Author : Hassana Abdulaziz Yakasai Category : A Books
dan bala'i duk inda zani kana biye dani kamar wani jela wallahi sai nasa anyi min maganin ka tunda naga kana neman wuce matsayin ka dad'in abinma ba ni kake aure ba yayata kake aure bare ka hanani rawar gaban hantsi, azahiri kuwa wani mugun kallo ta watsa masa tare da sakin tsaki ta rab'a ta gefanshi har tana bangaje shi ta wuce abinta.
Da kallo ya bita har ta fice daga layin zuciyar sa na wani irin tuk'uk'in bak'in ciki wayar sa ya zaro daga aljihun ya dannawa Deenah kira tana d'agawa yace "daga yau Deenah babu ni babu SUHANA kada ki k'ara sakani bin duddugin ta tunda ni ba d'an aikin ki bane" daga haka ya kashe wayar bai jira cewar ta ba ya juya a fusace ya bar wajen.
Deenah kuwa dafe kanta tayi cikin damuwa a sarari kamar tana gabanta tace "kai SUHANA kai SUHANA dan Allah wai so kike sai kinga bayan mu?"
Saiga wasu hawaye nabin kuncin ta.
. SUHANA kuwa daganan kasuwa ta wuce tayi cefanen abinda zata buk'atar ta dan ta jima bata cin komai daga Hajiya ko sauran yan uwan ta wai kada suyi mata asari (nace ikon Allah SUHANA lamarin naki azimunne).
Sanda ta shiga gidan babu kowa a falon sai Annur tace "kai Annur ina Hajiya?"
"Tana kicin" daga haka sai ta juya kicin d'in inda Hajiya ke kad'a miyar d'anyen kub'ewa wanda tayi musu tuwon semo" Hajiya ki fad'awa Abdul Samad ya fita hanyana idan ba hakaba zan yaga masa rigar mutunci wallahi?"
"Oh ni safiya naga ta kaina wai SUHANA dan Allah me yake damun kanki ne nidai na rasa wannan abu tsakanin ki da Abdul Samad wanda da sam babu wanda kuke shiri dashi kamarahi".
"Da kikace Hajiya a yanzu babu wanda na tsana sama dashi wallahi"
"To Allah ya kyauta" Hajiya ta fad'a tana ci gaba da aikin ta yayin da SUHANA tayi kwafa tabar kicin d'in
MAMAN ISLAM CE
NA MIJI K'UDAN ZUMA
By
MAMAN ISLAM
☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️
Page 8
Tana shiga d'aki ana kiran sallar magriba dan haka tashige toilet ta d'auro alwala tazo ta tada salla, bayan ta idar bata ja wata doguwar addu'a ba saboda uwar yunwar dake sakad'ar ta rabon ta da abinci tun wanda tayi da safe taci hakane yasa ta nufi kicin ta d'ebi manyan kifin da ta suyo tazo jikin sink ta wanke da lemon tsami tasa wuk'a ta daddatsa sannan ta d'auraye tukunya ta saka kifin a ciki ta kawo albasa mai yawan gaske ta yanka ta d'auraye ta watsa ta daka tafarnuwa da masoro da cita ta saka indai takaice muku wannan kifin dafa du tayi masa saboda yunwar da take ji komai ta had'a daga k'asa kafin ta kunna gas ta d'ora tukunyar akai bata sa ruwa ko kad'an ba saboda tasan kifin mugun ruwa ne dashi, cikin mintuna kad'an ka'mshi ya gauraye kicin d'in sai ga Annur ya shigo da gudunsa "anty me ake dafa mana ne haka ka'mshi duk ya cikamu?"
Harara ta galla masa harara tace "to akwad'aitu badai ci zakayi ba ware ta fad'a tana talle masa k'eya juyawa yayi zungwai zungwai yai waje.
Binshi tayi da kallo cikin tausayin yaron Allah ma ya sani tana matuk'ar k'aunar Annur duk wata d'awainiya ta yaron kusan ita tayita sannan akwai shak'uwa mai k'arfin gaske a tsakanin su.
Tana gamawa ana kiran sallar isha hakan yasa ta kashe gas din ta shige d'akin ta saida ta fara wanka sannan ta d'auro alwala tazo ta kabbara sallah bayan ta idar da gudu ta nufi kicin badan Hajiya tasan halin ta ba da babu abinda zai hana zuba da gudu itama saboda yadda ta fito d'in.
Tukunyar ta d'auko gaba d'aya ta nufi dining da ita "Annur d'ebo min flats a kicin" babu musu yaje ya kawo mata ta zuba ta bashi "kaiwaya" ya d'auka ya mik'awa Hajiya har ga Allah tana k'aunar girkin SUHANA dan har mamakin k'warewar yarinyar wajen girke girke.
"Annur taho muci" ta fad'a tana kai wanda ta d'auko bakinta d'auke kansa yayi yana girgiza mata kai alamun bayaci murmushi tayi bata kulashi ba Hajiya ma dake kallonsu tana cin nata kifin murmushi tayi dan taji abinda sukayi d'azu.
SUHANA kam batabi takan Annur ba saida ta fara samun nutsuwa sannan ta mik'e ta kamo hannun Annur da yai wani kicin kicin da rai tace "dalla malam taso wai kai me yasa bakasan wasa ba tsokanar kafa nakeyi".
Ta zaunar dashi tana tura masa kifin a baki tun yana kau da kai har ya fara bud'e bakin yana karb'a suna cikin cinne suhail ya shigo da gudunsa yana "momma momma gani daddyna ya kawoni da bakizo dani ba" ya fad'a yana hayewa jikin Hajiya "kaga ni d'aga ni kada karyani"
"Hajiya nima kibani inci"
"Na hanaka tafi ga uwarka can ta baka"
"Ni ba yuwa na da ita tazu tak'i zuwa dani Nan"
"Itaku babu ruwana da halinku"
Suna cikin haka Deenah ta shugo turtsi turtsi da tsohon ciki Hajiya ta bita da kallon tausayi tace "oh ni safiya Deenah har yanzun bazaki hak'ura da fitarnan ba?"
"Hummmm wallahi Hajiya suhail ne tunda SUHANA ta baro gidan ya hanamu sakat yana ta rigima shine Daddy yace mu kawo sa"
"Kun kyauta ai" Hajiya ta fad'a tana hararan Deenah data nufi wajen SUHANA tana fad'in "me ake cine haka ba a ko kula mutane"harara SUHANA ta galla mata tareda d'auke kai dan tasan wallahi saita kaiwa mayen mijinta wannan kifin dan tafi kowa sanin yadda yake masifar son irin wannan kifin.
Ilai kuwa bata bi ta kallon da take mata ba d'ebi tai waje dashi har suka gama suka bar wajen SUHANA ta shige d'akinta ta danna sakata, itama Deenah bata nemeta ba domin tasan bazata kulata ba tunda tasan tabawa makiyinta abinta
MAMAN ISLAM
NA MIJI K'UDAN ZUMA
Page 9
Washegari babu inda SUHANA ta fita zama tayi a gida tayiwa Hajiya kwalema tsab ta gyare mata d'aki ta goge ya koma Kal Kal dan SUHANA akwai lafiyar tsafta.
Ita kanta Hajiya tayi mamakin rashin fitar SUHANA musamman rana irin ta yau litinin wadda SUHANA ke k'aryar ta yafi office tayi tafiyar ta yawon d'aukar maganar ta amma yau sai taga ta kashe wayarta ma gaba d'aya ita dai Hajiya bata tanka mataba har rana ta d'an d'aga wajen sha d'aya taje tayi wanka ta dafa indomie ta d'an ci kad'an da bai dameta ba d'akin ta ta koma tayi kwanciyar ta bata jima ba kuwa bacci yayi awon gaba daita.
Hajiya kuwa zama tayi a falo tana mamakin abinda ya hanata fita arana irin ta yau da ko mutuwa zatayi wajen ganin ta hanata fita muddun ta sanyawa ranta to wallahi saita fitan.
Har Hajiya tagama abincin rana SUHANA bata farkaba saida ga lokacin salla na neman wucewa ne taje ta buga mata k'ofar ta d'an motsa tana addu'ar tashi daga bacci tayi mik'a gami da salati da gudu tayi bayi tayi wanka da alwala tazo ta kabbara sallah,
Bayan ta idar bata ja wata doguwar addu'a ba tayi saurin k'arasawa gaban merrow ta hau shiri a gaggauce sam yau so tayi dama sai k'arfe biyu zata fita sai kuma gashi har biyu da kwata bata fitan ba.
Cikin wani dandatsetsen less pink wanda yaji stone sai walwali yake ta shirya ba d'an k'aramin kyau tayi ba duk da kasancewar ta ba mai yawan son fenta fuska ba amma takanyi wani irin sihirtaccen kyau a duk lokacin da tayi iya abinda take ganin ta cancara kwalliya wato shafa powder da lipstick shikenan sai kuwa kwalli da yakewa idanunta masifar kyau.
Afalo ta samu Hajiya tana duba wani littafin addu'o'i "Hajiya ina Annur?"
Dag'owa Hajiya tayi jin fitinannen k'amshin dake tashi wanda hakan ke nuna mata SUHANA fita zatayi dan tasanta ko a gida take mayyar turarece tun tana'yar ficiciyar ta turarukan su suke shan bak'ar azaba a hannunta dan muddun ka bari suna taga turarenka to bashi kwana biyu ka dawo ka d'auki kwalbar.
"Ina zuwa haka SUHANA?" Hajiya ta tambaya zuciyar ta na falfala gudu murmushi SUHANA ta d'an saki tace "Hajiya na miki tambaya baki bani amsa ba kuma kema kin tambaye ni, to ni office zani" ta fad'a tana d'agewa Hajiya gira "uhm to ga abincin ki ci mana kafin ki fita"
Kallonta tayi kafin ta k'arasa kujeran da Hajiyan ke kai ta d'an rab'u da jikin Hajiyan tace "wallahi Hajiyata kina bani mamaki sau nawa zance miki ni bazanci ba gaskiyar magana ban yarda dake ba kada kije ki asurce ni"
Idan akwai babban abinda yafi k'untata ran Hajiyan bai wuce kalmar asiri da d'iyar tata ke dangantata dashi amma kuma a d'an k'aramin bayanin da suka samu daga SUHANA shekaran jiya sai taji d'acin baikai na kullum ba dan haka ta d'an yi murmushi tace "ai shkenan SUHANA tunda kina tunanin har uwa mahaifiya zata iya cutar da d'anta"
"Ni haifar tawama ina tantama wallahi yadda kuka tsane nin nan nasan ko kasheni akace kuyi keda yaya Abdul Maleek tsab zaku iya" ta fad'a tana hararan gefe kafin kuma ta mik'e tayi waje abinta.
Dafe kai Hajiya tayi saiga wasu irin zafafan hawaye sun zubo mata ta d'aga hannunta sama tace"ya Allah kanaji kuma kana gani babu wanda nasawa ko na zubarwa babu wanda na takawa balle ka kawo min mafita abisa halin da 'yata take ciki wanda nasan ba halin ta bane" ta k'arasa tana shafawa tare da zubowar wasu hawayen.
Da gasken office d'in ta nufa tundaga bakin k'ofar sakatariyarta take sanar mata oga ya amshi makullin office d'inta wai zai gwada wani abu dashi' wani dan iskan kallo ta wulla mata tace"wane shegen ne ya baki umarnin bawa wannan banzan makullin office d'ina?"
" Kiyi hak'uri ranki ya dad'e dama yana karb'a"
"What dama kinsaba bashi kenan wacce irin dak'ik'iyace ke"?
"Kiyi hak'uri ran"""''''dallah malama rufemun baki shaahasha kawai" ta fad'a tana aika mata da wani mummunan harara kamar idanunta zasu fad'o kafin a zafafe ta juya ta nufi office d'in Abdul Samad cikin k'unan rai
* MAMAN ISLAM CE
NA MIJI K'UDAN ZUMA
Page 10
A zafafe ta tura office d'in babu ko sallama sannan sam bata kula da anty Deenah ba wacce tazo kawowa mijinta abincin rana da kanta dan wani lokacin da kanta takan kawo.
"Ke SUHANA wannan wane irin haukane zaki wani shigowa mutane babu sallama kamar'yar kafurai?"
Sai lokacin ma ta kula da anty Deenah saboda tsabar idanunta sun rufe da masifa harara ta dalla mata tare da jan wani uban tsaki ta d'auke kanta ta mayar kan Abdul Samad tana jifansa da wani mugun kallo ji kake tau Deenah ta d'auke SUHANA da wani mugun marin da shi kanshi Abdul Samad saida ya mik'e tsaye tsabar firgita da k'arfin marin Deenan ta fallawa SUHANA wanda ba komai yaja hakan ba sai tsakin da taja mata wanda kuma inda sabo yaci ace dukansu sun saba da halin SUHANA wanda ta arawa kanta shekaru kusan bakwai Kennan.
Cirko cirko sukayi kamar wasu zakaru yayin da zuciyar Abdul Samad ta kama wani irin fitinannen bugu wanda har Deenah tana ganin irin yadda kirjinshi yake d'agawa sai ta d'an tsorata da hakan amma kuma sai ta dake tana fuskantar SUHANA da ta wani irin kafeta da idanunta da sukayi wani irin k'yallin hawaye "ni kika mara anty Deenah me nayi miki"?
Harara Deenah ta galla mata tace na'ma"""'"""""ya isa dan Allah kuna damuna ku fita?"
Ya fad'a cikin wani irin d'aga murya da tsawa Deenah kafeshi tayi da ido tana son gano wani abu tattare da mijin nata yayin da SUHANA itama cikin tsantsar damuwa da d'acin ran marin da 'yar uwartata tayi mata itama ta buga tebur d'in gabanshi tace "bai isa ba kuma baza'a fitaba me yasa ka amso min makullin office?"
Makullin ya d'auko ya mik'o mata tasa d'ayan hannunta ta amsa d'ayan hannunta kuma har lokacin yana dafe da kuncin ta, hanyar fita ya nuna mata, ta galla masa harara da idanunta da sukayi wani irin ja tsabar b'acin rai shi kanshi ganin yanayin idanunta saida ya bashi tsoro amma ya dake yana jifanta danashi mugun kallon.
"Wallahi babu wanda ya isa ya fitar dani daganan batare dana rama marina ba haka kawai uwatace ita da zata mareni" idanu suka zaro gaba d'ayansu suna mamakin furucin ta dan basuyi tunanin hakan daga gareta ba.
Juyowa tayi kan Deenah a fusace batareda tayi la'akari da tsohon cikin dake jikinta ba ta d'aga hannunta da iyakacin k'arfin ta ta saita fuskar Deenah wacce ganin da gaske fa SUHANA take marin ta zatayi tayi saurin runtse idanunta jikinta na wani irin masifaffen rawa.
Bansan ya akayi ba wane irin tsalle yayi ba me ya faru sai gani kawai nayi marin a sauka a saman tattausan fuskarsa ya wani irin runtse idanunsa da mugun k'arfi zuciyar sa na wani irin fitinannen gudu.
Ita kuwa Deenah da sauri ta bud'e idonta jin K'aran tabbas anyi marin amma kuma bai iso gareta ba, ganin Abdul Samad agaban ta ba k'aramin girgiza ta yayi ba kenan shine ya tare marin?
"Tunda kin rama jaki" ya fad'a da wani irin murya daya matuk'ar gigita Deenah yayin da SUHANA sam bata kula da hakan ba cikin hayaniyar da basu tab'a sanin ta dashi ba tace babu inda zani wallahi bazan fitaba naga duka kamfanin namune dan haka babu wanda ya isa yamin iyaka da inda zani a cikin sa"
Duka da kallo suka bita har Abdul Samad d'in yana mamakin yadda take hayaniya yau d'in nan yasan SUHANA bataji amma kuma yasan bata da hayaniya hasalima idan aka cika hayaniya a waje barin wajen take.
Juyawa yayi zai fita ya bar musu office d'in yaji Deenah na fad'in "SUHANA me yake damunki ne yau d'in nan" cak ya tsaya batare da ya juyoba "innalillahi wainnailahi raji'un SUHANA" jin yadda Deedah ta saki salatin da k'arfi tare da kiran sunan ta yasa ya wani irin juyowa da k'arfi gani yayi SUHANA ta nufi Deenah da wani irin fitinannen yanayi ai da gudu ya shiga tsakanin su dan hannunta ta dunk'ule ta saita cikin Deenah dashi.
Tana ganin shi a tsakanin su kawai ta fashe da kuka tana "ni wallahi bazan k'yaleta ba saina rama marina me na mata haka kawai dan sunga ba uwarmu d'aya ba sai su rik'a nunamin'yan ubanci"
Fashewa Deenah tayi da kuka tace"la'ilahaillallahu Muhammadu rasulillahi sallallahu alaihi wasalam SUHANA me zangani abinda Hajiya take fad'a innalillahi wainnailahi raji'un SUHANA wa juya miki tunanin ki haka" kafin Deenah ta ankare ta kawo mata wani wawan naushi da sauri Abdul Samad ya tare naushin ya sameshi a gefen ciki tsabar azabar k'arfin naushin saida ya rik'e wajen yace achh kansa tayi da nufin tureshi ya rik'e ta da k'arfin gaske,
Abinda ya bashi mamaki yadda ta rik'a k'ok'arin k'wacewa daga rik'on da yayi mata da k'yar ya samu ya d'aga ta ya makata akan kujeran dake gefe ya turmshe amma duk da haka k'ok'arin tureshi take Deenah kuwa in banda kuka babu abinda take"kiramin Abdul Maleek yarinyar nan inaga aljanune da ita"
"Kayi mata addu'a haka Hajiya take mata idan tayi bacci zata farka lafiya" shawaran Deenah yabi ya hau tofa mata addu'o'i tun tana k'ok'arin tureshi da mugun k'arfi har jikinta ya fara laushi daga haka kuma tayi bacci,
Wata irin ajiyar zuciya ya sauke ya dubi Deenah da har lokacin kuka take yace"kukan ya isa haka madam maza jeki kawo mota bakin nan mu wuce gida da ita kafin ta farka" idanunta ta goge ta d'auki makullin motar tayi waje ta matso da motar bakin office d'in Abdul Samad ne ya d'auko ta ya sakata a bayan motar ya gyara mata kwanciyar sannan Deenah ta shiga gaba suka bar office d'in.
"Mukaita d'akin ka dan kar suhail ya ganta a haka" k'ala baice da itaba ya nufi d'akinsa da ita ya shimfid'e ta a saman tattausan gadonsa ya juya zai fita Deenah tayi saurin rik'o hannayen sa tace "kada ka tafi ka barni da ita ni kad'ai dan Allah" duk da cewa zuciyar sa babu dad'i sai ya lumshe rinannun idanunsa ya bud'e akan matar tasa yace"ina zuwa" daga haka ya zare hannunta daga nashi yayi waje cikin motar ya koma ya d'auko takalman ta da mayafinta ya dawo.
SUHANA kuwa bata farkaba sai daf da magariba tayi mamakin ganinta a gidan Deenah amma babu wanda ta cewa komai daga Abdul Samad d'in dake ta binta da kallon da ta kasa gane ko na menene har Deenah dake binta da kallon tausayi.
Jitai jikinta yayi mata wani irin tsami yana mata ciwo sosai harara ta gallawa Deenah kafin tace"bayan kin gama cin zalina dan kinga a gaban mijinki ne shine ashe harda sumar dani kukayi keda mijin naki shine zaku wani kawoni wannan k'azamin gidan naku mai wari" ta fad'a tana cigaba da hararan ta tana d'aukar d'an kwali da mayafinta tayi waje tana mita babu wanda ya tanka mata acikin su har ta fice
MAMAN ISLAM CE
NA MIJI K'UDAN ZUMA
By
MAMAN ISLAM
☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️
Page 11
Yanayin da taje gida sai da ya d'an tsorata Hajiya sauk'in da ta d'an samu Deenah ta kirata tayi mata bayanin abinda ya faru hakanan taji ranta ya kuma dugunzuma fiye da ko yaushe akan halin data ganta yau, dan haka ta yankewa ranta zata nemarwa yarinyar ta magani ko Allah zaisa adace dan taga abin nata kullum k'ara gaba yake, wayarta ta zaro ta kira Abdul Maleek tace maza yazo yanzun tanason ganinshi.
Tana shiga d'aki tayi wanka tayi alwala bayan ta idar da sallar ne ta dawo falon nana ta tarar da Annur tace "dan Allah Annur d'an had'o min tea yunwa nakeji sosai"
"Ga abinci idan kinsha shayin sai kici"
"Dan Allah Hajiya kiyi hak'uri nace miki duk sanda nake buk'atar abu zanyi da kaina" kafin Hajiya tayi magana Abdul Maleek yayi sallama hakan ya dakatar da Hajiyan daga amsar dataso bawa SUHANA.
Bayan sun shiga d'aki Hajiya ta dubeshi "ya kukayi da malam Tijjanin?"
"Wallahi Hajiya abinne ya mugun d'aure min kai ya kuma bani mamaki kwarai"
Gaban Hajiya ne yai masifar fad'uwa tace "me yace maka Abdul Maleek kodai wani abun ne yasami SUHANAR?"
"Kusan haka domin yace jifa ne akayi mata wanda kuma sanadin hakan idan ranta ya b'aci take tada iska wanda shima had'ata akayi dashi halinta nada shine kawai wanda ta had'u dashi wajen haihuwa amma baya ga wannan duk sauran abubuwan asiri ne"
"Ya fad'a maka wanda ya aikatamin wannan abun Abdul Maleek?" Hajiya ta tambaya idanunta na cikowa da hawaye" haba mana Hajiya kada