Author : Hassana Abdulaziz Yakasai Category : A Books
sai na rama SAMAD wai ina ruwan ka dani da kake zuwa kullum ka katse min jin dad'i ne Allah sai na rama mugu kawai" tana maganar ne tare da son d'aga hannun ta wanda yai mata nauyi tsabar buguwar da tayi duk irin yadda taso d'aga hannun ta kasawa tayi sai kawai ta fashe da kuka tace "Allah ya isa kawai mugu ka katse min jin dad'i na."
Shi kansa bai san sanda wani irin zafafan hawayen da ya zubo masa ba ganin tana neman zamewa k'asa yajata ya rungumeta a jikinsa yayin da hawayen sa suke zuba saman kanta wanda dama tuni d'an siririn mayafin da ta yafa yayi nasa wajen.
Kallon sa tayi da idanunta da sukayi mugun rinewa tsabar buguwar da tayi cikin muryan nan dai ta mashayan tace "dan nace Allah ya isa shine kake kuka? to na yafe daina kukan ta samu da k'yar ta d'aga hannu tana share masa hawayen, kasa magana yayi tsabar bak'in ciki ya d'auke ta cak ya nufi motar sa da ita ya sa ta a baya sai shirme take zuba masa ya figi motar da mugun gudu
Pls manage bana gari yanzuma yakicewa nayi
MAMAN ISLAM CE
NA MIJI K'UDAN ZUMA
By
MAMAN ISLAM
☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️
Page 5
A kuntace yake tuk'in cikin wani irin takaici badan yana gudun kar Deenah tayi masa wani fassara akan k'anwar taba da babu abinda zai hana yau ya mik'awa Deenah ita a wannan tambad'en taga yarinyar da akullum suke samun matsala da ita akanta sai dai baya fatan abinda zai daga hankalin salihar matar tasa musamman a irin wannan halin da take ciki.
Ya rasa dalilin da yasaka ya kasa k'yale SUHANA taje tayi RAYUWAR ta kamar yadda take buk'ata take kuma jaddada masa ya rasa dalilin da yasa duk wani wajen lalacewar ta sai ya bita, daga yau yayi alk'awarin har abada bazai k'ara binta ba insha Allah.
Nikam nace bazaka iya ba Samad domin baka da wannan zuciyar.
Har suka kawo gidansu tana tunb'elan surutai, tace wannan tace wancen shi dai bai tankata ba tuk'in kawai yake cikin d'acin rai.
Ta k'ofar da ta fita yayi faking dan baya buk'atar mai gadi ya ganshi, k'ofar kuwa tananan a yadda SUHANA ta barta babu wanda ya rufe domin sunsan tanan zata dawo, yanzu ma kamar d'azun kasa tashi tayi daga zaunen da take dole ya tallafo ta jikinsa.
Yana bud'e k'ofar sukaci karo da Maleek ai kuwa yayi bala'in d'aure fuska dan baya buk'atar jin wani abu daga Maleek d'in, ganin yadda yai kicin kicin da rai yasa ya b'alla masa harara yace"wahalallen banza inda SUHANA ce kace zakasa abinta a ranka itace ajalinka wallahi"
Shima wata muguwar harara ya wurga masa tare fa k'ara tamke fuskar yace "ina ruwanka inta kasheni ne waikai Maleek me yasa kake hakane SUHANA fa'yar uwarmuce idan akace muna juya maka baya irin haka rayuwar ta k'ara tan'arb'arewa zatayi"
"Nidai ban maka alk'awarin shiga harkan wannan fetsararriyar yarinyar ba kai da kake ganin zaka gaka gata nan kaine ciwon zuciya zai kama a banza".
Tsaki kawai yaja batare da ya tankaba ya tura k'ofar falon cikin fargaban karsu had'u da hajiya, anyi sa'a kuwa lokacin ta shiga raka Annur d'akin shi dan haka ya lallab'a ya kaita d'akin ta.
Har ya juyo yaji ta rik'e masa riga, juyawa yayi yana kallon ta cikin buguwa tace "Kai Na'im ina koidin d'ina wallahi kasha sai munyi burauba dakai" wani irin runtse idanunsa yayi wani irin fitinannen abu na tsarga masa bai iya yace komai ba ya k'wace daga rik'on da tayi masa ya juya ya fice da sauri zuciyar sa na suya.
Yanzun ma babu kowa a falon sai Maleek hakan yasa ya fice batareda ko kallon Maleek d'in ya kumayi ba.
Allah sarki lokacin da yaje gida tuni Deenah tajima dayin bacci, dan haka shima wanka yayi ya kwanta a bayanta tare da rungmota jikinsa duk uwar yunwar dake damunshi bak'in cikin SUHANA bai barahi ya karb'i ko ruwa ba.
Washegari da safe garas ta tashi kamar ba itace ta rik'a tunb'ele jiya da dare ba duk lokacin da ta yi shaye shayen ta to sai ta makara wajen sallar asbah yau ma hakance ta kasance dan sai k'arfe goma ta farka cikin sauri ta fad'a toilet wanka tayi da alwala sannan tazo ta gabatar da salla da karatun alkur',ani mai girma, tana cikin karatun cikin zazzak'ar muryan ta taji kamar motsi a bayanta, tana juyawa sukayi ido hud'u da ya Maleek dake zaune saman lokar gadonta yana binta da wani mugun kallo.
Harara ta galla masa tare da had'e rai tana kai aya ta rufe k'ur anin ta mik'e ta fice falon gidan inda ta hango hajiya da Annur zaune saman kujera suna kallo, gaida haijyan tayi, ta amsa mata kadaran kadahan yayin da Annur ya gaidata shima babu walwala a tare dashi dan yana matuk'ar jin d'acin abinda yayar tasa take aikatawa.
"Ke dan uwarki har ni zan shiga d'akin ki dan muyi magana ki wani hahareni ki fito ki barni sa'anki ne ni?
Harara ta kuma galla masa harda murgud'a baki ta juyo tadubi hajiya tace "kiwa d'anki magana babu ruwan shi da harkana babu ni babushi idan ba haka ba wallahi saina d'auki matakin da sai ya girgiza kowa a gidananan"
Har Maleek ya hayayak'o zai maketa Hajiya ta kalleshi take ya rissinar da kanshi k'asa yana bawa hajiyan hak'uri.
Itako SUHANA dake wata azzalumar yunwa take ji kanta tsaye kicin ta shiga dan samawa kanta abinda zataci dan a cewar ta tadaina cin abincin Hajiya dan kar tayi mata asiri🤣🤣🤣(lallai SUHANA kina ruwa)
Bayan ta gama cine ta dawo falon ta zauna tana wani ciccin magani "SUHANA" Hajiya ta kirata cikin raunin murya d'ago manyan idanunta tayi ta sauke akan Hajiyan batareda ta amsaba "kin kuwa san cewa nice na tsuguna na haifeki?"
Kanta tsaye tace "ina tantamar haka Hajiya"
Da madaukakin mamaki Hajiya da Annur suka kafeta da ido kafin Hajiya ta d'ora da cewa cikin raunin murya "tunda kike a gidan nan kin tab'a ganin mahaifin ki da wata matar bayan ni har ya koma ga mahaliccinsa?"
"To Hajiya na sani ko tsinto ni kukayi yasa kike nuna baban banci tsakanina da'ya'yanki?"
"Innalillahi wainnailahi raji'un SUHANA ni kike fad'awa magana kanki tsaye?"
"Duk yaran gidannan wa kikasa aka marya jaki sama dani kullum ayi ta dukana kamar jaka kiyi ta nuna banbanci tsakanina da yaranki"
"SUHANA kema 'yatace JININA mafi soyuwa agareni"
."to in gani a k'asa ta fad'a tana mik'ewa ta shige d'akinta yayin da Hajiya da Annur suka bita da kallo kamar idanunsu zai fad'o.
Wani zumbulelen hijab ta sako akan riga da wandon dake jikinta wanda ganin damarta nema yasaka ta sanya hijabin in bata ga damaba tana iya fita a haka.
"Ina kuma zaki da safen nan SUHANA?"
Ta tsinkayo muryan Hajiya a bayanta.
Juyowa tayi ta d'an kalli Hajiyan tare da sakin murmushi kafeta nayi da ido sanda tayi murmushin ashe haka yarinyar nan take da masifar kyau idan tayi murmushi
"Hajajju na kenan zanje wajen khaleel ne ko zaki bani aron Annur ya rakani?"
Girgiza mata kai Hajiya tayi batareda ta iya magana ba tana kallon SUHANA ta fice daga gidan batare da wani damuwa tattare da itaba.
Juyawa Hajiya tayi kawai sukayi kicib'us da Maleek wanda ya gama sauraron su tas harara ta galla masa cikin b'acin rai tana k'ok'arin tureshi ta wuce ya dafe ka fad'unta da kyau cikin tsantsar tashin hankali yace "dan Allah Hajiya ta kiyi hak'uri ki yafemin"
Cikin rauni tace"Maleek kafasan duk wannan abun da SUHANA takeyi fad'a da hayaniya k'ara tunzura ta yakeyi amma ku bakwa ganewa duk cikin ku Deenah ce kawai take tausaya min akan halin da yarinyar nan take ciki"
"Kiyi hak'uri Hajiya insha Allah daga yau nima na fita harkanta indai hakan zai faranta ranki"
"Me kake nufi da hakan aikin banza kenan wato ku har kullum bakwa ganewa ko to Maleek idan ka fita a harkan SUHANA sai me Allah bazai tab'a barmin ita a hakaba dole wataran zata nutsu kamar ba itaba"
"Kiyi hak'uri dan Allah Hajiya" daga haka ya juya ya fice daga gidan gaba d'aya.
MAMAN ISLAM CE
Ina k'ara fad'a muku yawan comment yawan typing
By by
NA MIJI K'UDAN ZUMA
BY
MAMAN ISLAM
☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️
Page 6
SUHANA na fita gidan Deenah ta nufa inda ta iske Samad a haraban gidan suna buga kwallo dake lahadi ne baya fita aiki, da sauri Khalid ya saki boll d'in ya nufo SUHANA da gudu yana fad'in "yeeee ga mummy ga mummy saurin durk'usawa tayi tare da bud'e masa hannunta kamar dai yanda take masa, ya kuwayi saurin shigewa jikinta yana sakin dariya.
"My boy ina mammy?"
"Daddy ne yace mu k'yale mammy tayi bacci mu muzo tanan muyi wasa"
"Ok maza jeka salallab'a a hankali kaga ko ta tashi amma fa kada kayi motsi me k'arfi dan kakar kasaka little babynka kuka"
"To mammy"yaron ya fad'a tare da juyawa da mugun gudu Daddyn nasa na kiransa amma sai cewa yayi "bazan tasheta ba Allah kada little babyn da zaku siyo min yayi kuka"
Wani irin mugun kallo ya watsawa SUHANA batare da b'ata lokaci ba itama ta antaya masa wanda yafi nata ta fara takowa inda yake cikin d'acin rai da mugun d'aure fuska har saida yayi shakkar hakan amma ya dake yana kallon ta tare da zura hannunshi cikin aljihun wandon jikinsa idanunsa kuma akanta yana son ganin iyaka gudun ruwanta, saida tazo dab dashi ta kuma sakar masa wani mugun kallo tare da sakin wani arnen tsaki abinda ya mugun b'ata masa rai kenan ya kafeta da wani mugun kallo cikin tsantsar damuwa sai dai bai tanka mata ba har ta bud'e baki dankanta ta fara magana tana wani yatsina kamar tanayi da kashi
"Wannan shine karo na farko da k'arshe da zance ku fita a harkana Samad kaida abokin ka bana sonku bana k'aunar ku kamar yadda nima baku k'auna ta dan Allah ku barni inyi rayuwana yadda nake so tunda ai naga kabarin mu ba d'aya ba na fahimci kaike k'ara zuga abokin ka yana K'ara addabamin to ka sani wallahi ina da yan daban da zansaka suyiwa mutum kafirin duka" daga haka bata k'ara ba ta wani bangaje shi ta wuce tana wani shegen tafiyar da ka gani kuma kasan na shak'iyanci ne.
Wata irin ajiyar zuciya ya sauke yana busar da wani zazzafan numfashi ya godema Allah dayasa bata gane shike maidota gida daga mashaya ba da tujarar nata sai ya ninka haka.
Karo sukaci da Khalid ya danyi mata alamar ta kawo kunnen ta, ai kuwa k'asa k'asa tayi da kunnen ta dai dai bakin sa yace "mammy bata farka bacci take idan nataso ta bazaki fad'awa Daddy ba?"
"Zan fad'a masa mana kuma little baby zaita kuka arasa mai rarrashin sa dominfa shi yake sata bacci"
"Allah mummy?" ya fad'a yana zaro manyan idanunsa wanda suke matuk'ar kama dana SUHANA, dariya SUHANA tayi tare da sumbatar d'an k'aramin bakinsa tace "kaga wannan bakin naka ya rage magana maza muje nayi maka wanka" ai da gudu yayi d'akinsa tsab kuwa SUHANA ta wanke shi ta kimtsa shi cikin wasu fararen kaya Kal sun kuwa masifar yi masa kyau ya fita da gudu wai zaije ya nunama daddy, murmushi kawai tayi tare da girgiza kanta Allah ya sani tana matuk'ar k'aunar d'an 'yar uwartata hakanan duk cikin yayyenta tasu tafi zuwa d'aya da Deenah dan itama tana tsananin sonta, d'akin ta gyara Kal har band'aki ta wanke hakama falon sannan ta shiga d'akin Deenah ta gyara mata band'aki cikin nutsuwa dan gudun kada ta tadata ganin sha biyu tayi ta shiga kicin nanma ta gyara sannan ta hau dorama mata girki shinkafa da miya da salad a duniya Deenah tana matuk'ar son wannan abincin ko tuwon shinkafa miyar d'anyen kub'ewa, bayan ta gama takai dining ta gyara komai sannan ta koma ta kuma kimtsa kicin d'in ta fito falon tai karo da Deenah har tayi wanka harara ta galla mata ta fice batare da tayi mata sallama ba.
Murmushi Deenah ta saki tare da addu'ar shiriya ga 'yar uwartata tareda yabama tsantsar tsabta irin na SUHANA domin ko yanzu ta gama gyaran gida tayima Khalid wanka muddun SUHANA zata zo sai ta sake.
A haraban gidan ta had'u da Samad da Khalid yana ganin SUHANA yace"mummy zan biki"cikin d'aga murya tace "ba gida zani ba club zanje"
"Ke SUHANA wannan wane irin bala'i ne haka Khalid d'in kike fad'a ma clubs zaki?"
Harara ta juyo ta makawa Deenah da fad'in "to ki d'auki mataki mana idan kin isa" kafin ta bata amsa idanunta ya sauka kan Samad dake karatun jarida ko da wasa bai nuna yasan me suke tattaunawa ba, take Deenah ta gane inda SUHANA takeson tura sak'onnin ta hakan yasa bata k'ara tankawa ba gudun haifar da wata fitinar kuma.
Tana kallo ta juya ta fice cikin wani irin taku Khalid yana kukan sai ya bita ko kallonshi batayi ba.
Da k'yar Deenah taja k'afa ta k'arasa kujeran gefen Samad ta zauna tareda zuba tagumi tini idanunta suka cika da kwalla kallon ta Samad yayi shima zuciyar sa babu dad'i dan ya tsani ganin matar tasa cikin wani yanayin sai dai bai tankaba dan yanzu zata juye laifin akanshi Khalid yaja jikinsa yana rarrashin sa.
Ita kuwa tana fita kanta tsaye gida ta wuce lokacin Hajiya ta shiga sallar Azhar itama d'akin ta ta wuce tayi wanka da salla sannan ta fito falon nan ta tarar da Hajiyan da Annur har da ya Maleek "sannu da gida Hajiya" SUHANA ta fad'a tana zama kusa da ita.
"Dan Allah SUHANA ina kikaje kika bar wayoyin ki a gida?"
Yanayin da Hajiyan tayi magana ya bala'in bata tausayi tace"Allah Hajiya ina gidan Deenah ki tambaye ta kiji" wata irin ajiyar zuciya Hajiya ta sauke tare da lumshe kywawan idanunta wanda zance a gunta ne SUHANA ta koyi wannan tabi'ar murmushi SUHANA tayi tace Hajiya abinda kike tunani bazai tab'a faruwa ba tunda hakan bai tab'a faruwa daniba ko ga mazajen dana aura" a wani irin fitinannen rud'e Hajiya ta juyo ta rik'e SUHANA tana fad'in "me kike fad'a hakane SUHANA?"
Gaba d'aya jikin Hajiya wani irin rawa yake tsabar rud'ani da tashin hankalin da SUHANA ta jefata shi kanshi Maleek mutuwar zaune yayi, tabbas yasan SUHANA bata k'arya bata b'oye komai ta aikata saidai in zasu kasheta ne su kashe amma sai ta fad'i duk abinda tasan tayi ko hakan yasa suke jin haushin tabi'ar tata duk da sun san cewa SUHANA muguwar fitinanniya ce tun tana mitsitsiyar ta.
Maganar Hajiya ne ya katsewa Maleek dogon tunanin da ya fad'a hakan yasa baiji me Hajiyan taceba sai dai amsar da SUHANA tabama Hajiyar ta k'arshe ta masifar d'aga hankalin sa hakan yasa ya mik'e a mugun firgice jikinsa babu inda baya rawa ya juya zai fita a mugun fusace Hajiya tace "muddun naji ka d'aga zancen nan ban yafe maka ba Maleek domin hakan zai bawa mak'iyan SUHANA damar sake sabon shiri akanta".
Dab'ar Maleek ya zauna a tantagaryan falon yana dafe kansa saiga hawaye"kinsan abinda yake sani kuka Hajiya?"
Itama Hajiya kasa magana tayi sai girgiza mata kai da tayi, cigaba tayi da fad'in tsuntar kaina da nake a yanayin da bansan lokacin danake shigarsa ba Hajiya ki faramin addu'a ko zan daina abinda nake sannan ki fad'awa d'anki babushi babu ni da kuma surukin ki" ta fad'a tana hararan Maleek tare da mik'ewa tabar wajen saboda yunwar dake addabar ta da kallon tausayi duk suka bita cikin tsantsar damuwa da tashin hankali.
Wai to me SUHANA ta fad'awa Hajiyan da ya firgita Maleek haka?
Me Hajiyan ta fahimta game da matsalar 'yar tata?
Shin SUHANA tana sani take aikata wannan abubuwan ko kuwa dai bata sani ba?"
Shin meke tsakanin SUHANA da Abdul Samad mijin 'yar uwarta Deenah? duka wannanan amsoshin nima nake son nemo muku sai ku biyoni sannu a hankali dan samunsu
Daga alk'alamin
MAMAN ISLAM
NA MIJI K'UDAN ZUMA
By
MAMAN ISLAM
☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️
Page 7
"Hajiya dama kinsan da wannan amma kika k'yale yarinyar nan haka?"
Girgiza masa kai tayi tace "ko d'aya Abdul Maleek duk dana san cewa SUHANA muguwar fitinanniya ce amma ina mamakin yadda al'amarin ta yake k'ara tan'arb'arewa amma yanzu akan wannan maganar na fara hango wani haske"
Wani irin nannauyan numfashi Abdul Maleek ya sauke yace "Hajiya ko zamu sameta da maganar dan samo bakin zaren?"
"Baka da hankali Abdul Maleek tayaya kake tunanin zamu tari mutumin da bamu tabbatar da abinba zargine kawai kaga duk ba wannan ba abinda nake so dakai kawai ka taya 'yar uwarka da addu'a insha Allah komai zaizo da sauk'i"
Suna cikin tattaunawa SUHANA ta fito cikin shigar wasu matsatsun riga da wando ruwan kwanduwar kwai ta d'ora wata shara sharan a baya ruwan madara akan kayan ta d'an dubi Hajiyan kad'an tace" Hajiya ni zan wuce office ana nema"
"Kai SUHANA dan Allah yaushe ranonki da office Abdul Maleek nefa kawai yake duka aiyukan naki danashi shine zaki tsiro da wannan?"
"Nidai wallahi sai naje Hajiya"ta fad'a tana hararan Abdul Maleek da ya kafe ta da kallon tausayi, ajiyar zuciya Hajiya ta sauke tace "sai kin dawo SUHANA Allah ya tsare amma dan Allah karkiyi dare"
Murmushi SUHANA ta saki tare da karasawa ta sumbaci goshin Hajiyan tace "amen Hajiya Allah ya tsone idon mak'iyan da suka shiga tsakanin mu"
Itadai Hajiya bata tankaba tunda tasan dawa SUHANA take dan fitinar ta yawane da ita, Allah sarki shi wanda take dashi din ma bai nuna yasan dashi take ba domin kansa ma yana k'asa.
Da gasken office d'in taje amma batayi cikakkiyar awa gudaba tabaro can gidan Hajiyan Anwar ta nufa kamar yadda take zuwar mata jifa jifa, yaudai Hajiyan ba fitina take jiba dan haka suka gaisa da SUHANA a mutunci suka d'an taba hira kad'an tana shirin fitane Na'im ya shigo ko kallonshi batayi ba bare ta nuna tasanshi hakan kuwa yayi masa zafi amma bai kula ba saima kallon Hajiyan tasa suka wani irin inkiya da sam SUHANA bata kula ba Na'im yasaki wani shegen murmushi ya juya ya fice kamar yadda Hajiyan tayi masa alama da ido.
SUHANA kuwa bata baro gidan ba sai bayan sallar la'asar,a maikamkon tayi gida kamar yadda Hajiyanta ta rok'a kanta tsaye gidan su Sameer ta nufa tana zuwa taga d'akin sa a rufe sai ta juya da nufin komawa ido hud'u sukayi da Abdul Samad, batasan lokacin da ta dafe kanta ba aranta tace wannan wace irin masiface mutumin yake nema dani