayen ta.


Tana barin wajen ya Maleek ya dafe kansa yana binta da kallo har ta shige "Allah ka bayyana mana abinda yake damun wannan baiwar taka, idan ma wanine yake jifan ta da wannan BALA'in Allah ka maida masa da abinsa kansa" ya shafa tare da sauke ajiyar zuciya sai kuma ya mik'e ya nufi d'akin hajiya yayi mata sallama ya wuce gidansa.


Ita ko tana shiga d'akin ta, tayi wurgi da d'an kwalin ta da mayafinta da jakar duk anan tsakar d'akin sannan ta haye saman gadonta ta takarkare ta saki wani kafirin ihun da yasa hajiya dannowa aguje duk kuwa da ciwon k'afar da take fama da shi.


Ganinta a zaune idanunta a soye dan tuni ta goge hawayen ta gyara fuskar tas, kallon ta hajiya tayi cikin takaici tace "kai SUHANA kai SUHANA


Yanzun fisabilillahi SUHANA me nayi miki da zafi da yasa bakyason kwwnciyar hankali na?"


Fashewa SUHANA tayi da kukan gaske tace "to ni nayi miki magana ne hajiya ko nace wani abu duk kukabi kuka tsaneni keda d'anki anty Deenah ce kawai tasan matsala na ita ta damu dani take amsar uzurina take jana ajiki take bani shawara a maimakon ke hajiya me nayi da zafi wanda yasa kika watsar da tarin k'aunar da kulawar da kike min ko dan kaddara ya giftawa rayuwa ta shine kike fushi da ikon Allah?"


Ita kanta hajiyan bata san sanda hawaye ya zubo mata ba har ga Allah tana matuk'ar tausayawa autar ta sai dai kuma sauran yaran ta suna ganin ita ke d'aure wa SUHANA shiyasa take yadda taga dama, k'arasa wa tayi kusa da SUHANA tajata jikinta ta rungume tana d'an bubbuga bayanta tace.


"SUHANA bazaki gane bane abinda kike aikatawa kina sa mana zargin ki da damuwa mai yawa dukanmu muna tunanin ko kina fita ki zubar mana da mutunci awaje ZARGIN KI MUKE SUHANA ba iya 'yan uwanki ba harda ni mahaifiyar ki"


Kallo SUHANA tabi hajiya dashi wanda yake cike da wani k'unci da tsananin BUGUN zuciya tace "hajiya?"


"Eh SUHANA haka ne ina ZARGIN KI domin abubuwan da kike dole a d'iga miki ayar tambaya"


Take yanayin SUHANA ya sauya ta koma wani irin fitinannen mugun yanayi tareda k'arfin da yakanzo mata idan ranta ya b'aci cikin d'aga murya tace "cikani hajiya kar nayi miki illah"


K'ara k'ank'ame ta hajiyan tayi tace "SUHANA ai ni bana tsoron kimin illah kuma a ko wane yanayin kike ni bazan gujeki ba amma ko wace uwace a matsayin Ni DA KE SUHANA dole ta zargeki dan haka SUHANA Deenah ne kawai ta yarda dake duk cikin mu"


Wani irin kuka SUHANA ta fashe dashi tana tason kwatar jikinta daga hajiya ta k'arfin bala'i,amma ta kasa domin ba k'aramin rik'o hajiyan tayi mata ba sannan kuma ita d'in irin k'arfafan matannan ce dan haka duk sanda SUHANA ta shiga irin wannan yanayin ko Maleek baya iya rik'e ta sai dai hajiyar.


"Ni ki cikani gidanki zan bar miki wayyo Allah na Abba na mai yasa ka tafi ka barni da wanda basa k'auna na, ni ki sakeni".


Ta karashe da wani irin fitinannen kuka tareda wani irin fisge fisge, k'ara rik'e ta hajiyan tayi da kyau tana tofa mata addu'o'i, da k'yar ta samu bacci ya d'auke ta.


Shiru hajiyan tayi tare da zuba tagumi tana kallon SUHANA cikin wani irin tausayin ta ta rasa abinda yake damunta tun bayan rasuwar ANWAR bata k'ara ganewa SUHANA ba.


Tunda ta kama bacci bata farka ba sai bayan sallar magriba, sanda ta shiga ban d'aki saida ta fara wanka sannan ta d'auro alwala


Bayan ta idar da sallah bata bar kan abin sallar ba saida ta gabatar da sallar isha kafin ta nad'e abin sallar ta koma, gaban merrow ta hau shafe shafen ta, kwalliya ta tsantsara ta gani a fad'a, ta bude' wadrop d'inta wasu irin k'ananun kaya ta d'auko ma asu masifar d'aukan hankali ta saka ta taje dogon gaahin kanta tayi donut dashi yai wani irin tumtum saboda yawa da tsayin sa, wani d'an siririn mayafi ta yafa kalar kayan ta k'ofar bayan gidan tabi ta fice batare da ta bi ta babban falo inda su hajiya ke jiranta dancin abincin dare ba


MAMAN ISLAM CE






NA MIJI K'UDAN ZUMA


By
MAMAN ISLAM


FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION


Page 4


Babu wani jinkiri ta fad'a cikin motar dake fake a k'ofar gidan wanda daman ita yake jira ya figa da wani irin mugun gudu.


Tunda suka fara tafiya yake duban ta cikin tsantsar shi'awar ta sai dai wannan kadarar tafi k'arfin shi domin bala'in ta ya wuce da sanin sa ta wuce da tunanin k'ananun kwari irin sa.


Ita kama bayan ta, ta kwantar jikin kujeran tana fesar da wata iska mai zafi har yau ranta a jagule yake ta rasa me ta tsarewa SAMAD da yai mata wannan tsanar tun tana daurewa har ta fara jin tsanar sa har ma fiye da yadda ya tsane ta, tasha alwashin ta daina raga masa ko kad'an duk sanda ya shiga hanyar ta sai taci mutuncin sa fiye da tunanin sa rashin mutuncin da zatai masa ko kare baya ci ba.


Da haka suka k'araso club d'in da Na'im ya kawo su wanda kusan duk sanda SUHANA ta tsinci kanta cikin b'acin rai nan take zuwa tare da Na'im tayi mankas abinta ta koma gida a buge tatul.


"Kai Annur maza je ka kira SUHANA tazo muci abinci" da sauri Annur ya nufi d'akin SUHANA, wayam babu ita take yaron yaji ransa ya b'aci muddun babu SUHANA a gida a irin wannan lokacin to bata da wajen zuwa sama da wajen tam bad'ewar ta dan haka cikin fushi ya koma ya sanar da hajiya.


Dama tunda wannan abun ya faru tsakanin ta da Malik tasan za'ai haka itama ba k'aramin b'aci ranta yayi ba abincin da basu samu sunci ba kenan ita da Annur domin har yafi mahaifiyar tasu shiga damuwar halin da 'yar uwar tasa ta jefa kanta na banza.


Acan club kuwa suna shiga Na'im yasa aka kawo musu kayan ciye ciye kala kala suka ci suka sha sannan ta kora da kayan da suke d'ebe mata kewa sosai yau ta bugu fiye da ko yaushe tun daga zaunen ta fara layi ganin haka yasa Na'im ya rungumeta a jikinsa suka shiga filin rawar, take filin yazama nasu ita da Na'im domin duk ranar da Na'im da SUHANA suka shiga filin rawa babu wanda ya isa ya shiga domin bala'in su ma ya ishi mutum.


Wata irin rawa suke sunayi suna fad'uwa domin dukansu babu mai kwarin kirki sun riga da sun bugu da yawa.


Yau kam bak'in cikin yafi na ko yaushe ga SAMAD domin ji yake kamar ana daddatsa zuciyar sa ganin SUHANA rungume a k'irjin wani k'aton d'an iska, cikin d'acin rai ya k'arasa wajen ya wani irin finci kota ta fad'a jikin shi yayi saurin janye ta tare da d'auke ta da wani bahagon mari, ta d'ago narkakkun idanunta ta watsa masa cikin muryan mashaya tace


"Au ashe kaine jakin banza shine ka mare ni wallahi

1 / 7